CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association????
⚓ Captain Ahmad Junaid⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍????
6…..
El-Ameen ya juya yana kallon Junaid ganin ya ki karasowa da karfi yace “baxa ka xo ka ga abinda mahaukaciyar da ka sa na kawo gidana tayi ba, ya Salam!” Junaid na jin hka ya karaso da sauri yana leka parlon, kwalalo ido yyi yana kare ma palon kallo, palon komawa yyi kamar wanda aka yi karamin yaki, don duk ta tarwatse plasman palon da frames gaba daya, lafiyayyen centre table din ma bata raga masa ba, ko ta ina kwalabe ne a falo, duk ta tuttuge labulaye da karafunansu, kujeru kam upside down ta juyasu dukka, Junaid bae san lkcn da ya fashe da dariya ba har da rike ciki, El-Ameen ya bude baki yana kallonsa idon nan nasa ya kada, fixgosa yyi yana huci yace “Yhu see wat you’ve caused koh Ahmad, gud! this mad woman is adding not a minute more in my house” yana fadin hka ya turasa ya shiga palon, da sauri junaid ya hadiye dariyarsa ya rikosa yace “Haba frnd, Chill plss ka mance mahaukaciya ce ita kamar yanda kake kiranta, I promise wllh duk xan siya maka abubuwan da tayi damage, that’s a promise frnd!” marairaice masa Junaid yyi yace “Plss!” El-Ameen yyi kwafa yace “Yanxu naji bayani, kuma ga motata ma can a gida bbu kyan gani, kasan yanda xa kayi da shi, I need it the way it was before, nd don’t forget it’s my favourite car” Junaid yyi murmushi yace “Kar ka damu xa a gyara” El-Ameen yace “Gud! Kuma ynxu idan mu ka shiga naga tayi fitsari ko otherwise wllh kai xaka gyara min waje” Junaid ya d’aga kafada yace “Na yarda” Nan El-Ameen ya sa kai ya shiga falon yana bin ko ina da kallo, sae a lkcn ya kula da jinin da yayi littering din falon alamar duk ta ji ciwo, kamar ance ya kalli bayan kofar falon ya ganta durkushe wajen duk jini jikinta, suna hada ido ta mike da sauri xata yi waje ya yamutse fuska ya fixgota da karfi, kokuwa ta shiga yi da shi ya mata wani lafiyayyen rankwashi ae sae ga hawaye a idonta tana kallonsa, Junaid da yyi shiru yana kallonsu a hankali yace “Haba El-ameen rankwashi kuma?” Ko kallonsa El-Ameen bae yi ba, ya ja ta suka koma sama xuwa dakin da aka ajiyeta, bude baki yyi ganin duk ta fasa glass din windunan dakin ma, ita nan duk neman hanyar fita take, kwalo ma Junaid kira yyi da karfi, Junaid ya nufi stairs da sauri ya haura ya shiga dakin, El-Ameen na huci yace “Ohh my God! Dubi windows dina Captain” Junaid ya langwabar da kai yace “Duk xan gyara maka as soon as possible” El-Ameen yyi kwafa yace “Allah kar ya wuce kwana biyu, kuma ni ka xo ka ajiye mata abincin my frnd, I have important things doing a office” karasowa Junaid yyi ya ajiye abincin ya bude yana kallon yanda ya rike hannunta gam sai mutsu mutsu take, El-Ameen ya kai ta k’asa ya nuna ta da yatsa yace “Wllh Kika sake min barna a gidana sae na gaggalla maki mari, wawiya kawai” ita dae kanta na k’asa, tsaki yayi ya mike yana kallon Junaid yace “Mu je plss malam gashi ka kawo mata abincin hankalinka ya kwanta” Junaid yace “But ya kamata mu samo ‘yar dattijuwa yanxu koh?” Wani kallo El-ameen yayi masa yace “Ya kamata dai ka samo” daga haka ya fice daga dakin, Junaid ya bi sa da kallo sannan ya kalleta, har lokacin bata d’ago ba, abincin ya matsar mata gabanta a hankali yace “Ki ci abinci kin ji, we are only helping yhu Baiwar Allah” ita dae kanta na kasa sai d’ada takurewa waje daya take, kwala masa kira El-Ameen yyi ya fito da sauri, El-Ameen ya sa ma dakin key yace “barnan ya tsaya iya dakin” shi dae Junaid bae ce komae ba har suka fito, El-Ameen ya tafi gun tap din dake compound din gidan ya wanke hannunsa yana tsaki ya nufi gate Junaid na bin bayansa, a cikin mota El-Ameen ya ciro waya ya shiga neman nmbr, yana dialing ya sa hands free, sallama aka yi masa ya amsa yace “Jibril kana ji na,” d’aga daya bangaren aka ce ehh oga, yace “Gud mai gadi nake son ka samo min nan da ‘yan awanni don Allah, wanda ka sani kasan halinsa fa” D’aga daya bangaren aka ce “Toh oga, in’sha Allah xa ayi hkn” katse wayar El-Ameen yyi, Junaid ya tada motar suka bar layin, sae da ya fara ajiye El-Ameen clinic bbu wanda yace ma kowa komae, yana fice masa a mota ya ja motar ya nufi office shima, El-Ameen yyi murmushi yace “Ina xaune xa ka dawo ka same ni ne ae”
Karfe hudu da rabi Junaid ya koma gida daga gun aiki, tunaninsa daya karyar da xae ma Mumy ta bar shi ya fita, don ryt from time shi ba mae xuwa ko ina bane daga gun aiki sae gida sai in kuma yaje kallon kwallo shi ma ba ko da yaushe ba don yafi son kallon a gida, ko da yaushe yana manne da ita shi dai, yawanci ma El-Ameen ne ke xuwa gidansu shi bae fiye xuwa can ba sosae, yana xaune bangaren Mumy bayan ya gama lunch, ita kadae ke hiranta sai fatima dake ta shirin islamiyya, shi kam duk hankalinsa baya tare da shi kawae ya kafa ma tv ido ne kmr me kallo, agogo ya duba ya ga har biyar, ya fiddo waya ya kira lambar driver yace ya xo ya samesa bangaren Mumy, ba a dau lkci ba drivern ya xo, Junaid ya ciro dubu goma ya mika masa yace “Gashi wannan ka siyo fruits din dare kamar ynda kake siyowa ka kai ma kowa nasa” Drivern ya risina ya karba yace “Toh yallabai,” Junaid ya ciro Atm dinsa yace “ka d’an biya Atm Machine ka ciro min dubu talatin” Drivern ya karba yace “In’sha Allah yallabai” yana fita Mumy tace “Me xaka yi da dubu talatin Junaid” Junaid yace “Su Umma xan ba ko suna bukatar abu kafin Abba ya dawo jibi” Mumy tace “Ohk Hakan yyi” yana xaune sae kallon agogo yake a kai a kai har Ishaq ya dawo da ledoji hudu dauke da fruits kala kala, ya ajiye ma Mumy nata snn ya ciro 30k ya mika ma Junaid, Junaid yace “Yauwa ka raba dubu sha biyar biyar ka kai ma Hajiya daya Umma daya” Mumy tace “A’a kai ya kamata ka kai masu” bae yi musu ba ya karbi kudin hannun Ishaq, Mumy tace “Ajiye naku fruits din ka fara kai masu nasu” Ishaq ya ajiye leda daya ya fita da biyu don kai ma Umma da Hajiya, ba a dau lkci ba ya dawo ya dauki nasu ledan na masu gadi da masu wanki da share sharen gidan ya fita don xuwa su raba bayan yyi godiya. Junaid ya kalli Mumy yace “Mumy xan je gidansu El-Ameen!” Mumy tace “Gidansu El-Ameen kuma, wae wnn sintirin xuwa gidansu El-Ameen da kke kwana biyun nn kalau kuwa Ahmad? Ko dae gun budurwa kake xuwa?” Ta kare maganan tana murmushi, Dariya yyi ya shafa kansa yace “Kai Mumy budurwa kuma, shi dae nake rakawa fa” Mumy na murmushi har lkcn tace “uhn uhn kai dae fadi gskya Ahmad” ya shagwabe mata yace “Mumy ni da gske wllh ba gun budurwa nake xuwa ba, El-Ameen nake raka wa” Mumy tace “In ma gun ta kake xuwa ae ba laifi bne Ahmad, it’s high time yhu start planning of settling down with a wife yanxu son” murmushi yyi ya mike yace “Allah ya kawo lkci mumyna” tayi murmushi tace “Toh Ameen” yace “Bari in kai ma su Umma kudin Mumy, daga can xan wuce” Mumy tace “Toh Allah ya tsare kar dae ka yi dare plss Ahmad” yace “In’sha Allah mum” daukan wayarsa yyi ya fita daga falon, gun Umma ya fara shiga ya samu Muhibba ce da wata kawarta a falon, ya wani hade rae ba tare da ya damu da amsa gaisuwar da suka yi masa ba ya mika mata 15k din yace “Gashi ki ba ma Umma” juyawa yyi ya fice daga falon, Kawar Muhibba me suna Salima tace “Kai amma wllh kina bada mata Muhibba, har wannan dan karamin alhakin ne xaki dinga barin yana walakanta ki don yana da kyau, ubansa kuma na da dukiya, sae kace ba gogaggiyar ‘yar jami’a ba?” Muhibba tayi murmushi tace “Baki san Ahmad bane Salim, ya fice tunanin ki wllh….” Salima ta katse ta tana kalle kalle tace “Da’alla banxa tsaya ki saurareni, mu je daki in baki wani plan ki ga ko baxae yi aiki ba” mikewa Muhibba tayi suka yi daki da kawar tata cike da xumudin jin plan din. Junaid na fita bangaren Hajiya ya nufa ita ma ya bata kudin, tana jujjuya kudin tace “Duk kudin da Alhaji ya bari Ahmad ka rasa abinda xaka kawo min sae wani shegen dubu sha biyar, wato sauran kuma ka ba uwar ka koh, toh wallahi ka ji tsoron Allah don hakkinmu baxai bar ka ba” Junaid ya daga kafada yace “Ni Abba bae bar min kudi ba, kawae gani nayi hakan ya dace shi yasa na kawo maki na kai ma Umma don ko mahaifiyata ban ba kudi ba gidan nn, gobe ko jibi ae Abban xae dawo, in kina da wani bukatar da ya wuce na wannan idan ya dawo sae ki tambayesa” yana kai wa nn ya fice mata daga palo, ta bi sa da kallo baki bude, idonta ya kankance don bacin rai, rufe bakin tayi tana gyada kai tace “yaro yaro ne” kwafa tayi ta juya ta koma don ci gaba da abinda take tana wani murmushi. Karfe shidda saura Junaid ya isa gidansu El-Ameen sanin ya baro clinic yanxu, Mum din sa ya samu falo, bayan sun gaisa yace “Ummi El-Ameen ya dawo koh?” Hajiya Maryam da ake kira da Ummi tace “Ehh ya dawo daxu amma ya fita yanxun nan, ka kira sa kaji inda yake don nasan baya asibiti” Junaid yace “Toh shknn Ummi xan kirasa, ni xan koma” Ummi tace “Toh ko ruwa baxa ka sha ba Ahmad?” Yyi murmushi yace “Alhmdllh Ummi” Ummi tayi murmushi tace “Toh ka gaida min Hajiya Amina” yace “Xata ji Ummi” fita yyi daga falon yana tunanin inda El-Ameen ya tafi, sae da ya shiga mota snn ya kirasa, bugu daya ya d’aga Junaid yace “Kana ina ne?” El-Ameen yace “Au! ai nayi xaton xuciya kayi ka bar ni da mahaukaciyar taka” Junaid yyi tsaki yace “Kana ina nace?” Dariya El-Ameen yyi yace “Kai dae duk abun ka baxa ka iya xuciya da ni ba wllh, come over ina gidana, na samo mai gadi, ya kuma min hanya an samu wata dattijuwa, we are ol there 2gether ynxu, mind yhu duk wata xaka dinga biyan mai gadin dubu 30, ita kuma warce xata tsaya da mahaukaciyar xa’a bata dubu 50 monthly, coz its not an easy job, ga kuma risk din dake tattare da job din, and yhu make sure ka shiga kasuwa ka siyo mata kayayyakin da xata dinga sawa including inner wears” Junaid yace “Ni ban san inda ake sai da kayan mata ba” El-Ameen yace “So? Ba sae ka ce a raka ka ba, ko ka shiga kasuwar kayi tambaya” tabe baki Junaid yyi ya katse wayar ya kama hanyar gidan. A waje yyi parking ya shiga, sabon mai gadin da ke xaune compound din ya gaishesa da ladabi, Junaid ya amsa ya nufi kofar shiga palo, daga bakin kofar ya tsaya yana kare ma palon kallo, duk an share barnar daxu ko ina yyi fess, kallon El-Ameen dake xaune kan daya daga kujerun falon yana danna waya yyi snn ya karasa shiga falon, El-Ameen ya kallesa yace “Kayan fa, ni fa I can’t put her under medication da suturan jikinta, it’s very irritating, na dae yi mata alluran barci daxu don ban ga alaman tana yi ba” Junaid ya xauna gefensa yace “Toh don Allah ka raka ni mu siyo kayan mana, serious ban san ina xan samu women wears ba” El-Ameen yace “Nace idan ka shiga kasuwar kayi tambaya mana sae kace ba wayayye ba” shiru Junaid yyi yana kallonsa, wata yar dattijuwa ce da baxata haura sittin ba ta fito daga kitchen da alama ita ce ta yi gyaran gidan gaba daya, gaishe da Junaid tayi, yyi murmushi yace “Sannu da aiki mama” mikewa El-Ameen yyi ya haura sama ba a dau lkci ba ya sakko rike da sabulan wanka tsadaddu da sponge, sae toothbrush da toothpaste yana kallon dattijuwar yace “Mama ga wannan, wanka xa ki taimaka kafin mu dawo, xae kai maki ita bayin yanxu,” Matar tayi shiru tana kallonsa sae dae da ganinta kasan a tsorace take, El-Ameen yyi dariya yace “Babu abinda xata maki wllh mama, bacci ae take kuma baxa ta tashi ba yanxu, mu je ki ga” bin bayansa tayi suka haura sama, Junaid ya bi su da kallo kafin ya shafa kansa, El-Ameen ne ya fara shiga dakin snn ita ma ta shiga, tana nan kwance yanda ya bar ta bayan yyi mata allura, idanuwanta duk a rufe, kallon dattijuwar yyi yace “Kinga bacci take ko mama, kuma na gaya maki baxa ta tashi ba sae bayan awanni takwas,” kai kawae ta gyada masa, bayi ya nufa ya hada ruwan dumi da yawa snn ya fito dakin ya dauketa ya nufi bayin da ita ya kwantar da ita kasan neat bathroom din ya fito yana kallon tsohuwar da ya sa ma Mama yace “Gata can na kai maki bayin, don Allah ki wanke mata wannan gashin da kyau mama, nasan baxa kiyi wahalan fito da ita ba idan kin gama don bata da nauyi, xan fito maki da bargo kawae ki lulluba mata har mu dawo da kaya” tace “Toh yaro” juyawa yyi ya fita ta nufi cikin bayin. Siyayya ba kadan ba Junaid yyi ma Mahaukaciyar, tun daga kan normal English wears wato dogayen riguna, xuwa mayyukan shafawa, turarruka, da inner wears da jallabiyoyi, har man gyaran gashi da combs duk sae da ya siya da takalma sae huluna da ‘yan kunnaye, shi dae El-Ameen bin sa kawae yake yana dariya, ganin har xa ayi magrib yasa El-Ameen yace “Kai koh kayan lefe kake hadawa fa sae haka Junaid, for God’s own sake kayan nan sun isa haka it’s time for magrib” Junaid ya kallesa yace “Ohk” Karfe bakwae da rabi suka isa gida, shi ma don sun tsaya hanya sun shiga masallaci sun yi sllh snn sun tsaya eatry siyan abinci, xaune suka samu dattijuwar a falo kan dankwalinta alamar sllh ta idar, tayi masu sannu da xuwa, Junaid ya ajiye kayayyakin hannunsa, El-Ameen ya bude wani leda ya fiddo doguwar riga da man shafawa da na kai sae inner wears da turare ya mika ma matar yace “Gashi mama ki taimaka ki sa mata” ta mike tace “Toh” sannan ta karbi kayan ta haura sama, durkusawa tayi gabanta ta yaye bargon da ta rufe ta da shi ta bude tsadadden man da aka bata ta shiga shafa mata jikinta, cikin mintuna da basu fi goma ba ta gama shiryata, ta debi hair cream me yawa ta shafa mata a dogon gashinta sannan ta shiga taje gashin a hnkli saboda tsantsin sa, tana yin haka hawaye na xuba idonta kmr daxu da take mata wanka, rayuwa kenan duk yanayin da ka tsinci kan ka ka gode Allah, Coz he knows best, shi kadae yasan dalilin barin wannan Baiwar Allah haka, ba wae kuma don baya sonta ya bar ta a hakan ba, har ta gama tufke mata dogon gashinta da ya kusa bayanta hawayenta bae tsaya ba, gyara mata kwanciya tayi ta rufa mata bargon ta fito tana kallonsu El-Ameen tace “Na gama” El-Ameen ya mike yace “Kin sa mata komae dae koh mama” tace “Na sa mata” yana ‘yar dariya yace “Kin tabbata mama” murmushi tayi tace “Na sa mata komai yaro” kallon Junaid yyi sannan ya nufi stairs, Junaid ya mike ya bi bayansa, El-Ameen na shiga dakin ya karasa gabanta ya durkusa ya yaye bargon dake jikinta a hankali, rike breath dinsa yayi yana kallonta ko kiftawa bae yi har Junaid ya shigo ya same sa a hka, shima ya durkusa a hankali nan gabanta yana kallonta.