CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writers association????
Afuwan pls.
[3/19, 9:36 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid

By khaleesat Haiydar✍????

Da sallama ta tura kofar parlon ta shigo rike da wani babban tray mai dauke da abinci bayanta maids biyu wata dauke da bowl din fruit, wata kuma food warmers har biyu, kallonta kawai suke har ta karaso makeken parlon ba tare da ta dago ba ta ajiye tray din hannunta ta juya xata fita, a hankali El-ameen yace “Fatima!” Tsayawa tayi amma bata juyo ba, Junaid dai sai kallonta yake, jin ba ace komai ba tayi ficewarta daga parlon, saukowa El-ameen yayi ya dau fruit ya fara ci yana kallon junaid, tun xuwan su Bauchi ya rasa dalilin sanyin da yayi lokaci guda, har ya gama cin abinda xai ci junaid bai ko kalli abincin ba, El-ameen ya mike ya shiga bedroom ya bar sa parlon, rike kai Junaid yayi don shi kadai yasan abinda ke damunsa. Bayan isha ya fito makeken haraban masarautan sanye da kananun kaya ko ina farin wuta ne wanda hakan ya maida gun kamar safiya, tafiya kawai yake hannunsa cikin aljihu iska mai dadi na kadawa har ya karaso garden din da yasan xai ganta, ai kam xaune ya ganta ita kadai kan lallausan rug tana sanye da alkyabba kalan gold sai kyalli yake ta xauna kan kafafuwanta, ba wani wuta ne me haske gun shakatawar ba, gabanta bowl ne me dauke da apple fruit, ya rasa me ta tsura ma ido a gun, har ya karaso kusa da ita bata sani ba sai da sanyayyen kamshinsa ya bugi hancinta, duk da haka bata juyo ba idonta na kan grasses din wajen, ya xauna d’an nesa da ita cikin sanyin murya yace “Jasmine” bata kallesa ba bare tace komai, sake kiranta yayi nan ma dai bata amsa ba, dawowa kusa da ita yayi ya kuma kiranta a karo na uku, juyawa tayi tana kallonsa bbu yabo bbu fallasa tace “Sunana ba Jasmine ba” helplessly yake kallonta a hankali yace “Ohk fatima” dauke kai tayi bata ce komai ba, bai sake cewa komai ba lokaci lokaci ya kan juya ya kalleta, mikewa tayi daga karshe ta dau apple daya tace “Am going in” daga haka ta yi gaba ta bar sa wajen, ya bi ta da ido, lumshe ido yayi ya hade kansa da gwiwa, a hanya ta hadu da El-ameen ya mata murmushi yace “Princess!” D’an murmushin ita ma tayi ta wuce bata ce komai ba. Bangaren Ummanta ta nufa ta sameta xaune da baki da dama a babban parlonta, sallama tayi masu ta yi hanyar dakinta duk aka bi ta da kallo, mikewa Umma ta yi tayi excusing kanta ta bi bayanta, tana kokarin cire alkyabbarta ta shigo dakin, ta juya tana kallon uwar tata, Umma ta kamota ta xaunar gefen royal bed din dake dakin tace “Zahra!” Dago manyan idonta tayi tana kallonta tace “Na’am ummana” Umma tace “Why didn’t you greet at the parlor” a hankali tace “Na fa yi sallama ummana” Umma tace “No da kin tsaya kin gaida su, they are ol here because of you daughter” sunkuyar da kanta tayi tace “Am sorry Umma” Umma ta rungumeta sosai jikinta lokaci daya hawaye ya taru idonta tace “It’s OK sweetheart, kin kai ma su Ahmad din abincin kuwa” gyada kai tayi tace “Na kai” Umma tace “Good je ki gun Abba ki masa sai da safe, ko kin je?” tace “Naga yana da visitors ummana” Umma tace “Suna masauki yanxu, tashi ki je” tace “Toh ummana” mikewa tayi ta mayar da alkyabbar da ta cire suka fita dakin tare da umma, sai da ta fara karasawa cikin babban parlon ta durkusa ta gaida matan dake xaune, duk suka amsa suna kallonta da sha’awa, sannan ta mike ta fita, babban parlon Abbanta ta tafi sanin ya bar fada yanxu, ta gansa xaune kasa kan lallausan carpet din dake shimfide fruits gabansa daga gefensa Ya Abdul ne, sai yayyinta maza su hudu gaba, duk suka dinga kallonta har ta karaso gun Abba dake ta kallonta shi ma murmushi shimfide fuskarsa, mikewa xaune yayi yace “My princess” tayi murmushi tace “Abbana!” Ganin yanda yayyinta ke kallonta ta hararesu tace “Ni bana son kallon” dariya suka yi gaba daya har da mai martaba da ba kasafai yake dariya ba sai dai murmushi, da ganinsa kasan farin ciki ne karara tare da shi, ya Abdul kadai ne kansa a kasa sai dai lokaci lokaci ya kan dago ya kalleta, sun yi hira sosai da yayyin nata daga bisanni ta masu sai da safe har da Abba ta koma bangaren Umma. Washegari da ya kama Friday ana sakkowa juma’a, parlon mai martaba ya cika dam da ‘yan uwa da abokan arxiki da suka taho nuna masa farin cikinsu na bayyanar tilon ‘yar sa, haka kuma ranan da su Junaid xa su koma kenan kasancewar kwanan su uku a masarautan, Mai martaba sai kallon junaid da ko dago Kai bai son yi yake, can yayi gyaran murya yace “Ahmad?” Kallonsa junaid yayi sannan ya amsa, Mai martaba yace “Ka fadi duk abinda kake so nan duniya Ahmad in dai bai saba ma Shari’a ba kuma bai fi karfina ma na maka alkawarin yi maka shi koma menene” a baxata cewar sarkin ya xo ma junaid, ya sunkuyar da kai bai ce komai ba, haka kawai gaban El-ameen dake gefensa ya dinga faduwa, junaid ya dago da kyar yana kallonsa cikin sanyayyen muryarsa yace “Bana bukatan komai ran ka shi dade, I helped her for Allah’s own sake” kallonsa kawai sarkin ke yi daga bisanni ya juya yana kallon El-ameen dake kallon junaid yace “Kai fa Aminu?” Ido junaid ya xuba masa ya ji abinda xai ce, El-ameen da har lokacin gabansa bai bar faduwa ba cikin tsarkewar murya yace “Ina son ka min alfarmar bani aurenta ran ka shi dade, na maka alkawarin xan rike maka ita da amana….” wani mugun bugu xuciyar junaid yayi lokaci daya yaji kamar xuciyar ta bar aiki, mai martaba da ya kafa ma El-ameen ido yayi murmushi yace “Na baka! Bbu ko sisin ka kuma” Kallon mamaki duk occupant din fadan ke ma mai martaba don baya magana biyu. El-ameen da ya rasa wani irin godiya xai ma mai martaba ya mike ya isa gabansa ya durkusa yana kallonsa, shafa kansa mai martaba yayi yace “You are blessed in’sha Allah son” kama hannunsa El-ameen yayi ya lumshe idonsa da ya kada ya kai lips dinsa, junaid ya lumshe idonsa da ya kada shi ma lokaci daya yana jin xuciyarsa kamar ba tasa ba.

Haske writers association????
Toh ga Captain Ahmad Junaid yayi gaba har ya kusa end Tnx for everything. My novel inteesar if am not mistaken yana da pages kusan dari biyu, my novel ikram had a hundred nd 15 pages or so, my novel Aneesah had 112 if am not mistaken, Dr Khaleel had 120 pages also, ‘ya mace kyautar Allah na goni also have the same, kuma duk an san bbu ma banxa a novels din nan, I don’t write anyhow may be just once in a year, but idan nayi i will alwayz make sure it makes sense, am just in page 54 a Capt Ajay kuma nasan nan gaba xai kai har 120 ne but see what my fans are saying, you never judge a book by it cover, and am not in a haste while writing my books, ban taba novel da na dakata for weeks ba sai capt a jay, toh kullum xan dinga xuwa media ina announcement mahaifiyata bata da lafiya, ina ma nake da nutsuwar rubutu uwa ta ba lafiya yanxu haka ma bata kasar, ga kuma karatu da nake, i can’t be coming to media and giving excuses everyday, all the same am grown up yanxu I won’t retaliate but nagode kwarai Allah bar xumunci. in ma jan labarin nayi you don’t have to be giving me hurt words, sai ka bar karantawa ka jira in kai inda kake so sai ka ci gaba Meye a ciki. Duk Allah ya baku hakuri.
[3/19, 9:36 PM] El-hajj????: Captain Ahmad Junaid
By Khaleesat Haiydar
79
Da sauri ta sauka ta bi bayansa, junaid ya bi ta da kallo har lokacin xuciyarsa bai bar bugawa ba, da kamar ya koma part din Abdul sai kuma kawai ya bi bayanta, ji yayi gaba daya yaji haushin kansa, ya ja tsaki ya ci gaba da tafiya kamar bai son yi, tsaye Zahrah taga El-ameen da wasu dogarawa suna hira, ta kasa karasawa gun, juyawa yayi suna hada ido ya sakar mata murmushi, kasa mayar masa tayi, yace “ban san hanya ba, I’ve to wait for you…..” Karasowa tayi da kyar ba tare da ta ce komai ba ta ci gaba da tafiya, bai bari suka hada ido da junaid dake tahowa ba ya daga ma dogarawan hannu ya bi bayanta, tafiya kawai take amma ji take kamar xata harde ta fadi kasa, duk yana lura da ita hakan yasa ya karasa suka jera da ita yace “Masarautan nan naku da girma sosai” ta gefen ido ta kallesa tace “Yyeah!” Rasa abun cewa yayi shi ma can kuma yace “But kin gama sec sch kuwa?” Shiru tayi sai kuma ta gyada masa kai tace “Ehh!” Yace “Dat’s good” junaid dai na biye da su a baya, wata hanya daban ta dauka suka haura bene sannan ta bude wata babban kofa ta juya tana kallonsu, suna hada ido da El-ameen ta sauke idonta kasa ta ci gaba da tafiya, tsarin gun kamar na Kilishi da suka baro, babu kowa babban parlon sai jakadiya da wata me goge goge, Ta nuna masu kujera, jakadiya ta bi ta da kirari kafin tayi masu sannu da xuwa, El-ameen ne kadai ya amsa mata yana murmushi, Bedroom din Umma Zahrah ta nufa ba a dau lokaci ba sai ga ta sun fito da Umman, murmushi ne shimfide fuskarta har ta karaso parlon tana kallonsu gaba daya tace “Sannun ku da xuwa….” Sakkowa El-ameen yayi har kasa Junaid ya bi sa da ido kafin shima yayi kasa da kansa ya sauka, suka gaisheta gaba daya, tana murmushi har lokacin ta amsa, tuni jakadiya ta cike gabansu da kayan marmari da shaye shaye, Umma tace “To waye Ahmad waye takwaran mai martaba” El-ameen yayi murmushi yace “Ni ne El-ameen….” Ta kalli junaid cikin sanyin murya tace “Kai ne Ahmad kenan” kai ya gyada mata ba tare da ya dago ba, a sanyaye tace “Allah ya albarkaci rayuwar ku, yasa ku gama da iyayen ku da duniya lafiya…..” El-ameen yayi saurin cewa “Ameen Umma mun gode” Umma ta kalli Zahrah tace “Kin kai su gun Kilishi?” Ta gyada kai tace “Can muka fara xuwa” Umma tace “To Maa sha Allah” ba su wani dade part din Umma ba ta dalilin bakin da tayi, Zahrah ta nufi fada gun Abbanta da su, sai dai wannan karan sauri kawai take bata bari sun jera da El-ameen din ba, bai takurata ba ya jira junaid, junaid na isa gunsa yace “ya kuma ku ka raba tafiyar?” Murmushi yyi yace “Yea hakan yafi don ni ba runguma bane iyakar abinda zan mata idan na kasa jure shariyarta gare ni” Wani kallo Junaid ke yi masa kafin yace komai El-ameen yayi dariya yayi gaba ya bar sa nan, suna shiga fada ta juya ta bar su tare da Abbanta. Da rana Umma ta takurata ta kai masu lunch tace ai masu aiki xa su kai masu, Mikewa tayi d’aga karshe dai ta fita nemo Ummi ta rakata. Sae da suka fara xuwa kitchen don tabbatar da cewar an kai abincin taga an kai, fura ta tarar ana damawa kitchen din, ta dau babban jug ta diba snn ta dau tray ta daura kai da cups ta fita tare da Ummi, suna isa part din Abdul Ummi ce ta fara shiga da sallama kafin ita, Junaid ne kwance parlon yana danna waya, yayi masu kallo daya ya dauke kai, Ummi ta xauna tana kallonsa ta gaishesa ya amsa ba tare da ya kalleta ba, Ajiye trayn hannunta Zahrah tayi ta nufi bedroom ba tare da ta kallesa ba, El-ameen ta gani da Abdul suna kallo ga cake gabansu, El-ameen ya buda ido murya can kasa yace “princess!” Tace “Uhm, kun yi lunch?” Hararata Abdul yayi yace “Basu yi ba” ‘yar dariya tayi ta kalli El-ameen dake kallonta, can ta karasa ciki ta xauna kusa da Abdul ta kai bakinta kusa da kunnensa kamar me rada tace “Why is he alone?” Abdul ya kalleta yace “Ahmad?” Satan kallon El-ameen tayi sai kuma ta dauke kai da sauri, Abdul yace “He said he’s more comfortable there” da sauri tace “Alryt, ohk” sai kuma ta kalli El-ameen tace “Ga fura na kawo maku fa” ba tare da ya kalleta ba yace “Toh mun gode” mikewa tayi ta fita daga bedroom din, xaune ta samu Ummi har lokacin idonta na kan Junaid, “ki tashi mu je” ta fadi haka bayan ta dauke kai daga kallonta, shi dai idonsa na kan waya, Ummi ta mike tace “Ohk furan xa a xuba masu ne?” Da sauri Zahrah tace “Noo!” Sai kuma ta nufi tray din da ta dire daga gefensa ta durkusa ta dau cups din ta xuba furan ciki ta ajiye tana kallonsa fuskarta daure, kara wayarsa yayi a kunne ya mike xaune ya sakko da fararen kafafuwansa kasa kamar wanda aka tilasta yayi magana yace “kina ji na?” Kasa daina kallonsa Zahrah tayi, ya shafa kansa yace “Have you eaten?” Shiru ya d’an yi kafin yace “Ki dai daure ki ci, I will call back later” daga haka ya katse kiran ya ajiye wayar lokaci daya ya sauke idonsa kan Zahrah dake kallonsa har lokacin, da sauri ta dauke Kai ta mike ta nufi kofa ta fice, har dare bata kuma komawa part din Abdul ba, duk ta rasa me ke mata dadi mugun haushin Junaid kawai take ji, har shi xae nuna mata ji da kai? mikewa tayi daga karshe ta fice ta nufi bangaren Abdul, El-ameen da Junaid ne parlon wannan karan, kmr daxu kwance Junaid yake waya na kare a kunnensa, Bata ko kalli inda yake ba ta karasa gun El-ameen dake kallon wani movie ta xauna kusa da shi tayi fari da ido tace “Are you okay? Bbu damuwa koh” Yana kallonta yace “Yea, am just missing home” murmushi tayi tace “Nan ma fa gida ne” yace “Yeah haka ne” ta mike tace “Ina son ka rakani mu je garden” yace “Really?” Ta gyada masa kai tace “Yeah, I want you to keep me company” mikewa yayi yace “Alryt mu je,” duk da wayar da ke kare kunnen junaid gaba daya ya mance waya yake, ba kallon direction dinsu yake ba amma gaba daya hankalinsa na kansu, kofa ta nufa El-ameen ya kalli junaid da yayi saurin dafa wayar kunnensa yace “Will be ryt back” ko kallonsa Junaid bai yi ba har ya fita, ya mike xaune, ji yayi xuciyarsa na tafarfasa kawai, ya kusa minti ashirin xaune har Abdul ya shigo, ko da ya tambayesa El-ameen cewa yayi bai sani ba, yana shiga bedroom ya mike ya fice daga part din gaba daya, ji yayi da ma safiya ce ko rana da babu abinda xai hanasa komawa katsina duk da sarki ne ya tsaida su amma da tuni sun tafi da yamma, can wani waje da bbu hayaniya kuma babu wani haske ya samu ya xauna, har sha biyun dare bai da niyar tashi ya shiga ciki, gaba daya El-ameen yayi tunanin wucewa junaid yayi don yasan halinsa barin ma Atm card dinsa na jikinsa, Abdul da mamaki ya cikasa yace “Why is he acting that way?” El-ameen yace “That’s he’s hobby” Abdul bai san lokacin da ya fashe da dariya ba, El-ameen yace “Yeah, an only son, mumy’s pet” Zahrah dake tsaye ta tabe baki ta juya ta fita daga parlon sai dai duk jikinta yayi sanyi, kasa komawa part dinta tayi hakan yasa ta bi hanyar da tasan baxa a ganta ba ta fita waje, tafiya kawai take ba don tasan ina ma xata ba kuma meye ta fito yi, bata yi wani nisa da tafiyan ba tayi ido hudu da shi har lokacin yana xaune ya xuba ma taurari ido kamar me kirgan su, rasa abinda xata yi tayi a lokacin, ci gaba da tafiya xata yi ko juyawa xata yi ta koma, Dakewa tayi ta tsaya inda take, can ta karaso fuskar nan nata daure tana kallonsa tace “Don me xaka wani fito nan cikin dare ka ba mutum wahalan nemanka when I am suppose to be in bed” wani kallo ya watsa mata ta gefen ido ya ci gaba da kallon sky abun sa, fixge wayar hannunsa tayi tace “Malam magana nake maka fah?” Sai a sannan ya kuma kallonta suka yi ido hudu gabanta ne ya fadi sosai, ya mike ya warce wayarsa yace “Gadina aka baki ne?” Wani kallo tayi masa tace “Ehh sbda ta dalilina ka xo garin nan…..” Shiru tayi sai kuma ta turo Baki tace “I still can’t believe ma kai ka tsince ni, or are you angry don bance kayi accompanying dina bane” murmushi yayi yace “How will you believe it, tunda ba sani kika yi ba lokacin da kike xuwa in bude maki Zip, in raka ki toilet, kike xuwa bedroom dina daure da towel….. Infact har lokacin da nake taimaka maki idan kina menses…..” Xaro ido tayi, tayi wani kara tace “Nooo….” Ya gyada kai yace “Yesss! Har lokacin da……” juyawa tayi da gudu ta bar gun, bai san lokacin da ya fara dariya ba har da xama. Washegari kasa fitowa Zahrah tayi, kenan idan haka ne kila har nakedness dinta ya taba gani, har da kukanta da tayi wnn tunanin, sai da Umma ta bata rai sannan ta mike ta fita xuwa gaida su da safen, hijab tasa tsabar bata jin xata iya kallon junaid, tana shiga parlon ko ta gansa shi kadai xaune yana shan tea, kin dago kanta tayi ta kuma kasa karasawa can bedroom, kallonta kawai yake yana kokarin boye murmushin fuskarsa, juyawa tayi xata fita ya mike tana ganin haka ta kwasa da gudu, wani dariya ya taho masa bai san lokacin da ya fashe da dariyar ba, Abdul da El-ameen suka fito da sauri, buda baki Abdul yayi ganin ashe yana iya dariya haka, El-ameen kam karyar da kai yayi ya rungume hannu yana jinjina abinda ya ba junaid dariya haka, da kyar ya tsaida dariyar ya daga kai yana kallonsu, Abdul yayi murmushi yace “Ohh that’s more beautiful of you captain” El-ameen ya tabe baki yace “Ko xa mu iya sanin abinda ya baka dariya haka Ahmad, na tabbata mu sai mun yi fiye da wanda kayi” shafa kai junaid yayi yana murmushi yace “Bana son ku haukace da dariyar just let it” El-ameen ya daga kafada yace “Lallai kam” daga haka ya juya ya koma dakin, Abdul ya karasa ya xauna gefensa yace “Gist me more about ur self captain….” Murmushi junaid yayi yana kallonsa. Karfe sha daya junaid ya gaji da xama don Abdul da El-ameen sun fita, bbu kuma yanda basu yi da shi ya bi su ba yace A’a baxae je ba, suka yi tafiyarsu suka barsa, dama bayan azahar xasu gana da wasu yan uwan mai martaba kafin su kama hanyar kt ranan, mikewa yayi ya fita yana rike da wayarsa, tafiya sosai yayi ya ga wani waje kamar gun shakatawa ga tsuntsaye sai shawagi suke, carpet grass ne shimfide gun, shiga yayi ta wani babban kofa ya dinga tafiya yana bin ko ina na wajen da kallo, wasu kuyangu guda uku ya gani suna tahowa ya bi su da kallo kafin yace “Ana shigowa nan kuwa” a tare suka gyada masa kai, daya daga cikinsu tace “Sai dai Gimbiya na nan ita ma!” Yace “Wace gimbiyar?” Tace “Gimbiya Zahrah” bai ce komai ba yayi gaba abunsa, xaune take ita kadai tana kallon cartoon da laptop din dake ajiye gabanta ta xauna kan kafafuwanta, gefenta kuma bowl ne me dauke da kayan itatuwa, juyawa tayi jin taku bayanta, suna hada ido ta mike da sauri har tana ball da bowl din fruits din gabanta, ta kuma juyawa da shirin gudu tayi karo da laptop dake ajiye, tsallakesa tayi ta bi wani hanyar da gudu, bin ta yayi da kallo kafin ya tabe baki ya xauna ya daga laptop din, ya dau apple daya ya shiga ci ya canxa cartoon din xuwa something meaningful yana kallo yana murmushi. Da yamma misalin hudu da wani abu junaid da El-ameen ne xaune a fadar me martaba dake dauke da mutane da dama tun daga waziri, advisern sarki har xuwa kasa, sannan ga ‘yan uwansa da abokan arxiki, kanninsa mata da maza, Abdul na xaune daga gefen Abbansa, Ummi na xaune daga daya bangaren sa, Umma da Kilishi ma duk suna fadan xaune, Zahrah ce karshen shigowa ta nufi gun Ummanta ta xauna gefenta, kallon Junaid kawai sarki yake, can kuma sai ya kalli El-ameen, bayan kusan minti biyu na silence sarki yayi gyaran murya yace “Ahmad!” Dago kai junaid yayi yana kallonsa, Sarki yace “Nasan ba lallai in iya biyan ka abinda ka min ba amma ka fadi duk abinda kake so nan duniya in dai bai saba ma shari’a ba nayi maka alkawarin yi ma shi idan Allah ya yarda,” shiru junaid yayi, can ya dago ya kalli Zahrah da idonta ke kansa suna hada ido ta dauke kai, kallon El-ameen yayi yaga wani gu daban yake kallo, can ya girgixa Kai yace “Bana bukatan komai mai martaba, I helped her for Allah’s own sake” kallonsa kawai Sarki ke yi, can ya sauke ajiyar xuciya yace “Toh shknn, Allah ya albarkaci rayuwar ka Ahmad” cikin sanyin murya junaid yace Ameen, sarki yayi murmushi ya juya yana kallon El-ameen yace “Kai fa takwara na?” Kallon junaid El-ameen yayi suka hada ido junaid ya sauke kansa kasa, Zahrah ma idonta na kan El-ameen gabanta na faduwa, haka kawai junaid ma ya ji gabansa na faduwa, bayan kusan second ashirin El-ameen yace “Ina son ka min alfarmar bani aurenta, na kuma yi maka alkawarin xan rike ta da amana….” Wani mugun bugu xuciyar junaid yayi, Zahrah kam kallon El-ameen take ko kiftawa babu, Mai martaba da ya kafa ma El-ameen ido shi ma yayi murmushi yace “Na baka! Xan kuma biya maka sadaki” kallon mamaki duk occupant din palace din ke ma sarki sanin baya magana biyu, El-ameen da ya rasa wani irin godiya xai ma mai martaba ya mike ya isa gabansa ya durkusa yana kallonsa, shafa kansa mai martaba yayi yace “You are blessed in’sha Allah son” El-ameen ya kama hannunsa ya lumshe ido ya kai lips dinsa, mikewa Zahrah tayi hawaye cike idonta ta kalli junaid da yaki dago kai har lokacin tayi ficewarta daga fadan.
Haske Writers association

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button