CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

By Khaleesat Haiydar✍????

58__59
Kallon Hafsat da ta dauke kai El-ameen yayi, sannan ya juya ya fita daga dakin, Hafsat tace “Is there any need of you telling him I’ve not prayed?” Jasmine ta wara ido tace “Ohk sorry” murmushi Hafsat tayi ta ci gaba da danna laptop dinta, dab da magrib aka danna bell Jasmine ta mike Hafsat tace “Ina xa ki?” Jasmine tace “To open the door” Hafsat tace “No! Ur uncle will do that” komawa tayi ta xauna har aka kira sallah Hafsat tace taje tayi alwala. Karfe bakwai da rabi El-ameen ya shigo dakin ya ajiye basket din abincin hannunsa ya fita, Hafsat ta mike ta dauko abincin ta bude ta dibar ma Jasmine ta bata, har kusan karfe goma suna zaune dakin Jasmine tace “Baxa mu je muyi ma uncle hira ba?” Hafsat tace “Je ki samesa a parlor” mikewa tayi xata fita Hafsat tace “Tafi da plates din ki kai kitchen daga nan” dawowa tayi ta dauka sannan ta fita, yana xaune parlor yana kallon news ya bi ta da kallo har ts shiga kitchen din ta fito ta karaso cikin parlon ta xauna kasa kusa da shi tace “Uncle ka ci abinci?” Girgixa mata kai yayi tace “Why?” Yace “Ba a bani ba ai” mikewa tayi yace “Ina xa ki?” Tace “Ina xuwa” dakin Hafsat ta koma ta langwabar da kai tace “Anty Uncle yace yunwa yake ji ki kawo masa abinci” daga haka ta juya ta fita daga dakin, El-ameen yace “Me kika je yi?” Tace “Nace Anty ta kawo maka abinci?” Ya hade rai yace “Did I send you?” Girgixa masa kai tayi, sai ga Hafsat ta fito, kitchen ta shiga ta dau plate da spoon ta fito ta koma daki, El-ameen ya tabe baki ya ci gaba da kallonsa, ba a dau lkci ba Hafsat ta fito rike da plate din abinci ta shiga kitchen ta daura kan tray ta sa ruwa da cup ta fito parlon ta durkusa ta ajiye kusa da shi sannan ta mike ta bar wajen, sai da ya ji ta shi ga daki snn ya dau abincin ya fara ci, Jasmine tace “Har yanxu captain baxai xo ba?” El-ameen ya ajiye plate din hannunsa yace “I will knock fa idan kina damuna da captain ni nace kar ya xo?” Shiru tayi tana kallonsa, a hankali tace “Sorry!” Daukar abincin sa yayi ya ci gaba da ci. Yana gamawa yace “Tashi ki tafi dakinta ki kwanta, am also going to bed” mikewa tayi ta fara tafiya, yace “Baby!” Kin juyowa tayi har sai da ya kuma kiranta, ta juya a hankali ya ga hawaye idonta, buda ido yayi yace “Crying?” Ta girgixa masa kai, ya kwantar da murya yace “toh gaya min kukan da kike?” Shiru tayi yace “Am waiting fah!” A hankali tace “Captain ya….” Mikewa yayi yace “Get away!” Ta juya da sauri ta tafi dakin Hafsat, kuka ta fashe da Hafsat na kallonta tace “what happened?” Tana share hawayenta tace “He shouted at me” Hafsat tace “Ohk sorry, tafi kiyi wanka ga kaya na fito maki da” bathroom ta nufa a sanyaye Hafsat ta bi ta da kallo. Tana fitowa ta saka rigar da Hafsat ta fito mata da tayi kwanciyarta. Da asuba El-ameen yayi masu knocking kofa, Hafsat ta kalli agogo don dama tuni ta tashi, biyar da minti arba’in ne, jin ya kuma knocking ta mike ta nufi kofar ta bude, kallo daya yayi mata ya juya ya bar wajen ta koma ciki ta tada Jasmine tace “Tashi kiyi sllh.” Throughout ranan Jasmine a dakin Hafsat ta yini, Hafsat nata bata labarai, duk El-ameen na jinsu. A kwana biyun da Jasmine tayi gidan ba karamin sabo tayi da Hafsat ba, komai tare suke sai kayi tunanin sun dade da sanin juna, sosai Hafsat ke sonta ga tausayinta da take, duk abubuwan da tasan ya kamata gwada mata take, hakan yasa El-ameen ya d’an fara sake mata ganin yanda take kula da ita, ita kam ko a jikinta don sau dayawa idan yayi mata magana bata ma sanin da ita yake. Ran thursday da yamma suna kitchen su biyu suna girki shi kuma yana parlor aka danna bell, mikewa yayi ya isa gun kofar ya bude, Junaid ya gani tsaye, El-ameen ya shafa kai yana murmushi yace “Sai yau” Junaid bai ce komai ba ya shigo parlon, sai dai bai xauna ba yace “Tana ina?” El-ameen yace “Wa?” Junaid yace “Warce na kawo!” El-ameen xai yi magana sai ga ta ta fito daga kitchen, ta wara ido ganin junaid tace “Captain!” Karasowa tayi inda suke ta nufesa da fara’arta sai kuma ta ja ta tsaya ta fara dariya tana rufe baki tace “I missed you!” Ba yabo ba fallasa yace “Tafi ki dauko Hijab din ki” kallon El-ameen tayi sai kuma ta marairaice tace “Noo! I want to stay here Captain plss” ya wani hade rai yace “I will slap you ke da staying din” ta kalli El-ameen kamar xata yi kuka, El-ameen yace “Ae nan da can duk daya ne naga” Junaid yace “No ba daya bane” El-ameen yace “Why?” Yace “Coz a can tana xuwa makaranta….” Bai rufe baki ba tace “Toh ka kawo min kayan makarantar sai in dinga xuwa a nan ma” wani mugun kallo junaid ke mata kafin yace komai ta fashe da kuka sosai tace “This Aunt is kind, but the other one is otherwise I want to stay here plss captain!” Me El-ameen xai yi ban da dariya, cikin kuka tace “Uncle its not funny, I don’t like her, I prefer staying here plss” sakin baki junaid yayi yana kallonta, El-ameen na dariya yace “Gud nd fyn tafi gun kind aunt din ki” juyawa tayi da sauri ta nufi kitchen, El-ameen ya kalli Junaid ya d’aga kafada yace “Ka kawo mata kayan makarantar ta” wani kallo Junaid yyi masa ya juya ya fice daga parlon. Washegari da safe Jasmine na kitchen da Hafsat suna girka breakfast aka danna bell, Jasmine xata fita Hafsat tace “Ina za ki?” Tace “In bude kofa” Hafsat tace “Ci gaba da aikin ki” El-ameen ne ya bude kofar, wanda ke tsaye gun ya rusuna ya gaishesa sannan yace “Captain ne ya aiko ni in dauko bakuwar da ke gidan nan, driver ne ni” El-ameen ya shafa kai yace “Kaje kace masa nace bata tashi ba” da ladabi drivern yace “Toh sir” daga haka ya juya ya bar bakin kofar, El-ameen ya rufe kofar, Jasmine dake tsaye kofar kitchen ta fito da sauri tace “Who’s he uncle?” Kallonta yake daga sama xuwa kasa, sleeping gown red colour ne jikinta da ya haska farar fatar ta, ta bude ido tace “Uncle” kifta ido yayi ya karaso kusa da ita a hankali yace “Me kika ce” ta ce “Waye shi?” Murmushi yayi ya kamo hannunta ya kai bakinsa kusa da kunnenta, ta xaro ido xata koma baya taji ta jikinsa, runtse ido tayi tace “Uncle!” Ido hudu yayi da Hafsat dake kallonsu, ta juya da sauri ta koma kitchen, sake ta El-ameen yayi ya koma baya, ta turo baki tana kallonsa tace “What’s that?” shafa kansa yayi ya juya ya koma daki. ta juya ta shiga kitchen tana kallon Hafsat dake soyen dankali tace “Anty!” Hafsat ta kalleta tace “Ya aka yi” shiru tayi bata ce komai ba, Hafsat ta nuna mata ruwan lipton dake tafasa kan gas ckr tace “Ki juye a flask” kai ta gyada mata ta dau flask da cup ta nufi gun gas din, tara saura suka gama, ta dibar ma El-ameen nasa ta daura a tray tana kallon Jasmine tace “Kai masa!” Shiru Jasmine tayi sai kuma ta dauka ta fita, sau biyu tana sallama ya amsa ta tura kofar ta shiga ta karasa kusa da shi ta ajiye trayn, kallonta kawai yake ta mike tace “Ga breakfast mun yi” sauke idonsa yayi yace “toh xauna mu ci” ta wara ido tace “Ni da Anty xa mu ci” ya hade rai yace “Xauna na ce” murmushi tayi ta xauna ya mike ya dauko darduma ya shimfida ya daura tray din kai ya xauna yace “Toh dawo nan” dawowo kan darduman tayi ya hada tea a cup ya bude warmer din potatoe da kwai da plantain ya dau plate ya diba yana kallonta yace “Start!” Langwabar da kai tayi tace “Toh Anty fah?” Yace “Xata ci nata ai” daukar fork din tayi ta fara cin potatoe din sannan ta mika masa, idonsa na kanta ya karba shi ma ya ci ya kuma mika mata, girgixa kai tayi tace “I will use my hand” ya lumshe ido yace “Okay” kasa cin dankalin tayi ganin yanda yake kallonta, ya buda ido a hankali yace “Eat mana” sunkuyar da kai tayi sai kuma ta mike tace “Am coming” yace “Sit!” Kamar xata yi kuka tace “Uncle am coming” yace “Ina xa ki?” Ta sauke idonta kasa tace “ina son xan dauko hijab dina am feeling cold” murmushi yayi yace “Uhun?” Ta turo baki tace “Yes” yace “Toh tafi, kar ki dawo kuma” shiru tayi tana kallonsa, yace “Tafi” mikewa tayi xata fita yace “Xo ki dauki abincin ki” ta juya tana kallonsa can tace “Why?” Yace “Am ohk” ta bata fuska tace “Toh ai baka ci ba” ya tsuke fuska yace “Na koshi” turo baki tayi tace “Baka koshi ba joor” xaro mata ido yayi yace “Xo ki dauka na ce” karasowa tayi a sanyaye ta durkusa xata dauka tray din ya fixgota ya xaunar gefensa yana kallonta yace “What are you wearing hijab for?” Kamar xata yi kuka tace “You are looking at my body” xaro ido yayi ya fara dariya yace “How?” Shiru tayi bata ce komai ba, yace “What’s there idan na kalle ki?” Gyara xama tayi tana kallonsa tace “But you are not my muharram!” Da mamaki ya dinga kallonta, tal langwabar da Kai ita ma tana kallonsa, sauke idonsa yayi daga kallonta yace “Who told you that?” Shiru tayi sai kuma tace “Mu’allim!” Tabe baki yayi yace “Shi kuma captain muharramin ki ne kenan?” Tace “Yes, coz he’s my family, my elder brother” kallonta kawai yake can yace “Who told you that?” Tace “I know!” Yace “Then who am I to you?” Ta kallesa tace “you are captain’s frnd, nd… You are our family frnd” wani kallo yake mata kafin yace “Toh tashi ki tafi” ta mike ta nufi kofa ya bi ta da ido, tsaki yayi ya mike ya shiga bathroom. Dakin Hafsat ta shiga ta ganta xaune gaban mirror tayi tagumi ta karaso ta xauna tace “Aunty what’s wrong with you?” Kallonta Hafsat tayi tace “Nothing, ur breakfast is downstairs” Jasmine ta bata fuska tace “No kalli idon ki, are you crying?” Girgixa mata kai Hafsat tayi tace “Ba komai” a sanyaye Jasmine ta mike ta fita daga dakin ta koma dakin El-ameen, yana bathroom ta nemi waje ta xauna har ya fito bayan kusan minti ashirin daure da tawul, mikewa tayi ta karasa kusa da shi a hankali tace “Uncle may be Aunty is sick, she’s crying” hade rai yayi yace “you are not my muharrama, how dare you come into my room just like that without permission?” Ta buda ido tace “Ohh, I…..” Yace “Leave now” juyawa tayi a sanyaye ta fita daga dakin, nan corridor ta sulale ta fara kuka, ya gama shirinsa ya fito, kallo daya ya mata ya shiga dakin Hafsat ta mike ta bi bayansa, kwance ya ganta kan gado kamar me bacci, Ya tsaya daga bakin gadon yana kallonta, Jasmine ta karasa ta xauna gefenta tace “Anty na kira maki uncle xai duba ki, he’s a doctor….” Bude ido Hafsat tayi ta mike xaune ganinsa, ba yabo ba fallasa yace “What’s wrong with you?” Shiru Hafsat tayi, Jasmine ta matso kusa da ita tace “He said what’s wrong with you” Hafsat tace “Nothing” Jasmine ta hade rai tace “And you were crying mana” El-ameen ya tabe baki ya cire bargon da ta rufe da shi tana ganin haka ta fara kokarin komawa baya ya riketa ya daura hannunsa a forehead dinta, saketa yayi ya juya ya fita, Jasmine ta bi bayansa da sauri suka shiga har dakinsa, gaban mirror ya nufa ita ma haka ta tsaya daga bayansa tace “Uncle me ye ke damunta?” Banxa yayi mata ta kuma tambayar ya juyo ya fixgota yace “Am not ur muharram ko kin manta ne!” Shiru tayi ta bata fuska, kawai gani tayi ya rungumeta ta xaro ido tace “Uncle!” Bakinsa ya kai kunnenta yace “And Captain isn’t ur muharram also….” Jikinta ya dau rawa ya saketa ya fice daga dakin. Fitowa ita ma tayi ta shige wani daki ta fara kuka, har rana bata fito ba, karfe uku tayi wanka ta sa hijab dinta ta fita ta nufi gate, tafiya kawai take har ta iso main road, tsaye tayi tana kalle kallen ababen hawa dake wucewa, ko sanin yanda xata ce su tsaya bata yi ba, can dai tayi deciding ta jira motar captain, ta kusa minti sha biyar tsaye sai wasa da hijab take wani mota yayi parking gefenta ta bi motar da ido, wani ne ya fito ya kusa minti uki tsaye kafin ya karaso kusa da ita yana kallonta ya rungume hannu yace “Good afternoon!” Dauke kai tayi ta turo baki, ya karyar da kai yace “naga alamar kina jiran driver ne koh?” Kallonsa tayi tace “No motar captain nake jira in gani” ya dan wara manyan idonsa yace “Kike jira ki gani?” Tace “Eh” yace “Ohk yace maki yana xuwa ne?” Girgixa masa kai tayi, ya d’an yi shiru kafin yace “Toh ki kirasa” tace “Bana da waya” yace “Toh ga ta wa” tace “Bana da number” murmushi yayi yana kallonta yace “Ohh dat’s good, to in yi dropping din ki?” Kallonsa tayi tace “Toh” sannan ta nufi gaban motar, bin ta yayi da kallo har ta bude ta shiga, ya xaga shi ma ya shiga, sai da ya hau kan titi sannan yace “Ina ne gidan ku” buda hannu tayi tace “Nima ban sani ba” kallonta yayi da sauri yace “Baki sani ba?” Kamar xata yi kuka tace “Ehh amma kamar ta can captain ya biyo, sai yayi corner” waje ya samu yayi parking don kansa ya fara rikicewa yana kallonta yace “Ya sunan ki!” Langwabar da kai tayi ta wara ido tace “Jasmine, jewel baby!” Kallonta yake ko kiftawa bai yi, can yace “Daga ina kike yanxu?” Kamar xata yi kuka tace “Uncle ne yayi min ihu ya koreni, shine xan je gidan Captain” jinginar da kansa yayi jikin kujerar motar yace “Toh fah! Amma ba garin nan kike ba koh?” Tace “Ehh Mami na ta tafi UK in ji uncle a can muke sai muka xo nan yace min?” Xaro ido yayi yace “Toh yanxu ina xan kai ki?” Tace “Mu bi ta can kila xa mu ga gidan” tada motar yayi ya bi inda tace, tafiya kawai suke da sun yi nisa sai tace ba nan bane, duk ta daure masa kai nan ya fara tunanin anya bata da disorder kuwa, fashe masa da kuka tayi daga karshe wai ita sai ya kai ta gida, can dai ya fara tunanin anya ma ba aljana ya dauko ba, dafe kansa yayi yace “Look Jasmine ni ban san gidan ku ba wllh, ya sunan brother din naki?” Tace “Sunansa captain!” Yace “Real name dinsa fa nace?” Tace “Ehh” Bude motar yayi ya fita da nufin tambayar ko akwai wani captain a anguwar, ita ma ta fito da sauri ta fashe da wani kuka tace “ni dai ka kai ni gidanmu plss” da damuwa yace “Wait! idan na maida ki inda na dauko ki xa ki gane gidan?” Make kafada tayi tace “Ni baxan gane ba gidan captain dina xa ka kai ni” xaro ido yayi yana salati a xuciyarsa, tana share hawayen fuskarta tace “Ka ji?” Hannunta ta ji an kama ta juya da sauri lokaci daya ta warce hannun, wata mata ta gani tsaye tana kallonta baki bude, a d’an tsorace ta koma kusa da shi, matar ta saki salati tace ‘yar nan! Ashe Allah xae kuma hada mu” Jasmine ta turo baki tana komawa baya, shi kam kallon tsohuwar yayi yace “Yauwa mama kin san ta?” Washe baki tayi tace “Wllh na santa, kwarai kuwa na santa”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button