CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

[3/19, 9:36 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

80……

Ko k’adan Junaid bai kuma gane abubuwan da sarki ke cewa ba a wajen gashi bai yarda ya dago kai ba, mikewar da El-ameen yayi ya sa shi mikewa shi ma, kiran sunansa da ya ji anyi ya sa shi juyawa yaga sarki ne ya kirasa, sarki na kallonsa yace “Allah ya tsare hanya, ina kuma sauraron xuwar kakar ka” da kyar ya iya amsa masa yana kirkirar murmushi sannan ya juya ya fita, tun a hanya ya dake yayi patting shoulder din El-ameen yana murmushin karfin hali yace “Congrat frnd!” Kasa ce masa komai El-ameen yayi yana kallonsa, suna isa part din Abdul junaid bai ko kalli kayayyakin sawan da Abdul ya jido masu a boutique jiya ba, atm dinsa ya dauka da waya xai fita, wani abokin Abdul yace “Baxa ka canxa kaya ba Captain, Abdul din da xai kai ku airport ma bai gama shiri ba” cike da karfin hali junaid yace “Yeah, ina waje nan….” Daga haka ya nufi door, El-ameen dake tsaye ya bi sa da ido, a hanya Junaid ya hadu da Abdul, Abdul yace “A’a ina xa ka captain” junaid ya kirkiri murmushi yace “Ina jiran ku a waje” hannunsa Abdul ya kama yace “Noo baka isa ba, sai ka sake wanka ka canxa kaya” duk yanda Junaid ya so Abdul ya kyalesa kin saurarensa yayi har sai da ya mayar da shi part dinsa, dole yayi wanka ya canxa kaya, duk suka shirya, Abdul ya tafi da su xuwa gun Mum dinsa suka yi mata sallama ta hadasu da turarruka masu tsadan gaske, sannan ya kai su part din Umma, ita kadai ce xaune parlor da jakadiyarta, tana ganinsu ta saki fuska nan suka yi mata sallama ta dinga sa masu albarka, shi dai Junaid kansa na kasa, tsaraba sosai ta hada masu su biyun su kai ma Mum dinsu, El-ameen yayi mata godiya, shi ma junaid da kansa ke kasa yayi godiyar, Abdul yace “Umma ina Zahrahn fah?” Umma tace “Ina jin bacci take” mikewa yayi ya nufi bedroom din Umma, Umma ta bi sa da kallo har ya shiga, kwance ya sameta cikin bargo Ummi na xaune gefenta tayi tagumi, Abdul ya karasa da sauri yace “What’s wrong with her” a hankali Ummi tace “She’s just crying, me yasa Abba xai yi mata haka…. In ma haka ne ba sai ya basu kudi me yawa ba, ina jinin sarauta da auren…..” Wani kallo ya watsa mata ya cire bargon yana kallon Zahrah, mikewa xaune tayi ta fashe da kuka tana kallonsa, ya xauna yace “Look ki hadiye kukan nan ki min magana, aurensa ne baki so?” Shiru tayi bata ce komai ba sai hawaye, yace “Ki min magana mana” girgixa kai tayi a hankali tace “A’a….” Yace “Baki son auren?” Tana goge fuskarta tace “Ni baxan iya cewa bana so ba, they helped me and….” Ya mike yace “Good you know that! Kina hauka ma duk sun xauna da ke da amana bare aure, yarima kamar ki kike so ko wa?” Girgixa kai tayi yace “to yanxu tashi ki wanke fuska ki taho kuyi sallama da su” mikewa tayi da kyar tayi yanda yace mata ta daura alkyabbarta ta rufe kusan rabin fuskarta ta bi sa suka fita tare da Ummi, sosai Umma taji dadin ganin ta fito don bata yi tunanin xata fito ba a yanda ta dinga kuka, har mota ta rakasu Ummi na rike da hannunta, shi dai Junaid yana gaba sai dai yayi murmushi idan aka ce wani abu, Ummi tace “Ya Abdul mu raka ka airport din plss?” Yace “Alryt mu je” front seat junaid ya bude ya shiga, El-ameen ya koma baya Ummi ta shiga sannan Zahrah, Abdul da Ummi kadai ke hira a motar, daga Zahrah, Junaid har El-ameen bbu me cewa komai, a hankali ta daga alkyabbar fuskarta suka yi ido hudu da Junaid don kallonta yake ta madubi, ta sauke idonta da sauri, suna isa airport junaid ya fita sannan El-ameen, Ummi ma ta sauka, sai da Abdul ya fita sannan Zahrah ma ta fito, karasawa El-ameen yayi kusa da Zahrah ya mika mata wani disc din hannunsa, ta daga kai tana kallonsa, sai kuma ta karba, kallo daya junaid yayi masu ya fara tafiya, Abdul ya bi bayansa haka ma Ummi, da kyar Zahrah tace “What’s this?” Ya rungume hannayensa yace “Throw back! That period I do call you jewel, while captain call you Jasmine,” ganin kallon da take masa na rashin fahimta yayi murmushi yace “Rayuwar ki na kwanakin baya ne….. Watch it.. You might like it” shiru tayi tana kallonsa, ya gyada mata kai assuringly, a hankali ta sauke kanta kasa yace “Let go” ba musu ta bi bayansa tana jujjuya disc din hannunta, xaune suka tarda su junaid, ta xauna gefen Ummi, El-ameen kuma ya tsaya suna jiran a kira su, lokaci lokaci ta kan juya ta kalli junaid kuma duk kallon da xata yi masa sai sun hada ido alamar shi ma kallon nata yake, can dai ya mike yace ma Abdul xai siyo ruwa ya bar wajen, bai kuma dawo ba sai da aka fara announcing jirginsu ne next din tashi, hannu kawai ya daga ma su Abdul ya shiga tafiyarsa, bin sa da ido Zahrah tayi, can ta kalli El-ameen dake kallonta ta d’aga masa hannu ta juya da sauri ta bar gun. Har suka sauka kt bbu wanda yace komai tsakanin junaid da El-ameen, taxi El-ameen ya tsayar masu ya kallesa alamar ya shiga, a karo na farko junaid yayi magana yace “Ae tafiyar mu ba daya bace, ka tafi xan samu wani” kallonsa kawai El-ameen yake can kuma ya shiga taxin da kayan tsarabarsu ya fadi ma driver din inda xa shi drivern ya ja motar suka bar junaid tsaye, kalle kallen inda zai xauna ta dalilin jirin da yake gani junaid ya shiga yi, can ya samu dakali ya xauna ya rike kansa, ya kusa minti goma xaune kafin ya mike da kyar daga karshe ya samu wani taxin ya shiga. Biyar saura ya shiga gida har lokacin yana ganin jiri, part din Mumy ya nufa, bbu kowa parlon ya shiga bedroom dinta, xaune ya sameta Hisnul Muslim a hannunta, kallonsa ta shiga yi har ya karaso gabanta ya durkusa ya daura kansa kan kafarta, ita dai kallonsa kawai take, dumin da taji a kafarta ya sa ta dago kansa tana kallo, hawaye ta gani fuskarsa, da mamaki tace “Me ya faru?” Kasa ce mata komai yayi sai hawaye, nan da nan hankalinta ya tashi tace “Ahmad!” Mayar da kansa yayi kafarta ta sauko kasa hankalinta ya tashi sosai tace “Talk to me son, me ya faru” rasa abun da xai ce mata yayi kawai ya rungumeta cikin sanyayyan muryarsa yace “Nothing mum, just forgive me plss” ji tayi hankalinta ya kwanta, a sanyaye tace “I’ve done that since son” a hankali ya xame jikinsa kansa a kasa yace “Nagode mum” daga haka ya mike ya fita daga dakin ya koma part dinsa yana shiga ya rufe kofar yasa makulli ya hade kansa da kofar wasu sabbin hawayen na xubo masa, ya kusa minti talatin tsaye kawai kuma ya bude kofar ya fice, can gidansa ya nufa cikin a dai daita, yana sauka ya ba sa kudin sa ya shiga gidan, ya kusa minti goma tsaye parlor sannan ya haura sama, dakin da Zahrah take ya fara budewa, hular ta ne kwance kan gado da ribbon sai zaninta, gadon na nan yanda yake tun daren da ya shigo ya tada ta bayan yaji an shigo gidan, karasawa cikin dakin yayi a sanyaye ya dau hular da ribbon yana kallo, juyawa yayi yana kallon takalminta dake ajiye a kasa daga kusa da gadon, ya kalli gaban mirror dake dauke da kayan shafanta, sai Qur’aninta dake ajiye daga gefe, xaunawa yayi gefen gadon ya lumshe ido ya rike kansa da yayi masa nauyi. A can masarautan bauchi kuwa tunda Zahrah suka dawo take kuka a dakinta bayan ta kulle kanta, bbu wanda ta saurara ta bude kofar har kusan goma na dare, mikewa tayi xaune da sauri tana kallon disc din da El-ameen ya bata da ta ajiye gefenta, dauka tayi ta mike ta nufi inda laptop dinta ke ajiye ta dauka ta dawo ta xauna gefen gado ta bude ta kunna.
.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button