CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writer’s Association
⚓ Captain Ahmad Junaid⚓
By Khaleesat Haiydar✍????
64__65
Tashi ka je, k’asa tashi yayi Abba yace “Baxa ka bar min parlor ba?” A hankali yace “Abba kayi hakuri don Allah, sharrin….” Mikewa Abba yayi yace “you are stupid, get away” mikewa yayi da kyar ya fita daga parlon, ya nufi gate, yana bude motar Jasmine dake xaune yanda ya bar ta har lkcn idonta rufe tace “Captain!” Ba tare da ya kalleta ba bai kuma ce komai ba ya tada motar, kiransa ta kuma yi bae tanka ta ba ya ja motar, laluba sa ta shiga yi, ya kama hannunta yana driving da hannu daya yace “Open ur eyez!” Ta girgixa kai tace “It’s hurting me” bai kuma cewa komai ba har suka isa gida, kallon b’akin motar dake Parke daga gefen flowers din da ya xagaye frontage din gidan ya dinga yi, mai gadi na bude masa gate ya sauke glass yace “Waye yayi parking can?” Mai gadin ya kalli motar yace “ca yayi wani yake jira a can gidan yallabai” junaid bai kuma cewa komai ba ya sake kallon motar sannan ya ja motarsa ya shiga compound, yana gama parking ya juya yana kallonta yace “Jasmine open those eyez idan ba haka ba xan yi tafiya ta in bar ki” da sauri ta kamo hannunsa kamar xata yi kuka tace “yana min ciwo captain, don’t leave me plss, ka kira uncle kace ya kawo min Magani” wani kallo yake mata kamar tana ganinsa, can ya janye hannunsa xai sauka ta rikosa da sauri tace “No plss” hade rai yayi yace “toh ba sai na fita ba sannan xan fito da ke” a hankali ta sakesa ya fita ya xaga ya bude side din da take ya kama hannunta ta sauko ya rufe motar suka nufi cikin gidan, parlor ya xaunar da ita ya koma wani kujerar ya xauna ya dau remote yayi powering tv, a hankali tace “Captain!” Ya kalleta bai ce komai bs, kuma kiransa tayi yace “Yess!” Tace “kar ka tafi ka barni” dauke kai yayi bai tanka ta ba ya maida dubansa gun tv, can ya mike ya shiga toilet din dake parlon ya dauro alwala ya fito, nan parlon yayi don har anyi isha a mosque, yana idar wa ya koma ya xauna ya ci gaba da kallonsa, kiransa tayi ya juya ya kalleta yace “What?” A hankali tace “I want to ease my self” kallonta kawai yake har sai da ta kuma kiransa yace “Toh ki bude idonki ki je kiyi mana” girgixa masa kai tayi tace “Yana min ciwo ne” bai kuma cewa komai ba ita ma tayi shiru, har bayan kusan minti goma tausayinta ya ji ya mike da kyar ya karasa kusa da ita yace “Stand up” mikewa tayi ya kama hannunta ya nufi toilet da ita nan bakin kofar ya bar ta yace “Go in” daga haka ya juya ya dawo parlor, ba a dau lokaci ba ta fito tana kiransa yace “What?” Tana lalube ta shigo parlon ta xauna, sun fi awa daya xaune ganin yanda tayi lamo jikin kujerar kmr me bacci yace “Me xa ki ci?” Da sauri ta bude ido alamar baccin ya fara daukarta, ya mike yana kallonta ya karaso kusa da ita ya durkusa yana kallon idanuwanta da suka yi ja sosai yace “Good you open the eyez, ya daina ciwo yanxu” shiru tayi sai kuma tace “Yana min” yace “Me xa ki ci?” Bata ce komai ba ta yi kasa da kanta yace “Xa ki sha tea nd bread?” Ta kallesa tace “No! Only tea” mikewa yayi ya nufi kitchen ba a dau lokaci ba ya dawo rike da cup din tea, ya mika mata ta karba tace “Thank you!” Komawa yayi ya xauna, tana gama shan tean ya sa ta taje tayi alwala tayi sllh. Karfe goma saura ganin ta fara bacci yace “Go to bed if you are sleepy” mikewa tayi ta nufi stairs ya bi ta da kallo. Washegari da asuba ya kwankwasa mata kofa, cire bargon jikinta tayi ta xauna tana murxa ido, can ta sauka daga kan gadon ta nufi kofar ta bude, kallonta yake daga sama har kasa, yar rigar bacci ne jikinta tace “Captain” ya sauke idonsa yace “It’s time for prayer,” har ya juya xai tafi ya kuma juyowa yace “kina gama sllh ki shirya for islamiyya” ta gyada masa Kai ya juya ya bar bakin kofar, yana xaune parlor shirye cikin uniform rike da cup din coffee Jasmine ta sauko, kallon agogo yayi yaga Karfe bakwai saura minti goma yace “Tafi ki dafa indomie” tace “Toh” ta nufi kitchen, bin ta yayi da kallo yace “Come here” ta juyo ta dawo inda yake ta tsugunna tace “Na’am” yace “Baki iya gaisuwa ba” kallonsa kawai take wanda hakan ya sa shi dauke kai, a hankali tace “Good morning captain” ajiye cup din hannunsa yayi ba tare da ya kalleta ba ya mike yace “Morning” tashi tayi ita ma tana kallon white uniform din jikinsa tace “You’ve not buttoned all the buttons captain” kokarin barin wajen yake ta shiga gabansa tace “Let me help you” da sauri ya koma baya ya hade rai yace “No! I will do that my self” daga haka ya nufi stairs, ta bi sa da kallo. El-ameen ne xaune a study room dinsa earpiece makale a kunnensa yana duba wani littafi, aka turo kofar dakin hade da sallama ya daga kai ya mata kallo daya ya maida dubansa kan littafin gabansa, karasowa tayi tace “You have a visitor!” Yace “Who?” Tace “Yana parlor” rufe littafin gabansa yayi yace “Alryt!” Ta juya ta fita, ya mike ya fita xuwa bedroom dinsa, jallabiya ya daura kan kananun kayan jikinsa ya sauko parlor, Aliyu ne xaune parlon, El-ameen yace “uhn! Ashe ka san gidana Dr” Aliyu ya kallesa yace “No! da map na xo” El-ameen yayi murmushi yace “Da alama” karasowa yayi ya xauna yace “Toh ya aka yi Dr, don nasan ba haka nan ka xo ba” Aliyu yace “It’s private, let move out” El-ameen yace “Uhm toh mu nawa ne a parlon?” Mikewa Aliyu yayi ya nufi kofa El-ameen yayi murmushi ya bi bayansa. Bayan kwana uku Humainah na xaune kasa a parlor ta daura kai kan kujera duk ta rame ba kadan ba don ba karamin wahala take sha ba, Mumy ce xaune daga gefenta da sisternta Anty Nafee sai Abba dake parlon shi ma, Anty nafisat tace “Wai baxa kiyi magana ba Humainah, Meye haka kike yi” ta fashe da kuka tace “Ni ba abinda ya hadamu Mumy, ni ban masa komai ba” shiru duk suka yi suna kallonta, hawaye ne ya shiga sauko mata, Mumy ta jinginar da kanta jikin kujera a sanyaye, she’s just imagining anya Ahmad dinta ne kuwa, Ahmad din da ta yarda da tarbiyar da tayi masa, Ahmad da tayi raise da hannunta, Ahmad da ko kadan bai son bacin ranta, wai yau har kwana biyar bai sake waiwayo gidan ba, girgixa kai tayi ta lumshe ido, mikewa Humainah tayi da sauri Anty nafisat ta bi bayanta, bedroom ta kai ta bayan ta gama aman, ta kwantar da ita sannan ta xauna gefenta tace “Humainah idan ma baxa ki iya gaya ma su Mumy abinda ya hada ku da Ahmad ba ni ki gaya min, take me as ur mum kin ji” girgixa kai tayi tace “Ba abinda ya hadamu Aunty” sai kuma ta fashe da kuka, Anty nafisat tayi shiru tana kallonta cike da tausayinta. Junaid na xaune parlor da evening yana kallon wani program though absentminded, duk ya rasa dalilin da yasa ba shi da rest of mind daga jiya, haka kawai sai ya ji gabansa ya fadi, gashi yana son xuwa gida amma ya kasa, ko kadan bai son xamansa da Jasmine su biyu kadai, har aka kira magrib yana xaune parlon, can ya mike ya je yayi alwala ya wuce masallaci, yana dawowa sama ya tafi ya sameta xaune kan darduma, daga bakin kofar ya tsaya yace “Me za ki ci?” Ta d’an bude ido tace “Potatoe nd ketchup!” Tabe baki yayi ya juya ya fita ya dau makullin motarsa. Sha biyu saura na dare yana kwance idonsa biyu sai dai ya kashe wutan dakin yana son yin bacci amma ya kasa, murda kofa dakin aka yi jasmine ta shigo da sallama, ya mike xaune ya kunna bedside lamp yace “What’s it?” Karasowa take son yi yace “Tsaya nan, nd what did you want?” Tsayawa tayi tace “Cikina ke man ciwo” yace “Go nd sleep gobe xan baki Magani, stop disturbing me” a hankali tace “Ohk” ta juya ta fita, ya sauke ajiyar xuciya ya koma ya kwanta, har daya bai yi bacci ba yana son dubata amma ya ki xuwa daga karshe ya mike ya dauro alwala ya shimfida darduma. Yana xaune cikin mota idonsa a kanta ko kiftawa bai yi har ta karaso gun motar, sanye take da hijab dinta har kasa ta bude front seat ta shiga tana kallonsa tace “Na gama” bai ce komai ba ya ja motar suka bar gidan, sai da suka dau hanya sannan yace “Cikin ya daina ciwon ne?” Girgixa masa kai tayi tace “Yana yi har yanxu” bai kuma cewa komai ba har suka iso wani gida bayan tafiyar kusan minti ashirin, kallonta yayi ita ma haka, ya dauke kansa ya bude motar xai fita tace “Where is this captain?” Juyowa yayi yace “You wait for me, ba dadewa xan yi ba!” “toh” kawai tace ya fita ya kulle motar ya shiga gidan. Tsakar gida ne babba me dauke da sashi daban daban, xaune a tsakar gidan wata ‘yar dattijuwa ce da yara mata biyu da baxa su wuce sha takwas ba, tana ganinsa tace “Ikon Allah, Ahmad ne a gidan namu yau!” Tana magana ne tana kokarin bude masa wani tabarma ya xauna, D’an murmushi yayi ya xauna kan tabarmar yace “Ni ne Hajiya, ina yini?” Da fara’a tace “Lafiya lau Ahmad, ya gida ya su Amina?” Yace “duk lafiya lau” gaishesa yan matan suka yi ya amsa hade da tambayar su makaranta, Hajiya tace “Toh ina amaryar taka, ai ya kamata ka kawo min ita mu gaisa ko Ahmad” ya shafa kai yace “Xan kawo ta Hajiya” Hajiya tace “Toh muna xuba ido” yace “Baba na ciki kuwa?” Tace “Ehh bai jima da shigowa ba ma, tashi ka je” mikewa yayi ya nufi babban parlon gidan, da sallama ya shiga ya samesa xaune kan babban darduma a kishingide, dattijon na ganinsa yace “Ikon Allah, Ahmad!” Karasowa Junaid yayi kansa a kasa ya xauna hade da yi masa sallama ya gaishesa, da fara’a dattijon ya amsa masa yana tambayarsa gida da Abbansa, junaid yace “Duk suna lafiya Baba” Dattijon yace “toh ya aka yi, ko Muhammad ne ya aiko ka?” Girgixa kai yayi yace “Shawara na xo nema gun ka baba” Gyara xama dattijon yayi yace “Toh bismillah, ina jin ka Ahmad” shiru Junaid yayi na d’an lokaci kafin ya fara basa labarin Jasmine tun daga lokacin da ya ganta har xuwa yanxu, kallonsa kawai dattijon ke yi, can yayi murmushi yace “Ahmad kenan, to amma meye ka boye ma iyayenka wnn aikin ladan da kayi, ai abun su yi alfahari da kai ne wannan” girgixa kai yayi yace “A’a ba lallai su fahimce ni ba ma” shiru dattijon yayi sannan ya sauke ajiyar xuciya yace “Ikon Allah, to tana ina yarinyar?” Junaid yace “Gidana take” “tare da matar ka?” Ya tambayesa yana kallonsa, shiru yayi kafin yace “Ehh!” Dattijon yace “Amma da amincewar matar taka kuwa” shiru junaid yayi nan ma, can kuma yace “A’a” dattijon yace “Toh maido ta nan Sa’adatu ta rike ta har Allah ya bata lafiya ya bayyana danginta” kallonsa junaid yayi da sauri, can ya sunkuyar da kai, dattijon yace “Hakan yayi maka?” Gyada masa kai kawai yayi yace “Nagode Baba” ya ciro kudi aljihunsa ya ajiye masa dattijon yace “A’a je ka da abun ka Ahmad, duk lokacin da ka taso takanas don gaida ni xan karba” murmushi junaid yayi yace “Kayi hakuri baba, abubuwa ne suka yi yawa” dattijon yace “Allah kuwa” duk yanda junaid ya so tsohon ya amshi alkhairin kin karba yayi, haka yayi masa sallama ya fita bayan ya kuma jad’d’ad’a masa ya kawo Jasmine kar ya shiga hakkin matarsa, jinsa kawai junaid yayi ya fice daga parlon, yaran gidan ya bai ma kudin hannunsa yayi ma babarsu sallama ya fita, Malam tukur malamin mahaifinsa ne tun fil’azal, kusan gun sa junaid ya sauke littattafen addini da dama hakan yasa yake girmama tsohon. Bacci ya tarda Jasmine ke yi a motar bai tasheta ba ya tada motar ya bar layin bayan ya kwantar mata da kujerar. Yana xaune shi daya parlor ya jinginar da kansa jikin kujera, gaba daya hankalinsa yayi gun mumynsa a lokacin, dama akwai tym din da xai xo ya dade haka bai je inda take ba without any reason, lumshe ido yayi duk ya rasa abun da ke damunsa yanxu, gashi ko kadan shawarar da Malam Tukur ya basa bai masa ba, muryar Jasmine yaji tace “Captain!” Ya bude ido da sauri yana kallonta tace “Anty baxa ta dawo ba?” Hade rai yayi yace “leave!” Da sallama El-ameen ya shiga parlon, Mumy dake xaune da fatima suka amsa masa ya karasa cikin parlon ya gaida Mumy da fara’a bayan ya xauna, da murmushi ta amsa masa tana kallonsa, fatima ta gaishesa ya amsa hade da tambayarta sch, kallon Humainah dake kwance yayi kan yace komai ta gaishesa, ya amsa da murmushi lkci daya ya gano ba ita daya bace, ya kusa minti sha biyar parlon kafin Mumy tace “kana ji na Ahmad?” Ya kalleta yace “Ina ji Mumy” kasa cewa komai tayi da ganinta kasan there is something eating her in, gashi duk ta rame, sunkuyar da kansa yayi ko bata fadi ba yasan kan junaid ta kirasa, a hankali yace “Mumy kin yi shiru” cikin sanyin murya tace “I don’t know what has come over ur frnd….” Kallonta yayi yace “Me ya faru Mumy?” Tuni idonta ya kada ta kasa ci gaba, jikinsa yayi sanyi ya kasa cewa komai kuma, bude kofar aka yi Abba ya shigo yana ganin El-ameen yace “Good u are here” xaunawa yayi ya fiddo wayarsa yyi danne danne ya kara kunne, junaid dake durkushe a lokacin kusa da Jasmine dake juye juye wai cikinta na ciwo ya kalli screen din wayar hannunsa gabansa ya fadi ganin Abbansa ne, da kyar ya d’aga daga daya bangaren Abba yace “Ka taho ina jiran ka yanxu” daga haka ya katse, bbu tunanin da junaid bai yi ba daga karshe dai ya mike bayan ya lullube Jasmine ya fita, xuciyarsa na raya masa Humainah ta fadi abu kenan a gida, cikin yan mintuna ya isa gida, yayi part din Mumy jiki ba kwari, bai yi tunanin Abba na can ba, yana bude kofar yayi still ta dalilin ido hudu da suka yi da Abban nasa, da kyar ya karaso parlon yayi ma El-ameen kallo daya ya dauke kai gabansa na faduwa, kasa kallon inda Mumy take yyi, ga Anty Nafisa ma dake parlon sai Aysha da Humainah dake jikinta, ya xauna ya gaida Abba, yaji no answer, a sanyaye ya gaida Mumy nan ma no answer, bai kuma gaida kowa parlon ba, cikin kaushin murya Abba yace “Ahmad!” Da kyar ya dago kai ya kallesa, Abba yace “Bani takardar Humainah!” Kallonsa kawai yake kamar bai fahimce sa ba, Abba ya mike yace “Ni kake ma wannan kallon?” Sunkuyar da kai yayi, A nutse Abba yace “Bani takardarta nace” junaid ya lumshe ido ya bude yace “Abba ni bbu abinda ya hada mu……” Bai rufe baki ba Abba ya sauke masa mari yace “You are very stupid ka bani abinda na tambayeka ko sai na saba maka” shiru yayi na d’an lokaci sai kuma yace “Babu takarda hannuna” Abba ya kalli Aysha yace “Ke tafi nemo min takarda” da kyar ta mike jiki a sanyaye ta shiga daki, ba a dau lokaci ba ta dawo rike da takarda Abba ya karba ya mika masa, karba yayi ya ciro pen din dake aljihunsa duk aka xuba masa ido a parlon barin Mumy da ko kiftawa bata yi, Humainah kam jikin kujera ta rufe fuskarta hawaye na sakko mata, cikin ‘yan mintuna ya gama rubutunsa a jikin takardan ya mika ma Abba ba tare da ya bari sun hada ido ba, wani kallo El-ameen ke ma junaid yana son assuring kansa ba saki ya rubuta ba, Abba ya kusa minti uku idonsa na kan takardan kafin yayi wani murmushi ya mika ma Mumy da tuni hawaye ya cika idonta, ajiye takardar tayi don baxata iya gani ba, Anty Nafisat ta dauka da sauri cikin few seconds ta gama karanta takardan, mikewa tayi lokaci daya idonta ya canxa launi tace “Ehh lallai ka xama dan iska Ahmad, sakin ka rubuta da gaske?? Ashe kai mara imani ne?” Hannu Abba ya daga mata sannan ya kalli Junaid yace “Tashi ka tafi” mikewa yayi kansa a kasa ya nufi kofa, Mumy ta fashe da kuka haka ma Aysha, Humainah kam kin dago kanta tayi, El-ameen ya mike da sauri ya bi bayansa, karo junaid ya kusa ci da Umma da Hajiya dake labe balcony, bai ko bi ta kansu ba ya sauka, taku daya biyu yayi still yana kallon Hadiza dake tsaye balcony din Hajiya lokaci daya ya ganeta, tana ganinsa tayi saurin shigewa parlor ta rufe kofa, ji yayi kansa na juya masa, kan kace me har ya fice daga compound din ya isa gun motarsa, fixgosa El-ameen dake biye da shi yayi yace “Sakin ta kayi Ahmad?” Wani kallo Junaid yayi masa yace “Ehh” murmushin takaici El-ameen yayi yace “Good!” Junaid ya shige motarsa ya tada ya bar layin.