CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writers association
[3/19, 9:34 PM] El-hajj????: Captain Ahmad Junaid
By Khaleesat Haiydar????
60…../65
Kallon mama jummai kawai yake, can ya girgixa kai yace “Toh yanxu ya xan yi da ita?” Da sauri tace “Ka bani ita in tafi da ita nasan inda xan samo su” Jasmine ta saki wani kara da ya tsorata mama jummai tace “Nooo I don’t know herrr” ta fad’a tareda k’ura mishi ido tana kallonshi, tada motar kawai yayi ya fara tafiya, suka yi tafiyar kusan minti sha biyar ya isa wani babban gida yayi parking gaban gate ya juya yana kallon mama jummai yace “Idan kin samo yan uwan nata ki kawo su nan, gidan iyayena ne nan din” shiru mama jummai tayi ya d’an yi murmushi yace “Ehh” tace “A’a kaga ni dai duniya bbu gaskiya yanxu, ina iyayen naka?” Wayarsa ya dauka ya yi dialing number ya kai kunne, bayan few seconds yace “Farida ku fito ke da Ramla” daga haka ya katse wayar, ba a dau lkci ba wasu yan mata da baxa su wuce Jasmine ba suka fito, yace “Toh kin gani mama, kanne na ne wa ennan” daga haka ya bude motar ya fita ya xaga ya bude side din Jasmine ita ma ta fito tana kallon Mama Jummai k’asa k’asa, yana kallon kanninsa yace “Ku tafi da ita ciki” Farida dake ta kallonta tace toh, ta fara tafiya haka Ramla ta bi bayansu, mama jummai ta fito a sanyaye, ya fiddo dubu biyu ya mika mata yace “Kiyi kudin mota” godiya tayi ta fara tafiya tana waige waigen gidan, ya koma motar aka bude masa gate ya shiga yayi parking, da sallama ya tura kofar babban parlon gidan, durkushe ya ga jasmine jikin kujera kannin nasa na kusa da ita, xaune a kan kujera mahaifiyarsa ce sai stepmother dinsa dake parlon ita ma, Mahaifinsa ma na parlon xaune sanye da farin glass dinsa ga laptop gabansa kan centre table, karasowa yayi ya xauna daga gefen mum dinsa a kasa, mahaifiyar tasa Hajiya Mariya tace “Wacece wannan Abdul?” Sosa kai ya shiga yi a hankali yace “Hajiya bakuwa ce….” Wani kallo take masa tace “Bakuwa daga ina?” Rasa abinda xai ce mata yayi can yace “Mance gidansu tayi wai” wani kallo yan parlon suka shiga yi masa, Dad dinsa ma ya dago for the 1st tym yana kallon abinda ke faruwa, Hajiya ta daka masa tsawa tace “Waye abokin wasan ka a nan?” Yace “Hajiya ga ki ga ta ki tambayeta ni wllh bn santa ba ma, taimakon ta kawai nayi” Hajiya ta kalleta tace “Ke daga ina kike” Jasmine ta sauke idonta daga kallon da take ma Hajiyar a hankali tace “Gidan uncle?” Hajiya tace “Xa ki ina?” Ta dago manyan idonta tace “Captain!” Hajiya tace “ikon Allah, to daga wani garin kika xo?” Shiru tayi sai kuma tayi maza tace “UK” duk suka buda ido suna kallonta, stepmum dinsa Hajiya karima tace “Ina kenan a UK?” Buda musu hannu Jasmine tayi alamar bata sani ba, Hajiya ta kallesa ta juya xuwa harshen fullanci tace Maxa ya tafi da ita station right away, marairaice mata yayi yace “Ammi taimako….” Harara ta watsa masa tace “Xan saba maka wllh” Dad dake ta kallon Jasmine yace “Ke Ramla ku tafi da ita daki” mikewa suka yi gaba daya suka bar parlon, Abdul ya kalli Mum dinsa da ta hade rai sosai ya mike kansa a kasa ya bar parlon. Karfe bakwai da kusan rabi El-ameen ya shigo parlor junaid na bin bayansa, duk da ganinsu kasan ba karamin gajiya suka yi ba, ganin hanyar daki El-ameen ya nufa junaid ya fixgosa a fusace yace “Look am tired of this game ka gaya min inda yar mutane take Ahmad….” Juyawa El-ameen yayi yace “plss don’t make me loose my temper…” Daga haka ya bar sa gun tsaye, dakin Hafsat ya shiga ya ganta xaune kan pray mat ya hade rai yace “Wai ma kina me ta fita gidan nan baki sani ba” kallonsa tayi tace “Ba tare ku ke da ita a daki ba, ta ina xan san ta fita ko bata fita ba” kallonta ya tsaya yi can ya fice daga dakin, bedroom dinsa ya shiga ya xauna gefen gado ya rike kansa. Jasmine ce xaune ita kadai dakin bayan isha, tun xuwanta gidan take xaune ita kadai a dakin sai dai su shigo su yi abinda ya kawo su su fita, Farida ce ta shigo mata da abinci ta fita, kamar xata yi kuka ta jawo abincin ta bude tana kallo, cokali ta dauka ta fara ci don dama yunwa take ji, bude kofar dakin aka yi wani guy da baxai wuce 33 ba ya shigo dakin har xai fita ganin ba kowa sai kuma ya dawo yana kallonta, bata sake kallonsa ba ta ci gaba da cin abincinta, farida ce ta shigo dakin ya kalleta yace “Who’s she?” Tace “Ya Abdul brought her” yace “Abdul?” juyawa yayi ya fice daga dakin ya tafi dakin kanin nasa, Abdul dake xaune dakin yana kallo a system yace “Ka dawo bro?” yace “Yea, wace yarinyar!” Abdul ya ci gaba da kallonsa a laptop yace “Amm, i just saw her on the way… No I helped her wai ta mance gidansu,” wani kallo yake masa kafin ya juya ya fita, ya koma dakin da Jasmine take, cikin dakin ya karasa yana kallonta yace “daga ina kike?” Kallonsa tayi ta ajiye spoon din hannunta tace “Daga gidan uncle” yace “xa ki ina?” Tace “Gidan Captain!” yace “Toh me ya kawo ki nan?” Ta kalli kofar dakin tace “Wani mutum ne” yace “A ina ya gan ki?” Xata yi magana Abdul ya shigo dakin, yana kallon yayansa, Jasmine tace “Ga shi nan” Yayan nasa me suna Aliyu yace “I gat you will one day bring what will lead you to ur grave Abdul, you saw a gal like this on the road, she lied to you, you picked her up nd brought her home ryt?” mikewa Jasmine tayi kamar xata yi kuka tace “Am not lying, am not a liar…” Aliyu ya kalleta yace “I see, to wacece ke?” Tace “I am Jasmine” yace “Ur family?” Tace “They are in UK” yace “Where in UK?” Ta langwabar da kai tace “I don’t know!” Tabe baki yayi ya juya zai fita ta kalli Abdul tace “I don’t like him…” Juyowa yayi yana kallonta yayi murmushi ya fita, Abdul ya sauke ajiyar xuciya yace “Ki ci abincin ki” ta koma ta xauna shi ma ya fita. Sha daya saura Ramla da farida suka shigo dakin suka shiga shirin kwanciya, ita dai Jasmine na xaune kan carpet har lokacin, Ramla ta nuna mata gado tace “Ki kwanta in xa kiyi bacci” daga haka ta shiga bathroom neman bathromm dan tanason tayi wanka amma babu k’ofa, bude kofar aka yi Aliyu ya shigo dakin, ya karaso ya durkusa kusa da ita yana kallonta yace “Ki ka ce baki so na?” Ta kallesa tace “Yess” yace “Why?” Ta ce “I don’t know” kamar wacce tayi tunani sai kuma tace “Okayy you are mean” giranshi d’aya ya d’age yana examining fuskarta yace “Ohkk…?, have you eaten?” Gyada masa kai tayi yace “Kin yi sllh?” Ta girgixa masa kai yace “Why?” Tace “No bathroom no toilet” murmushi yayi ya nuna mata kofar bayin yace “There it is” tace “Someone went in ” yace “Ohk idan ta fito sai ki shiga” mikewa yayi yace “Good nyt,” daga haka ya fita daga dakin. Washegari da safe Jasmine na xaune bayan tayi wanka da ruwan da Ramla ta hada mata Aliyu ya shigo dakin, yana kallonta daga bakin kofar yace “Come down for breakfast” mikewa tayi ya juya ya fita ta bi bayansa, a bakin stairs yace “you make sure you greet everyone out there” tace “toh” xaune duk yan gidan suke a dinning, duk aka xuba mata ido ta kasa ci gaba da tafiya, juyawa yayi ganin ta tsaya yace “Taho” karasowa tayi har dinning din ya nuna mata kujera ta xauna, sai hararansa Hajiyarsa take da step mum dinsa, shi dai Abdul kansa na kasa, gaishesu tayi gaba daya stepmum dinsu kadai ta amsa, Aliyu yasa Ramla ta yi serving dinta yace “Eat” ba musu ta fara cin chips and Egg da soup, shi ma ya hada tea ya fara sha, ko minti goma yan gidan basu kara dining din ba duk suka mike banda Abdul, can dai shima ya mike ya fita waje, ta kalli Aliyu tace “They all don’t want me to stay with them ryt?” bai ce mata komai ba ya ci gaba da shan tea dinsa, kallonsa kawai take hakan yasa ya ajiye cup din yana kallonta shi ma yace “Ya aka yi?” yar dariya tayi tace “You are fyn, just like my captain and uncle” ya buda ido yace “Really?” Kallon wayarsa da yayi vibrate tayi daga gefensu ta dauka tace “Your phone!” Bai ce komai ba ya ci gaba da shan tean sa, ta dawo kujerar dake kusa da nashi ta mika masa wayar tace “Sa min pictures in gani” karba yayi yana kallon kwayar idonta ta sunkuyar da kanta, mika mata wayar yayi bayan ya shiga gallery yace “Take Jasmine!” Karba tayi ta koma inda take tana kallon hotunan, har lokacin idonsa na kanta, can yace “When did you come to Nigeria?” Ta kallesa snn ta ci gaba da kallon hotunan tace “Last month” yace “And baki san gidanku ba har yanxu?” Mikewa tayi da sauri tana wara manyan idonta tace “Uncle!” Gunsa ta koma har tana tuntube tace “Look kun yi hoto da uncle dina” karban wayar yayi da sauri ya ga hotonsa ne da abokinsa Dr El-ameen wanda suka yi just last week ranan daurin auren El-ameen din, ya kalleta yace “You know him?” Gyada masa kai tayi da sauri tace “Yess he’s my uncle” ajiye wayar yayi yace “Da gaske?” Tace “Yes, call him to pick me plss” kamar xata yi kuka ta kare maganar, shiru yayi yana kallonta, tace “plssss nah, am missing him” ajiyar xuciya ya sauke, ya dau wayar ya nemo number El-ameen, bugu uku El-ameen dake station da junaid ya dauka, Aliyu yasa a hands free yace “Assalamu alaikum, Where are you Ahmad?” El-ameen yace “Ya aka yi Aliyu?” Jasmine ta wara ido xata yi magana Aliyu ya daura hannu a lips dinsa alamar tayi shiru, yace “Kana dai ina yanxu?” El-ameen yace “Am very busy frnd!” Aliyu yace “me kake yi?” El-ameen yace “Bari dai xa mu yi waya anjima” Aliyu yace “Wait….” El-ameen yace “Kaga am in station yanxu, am not my self, a sister of mine is missing tun jiya” Aliyu ya lumshe ido ya bude yace “Jasmine?” Mikewa El-ameen yayi daga xaunen da yake yace “Exactly, you know anything about it?” Aliyu yace “Come over yanxu…” Kallon junaid El-ameen yayi yace “It seems he knows her whereabout” mikewa Junaid yayi fuskar nan tasa a daure ya fice daga station din, El-ameen ya sallami yan sandan ya bi bayansa da sauri, shi yayi driving din har ya isa gidansu Aliyu, parking yayi daga waje ya kira sa, Aliyu na dagawa El-ameen yace “ga mu a waje” Aliyu yace “Ka shigo mana” El-ameen ya kalli Junaid ya bude motar ya fita shi ma ya bi bayansa, har lokacin Jasmine na xaune parlo da Aliyu El-ameen ya bude kofar parlon, suka shigo tare da Junaid, mikewa Jasmine tayi da sauri ganinsu ta wara ido, da gudu ta nufesu idonta har ya fara cikowa, sai dai idonta na kan captain dake kallonta ko kiftawa bai yi, bata san lokacin da ta nufesa ba ta rungumesa tace “Captain!” Wajen seconds goma bai ce komai ba yana jin yanda ta rirriqeshi duk k’arfinta kamar za a rabasu kamin ya janyeta daga jikinsa a hankali, juyawa tayi da sauri ta kalli El-ameen tace “Uncle” xata rungumesa shi ma ya matsa daga wajen ya hade rai, shi dai Aliyu kallonsu kawai yake, murmushi ta kirkira tana kallon El-ameen a hankali tace “Uncle!” Kallo daya Junaid ya ma Aliyu ya kama hannunta ya nufi kofa, ta xaro ido tana kallonsa, bin sa da kallon mamaki suka yi su ma, Jasmine tace “Captain plss wait let me say goodbye to my new friends, they helped me….” Tuni ya fice da ita daga parlon, ta juya kamar xata yi kuka tana kallon Aliyu da ya bi ta da ido ta daga masa hannu, titi junaid ya nufa da ita don makullin motar na gun El-ameen, ya tsare me adai daita, yasa ta shiga shi ma ya shiga. Xaunawa El-ameen yayi a parlon xuciyarsa na tafarfasa, Aliyu ma ya xauna yace “Who’s that barbarian?”El-ameen ya girgixa kai yace “Rabu da shi, where did you get her?” Aliyu ya dau wayarsa ya kira Abdul cikin yan mintuna ya shigo parlon, gaida El-ameen yayi ya xauna yana kallon yayansa, Aliyu yace “Where did you say you picked the gal!” Bayanin inda ya ganta Abdul yayi, El-ameen yace “Ohh amazing, tnx very much bro you helped us gaskiya” Abdul yayi murmushi yace “But how did you get to know tana nan” Bayanin yanda aka yi taga hoton El-ameen a wayarsa Aliyu yayi masu, El-ameen ya wara ido yace “Ikon Allah, but please don’t tell Hajiya anything about cewar na santa….” Aliyu yace “Why?” El-ameen ya shafa kansa yace “Kawai ku dai kar ku ce komai” Abdul yace “tana ina?” El-ameen yace “Abokina ya tafi da ita” Abdul ya mike yace “Ohh without even a goodbye!” daga haka ya fita daga parlon. Aliyu yace “Don Allah ya ku ke da yarinyar?” El-ameen ya sauke ajiyar xuciya yace “It’s a long story….” Labarin jewel ya fara basa tun daga farko har ixuwa yanxu, Aliyu da tausayinta ya cikasa sosai, duk jikinsa yayi sanyi yace “Allah Sarki! Dat’s so sad” El-ameen ya gyada kai yace “Yea it is” Aliyu ya had’e rai yace “Toh shine zai wani dinga nuna isa a kanta don kawai shine silar tsinto ta” El-Ameen ya tabe baki baki yace “Haka nan yake”, tsaki Aliyu yayi yace “Ni ko xan nuna masa helping her doesn’t mean yafi kowa authority a kanta” El-Ameen yayi dariya yace “Toh a ina xaka kuma ganinsa”, kwafa Aliyu yace “Just watch and see what I do”.