CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writer’s Association
⚓ Captain Ahmad Junaid⚓
By Khaleesat Haiydar✍????
68__69
Har washe gari Junaid na kwance unconscious, duk wani taimako Dad d’in El-Ameen saida ya tabbatar sun bashi amma ko kadan baya responding to treatment, El-Ameen gaba daya hankalinshi ya tashi duk tausayinshi ya cikashi, Har lokacin babu wanda ya lek’o daga gidansu Junaid, a bangaren Jasmine kuwa kuka ta dinga yi ita a kaita gidan captain, shareta Aliyu yayi da farka can kuma yace “Toh tashi” mik’ewa tayi ta nufi gun slippers d’inta xata sa, kamar wacce ta tuna wani abin ta juyo tana kallonshi tace “Are you sure you are taking me to captain?” murmushi yayi ba tare da ya kalleta ba ya kad’a kai yace “Yes Jewel, amma zaki dena wannan kukan and clean your face” Kamin ya gama magana ta shiga share hawayen dake fuskanta tace “Av cleaned it” yace “Good”, daga haka yayi gaba ta biyoshi a baya, hanyan da yabi jiya shi taga yabi yauma, yana bud’e k’aramin k’ofar garden d’in ta had’e rai taja ta tsaya daga wajen, juyowa yayi ya yaga ta had’e rai, murmushi yayi ya dawo gabanta yana kallon kyakkyar fuskarta da manyan idanunta da hawaye ya cika zubowansu any moment yace “Don’t you want to see Captain?”, kamar bataji mey yace mata ba tayi shiru tana kallon k’ofan, ganin baza tace komai ba yasa yace “He said we should wait for him there”, ya fad’a yana nuna mata garden d’in da yatsanshi, yaci gaba “Captain is waiting for you in there”, kamin ya rufe baki ta maza ta k’araso ta sa kai cikin garden d’in, murmurshi kawai yayi tareda shafa fuskarshi ya biyota a baya, waige waige ta dingayi ko zata ga Captain amma bata ganshi ba, ta juyo da idonta da suka kuma cikowa zatayi k’ofan taga ya shigo, hawayen na k’arasa gangarowa tace “You said he is waiting for me in here”, ya girgiza kai yace “Erhm No, he said we should wait for him here, he is coming to pick you ltr” jiki a sanyaye batace komai ba ta koma kan bench d’in ta zauna tareda kifa kanta kan cinyoyinta, daga gefenta ya samu waje ya zauna, yace “Jewel!” Kin dagowa tayi, kamar bai son magana yace “Tell me what you see in here” dago kanta tayi ya nuna mata carpet grass dake shimfide yace “Me kika ga” shiru tayi bata ce komai ba tana bin ko ina na garden din da kallo, mikewa yayi ba tare da ya bari ta lura ba ya bar gun. Da rana El-Ameen na zaune d’akin Junaid yayi xurfi a tunanin da yake, kamar daga sama yajiyo muryan Junaid na ce mishi “Where is she? Where is Jasmine?”, Da hanzari ya mike ya iso gaban gadon yana kallonsa, dukawa yayi murmushi yayi escaping lips dinsa yace “Ahmad how you feeling now?” Dauke kai Junaid yyi ya shiga k’ok’arin mik’ewa yaji kanshi na wani mugun sara mishi komawa yyi ya kwanta ya lumshe ido hade da dafe kai yace “Where is she?, I need to get to her, she is in trouble” da kyar yayi maganan yana kokarin sake tasowa, wani sarawa da kanshi yayi yasa yayi maza ya koma ya kwanta, El-ameen ya rik’o shi yace “Ahmad stop proving stubborn, you are still weak”, Junaid yace “No! Help me get up pls, she’s in trouble frnd!” rasa me zai ce masa El-ameen yayi, duk yaji tausayinshi ba kad’an ba, bai kuma ce masa komai ba ya koma ya xauna don yasan ba lallai ya iya mikewa ba, Allura kawai ya had’a daga karshe ganin Junaid ba shiru xai yi ba yayi mishi, a hankali ya dinga lumshe ido har bacci ya d’aukeshi, Yana fara bacci El-ameen ya k’ira wasu nurses d’in yace su kula da shi yanzu zaije ya dawo, ya jadadda musu da he should be under well supervision yanxun nan zaije ya dawo, a risine suka amsa mishi daga haka ya d’auki key yayi waje, kai tsaye gidansu Junaid ya nufa, daga bakin gate ya tsaya ya shiga k’iran Khadeejah a waya, tana d’auka yace “Ina bakin gate Khadeejah, ki fito yanzu”, bata fi 5mins ba ta fito tunanin Yayanta duk ya cikata, da kanshi yasa hannu ya bud’e mata k’ofa tana shiga yaja motar, jikinta duk a sanyaye tace “Yaa El ina wuni”, amsa mata yayi ba tare da ya kalleta ba tace “Ya jikin Yaa Aj?” ta k’arasa maganan kaman zatayi kuka, saida ya kalleta kamin ya maida kallonshi kan driving din da yakeyi yace “Wajenshi zamu yanzu”, bata sake cewa komai, yace “me ya hana ku xuwa?” Hawaye ne ya gangaro mata tace “Abba!” yace “Mumy fa?” Tace “Tana gida” bai kuma cewa komai ba har suka isa asibitin ta biyoshi a baya bayan sun fito motan, shi ya fara shiga d’akin, zaune ya tadda nurses din kan sofa dake d’akin, suna ganinshi suka mik’e ya tambayesu ko sunga wani movement bayan fitanshi suka ce a’a, daga haka ya sallamesu sukayi Waje, Khadeejah da har ta k’arasa gaban gadon idonta cike da hawaye ta durkusa tana kallon yayan nata, kuka ta shiga yi, El-ameen yace “Ba abinda na kira ki kiyi ba kenan” da kyar ta tsaida kukan nata tana share hawayen fuskarta tace “Yaa El wai su waye suka mishi haka, kuma ba a sansu ba?” El-ameen yayi mata assuring murmushi yace “Kiyi mishi addu’a kawai, he will be fine”, ta kad’a mishi kai, karasowa yayi ya shiga Examining Junaid yana gamawa ya fita. Wajen hud’u da wani abu Khadeejah na zaune Junaid ya farka, da saurinta ta isa wajenshi ta zauna kan kujera kamar zatayi kuka tace “Yaa Aj ya jikinka?”, bai bata amsa ba ya shiga kokarin mikewa xaune yace “Mumy fah?” A hankali tace “tana gida” komawa yyi ya kwanta yace “Humainah?” kai ta kad’a tace “um tana gida”, daga haka babu wanda ya sake magana cikinsu, kiran da Hajiya tayi mata yasa ta koma gida ba don ta so ba. Da daddare Junaid na kan gado idanunshi lumshe sai dai ba bacci yake ba shi daya yasan abinda yake ji a lokacin, bude kofar dakin aka yi duk da yana son bude ido amma ya kasa, Humainah ce ta shigo dakin, ta kusa minti biyu tsaye bakin kofar kafin ta karaso a sanyaye ta isa gabanshi ta durk’usa, lkci daya hawaye ya cika Idonta, da kyar ya bude idanunshi ya sauk’e kanta jin motsin mutum kusa dashi, sunkuyar da kanta tayi hawayen da ke makale idonta ya gangaro, ya lumshe ido a hankali ya kamo hannunta ya rik’e cikin nashi dan bazai iya kallonta ba, kuka ta fashe da sosai, cikin sanyin murya yace “Am.. Am sorry, for everything” bata iya ta ce masa komai ba sai kukan da take yana son lallashinta amma ya kasa, bude kofa aka yi El-ameen ya shigo, jim yayi ganinta, can ya karaso ciki tun kan yace komai ta mike ta fice daga dakin da sauri. Washegari da safe junaid na bacci El-ameen ya fita, gidan Aliyu ya nufa yana gama parking a waje ya shiga gidan, bin compound din yayi da kallo ganin bai ga motar Aliyu ba, ya bude kofar parlor ya tsaya yana bin ko ina da kallo, Jasmine ce ta leko daga kitchen tana ganinshi ta fito a guje tayi inda yake ta wara ido tace “Uncle!” Gira ya daga mata yace “Uhmm” bata fuska tayi tace “plsss take me away from here, take me to Captain, kallon stairs yayi yace ” Dauko hijab din ki” da sauri ta tafi dauko hijab din, ya fita ta bi bayansa. Asibiti ya koma da ita dan ya gaji da tambayarta da junaid ke jefo masa a ko da yaushe, tana biye da shi a baya suka shiga ward din, idon junaid biyu a lokacin don Dad din El-ameen bai dade da fita ba, ido ya kafe su da har suka karasa shigowa dakin, El-ameen i xamansa kan kujera yana kallonsa, gadon ta nufa tana kallon ruwan hannunsa ta durkusa kusa da shi kamar xata yi kuka tace “Whats wrong with you captain, are you sick?” Kallonta kawai yake kamar bai gane me take nufi ba, ganin bai ce komai ba yasa tace “Aren’t you happy am back Captain….? Talk to me plss” hawaye ne ya taru idonta ganin yaki cewa komai still, ta juya tana kallon El-ameen, tabe baki yayi ya mike ya fice daga dakin. kamar jira Junaid yake ya fita yana fita ya fixge drip d’in dake hannunshi ya mik’e tsaye da k’yar, ji yayi jiri na neman k’ada shi hakan yasa ya dafa kanshi ya jingina da bangon, tana ganin haka ta mik’e da sauri tazo gabanshi tana kokarin rik’eshi tace “Captain you didn’t tell, are you sick?”, makullin motar da El-ameen ya ajiye kan table ya d’auka yace “Let’s go” xaro ido tayi tace “You are sick Captain, you can’t even stand right lemme call Uncle for you”, ganin zata b’ata mishi lokaci ya samu da k’yar yayi regaining balance d’inshi ya jefa mata wani kallo ya kamo hannunta suka fice daga d’akin, haka ya dinga tafiya da k’yar har suka iso gun mota, Jasmine sai ce mishi takeyi “Captain ina xa mu tafi” bai tanka mata ba, ganin yanda yake tafiya tace “Kafar ka ne ke ciwo” motar yasa ta shiga, ya shiga shima ya tada suka bar asibitin, El-ameen da ya fito da sauri dan ya koma d’aki bai gansu ba a kan idonshi motar tabar premises din asibitin, driving kawai Junaid yake ba tare da yasan me yakeyi ba, Roughly yake driving d’in kamar wani mai tseran formular, he just want to take her away, Jasmine na ganin irin driving d’in da yakeyi lokaci d’aya ta rikice ta shiga k’iran sunansa, sosai take ihu da ya rikita Junaid d’in shima lokaci d’aya yayi loosing control d’inshi motar ta kufce daga hannunshi, har lokacin babu abinda jasmeen take banda ihu, rintse ido kawai Junaid yayi dan shima yana jiran hukuncin Allah a kansu, da k’arfi yaji sunyi hitting wani abu da yasa kanshi yin baya, yakai 5mins zaune idonshi rintse, a hankali ya samu ya bud’e idonshi ya sauk’e kan Jasmine, kallonshi kawai takeyi da wasu irin expressions shimfid’e fuskarta, ganin irin kallon da take mishi yasa ya kawo hannu zai tab’ata to check if she is fine, gani yayi tayi Luuu zata fad’a baya yayi maza ya rikota, wani irin skipping heart d’inshi yayi ganin yanda ta sakar masa jiki bata motsi, Sosai ya rud’e ganin suma tayi, bai damu da mutanen da suka tarar mai jikin mota ba don ba ma jin abinda suke cewa yake ba, da k’yar ya samu ya kwantar da ita daga gefe ya shiga k’ok’arin tada motar, Luckily ya samu yayi igniting motar tareda yin reverse, ikon Allah kawai ya maidasu asibitin, ko gama parking baiyi ba ya fito daga cikin motar, jingina yayi jikin motar jin yana neman faduwa, El-ameen dake tsaye har lokacin inda yake cos he was still surprise, ya karaso gun motar yana kallonsa yana son gano abinda yasa ya dawo. Kin ce masa komai Junaid yayi, can ya nufi cikin asibitin ya bar sa nan tsaye, bude motar El-ameen yayi ya ja baya da mamaki ganinta a kwance, bin junaid yayi da kallo kafin ya matso kusa da ita ya kai hannu kan fuskarta breathing d’inta yaji na hitching sama sama, reception ya nufa da sauri sai ga shi da nurses da stretcher, bedroom dinsa na office ya kwantar da ita ya fiddo oxygen bag cikin wani wardrobe daidai bakinta ya jona tube snn ya koma ya kunna socket d’in da Oxygen d’in ke jone, kan sofa El-ameen ya koma ya zauna ya da rik’e kanshi da duka hannayenshi biyu yana jin yanda kan ke sara mishi sbd stress amma bashida strength d’in koda nemawa kanshi magani, mikewa yayi a fusace ya fita nemo junaid, tsaye ya gansa daga waje ya karasa kusa da shi ya fixgosa yace “What happened to her?” Kallonsa kawai Junaid yake da wani expression a fuskarsa don a tunaninsa abu ne ya sameta, turasa yayi ya shiga office din da sauri ya nufi bedroom direct, lumshe ido yayi xuciyarsa na bugawa ya durkusa kusa da ita cikin sanyin murya yace “Am sorry jasmine, am sorry” ya kusa minti uku kafin ya bude ido ya zuba mata yana kallon yadda breathing d’inta ke dawowa dai dai a hankali, duk sai ya nemi ciwon kai da dizziness din da yake ji ya rasa, Shigowa El-ameen yayi dakin yace “Yea ka kasheta kawai kowa ma ya huta Ahmad, just kill her” ko kallonsa junaid bai yi ba idonsa a kanta, a hankali ta bude ido ta sauke kansa, lumshe ido yayi yana hamdala a xuciyarsa, ta kusa minti daya tana kallonsa kafin ta mike zaune da sauri tana bin ko ina na dakin da kallo, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya shi ma, kallon El-ameen ma tayi sannan ta sake kallon junaid, kusa da Ita El-ameen ya dawo ya cire oxygen din yace “Baby are you okay?” Jin bata ce komai ba ya kai hannu xai dafa goshinta ta koma baya da sauri tana masa wani irin kallo, Kallon junaid yayi junaid ma ya kallesa, ta shiga kokarin sauka daga kan gadon junaid ya mike yace “Where are you going to?” Ko kallonsa bata sake yi ba ta nufi kofa da sauri, bin ta junaid yayi ya wani fixgota yace “keee” tana juyowa bai ankara ba sai ji yayi ta sauke masa mari, a hankali ya saketa yana kallonta, ta fashe da kuka ta durkushe wajen tace “Where is this?”