CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writer’s Association
[3/19, 9:34 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

66__67 to 70

Ko parking din arxiki bai yi ba ya shige cikin gida ya nufi dakinsa direct ya kwanta xuciyarsa na bugawa, har aka kira magrib yana kwance can ya mike yayi alwala ya fita xuwa Masallaci, sai da ya dawo ya shiga dakin Jasmine yaga bacci take, tashinta yayi ta bude ido a hankali, kallonta ya tsaya yi, ta mike xaune tace “Captain” kifta idonsa yayi yace “Cikin ya daina?” Ta gyada masa kai yace “Me xa ki ci?” Cikin sanyin murya tace “am not hungry” mikewa yayi yace “toh kiyi sallah” daga nan ya fita daga dakin. Har kusan daya na dare junaid bai yi bacci ba yana dai kwance, mikewa xaune yayi jin kamar an bude kofar parlor ya kalli agogo, jasmine? Toh ina za ta? ya mike tsaye ya nufi kofa da sauri ya fita, dai dai lokacin da haske ya gauraye downstairs, still yayi a gun, can kuma ya bude kofar dakinta, ga mamakinsa sai ya ganta kwance, kansa ya daure ba kadan ba don ya kulle kofar ai, karasawa dakin yayi da hanxari gun gadon ya cire bargon jikinta ta bude ido a tsorace, dagota yayi tace “Captain” bai saurareta ba ya fice ya koma dakinsa yana rike da hannunta ya rufe kofar da key, tace “What’s that captain?” Wani kallo ya mata ba shiri tayi tsit, ya bude closet dinsa ya binciko pistol dinsa har biyu, xaro ido tayi a tsorace tana komawa baya tace “Captain!” Ya kalli kofa jin ana haurowa sama, da sauri ta dawo bayansa ita ma tana kallon kofar a mugun tsorace, hannunta ya rike gam har lokacin idonsa na kan kofar, xaro ido yayi ya ganin key din hannunsa ya nufi kofar da sauri da nufin sakalawaa yaji an riga sa slotting key, baya ya koma yana kallon kofar yana kiran Allah a xuciyarsa har aka bude, su uku ne ko wannensu sanye da bakar facemask, yayi ma biyu pointing din duka bindigan hannunsa, rungumesa Jasmine tayi ta baya ta runtse ido ta fasa ihu jikinta na rawa tace “Captain! Who are theyyy” Baya ya dinga komawa tana jikinsa, daya daga cikinsu ya karaso yayi pointing ma Jasmine bindigar hannun sa yace “Her life or you drop ur weapon” sauran ma duk suka karaso suka yi yanda yayi, ba karamin tashi hankalin Junaid yayi ba, lumshe ido yayi a hankali ya sake pistols din hannunsa ya rungumeta gam, cikin dakiyar murya yace “What did you want from me?” Dariya duk suka yi daya daga cikinsu yace “Money, cars, houses, infact everything” yana rungume da ita ya nufi inda atm dinsa yake ya dauka ya jefa masu ya fadi pin, ya kuma dauka makullin motocinsa har biyu ya jefa masu, da na gidansa daya, cikin dakiyar murya yace “What again?” Wani dariya duk suka yi, daya daga cikinsu ya tako har gabansa yana kallonsa, sake kankame Jasmine yayi a karo na farko xuciyarsa ya soma bugawa, ita ko ko ina na jikinta rawa yake sai kiransa take tana kuka, hannu mutumin yasa a aljihu ya ciro wani abu fari a leda ya jefar fuskar Junaid, daya daga cikinsu ya fixge Jasmine, daga nan suka fice daga dakin gaba daya taku daya biyu junaid yayi da niyar binsu ya xube nan gun, duk kokarin da yayi na son mikewa hakan bai yiwu ba, wani juyi yaji kansa yana yi, da kyar ya iya mika hannunsa ya jawo wayarsa dake gefen gado, number El-ameen yake son nemowa amma ya kasa, cikin ikon Allah ya fiddo lambar, ji yayi kamar numfashinsa na neman daukewa, wayar ya xame daga hannunsa shi ma ya kuma faduwa nan kasa, a hankali idonsa ya fara rufewa daga haka bai kuma sanin abinda ke faruwa ba, El-ameen dake xaune da laptop gabansa ya kalli agogo jin ringing din wayarsa, mikewa yayi ya dauko wayar daga charging da yake, tsayawa kallon screen din wayar yayi ganin number junaid, da kamar baxai dauka ba sai kuma ya tabe baki ya daga, shiru yayi bai ce komai, jin shirun yayi yawa yace “Ya aka yi, mistake i guess, ryt?” Jin ba ace komai ba ya kalli screen din yaga ba a katse ba, mayarwa yayi kunnensa yace “Hellow?” Tabe baki yayi ya katse wayar, har xai ajiye sai kuma ya kuma kiransa, har ya gama ring ba a dauka ba, ajiye wayar yayi ya koma ya xauna sai dai haka kawai hankalinsa yaki kwanciya. Kuka kawai Jasmine take tana kiran Captain har suka sa ta bayan motar, babu wanda ya ce mata komai har suka iso wani gida bayan tafiyar kusan minti talatin drivern yayi horn a bakin wani babban gate, ba a dau lokaci ba aka bude gate din, a parking space suka yi park din motar drivern motar ya fito kafin sauran su fito, nan take suka cire mask din fuskarsu daya daga cikinsu na kallon Jasmine yace “Fito!” Ta fashe da wani sabon kuka tace “Nooo!” Hade rai suka yi gaba daya mai tukin motar ya fito da bindigar aljihunsa yace “C’mon fito malama” ihu ta fasa a tsorace, ya fixgota yana nuna mata bindigan ba shiri tayi tsit ko ina na jikinta na rawa, yana kallon sauran dake tsaye yace “Sai mun hadu gobe you can go with the car” daga haka ya tasa ta gaba xuwa balcony, suna shiga parlon ta durkushe kasa tana bin ko ina na parlon da kallo, kamar me counting stairs din ya dinga saukowa yana kallonta, hade rai yayi yace “Amma na ce you guyz shouldn’t scare her fa Salim” Wanda ya kira da Salim ya xauna saman kujera yace “We didn’t” mikewa Jasmine tayi da sauri tana kallon stairs din jin muryarsa, ya sakar mata murmushi ya buda manyan idonsa yace “Jewel!” Da gudu ta karasa kusa da inda yake sai kuma ta ja ta tsaya ta fashe da kuka tana kallonsa, Yace “Amma ba mu yi haka da ku ba salim” mikewa salim din yayi yace “What did you expect idan bata yi kuka ba toh? Were you expecting her to be laughing bayan mun dauketa daga gida?” Daga haka ya shiga daki dake parlon, Aliyu ya d’an bude ido yace “Sorry jewel, they didn’t mean to hurt you” hade rai tayi tace “Why am I here?” Bai ce komai ba ya karasa cikin parlon ya xauna. Washegari da safe El-ameen ya gama shirin fita office Hafsat ta shigo dakin tace “Breakfast fah?” Kallonta yayi yace “Sai na fita office” tace “Ohk” ta juya ta fita, mikewa yayi ya dau wayarsa har xai sa a aljihu junaid ya fado masa ya shiga kiransa, har ya gama katse wa ba a dauka ba, tsaki yayi ya dau brief case dinsa xai fita wayar ya fara ring ya duba yaga Aliyu ne, dagawa yayi, daga daya bangaren Aliyu yace “Good morning” El-ameen yace “Morning Dr, ya gida” Aliyu yace “Alhmdllh, ga ni ga Jewel!” El-ameen ya xaro ido yace “Jewel kuma?” Kallon Jasmine dake xaune ta takure waje daya Aliyu yayi ya mika mata wayar yace “Ur uncle” kin karba tayi ta fashe da kuka a hankali tace “Ka kai ni wajen captain plss” Katse wayar El-ameen yayi ya fice ya dau motarsa a parking space ya bar compound din, cikin ‘yan mintuna ya isa gidan Junaid, bedroom ya nufa direct, ya kusa second goma tsaye bakin kofa yana kallon hodar dake xube a kasa ko ba a gaya masa ba yasan ta meye, ya ciro handkerchief ya rufe hancinsa ya karasa cikin dakin ya durkusa kusa da shi yana kallonsa, mikewa yayi ya fice daga dakin ya fiddo wayarsa ya shiga kiran Aliyu, bugu biyu ya daga, a fusace yace “Was that the deal, don me xa kasa ayi masa haka….” Dariya Aliyu yayi yace “Girman kansa nake son sauke masa, kuma da ca suka yi ya basu ita cikin lamana ba yarda xai yi ba” daga haka ya katse wayar, dafe kai El-ameen yayi can ya juya ya koma dakin. Abban El-ameen ne tsaye kan Junaid yana kallonsa, awan sa kusan hudu kenan hospital din still unconscious, El-ameen ma na jingine daga jikin bango tun safe bai bar dakin ba yana tare da shi, dad din nasa ya kallesa yace “Wai an sani ma kuwa a can gidansu?” El-ameen ya girgixa kai, Dad yace “Why? You mean baka kira su ba har yanxu” yace “Xan kira yanxu Dad, bana son daga masu hankali ne” Dad din yace “No call them right away! Kuma ka sake masa alluran” daga haka ya juya ya fita, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya ya ja kujera ya xauna ya dau wayarsa ya shiga kiran Abban Junaid, bugu uku ya daga, ya gaishesa da ladabi yace “Abba dama Ahmad ne ke asibiti tun safe…..” Bai kai karshe ba Abba ya katse sa ta hanyar cewa “Allah ya sauke, ka kira uwarsa” daga haka ya katse wayar, El-ameen ya tsura ma wayar ido, lumshe ido yayi yana addu’ar Allah yasa ya farfado kafin yamma. K’in sakin jiki Jasmine tayi duk kuwa da Kanwar Aliyun dake gidan, hatta abinci taki ci, banda kuka babu abinda take ita ya kai ta gidan Captain, bayan la’asar gari yayi sanyi Aliyu yace “Toh tashi in kai ki” mikewa tayi tana share fuskarta ya fara tafiya ta bi bayansa, Ramla da duk xaman gidan ya isheta ta bi su da kallo, wata kofa ya bude ya fita tana biye da shi a baya, babban garden ne sosai ga carpet grasses Kore shar shimfide a ko ina na garden din, sannan ga babban swimming pool xagaye daga gefe, tsuntsaye ke ta shawagin su a wajen gwanin sha’awa, kare idonta ta shiga yi tace “Ohhsh, My head is aching, I can’t follow here” ya kalleta yace “This is the only road” tana kare fuskarta ta shiga takowa a hankali, xaunawa yayi ya nuna mata gefensa yace “Sit” ta ki xama tace “Noo mu wuce plss, I don’t like here, it’s making me dizzy” hade rai yayi yace “Sai in kira dog yanxu idan baki xauna ba” da sauri ta xauna tana rurrufe idonta, a hankali yace “Open ur eyez!” Girgixa kai tayi kmr xata yi kuka tace “It’s aching me” yace “Ki bude a hankali” a hankali ta shiga bude idon ta shiga bin ko ina na garden din da kallo, yace “What did you see?” Shiru tayi sai kuma murya can kasa tace “Green grasses!” Yace “No! Look deep, I mean don’t blink your eyez nd tell me what you see” shiru tayi bata ce komai ba idonta na kan koren ciyayin ko kiftawa bata yi, a hankali ya mike ya juya ya bar gun ya koma cikin gida. Sai kusan Magrib ya koma garden din ya ganta kwance tana bacci, durkusawa yayi kusa da ita a hankali yace “Jasmeen” firgit ta farka tace “Ummana” sai kuma ta mike tsaye da sauri, rike kanta tayi tace “Wayyo Kai na” mikewa yayi ya komawa baya yana kallonta ganin faduwa xata yi, kasa tabata yayi har ta kai kasa, sannan ya durkusa har lokacin idonsa a kanta, ta kusa minti biyar bata dago ba, can ta dago a hankali idonta ya kada sosai ba kadan ba, da kyar tace “Ka kai ni wajen captain pls, I want to go to him” yace “Toh bari in baki Magani sai in kai ki” mikewa yayi ita ma ta mike da kyar, kasa tafiya tayi ganin faduwa xata yi ya juya da sauri ya koma cikin gidan ya kira Ramla ta fito ta kamata suka shiga cikin gidan, tea me kauri ya hada mata ya tilasta ta ta sha, sannan ya bata Magunguna tana sha bacci ya dauketa, Ramla ce ta rufa mata bargo ya mike yana kallonta yace “You stay with her kar ki bar ta ita kadai” kai ta gyada masa ya juya ya fita daga dakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button