CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writers association????
[3/19, 9:36 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid⚓
By Khaleesat Haiydar✍????
77……
Bin bayansa Zahrah tayi, ya ki tsayawa ita ma bata ce ya tsayan ba ya nufi part din Mumy, yana bude kofar ta ja ta tsaya tace “Amm… Ahmad Junaid!” Lokaci daya ya juyo ya sauke idonsa kanta yace “Yess!” Wani mugun kwarjini ya mata ta kasa cewa komai sae kallonsa take, daga kasa har sama ya kalleta sannan ya juya yayi shigewarsa parlor, still tayi gun kamar warce ruwa ya cinye, duk wannan abun El-ameen na tsaye balcony yana kallonsu, juyawa tayi suka hada ido da shi, hawaye ne ya ciko mata ta sauka daga balcony din da sauri ta nufi gunsa tana kallonsa lokaci daya hawayen idonta ya silalo tace “kaga abinda yayi min koh?” Murmushi El-ameen yayi ya buda ido yace “Yea! Haka nan yake! but idan ya sauko xa ki ga he is the sweetest guy you never expect…. He’s still angry at you ne shi yasa” a sanyaye tace “But he shud have listen to me….. He’s a sadist I notice” dariya sosai El-ameen yayi ta turo baki, tace “I just have to make him forgive me before leaving that’s all!” El-ameen ya d’age gira yace “Go in ki samesa….” Shiru tayi sai kuma a hankali tace “In je?” Gyada mata kai yayi ta juya ta koma part din Mumy, tafiyarta kawai yake kallo har ta isa kofa ta murda a hankali ta tura ta shiga, durkushe ta gansa a parlon kusa Humainah dake kwance kan doguwar kujera idonta lumshe, tsaye tayi bakin kofar ta kasa karasowa, kallo daya yayi mata ya dauke kai, Dakewa tayi ta karaso parlon cikin rashin kuxari, dai dai lokacin da Humainah ta mike xaune da sauri, ya mike ya xauna gefenta yana kallonta ganin yanda ta rame, hannunta ya rike kamar bai son magana don bakinsa kadai yayi motsi yace “What wife!” Ta dafe kanta bata ce komai ba, can ta d’ago da kyar tace “Amai nake ji” mikewa yayi ya daga ta suka bar parlon, ita ko lura da Zahrah da tayi still tana kallon ikon Allah bata yi ba har ya shiga da ita daki, Zahrah taji ta ma kasa tsayuwar, tunda take bata taba jin abinda ta ji a lokacin a xuciyarta ba, kawai ji tayi hawaye ya cika idonta, ta juya da sauri har tana neman faduwa ta fice daga parlon. Bata ko kalli El-ameen dake tsaye har lokacin ba ta tafi can karkashin bishiya tayi xamanta gun ta fashe da kuka, juyawa El-ameen yayi ya koma parlon Abba, drinks ne da ruwa gabansu mai martaba kuma ga dukkan alamu hajja ce ta debo masu, yana shiga tace “yauwa tafi ka kira Amadin su yi sallama da Sarkin wai xa su koma” fita ya kuma yi ya tafi part din Mumy, khadija da fatima ne parlon don dama suna ganin shigowar junaid suka shiga daki, amsa gaisuwar fatima yayi yace “Ina Junaid din?” Khadija tace “Yana daki” yace “Tafi ki ce masa Abba na kiransa” mikewa tayi shi kuma ya juya ya fita, ba a dau lokaci ba Junaid ya fito ya karasa gun El-ameen, El-ameen yace “Hope ka saurareta dai yanxu?” Girgixa kai yayi yace “Bani da lokacin ta, bana kuma bukatan godiyar da xata min ko hakurin da xa ta ban, don Allah nayi mata ba don ita ba wllh” Murmushi El-ameen yayi yace “Gaskiya ne” Junaid ya shiga parlon Abba, nan dai suka yi sallama da mai martaba dake sauraren xuwansa da El-ameen nan da kwana biyu, Zahrah na ganin fitowar Abbanta ta mike ta nufi gate da sauri, Ummi ta bi bayanta ganin mood dinta, Abdul ma bin ta yayi da kallo, har bakin mota Hajja da su Abba suka raka mai martaba, sai surutu take masa kamar irin ta san sa da can, junaid dai na biye da su a baya, lokaci lokaci mai martaba kan juyo ya kallesa, ita ko Zahrah can wani mota ta tafi ta tsaya a baya Ummi sai tambayarta take meyasa mood dinta ya canxa amma ta ki cewa komai, a hankali junaid ya dinga bin wajen da kallo ganin bai ganta ba, har cikin motar dake gabansu sai da ya kalla bbu ita, El-ameen dai na tsaye rungume da hannayensa yana kallonsa, tsaf ya gane me yake nema, kawai yayi murmushi, Mai martaba kansa sauraren Hajja kawai yake amma rashin ganinta ya sa ya fara waige waige shi ma, can dai yace “Ina Zahrahn ta xo ta shiga mota” Ummi ce tace “Toh kinji Abba na neman ki ma, ki taho mu je” ba musu Zahrah ta fito daga bayan motar sai dai duk jikinta a sanyaye, satan kallonta Junaid ya dinga yi har ta iso gun motar da suka taho da, Hajja ta jawota ta rungume tace “Kice ma Uwar ki ina nan xuwa, xata yi babbar bakuwa don tare xamu taho da su Amadi, Allah ya maki albarka ni dama tun farkon ganin ki kika kwanta min don akwai ni da tausayi” kai kawai Zahrah ta gyada mata ta bude bayan mota ta shiga Ummi ma ta shiga, junaid bai fasa mata kallon sata ba, ita ko bata ko kalli su waye a tsaye gun ba, tana shiga motar ta rufe ido, bata kuma bude ba sai da taji tashin motar da fatan kai wa gida lafiya da su Hajja keyi masu, ta kalli tagar motar suka yi ido hudu da junaid, dauke kai tayi da sauri, can kuma ta kalli El-ameen dake kallonta shi ma, d’an murmushi ta kirkira ta daga masa hannu a hankali, shi ma ya mayar mata da murmushin, driver ya ja motar suka dau hanyar fita daga layin. Tuni su Abba suka shiga gida, Hajja dai har lokacin bata fasa daga ma motocin da har sun bar layin hannu ba baki a wangale, El-ameen yace “Toh ae sai ki sauke hannun haka” juyowa tayi da sauri tace “Kaga ikon Allah ko Aminu, ashe dama tsinannun matan Muhammadu ne ke tare mana hanyar arxiki a gidan nan, yo gashi suna barin gidan sai ga sarki sukutum ya kwaso kafafuwa ya xo ganin jikana….” El-ameen yayi dariya yace “Toh jikan naki dai ba mutumin kirki bane don walakanci ya ma yarinyar daga ta bi sa tayi masa godiya kin dai san hali…” Tsuke fuska tayi ta kalli Junaid dake tsaye da sauri tace “Wato don ubanka ni xaka ma bakin ciki koh? Toh Allah ya isa idan aka hanani kujerun makka nah, kai baka yi murnar ta dalilin ka sarki ya shigo gidan ubanka ba, kasan alkhairin da yake shirin yi ma xuri’ar mu…. Ka xata sarauta abar wasa ce… Toh gobe gobe ka shirya mu je ka bata hakuri, kasan alkhairin da ubanta ke shirin maka….” Junaid da takaici ya ishe sa yace “Bana bukatar komansu don ni sbda Allah nayi, mahaifina na da rufin asiri dai dai gwargwado, nima ina da nawa rufin asirin don haka babu abinsu da xae rude ni, ke dai ki je a kai ki makkan…..” Bude baki Hajja tayi tana kallonsa cike da masifa can ta gyada kai tace “Shegiya nake idan ban je na ce ma Ubanka mari ka sharara mata ba” daga haka ta shige gate fuu, El-ameen ya fashe da dariya, junaid ya hade rai sosai yace “Ka bar min irin wannan abun Ahmad bana so” El-ameen ya tabe baki yace “Haka kawai mutum ya daura ma kansa wani hali da baxai fishesa ba a rayuwa, to riban me ka ci don ka walakantata Ahmad, ka dai san tafi karfin ka….” A fusace Junaid yace “Ni dai na fi karfinta don bata ma gabana, don Allah nayi abinda nayi” dariya El-ameen yayi yace “Shi yasa naga ka dage sai satan kallonta kake….” Daga haka ya daga kafa ya shiga gidan ya bar sa nan tsaye.
Haske Writers association????
[3/19, 9:36 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid⚓
By khaleesat Haiydar✍????
78…..
Ranan laraba da safe misalin goma su Junaid suka yi set off din xuwa bauchi sai dai ta plane don yace baxae iya xaman mota ba, shi ma din ba karamin takurasa Abba yayi ba kafin ya amince xai je don da ca yayi shi baxae je ba don sbda Allah yayi abinda yayi, xuwa lokacin dae ba laifi Mumy na amsa gaisuwarsa sae dai ba kamar da ba hakan yasa duk ya ji ba dadi, tun ranan litinin yake gidan, ko yaje aiki nan yake dawowa da yamma, tausayin Humainah yake sosai hakan yasa ko da yaushe yana kusa da ita, part dinsa ya mayar da ita daga karshe ita dai Mumy nata ido, duk da luran da yayi su Umma basa gidan haka ma Suhaima da Muhibba ko sau daya bai taba tambayar inda suke ba, harkokin gabansa kawai yake, Hajja dake ta shiri tun daga ranan litinin din tana jiran ranan jumma’a da Abba yace za su je bauchi da su Junaid bata san har sun tafi ba safiyar laraban, suna cikin taxi da xai kai su Airport wayar El-ameen ya fara ringing, cirowa yayi yaga Aliyu ne ke kiransa, shi har ya ma mance da shi, d’an murmushi yayi ya daga kiran, daga daya bangaren Aliyu yace “Masu Jasmine/jewel/baby!” Murmushi El-ameen yayi yace “Yea, mara mutunci da abokina bai dawo sense dinsa ba sai dai ka ga sammaci wllh” dariya Aliyu yayi yace “Ae nasan ya dawo ne, bayan ka xo ka dauketa ka mayar masa ae magana ta kare” El-ameen yace “Exactly, kuma albishirin ka, ita ma ta dawo, ka dai gane me nake nufi…” Aliyu yace “Ohh really, dama na ga alama soon xata dawo…. But what brought her back!” El-ameen yace “That’s a long story, yanxu ina hanyar bauchi ne” Aliyu yace “me xaka yi bauchi” El-ameen ya saci kallon junaid dake kallonsa yace “Ohk! Let’s chat!” Daga haka ya katse wayar, wani uban tsaki Junaid ya ja ya dauke kansa, El-ameen yayi dariya, junaid bai kuma kallon inda yake ba har suka isa airport. sha daya suka sauka bauchi, El-ameen ya tare masu taxi duk suka shiga baya ya fadi ma me taxin inda xai kai su, Sai a sannan ya juya yana kallon junaid yace “ka cika umarnin da sarki ya baka kuwa?” Junaid ya kallesa yana jiran jin umarnin me, ganin El-ameen bai kuma cewa komai ba har bayan kusan minti biyar yace “Wani umarnin?” El-ameen yace “Ashe kana da baki” dauke kai Junaid yyi, El-ameen yace “Na mayar da Humainah da yace kayi!” Shiru Junaid yayi masa na kusan minti sha biyar kafin ya juya ya kallesa yace “Ehh” ko kallonsa El-ameen bai yi ba idonsa na kan titi, murmushi Junaid yayi ya shafa kai, sha biyu saura suka isa masarautan, El-ameen ya fito daga taxin haka ma Junaid dake bin ko ina da kallo, Kudi El-ameen ya ciro ya ba mai taxin sannan ya nufi Entrance din masarautan junaid ya bi bayansa, gaba dayansu dakakkiyar Shadda ce jikinsu, shi El-ameen ruwan hoda, shi kuma junaid fari, yana biye da shi ne yana danna waya, tafiya sosai suka yi kafin su iso main Entrance din da xai kai su har palace din, fixgosa Junaid yayi ganin tafiyarsa kawai yake yace “Meye xaka wani dinga wucewa kana kyaleni a baya, ko na ce ma nasan hanya ne” kallon mamaki El-ameen yayi masa kafin ya duka yace “To hau!” Junaid bai san lokacin da ya fara dariya ba yace “Ka ji dan iska, kai har xaka iya goya ni?” Murmushi El-ameen yayi ya mike don ko ba komai ya sa shi dariya baxae shiga yana murtuke ma mutane fuska ba, a tare suka jera suna tafiya, Junaid yace “Wani disc ne na gani daxu a hannun ka a plane” El-ameen yace “Na ban mamaki ne” Abdul dake tsaye da abokansa biyu gun mota da alamar xa su fita ne ya hangosu ya karaso da sauri yace “Ohh baki gare mu haka… Welcome to you guyz, sannun ku da xuwa” hannu ya basu gaba daya biyun sannan yayi masu jagora har xuwa fada, ganin Abbansa na da baki ya nufi part dinsa da su, suna shiga parlonsa Junaid ya nemi gu ya xauna ya cire hular kansa, Abdul yace “Amma flight ku ka biyo koh?” El-ameen yace “Eh my oga at the top yace bai iya xaman mota ba sbda kura” dariya Abdul yayi yana kallon Junaid, junaid yayi murmushi yace “Manta da shi basir gare sa bai iya xaman mota shi yasa muka biyo jirgi” dariya suka dinga yi gaba daya, El-ameen ya jefa masa hular kansa yace “Kaji sharri….” Drinks kala kala da kayan marmari Abdul ya dire masu ya xauna yace “Toh ya mutan gidan, ya muka baro ku?” El-ameen ne kadai ya amsa don shi junaid kallonsa kawai yake ganin ba kaman wasa suke da kanwarsa ba, waya Abdul ya dauka ya ce bari in kira maku mutuniyar ku gaisa kafin Abba ya sallami b’akinsa, yana kara wayar a kunne bayan ta daga yace “Lil sis, ki taho ina jiran ki part dina” daga haka ya katse wayar, bayan kusan minti goma sai ga ta ta shigo parlon, wani alkybba dake daukar ido ne jikinta har yana jan kasa, shi kansa takalmin kafarta abun kallo ne, hular kanta ya rufe kusan rabin fuskarta, tana ganin mutane xaune parlon ta turo baki ta nufi bedroom don ta gaji da gaishe gaishe, Abdul yace “Ina kuma xa ki bakin ki ne fa” daga kai tayi da sauri ta maida hular saman kanta, ido hudu suka yi da junaid ya kasa dauke idonsa kanta, tayi saurin kauda idonta ta kalli El-ameen dake kallonta shi ma ko kiftawa babu, wani kyalli take gaba dayanta, tayi wani kyau na musamman duk da ba make-up bane fuskarta, murmushi tayi da ya bayyana fararen hakoranta ta karasa gun El-ameen ta durkusa nan kasa cikin sanyayyen muryarta tace “Welcome!” Kai kawai ya iya gyada mata, Abdul kuma yayi excusing kansa ya fita, da kyar El-ameen ya samo abun cewa yace “Ya gidan, ya su mama!” Ta langwabar da kai tace “Taso mu je ku gaisa da su” Junaid dai danna wayarsa kawai yake, El-ameen yace “Baku gaisa da captain ba?” Gefenta ta d’an kalla tace “Ohk, sannu da xuwa” daga haka ta mike tace “Mu je gun Ummata” mikewa El-ameen yayi
ya dau Apple daya ya kalli junaid yace “taso mu je muyi gaisuwa frnd” junaid yi yayi kamar bai ji sa ba, Zahrah tuni ta nufi kofa ta fita abunta, warce wayar El-ameen yayi yace “kaga ka ajiye halin nan naka aside har mu bar garin nan, in girman kai ne da ji da kai toh gidansa ka xo, bbu wanda xaka nuna ma a nan sai dai ma ka kara course wajen su” mikewa junaid yayi yace “Dama don ku ci min mutunci yasa kuka dage sai na xo garin nan, how dare her xata shigo ta ki gaisheni tana min kallon rainin wayo, da ana rubuta hali a goshi wllh da ban fara ko da kallon inda take ba bare har na tausaya mata” yar dariya El-ameen yayi yace “Yau kuma ba don Allah kayi ba kenan……” Wani tafarfasa xuciyar junaid yake, El-ameen ya tabe baki yace “If you like kar ka fito muyi me ya kawo mu bar garin nan” daga haka yayi ficewarsa ya barsa gun tsaye, tsaye ya ga Zahrahn tana jiransu ga dukkan alama taji abinda suka ce, murmushi ya mata yana fatan Allah yasa ba jin dai tayi ba. Ta mayar masa da murmushin tayi gaba tana cewa “Kila yana da matsalar kunne ne, shi ya hanasa jin sannun da nayi masa,” da sauri El-ameen ya kalli bayansa ya ga ko yana gun, ya ga ko fitowa bai yi ba, can ko sai ga shi ya fito, Tana gaba El-ameen na biye da ita a baya shi kuma junaid na bayan El-ameen, bangaren Kilishi ta fara kai su, sosai tayi farin cikin ganinsu, ta sa aka cika su da kayan ciye ciye da sha, Shi dai junaid idonsa na kan makeken plasman parlon dake cike da kayan alatu, ganin yaki taba komai tace “Kai ya sunanka, ko kai ne takwaran mai martaba?” Girgixa kai yayi yace “A’a, Ahmad” tace “Babana ne ma ashe, to baka ci komai ba…. Ba a mana haka fa” da ganin murmushin da yayi kai kan ka kasan kirkira yayi, ya dau slice din kankana ya Kai baki yana tauna da kyar, ta gefen ido Zahrah ke kallonsa can ta tabe baki hade da murguda bakin, El-ameen kuma hararansa kawai yake ta gefen ido, ita ko Kilishi sai kallonsa take haka nan taji ya burgeta, jikinsa ne ya basa kowa kallonsa yake ya ki daga kai ya kuma daukar apple ya kai baki ya gutsura a hankali, Zahrah tace “Mumy bari in kai su gun Umma” Kilishi tace “Toh maxa ku je Zahrah” mikewa tayi tana kallon El-ameen tace “Mu je” mikewa yayi shi ma yayi mata sallama tace “A’a mai gida ai xaku dawo” kallon Junaid tayi tace “Toh tashi ku je babana” d’an murmushi yayi ya mike yace “Sai mun dawo” daga haka suka fita gaba daya daga parlon, a tare suke tafiya da El-ameen suna hira jefi jefi, El-ameen yace “Yayanki ne Abdul din nan koh?” Ta gyada kai tace “Yea, stepbrother nah” ya wara ido yace “Waow, mum dinsa ce kenan wannan!” Ta gyada kai tace “Ehh shi da Ummi” yace “Ayya, amma kina da kanni ko yayyi the same mum kuwa” girgixa kai tayi tace “I am the only one gun Ummata” kallonta yake da mamaki, yaji tausayin mahaifiyarta sosai, ko ya tayi da Allah ya rabata da only child dinta, junaid dai distance me d’an tsayi ya bari tsakaninsu yana biye da su hakan kuma bai hanasa jin hiran tasu ba, daya daga masu girke girken fadan ne ta washe baki ganin Zahrah tace “Gimbiya ban ganki kitchen yau ba” d’an murmushi tayi ta tsaya har ma’aikaciyar ta karaso kusa da ita, El-ameen ya ci gaba da tafiya, Zahrah na kallonta tace “Ina ciwon kai ne shi yasa… Ya aiki?” Matar tace “Alhmdllh, b’aki kika yi?” Kada mata kai tayi dai dai lokacin da Junaid ya karaso ya wuce su, ta bi sa da wani kallo kafin ta tabe baki tace “Da rana xan shigo kitchen Karima” daga haka ta nufi El-ameen dake tsaye wani stairs yana jiranta, ita kuma matar ta bi ta da kirari, ta gefen ido junaid dake tsaye gefen El-ameen ke satan kallonta har ya ga ta kusa isowa, El-ameen na ganinta ya ci gaba da tafiya, shi kuma yana ganin xata wuce sa ya sa mata kafa, ko lura bata yi ba sai ji tayi ta tafi luu xata fadi, tayi k’ara a tsorace tana neman regaining balance, bai san lokacin da yayi saurin tarota ba ta fado jikinsa, still tayi da farko sai kuma ta dago kai da sauri suka yi ido hudu, kasa motsi tayi ta kuma kasa dauke idonta cikin nasa, shi ma kallonta kawai yake gabansa na faduwa, bakinsa ta ga yana motsi a hankali ta sauke idonta kai underneath his breathe taji yace “Jas…jasminee!” Gaba daya ta shagala da kallonsa, shi ya fara dawowa hankalinsa ya saketa da sauri, sai a sannan ta koma baya duk ta daburce, a tare suka juya da sauri kallon El-ameen suka ga gun wayam babu shi.