CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writer’s Association

Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

61__62

Fitowa Junaid yayi daga napep din yana kallon Jasmine da ta tsuke baki yace “Sauko kar in baki knock” kamar xata yi kuka ta sauko ya ciro kudi ya mika ma mai adai daitan ya kama hannunta ya nufi gate, Humainah ce xaune parlor da Hadiza suna ta hira, yayi tsaye bakin kofa yana kallon hadiza, jasmine ta karasa cikin parlon ta tafi gun Humainah ta durkusa tace “Anty na dawo” ko kallonta Humainah bata yi ba, junaid yace “Tashi ki wuce daki” mikewa tayi ta nufi stairs ya bi bayanta, Hadiza ta mike tace “Tabdin, kinga tafiya ta Humainah, sai mun hadu gobe” Humainah bata ce komai ba har ta fita, can ts mike ta tafi sama ita ma, dakinsa ta shiga ta ga baya nan, ta fito ta shiga dakin da tasan Jasmine na ciki, tsaye ta ganshi a dakin, kallo daya ya mata ya maida dubansa ga Jasmine yace “Ina jin ki” kmr xata yi kuka tace “Shine sai ne sai na sa hijab na fita naje main road ina jiran motar ka, sai baka xo ba, shine sai wani mutum yace in shiga motarsa na shiga” wani kallo ya watsa mata yace “Daga yanxu na sake jin sunan Uncle a bakin ki sai na fasa bakin” juyawa yayi ya fice daga dakin, Humainah ta bi bayansa har cikin dakinsa tace “Bari ka ji, ni yarinyar nan baxa ta kuma xama min a gida ba wllh, It’s either ta bar min gida ko kuma inyi reporting dinka….” Bata rufe baki ba ya fixgota da shirin watsa mata mari sai kuma ya fasa, yana huci ya jefar da ita kan gado yace “Don uwar ki a kanki take xaune?” Mikewa xaune tayi tace “Uwata?” Sai kuma ta fashe da kuka tana kallonsa tace “Uwata ka xaga ya Ahmad” juyawa yayi ya fice daga dakin ya koma downstairs. Bayan magrib ya tafi siyo masu abinci don har lokacin Humainah na aikin kuka a daki, tana jin fitarsa ta dau hijab dinta da jaka ta fice daga gidan, Jasmine ya fara kai ma abinci da ya dawo ya sameta tana bacci ya tada ta tayi sllh ya ajiye abincin ya fita, har xai shiga dakinsa sai kuma ya tsaya, ya kusa minti biyar tsaye kafin ya shiga dakin Humainah, ganin bata ciki ya ajiye ledan hannunsa xai fita sai kuma ya nufi bathroom ya bude, juyawa yayi ya fita da sauri ya tafi gun mai gadi, mai gadin na ganinsa ya mike tsaye, yace “Yaushe ta fita?” Mai gadin yace “Bayan fitar ka, tace kati xata siyo” junaid bai ce komai ba ya nufi motarsa ya bude ya shiga ya fice daga gidan, cikin minti sha biyar ya isa gida yayi parking a waje, lokaci daya gabansa ya fara faduwa, da kyar ya ja kafa ya shiga compound din, ya kusa minti uku tsaye balconyn Mumy kafin ya tura kofar a hankali ya shiga, ido hudu suka yi da Mumy dake xaune parlon sai Aysha dake parlon ita ma, jikinsa yayi sanyi ganin Humainah xaune parlon kan carpet kusa da Mumy, Mumy bata kuma kallon inda yake ba har ya karaso parlon ya durkusa nan kasa da kyar yace “Ina yini Mumy” kallonsa tayi tace “Uhn Ahmad kenan, ita Humainahr ce ta xama abar walakantawar ka yanxu, har ka kalleta ka xagi Uwarta da ke kabari sbda ka isa koh?” Sauke idonsa yayi a hankali daga kallonta, Mumy tace “Tunda har ka iya bude baki ka xagi uwarta nima xaka iya xagina, infact nima ka xaga…” Da kyar yace “Don Allah kiyi hakuri Mumy, wllh sharrin shaidan ne I didn’t…..” Tsawa ta daka masa tace “Rufe min baki” ya sunkuyar da kansa, ta kalli Humainah da har lokacin take hawaye tace “Kema rama ki ce masa uwarsa” kallon Mumy tayi, Mumy tace “Ehh kice masa uwar sa shi ma” ta kallesa ta ga shima kallonta yake, murmushi tayi ta sunkuyar da kanta, shi ma yyi murmushin ya sauke kansa, Mumy tace “Fice min a parlor” mikewa yayi ya fita daga dakin, Aysha tace “Me ya hada ku Humainah?” Shiru tayi bata ce komai ba, can ta kalli Mumy, Mumy ta mike ta bar parlon, Aysha ta dawo kusa da ita tace “Tell kar ki ji komai kin ji sis, me ya hada ku?” Kuka ta saki a hankali tace “Aunty kin ga fa har yanxu yarinyar tana nan gidan…..” Hade kanta tayi da kujera ta kasa ci gaba, Aysha tayi shiru tana kallonta da tausayi, can ta dago tana share hawayen idonta tace “Amma Anty kar ki gaya ma Mumy” Aysha bata iya ta ce komai ba, ta mike ta fita daga parlon, tsaye ta gansa a balcony ta karasa kusa da shi tace “Ya Ahmad?” Juyawa yayi yana kallonta yace “What did she tell mum?” Girgixa kai tayi tace “Bata ce komai ba, amma ya Ahmad kai ma kasan baka kyauta mata kuma Allah….” Hannu ya daga xai wanka mata mari ta bar wajen yace “Xan baki mamaki idan baki fita sabgata ba wllh” juyawa tayi ta koma parlor, ido hudu yayi da Hajiya dake tsakar gida for the 5th time ya sauke kai, tace “Ina yini Ahmad” kallonta yayi fuska daure yace “Ina yini” tayi wani murmushi ta ci gaba da abinda take, jasmine ce ta fado masa ya shiga parlor yaga ba kowa ya nufi bedroom, xaune ya ganta ita da Aysha, Aysha na ganinsa ta mike ya bi ta da harara har ta fita, ya dawo kusa da Humainah ya xauna yace “Ohk, Alryt! Am sorry, tashi mu tafi gida” ta hade rai sosai tace “Bbu inda xan je” yace “Koh?” Juyawa tayi xata kwanta ya fixgota, ta shiga turasa ya hade ta da jikinsa, kasa kwace kanta tayi, ta fashe da kuka tace “Allah ni ka kyaleni….” Bai bari ta rufe baki ba ya hade bakinsu, sai da ya gaji don kansa ya kyaleta, xata kwanta ya dauketa ya mike, bude ido tayi da sauri tace “Meye haka?” Bai saurareta ba ya fita daga dakin, rufe fuskarta tayi da sauri a jikinsa tana cewa “Na shiga uku” Aysha dake parlor ta bi su da ido, har ya fita parlon, xaro ido Hajiya tayi tana kallonsu ta dau waya da sauri tana kiran Umma, Umma na dagawa tace “Bilki fito fito ki ga ikon Allah, fito waje yanxun nan” da gudu umma ta fito daga part dinta, ta bude baki tana kallonsu ita ma, lamo Humainah tayi a jikinsa har suka fita gate, Umma ta yi side din Hajiya da sauri tace “kinga tsiya koh? Kar dai ace wannan karan ma aikin banxa muke, wllh kila ciki ne da ita ma laulayi take” Hajiya da bata samu bakin cewa komai ba ta rafka tagumi, Umma tace “Kinyi shiru” Hajiya ta sauke wani shegen ajiyar xuciya ta mike tace “Mu je ciki balki” ba musu Umma ta bi bayanta. Junaid na gama parking a gida har bedroom ya kai ta, yana ajiye ta ya fice daga dakin ya shiga dakin da Jasmine take, kwance ya ganta ta takure waje daya, ya durkusa kusa da ita yace “Jasmine!” Bude ido tayi a hankali, tana ganinsa ta mike xaune yace “Me ya faru?” A hankali tace “My head is aching” abincin da ya ajiye mata ya jawo ya bude ya ga bata ci ba, yace “Me yasa baki ci ba?” Shiru tayi bata ce komai ba, ya bude take away din ya dau spoon ya sa mata a ciki ya mika mata ta karba, yace “Eat” ba musu ta fara cin abincin yana kallonta, da ta dago ido sai taga kallonta yake, ganin irin kallon yasa ta matso kusa da shi a hankali tace “Captain!” Ko kadan bata ga alamar yasan tana yi ba, ta kirasa yayi sau biyu kafin ta dafa hannunsa, kifta idon yayi da sauri yace “Jasmine!” Langwabar da kai tayi tace “You are looking at me” sauke idonsa yayi kasa, kamar xata yi kuka ta sauko kasa ta durkusa kusa da shi tace “Did I wrong you again?” Murmushi ne yayi escaping lips dinsa yace “No!” Mikewa tayi ta koma kan gadon ya bi ta da kallo ta xauna ta ci gaba da cin abincinta, ya tashi ya fita daga dakin ya koma nasa, sha daya da wani abu ya sake dawowa dakin, kwance ya ganta ya karasa kusa da gadon ya durkusa ya ga bacci take, ya cire bargon jikinta yana kallonta, sleeping gown ne jikinta, ya dinga kallonta, lumshe ido yayi ya daura lips dinsa a goshinta ya gangaro a hankali har xuwa kan lips dinta, bude ido tayi da sauri ya koma baya, ta mike xaune tana kallonsa, kasa motsi yayi a gun bai kuma bari sun hada ido ba can ya mike da kyar ya fice daga dakin, ya koma nasa, ya kusa minti talatin xaune kafin ya mike ya fita ya shiga dakin Humainah, kwance ya ganta cikin bargo ya karasa gadon ya xauna ya cire bargon, ta bude ido tana kallonsa, shiga yayi cikin bargon ta mike xaune xata sauka ya jawota jikinsa ya kashe wutan dakin. Washegari da safe karfe bakwai ya gama shirin fita aiki, kasa shiga dakin Jasmine yayi, Humainah ta gama shirin makaranta ita ma bayan ta hada breakfast don tun asuba da suka tashi bata koma ba, yana xaune parlor rike da cup din tea ya kalli Humainah da saukowarta kenan yace “Tafi kice mata ta shirya driver xai xo kai ta makaranta” yi tayi kamar bata ji sa ba ta ci gaba da goge takalminta, yace “Humainah!” Ta daga kai tana kallonsa, repeating kansa yayi ta hade rai tace “Takalmi na nake polish” yace “Kawo in maki ki tafi” tabe baki tayi ta ajiye takalmin ta haura sama, samunta tayi ta fito daga wanka daure da towel, tana mata wani kallo tace “Ki shirya wai” daga haka ta fita, shi ya ajiye Humainah, Jasmine kuma driver ya ajiye ta. Tun daga lokacin da Junaid ya taho da Jasmine El-ameen bai sake bi ta kansu ba duk da yana son ganin Jasmine amma yaki xuwa gidan, ba karamin takura masa Aliyu yayi a kan ya nuna masa gidan junaid ba ya dinga kakkauce masa don yasan ko kadan bai da mutunci, Jasmine kam tun bata damuwa da abinda Humainah ke mata har ta fara damuwa don da tayi mata abu sai ta fara kuka, duk ran da hadiza ke gidan kuwa bata da kwanciyar hankali don ita tsoronta ma take ko da yaushe cikin tsangwamarta suke, tana son ganin Uncle dinta ta tambayesa yaushe Maminta xata dawo amma har ranan bata gansa ya xo ba, gashi tana tsoron tambayar captain shi, shi ma captain din ba sosai take ganinsa ba don tun bayan incident din daren ranan bai barin su hadu sai tayi bacci, duk dare kafin ya kwanta sai ya shiga to make sure she’s fyn, a haka ta cika wata daya a gidan, ranan wani lahadi tana sharan parlor don yanxu kusan ita take duka aikin gidan idan captain baya nan taji an danna bell, ajiye broom din tayi ta mike da kyar don tun jiya cikinta ke mata ciwo, karasawa gun kofar tayi ta bude xaro ido tayi tace “Aunty!” Sai ta rungumeta ta saka kuka tace “plss go with me aunty” Hafsat dake kallonta ganin yanda ta rame tausayinta ya cika ta tace “Ohk I will dear” kallonta kawai El-ameen yake, tana daga kai ta gansa ta karasa da gudu ta rungumesa hawaye na sauko mata tace “Don Allah Uncle ka tafi da ni kar ka bar ni” janyeta yayi jikinsa ya gyada mata kai kawai, Hafsat ta karasa cikin parlon, El-ameen ya kama hannunta suka shiga, kasa ta xauna kusa da shi tana kallonsa tace “In dauko kayana?” Yace “Captain fah?” Bude hannu tayi tace “Ban sani ba nima” xai yi magana aka bude kofar Junaid ya shigo, ya d’an yi mamakin ganinsu ya karasa cikin parlon suka gaisa da Hafsat, ya xauna yana kallon El-ameen da ya hade rai yace “Welcome Doctor”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button