CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writers association????
[3/19, 9:36 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid⚓
By Khaleesat Haiydar✍????
73…..
A bangaren Junaid kuwa suna barin gidan yayi kwanciyarsa, duk ya rasa me ke masa dadi, har magrib yana daki ga wani xaxxabi da yake ji, sllh yayi ya dau makullin motarsa ya fita, gida ya nufa duk jikinsa a sanyaye, he regret ever meeting her, he regret helping her, he regret all that have happened, parking yayi kofar gidan ya kasa fitowa, ya hade kansa da steering, ya kusa minti sha biyar kafin ya fito jiki ba kwari ya shiga compound din, tafiya yake kamar bai son yi don bai ma san me xai fara ce ma Mumynsa ba, bai san ta inda xai fara ba, why did all this happen to him? Shi kuma irin tasa kaddarar kenan, shafa kansa yayi ranan da ya fara ganin Zahrah ya fado masa, murmushin takaici yayi, yayi saurin kauda tunanin, ido hudu yayi da Hadiza da ke tsaye sakale da jakarta alamar tafiya xata yi ga nikab a hannunta, Umma da Hajiya ma na tsaye balcony din, suna hangosa Umma tayi mata alamar da ta shiga parlor, da sauri ta shiga ta kullo kofa, girgixa Kai yayi nufi balcony din, Umma da Hajiya aka kafa masa ido da mamaki don a tunanin su gaishesu xai xo yi, ko kallonsu bai yi ba ya bude kofar ya shige parlon, Hajiya ta xaro ido tace “Ikon Allah Meye haka Ahmad?” Hadiza dake tsaye parlon ta xaro ido ganinsa, bai yi wata wata ba ya fincikota ya kai mata naushi a baki, wani kara tayi Umma da Hajiya da tuni suka shigo parlon suka shiga salati suna tambayar yana da hankali kuwa, ko sauraransu bai yi ba ya fixgota ya fito da ita tsakar gidan, dukanta ya shiga yi yana ball da ita kamar an aikosa, ta dinga ihu tana cewa a taimaketa, tuni ‘yan matan gidan suka fiffito, Mumy ma ta fito, su Hajjo da aka diro daxu ma aka fito, Hajiya da ko ina na jikinta rawa yake ta dinga jan Junaid murya can kasa tana cewa “In ma laifi tayi maka kayi hakuri Ahmad…. Ka rufa mata asiri” ko saurarenta bai yi ba bugunta kawai yake kamar an aikosa, a fusace Hajja ta karaso ta fixgoxa ta sauke masa mari tace “Don uwar ka Amina dama shirin tafiya gidan ka nake yanxu, ban taba tunanin cewar da mahaukaci Muhammadu xai hada jikata ba, ita Humainahr ka sakar min, tsabar haukan naka ya girmama har gida kake xuwa jibgan mutane yanxu” kokarin gudu Hadiza take ya wani fixgota ya kuma sauke mata mari, Abba ne ya shigo compound din daga masallaci, ya tsaya da mamaki yana kallon tsakar gidan, Junaid da ban da tafasa babu abinda xuciyarsa yake ya fara waige waigen inda xai ga Humainah, ganin bata compound din ya ja Hadiza har part din Mumy duk aka bi sa da ido ya shiga har parlor da ita, salati Umma ta dinga yi tana cewa anya Ahmad lafiyarsa kuwa, ku ceci ‘yar mutane don Allah, fitowar Humainah kenan daga daki ya jefar mata da Hadiza nan gabanta yana kallonta sannan ya juya ya fice daga parlon, kallon mamaki Humainah ke mata, tuni duk aka shigo parlon, Abba kam dama part dinsa kawai ya nufa, Hadiza da ko ina na jikinta rawa yake ta mike da sauri xata fita, Humainah ta rikota tace “Me ya kawo ki nan?” Juyawa tayi tana waigen inda xata ga su Umma, Hajjo tace “Ina kika santa?” Hawaye ne ya cika idonta tace “Ita ta ja min komai, ni ban santa ba….” Hajjo tace “yo ni daxu tare muka shigo gidan nan da ita, ita ce ma ta shigo min da kayana daga adai daita kuma tace min Ita ‘yar wan Bilki ce, me ta maki?” Kuka sosai Humainah ta fara ta durkushe gun tace “Ita ce silar komai, ita ke xuwa gidana kullum….” Salati Hajja ta saki tace “Ita ta sa ya sake ki kenan?” Humainah ta gyada kai hawaye na sauko mata, Hajja ta cakumo Hadiza tace “Ni dama nasan ba yin kan jikana bane wannan, nasan baxai aikata haka a banxa ba, to ko ki fadi wanda ke tura ki gidan ta ko in xuba maki fetur yanxu in babbakaki” juyawa Umma tayi ta fice daga parlon Hajiya ta bi bayanta da sauri, Hajja ta kwada mata mari tace “Baxa kiyi magana ba” Mumy da duk jikinta yayi sanyi ta karaso tace “Ki yi hakuri Hajja ki sake ta….” Wani kallo Hajja ta watsa mata tace “Ke ja can dalla” shaketa Hajja ta yi tace “Baxa kiyi magana ba?” Hadiza ta fashe da kuka tace “Ni Umma ce da Hajiya suke tura ni” salati Hajja ta saki tace “Suke tura ki kije kiyi me?” Shiru Hadiza tayi Hajja ta ja ta xuwa gun tv tana neman wayar wuta tace “Toh xa ki ga ikon Allah idan ba ki bude baki kin ban labari ba” juyawa Humainah tayi hawaye na bin kuncinta ta koma daki, Hadiza da tayi mugun tsorata jikinta na rawa tana hawaye tace “Wllh tura ni suke in je in dinga xugata” Hajja ta saketa tana tafa hannu tace “Naga abinda ya isheni bai ishi Allah ba, dama su suka kashe ma jikata aure, to su ma na su na rawa yanxu, ina Muhammadu” daga haka ta fice daga parlon kamar xata tashi, jigum Mumy tayi tana kallon Hadiza dake ta waige waige kamar munafuka, can kuma ta fice da gudu daga parlon. Tafiya kawai El-ameen ke yi a hankali, haka kawai gabansa ke faduwa ganin anguwar da ta nuna masa wai nan xa su bi, tafiya me nisa suka yi tace “Here!” Juyawa yayi da sauri yana kallonta yace “Where?” Nuna masa babban entrance din tayi tana bin ko ina da kallo ganin canji da dama tace “there!” Kasa daina kallonta yayi tace “Just horn, sai ka sauke glass xan masu magana” girgixa kai yayi yace “Wai gidan sarautan nan?” Kallonsa ta tsaya yi kafin tace “Eh gidanmu ne!” Dauke kai yayi can ya juyo yace “Kina nufin ur father is a king?” Bude motar ta shiga kokarin yi tace “Yeah my father is a king” danna horn yayi kamar yanda tace har lokacin idonsa na kanta, ita ko sai kalle kalle take fuskarta dauke da mamaki ganin changes da dama, wasu dogarai ne suka fito suna kallon motar, karasowa suka yi ta sauke glass tana kallonsu, ganin bata gane ko daya daga cikinsu ba ta bude motar ta fito tace “Ku bude mana hanya” daya daga cikinsu yace “Daga ina?” Fitowa El-ameen yayi yace “Baki daga katsina” bude masu hanyar aka yi, ya koma mota ita ma haka, ya ja motar ya shiga ciki, tafiya mai tsayi suka yi kafin su kai wani gate, kallon El-ameen tayi kamar xata yi magana sai kuma ta fasa, wasu guards suka karaso gun motar, sauke glass tayi daya daga cikinsu yace “Daga ina?” kallonsa kawai take don shi ma bata san sa ba, toh yaushe aka canxa guards din bakin gate kuma, a takaice tace “Bude mana gate” El-ameen yace “Sorry, baki daga katsina, mai martaba na sane da xuwan mu” komawa yayi aka bude gate din ya ja motar xuwa babban haraban palace din, juyowa tayi da sauri ta kallesa tace “Everywhere looks strange” kashe motar yayi yace “How strange” a hankali tace “Naga changes da yawa ne”
Haske Writers association????
[3/19, 9:36 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid⚓
By Khaleesat Haiydar✍????
74…..
Bude motar tayi ta sauka, shi ma ya sauko, har ta nufi kofar shiga fada sai kuma ta juyo tana kallonsa tace “Ni xan bi ta baya, may be Abbana na tare da baki, you follow there” girgixa kai yayi yace “No i will wait out here” tabe baki tayi ta juya ta dau wata hanyar daban ya bi ta da ido har ta bace masa, ajiyar xuciya ya sauke ya koma can inda wasu bishiya ke a jere ya ja daya daga fararen kujerun dake gun ya xauna, wayarsa ya ciro ya shiga kiran layin Junaid, bugu uku ya daga, El-ameen yace “Amm muna bauchi Man” Junaid dake xaune laptop gabansa yace “Ohk, it’s good” Shiru El-ameen yayi kafin yace “Guess what frnd?” ajiye laptop din yyi a gefensa yace “Not in the mood” Murmushi El-ameen yayi yace “Ohk Gudnyt” katse wayar junaid ya jefar da wayar hannunsa ya mike ya fice daga dakin. A hankali Zahrah ta tura kofar ta shiga babban parlon da nan ne masaukin manyan baki a fadan, bbu kowa parlon, ta dinga bin parlon da kallo ganin shi ma ya canxa mata, hanyar da xai sada ta da bangaren Ummanta ta nufa da sauri, lokaci daya taji gabanta na faduwa, jakadiyar Umma ce mutum ta farko da ta fara haduwa da a hanya, wara manyan idonta tayi ta karasa da sauri tace “Baaba na dawo, ina ummana, ina su Ummi…..!” Wani kara jakadiyar tayi a gigice ta saki kayan hannunta ta juya da gudu ta bar gun tana salati, still Zahrah tayi ta bi ta da kallon mamaki, kan kace me sai ga ma’aikatan fadan sun bubbullo jin ihun jakadiya, sai dai duk wanda yayi tozali da ita sai ya bar gun a guje, duk ko ina ya hargitse, ita dai tana tsaye kamar warce aka dasa a gun cike da mamaki, a hankali ta shiga bin jikinta da kallo ko wani abu ne jikin nata, bata gama recover ba sai da yayanta ya shigo parlon taga yana mata wani kallo, da sauri ta nufesa ta ga ya juya ya bar gun, sosai jikinta yayi sanyi ta ji kafafuwanta sun kasa daukarta, Umma ce ta fito da stepmum dinta, sai dai ga mugun mamakinta sai gani tayi ita duk sun yi still a position dinsu suna kallonta ko kiftawa babu, Ummi ce ta shigo ita ma suna ido hudu ta fasa wani kara a rikice ta juya da gudu ta bar gun, juyawa Zahrah tayi da sauri hawaye cike idonta ta fita da gudu, a hankali Umma ta sulale gun ta fadi kasa a sume, rikicewa jakadiyar ta da sauran ma’aikatan dake gun suka yi suka yo kanta, Zahrah na fita dama inda ta hango El-ameen ta nufa tana isa gunsa ta xube gun ta fashe da kuka sosai tace “Why is everybody running away from me, mene a jikina da suke gudu plss tell me” shiru yayi yana kallonta, sai ya ji tausayinta, a hankali yace “Bbu abinda ke jikin ki, they are just surprise ne….” Girgixa kai tayi cikin kuka tace “Noo, what are they surprise at, do I look new? Tell me plss, dukkansu guduna suke yi” lumshe ido yayi yace “Kila basu yi xaton ganin ki yanxu bane” buda ido tayi tace “Why is that?” Takun da suka ji yasa su juyawa gaba daya, Mai martaba ne tafe da dogaransa a baya, mikewa tayi da sauri ta nufesa da sauri tace “Abba!” Kallonta kawae yake, ta fashe da kuka ta tafi da gudu ta rungumesa cikin kuka tace “Abba ni ce pa Fatima” daura fuskarsa yayi a kanta cikin sanyin murya yace “Fatima!” Rungumesa tayi sosai, hawaye na sakko mata tace “Abba kila su Umma basu gane ni bane koh?” Kasa ce mata komai yayi, El-ameen dai sai kallonsa yake yaji tausayinsa ba kadan ba, dago kai sarkin yayi yana kallonsa, mikewa yayi ya karasa inda suke ya sunkuyar da kai yace “Barka dai mai martaba, ga Zahrah na maido gida, Allah ya kiyaye gaba” kallonsa kawai sarkin yake, El-ameen yace “Na bar ku lafiya” juyawa Zahrah tayi tana kallonsa, Sarki ya taka ya isa har gabansa, hannunsa ya kama ya nufi fada da shi, tsaye duk occupant din masauratan suke ko wanne a tsorace, Mai martaba da har lokacin bai sake El-ameen ba ya nufi babban parlonsa da shi, Zahrah dai na biye da shi a baya kamar xata shige jikinsa ganin wani kallo da ake mata duk inda suka wuce, xaunawa sarki yayi ya nuna ma El-ameen kujera ya xauna, ya kusa minti biyar bai ce komai ba, Zahrah dake xaune kusa da Abban ta sai jiran jin me xai ce take, hawaye ne ya sakko idonta tunawa da tayi da irin kallon da ake mata, ta daura kanta kan kafar Abban nata muryarta na rawa tace “Abba na canxa ne wai, me yasa ake guduna?” Da kyar me martaba ya saita kansa, yana rike da hannunta yace “Baki canja ba mamata” kallon El-ameen yayi yace “Bawan Allah, a ina ka ga Fatima?” Shiru El-ameen yayi kamar baxae ce komai ba, sarki dai sai kallonsa yake, sunkuyar da kai yayi yace “Bani na ganta ba ranka ya dade….” Sarki yace “Waye shi?” Dago kai yayi yace “Aminina ne, shi ne silar komai” Sarki yace “Kana da masaniyar inda ya ganta, kuma yana ina?” El-ameen yace “Ehh nasan inda ya ganta, yana katsina yanxu haka,!” Sarki yace “Ina ya ganta” kallonta El-ameen yayi yaga yanda ta kafa masa ido tana jiran jin me xai ce, lumshe ido yayi ya bude ya kalli Sarkin yace “Tana da matsala ne a lokacin” sarkin yace “Wani irin matsala?” El-ameen yace “Ehh toh, A lokacin ta samu matsalar kwakwalwa” mikewa tayi tana kallon El-ameen, sarkin ma kallonsa yake ko kiftawa bai yi, da kyar yace “Matsalar kwakwalwa?” El-ameen ya gyada kai yace “ehh, Ban mancewa dawowarsa Egypt kenan ya taso xae xo guna da yamma ya ganta gefen titi a halin Hauka…..” Labarin yanda Junaid ya ganta, da irin tausayinta da yaji El-ameen ya shiga ba sarkin, bai boye masa komai ba har lokacin da junaid din ya nemi shi ma ya taimaka ya nuna shi bbu ruwansa, da yanda dai ya amince daga karshe, kuma bbu abinda ya rage tun daga hidimar da Junaid yayi da ita na Magani abinci sutura, nemo me kula da ita da yayi, har da irin matsalar da ya shiga gun iyayensa ta dalilin ta, da challenges din rayuwa da ya dinga fuskanta, duk da haka kuma bai taba gujenta ba, bai kuma fasa yi mata duk abubuwan da ya dace ba, har gidansu da ya kaita da niyar aurenta lokacin da iyayensa suka takurasa yayi aure, da dai yanda abubuwa suka gudana a lokacin, hatsarin da suka yi da ya maido mata da hankali sai dai kuma tayi loosing memory, da aurensa da Humainah da sakinta da yayi kan Zahrahn, kai bbu abinda ya boye ma sarkin har xuwansu bauchi sai dai bai fadi tijaran da Zaharar tayi masa ba, rike kai sarkin yayi don tuni idonsa ya canxa launi, Zahrah kam hawaye ne kawai ke saukowa idonta jikinta yayi mugun sanyi, tuni ta kasa ci gaba da tsayuwa ta durkushe wajen ta fashe da kuka sosai, da kyar sarkin ya iya dago kansa daga karshe, ya goge idonsa da Handkerchief din hannunsa cike da karfin hali yace “Shekara daya da watanni biyar kenan rabon mu da fatima, tun da suka yi hatsari a hanyar Kano, and…..” Kasa ci gaba yayi ya mike yace “Gobe da safe xa mu tafi katsinan” daga haka ya dau hanyar da xai sada sa da Bedroom dinsa, kallon El-ameen kawae take, can ta mike a hankali ta isa gabansa ta durkusa wasu sabbin hawayen na sauko mata cikin sanyin murya tace “Will he ever forgive me?” Kallonta El-ameen yake, yayi murmushi bai ce komai ba, ta fashe da kuka sosai tace “Don Allah ka gaya min xae iya yafe min…..” Saukowa El-ameen yayi yace “He will in’sha Allah” tana share hawayen da ya ki tsaya mata tace “toh Meye sunansa?” Yana kallon kwayar idonta yace Captain Ahmad Junaid a hankali tace “Ahmad Junaid” gyada mata kai yayi yana murmushi ta sauke idonta kasa.