CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writers association????
[3/19, 9:36 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid⚓
By Khaleesat Haiydar✍????
82…..
El-ameen ya gama danne dannensa ya Kai wayar kunne bayan few seconds yace “Hello Zahrah, here is the captain” daga haka ya mika ma junaid wayar yana kallonsa, kin kallon inda yake junaid yayi, har sai da yace “Ahmad!” Sai a sannan junaid ya kallesa yace “Did I told you am sick?” El-ameen yace “Yeah! I know you are okay, but karbi wayar….” Wani kallo junaid ke yi masa kafin ya karbi wayar ya kai kunne, gabansa ya fadi sosai jin muryarta da ya daki ear dinsa tace “Hello!” Dakewa yayi yace “Yeah, ina ji” shiru tayi shi ma haka, bayan kusan second ashirin ya kalli screen din wayar ya ga ba a kashe ba, mayarwa yayi kunnensa ya hade rai yace “Hello!” Tace “Yeah! Ina ji nima” tsaki ya ja ya katse wayar ya jefar kan gado ya juya yana kallon El-ameen yace “Kaga ka bar ja min raini gun yarinyar nan plss, ku je can ku karata ka daina sako ni a abun ku….” Murmushi El-ameen yayi yace “Alryt…. Yanxu dai bari in sa maka ruwan nan in maka allura am leaving” a fusace junaid yace “Wai ca nayi maka bani da lafiya ne, let me plss” mikewa yayi ya shige toilet ya kulle ya hade kansa da kofa, Murmushi El-ameen yayi ya fita ba a dau lokaci ba ya dawo tare da Mumy, tana kallon kofar toilet din tace “Ahmad!” Sai da ta kuma kiransa sannan ya amsa a hankali, strictly tace “Come out” ba musu ya fito jiki ba kwari ya karasa kan gadon, Mumy na tsaye El-ameen ya sa masa drip din sai a snn ta juya ta fita, El-ameen yayi ‘yar dariya yace “Gaskiya ne Mumy’s boy” ko kallonsa Junaid bai yi ba ya koma ya kwanta kan gado, El-ameen ya dau makullin motarsa da waya ya fita, lumshe ido Junaid yayi xuciyarsa na bugawa, bayan minti goma da fitar El-ameen aka bude kofar dakin, Humainah ce ta shigo ya bude ido yana kallonta, karasowa tayi kusa da gadon ta durkusa tana kallonsa tace “Baka da lafiya ne?” Chin dinta ya dago yana kallon fuskarta yace “How are you feeling now” a hankali tace “Alhmdllh” yace “Kina cin abinci yanxu?” Girgixa masa kai tayi ta kwantar da kanta kan gado har lokacin tana kallonsa tace “Only tea” gefensa ya nuna mata, ba musu ta mike ta dawo kusa da shi, ya daura hannu kan tummy dinta yace “Ya babyn?” Hannu ta buda masa alamar bata sani ba, yayi murmushi tayi kwanciyarta gefensa, komawa yayi shi ma ya kwanta tare da lumshe ido. Sha daya saura aka buda kofar dakin Hajjo ta shigo, fashe wa da kuka tayi sosai ta karaso kusa da gadon tace “Ya baxa ka kwanta ciwo ba ka yaudare ni ka ci amanata Ahmad, har ni xaka dinga ma bakin ciki, to dadin abun dai ni ba talaka bace, kuma dukiya me uban yawa mijina ya mutu ya bar min wanda ko da xanje makka sau dari baxa su girgixa ba, ku abun duniya ya tsole ma ido kai da uban ka” tana kai wa nan ta nufi kofa fuu, junaid ya bita da kallo har ta fita, Humainah kam murmushi tayi ta koma ta kwanta. Da yamma junaid na kwance duk ya rasa me ke masa dadi so yake kawai ruwan ya kare ya cire ya fita daga gidan ko xai ji dadi, ba don Mumy ba da tuni ya tuge drip din, Humainah na kwance nesa da shi tayi bacci tun daxu, bude kofa aka yi El-ameen da Aliyu suka shigo dakin, kallonsu kawai yake Aliyu ya karaso shi ma yana kallonsa yace “Baka ji dadi ba ashe” junaid bai ce komai ba, Aliyu ya kara da cewa Allah ya sauwake” sai a sannan yace “Ameen thank you” El-ameen yace “My frnd Dr Aliyu hope ka gane sa” Junaid bai ce komai ba ya nuna ma Aliyu kujera ya xauna, Aliyu yace “Am ohk here” El-ameen yace “How are you feeling now Ahmad?” Dakewa junaid yyi yace “Naji sauki ka cire min ynxu” El-ameen yace “No! Sai ya kare, am coming back later” Junaid ji yayi kamar ya shakesa sai dai bai ce komai ba, El-ameen yace “Idan kaji sauki in shaa Allah xuwa gobe xa ka rakani bauchi, sarki na nemana” duk da faduwar da gaban junaid yayi bai nuna ba yace “baxan iya barin aikina in je bauchi ba” El-ameen yace “Alryt, Aliyu sai ya rakani,” daga haka ya juya ya nufi kofa yace “Sai na dawo ltr” ba tare da Aliyu ya kuma kallon Junaid ba yace “Allah ya kara afuwa” daga haka ya fita shi ma, mikewa xaune junaid yayi ya dafa kansa. A can bauchi kuwa Zahrah duk ta daga ma mahaifanta hankali ita fa sai an kai ta gun dattijuwar matar nan duk inda take, da farko lallabata mai martaba ya dinga yi yace ta bari xa a nemo matar a kawo ta masarautan ganin ba hakura zata yi ba yasa yace a kira masa El-ameen. Washegari El-ameen ya dau hanyar bauchi tare da Aliyu, haka kawai yaji gabansa na faduwa, addu’a ya dinga yi a xuciyarsa Allah yasa ba fasa basa auren mai martaba yyi ba, Aliyu dai sai dariya yake masa yace “Ana xaune kalau xaka jajibo ma kanka aure, auren ma daga gidan sarauta…. Tab xaka sha takaici kuwa” murmushi El-ameen yayi yace “Can xa a sha takaici ba ni ba” Aliyu yace “Ni dai don kawai ina son ganin babe din ne shi yasa xan bi ka amma bbu ruwana da neman aurenka, ni bayan Hafsat nake” El-ameen bai tanka sa ba ya kuma cewa “Toh wai yasan kana da mata kuwa?” Gyada kai El-ameen yayi yace “Yeah, I told him everything” Aliyu ya xaro ido lkci daya ya fara dariya yace “Ni i thought gidan sarauta basa bada ‘ya yansu wa mai mata, Toh did your parent know about this?” El-ameen ya masa wani kallo yace “Yeah i told my dad, nd stop dusturbing me plss” Aliyu yace “Toh me yace?” El-ameen bai sake tanka sa ba har suka isa bauchi, sun jima hotel din da suka yi lodge kafin su tafi can masarautan don Aliyu yace baxai sauka gidan mutane ba, babu bata lokaci aka gabatar da su gaban mai martaba, El-ameen dai har lokacin gabansa bai bar dukan uku uku ba, duk ya kagu yaji kiran me sarki yayi masa, bayan gaisuwa sarki yace “Ina Ahmad din?” El-ameen yace “Ba tare muka taho ba, baya jin dadi” Sarki yayi masa addu’ar samun sauki, bayan few seconds yayi gyaran murya yace “Al-ameen!” Kallonsa El-ameen yayi ya kasa amsawa, Sarki ya ci gaba da cewa “Na yarda da kai na aminta da kai yasa xan hada ka da Zahrah da yar uwarta ka kai su duk inda matar nan me kula da ita take, kwana biyu kacal xasu yi a katsina idan ka tashi dawo da su kuma har da dattijuwar nan xa ku dawo” wani boyayyen ajiyar xuciya El-ameen ya sauke a hankali yace “In’sha Allah ran ka shi dade….” Daga haka ya sallamesu suka bar fadan, Wazirin sarki dake fadan yace “Is this a good decision kuwa, in suka sauka katsinan ina xai ajiye su, its not safe tafiyar su su kadai, i think gwara Abdul ya bi su” Sarki yayi murmushi yace “Da tuni sun cutar min da Zahrah” Aliyu sai dariya yake bayan sun fita yace “Tun ba ayi aure ba ka fara xama masinja, anya abun nan xai yiwu kuwa Dr….” Murmushi El-ameen yayi yace “Xa dai su xama masinja can…” Washegari da safe suka kuma daukar hanyar kt tare da Zahrah da Ummi, Zahrah dai sai kallon Aliyu take lkci lkci a jirgi, yana lura da haka can dai yace “Ya dai ‘yan mata da kallo haka?” Tabe baki tayi tace “Just that you look familiar, nothing else….” Ya wara ido yace “Really? A ina kika san ni toh?” Shiru tayi kafin tace “I think… Ohk sorry it might be a dream” yana gyada Kai yace “That’s woaw, a ina kika gan ni a dream din?” Kallon El-ameen dake ta kallonsu tayi tace “Wani waje, I think it’s a garden… Ohh I really can’t remember, yes a garden…” murmushi sosai Aliyu yayi yana gyada kai yace “It’s a pleasure meeting u in dream land” bata kuma tanka sa ba ta dauke kai. Suna sauka kt El-ameen ya tare masu taxi, sun dau hanya Zahrah tace “Ina xa mu yanxu?” Kallonta yayi yace “My home, Hafsat will be glad to see you” girgixa kai tayi tace “Noo! Kai ni gun Granny din Ahmad Junaid” kallonta El-ameen ya tsaya yi, can ya lumshe ido yace “Ohk, Alryt” daga haka ya fadi ma me taxin inda xai kai su, Aliyu yace “Bari in sauka nan, kar ya rainani idan ya sake ganina gidansu” murmushi kawai El-ameen yayi yasa mai taxin yayi parking Aliyu ya sauka, El-ameen yace “Thanks frnd sai mun yi waya” d’aga ma Zahrah da Ummi hannu Aliyu yayi ya bar wajen. Suna isa kofar gidansu Junaid El-ameen ya fara fitowa sannan Ummi da Zahrah, ya ba mai taxin kudi ya kallesu yayi murmushi yace “Mu je” bin bayansa suka yi ya nufi gate. Part din Hajja ya nufa da su, khadija ce kwance parlon da Rahma mikewa xaune suka yi gaba daya suna kallonsu barin Khadija dake ta kallon Zahrah, El-ameen yace “Hajja fah?” Rahma xata yi magana sai ga Hajja ta fito cike da masifa jin muryar El-ameen, sororo ta tsaya tana kallon Zahrah, El-ameen yace “Kin yi bakuwa Hajja…” Wani shewa tayi ta karaso ta rungumeta tace “Ikon Allah, dama idan Allah ya so ka da arxiki duk nacin mahassadi sai dai ya mutu don sai kayi arxikin nan, sannu yar sarki jikar sarki, kiri kiri suka gudu suka bar ni sai gashi kin xo daukata…” El-ameen yayi murmushi ya nuna ma Ummi dake ta kallon ikon Allah kujera ta xauna, ya kalli Zahrah yace “Xan dawo da dare” daga haka ya fice daga parlon, Hajja ta rasa inda xata sa Zahrah da yar uwarta kawo wancan kawo wannan duk ta cikasu da kayan ciye ciye, Su khadija suka xama ‘yan kallo, hannun Zahrah ta kama daga karshe tace “Mu je ki gaida Amina ita daya ce mata a gidan yanxu, kinsan sauran duk nasa an mayar da su gida, sbda jikokina da suka sa ma ido barin Ahmad” Ita dai Zahrah bin ta kawai take har suka shigo parlon Mumy, nan gabanta ya shiga faduwa, Fatima ce ke shara a parlon, Hajja tace “Ke ina uwar ki?” Fatima na kallon Zahrah tace “yanxu ta fita kasuwa….” Hajja tace “Toh dama wa xai aike ku ya sha takaici duk baku da amfani ai, Ahmad din na ciki har yanxu?” Girgixa kai fatima tayi tace “Yana bangaren sa” kama hannun Zahrah Hajja ta kuma yi suka fita tana cewa “Mu je ki gaida sa ba lafiya, kinsan Allah baya kyale ma ci amana da mai bakin ciki…. Toh abinda ya samu Amadi kenan” d’an murmushi Zahrah tayi duk da bata gane inda xancen Hajja ya dosa ba, bbu kowa parlon junaid haka yasa ta kuma jan ta har bedroom, ita dai gabanta ya ki daina faduwa tana biye da ita, yana xaune gefen gado idonsa na kan abinda Humainah take, sanye yake da 3qtr da singlet fari, kana ganinsa kasan har lokacin he’s not his self, Humainah kuma na durkushe gabansa tana xuba masa pepper soup din kayan ciki da Mumy tayi masa, juyawa suka yi gaba daya suna kallon bakin kofar, Hajja ta washe baki tace “Amadiii….” Kallon mamaki kawai yake ma Zahrah ko kiftawa babu gani yake kamar mafarki yake, ita kanta kallonsa take ta kasa karasowa, Hajja ta janyo ta hakan yasa ta saurin dauke kai daga kallonsa Hajja tace “Mai martaba ne ya turo ta ta gaisheni….” Humainah da tayi ma Zahrah kallo daya bata kuma dago kanta ba, xuba pepper soup din kawai take ba tare da tasan abinda take ba ga wani bugu da xuciyarta yake, Can ta mike bayan ta rufe kulan xata fita Hajja ta fixgota tace “Keee baxa ku gaisa ba, me sunata kenan fatima, ita ce wanda yayanki ya ceci rayuwarta tana ganiyar hauka, baki ganeta bne…” Humainah da xuciyarta ke bugawa har lokacin ta kalli Zahrah a karo na biyu, ita kanta Zahrah kallonta take, Hajja ta kalli Zahrah tace “Kin ga matarsa kenan, ita ma jikata ce, na ma fi sonta a kan sa wllh, xan iya komai a kanta, sunanta Humainah” kasa cewa komai Zahrah tayi, ita kanta xuciyarta bugawa yake, Da kyar dai ta bude baki tace “Sannu!” Ba karamin Dakewa Humainah tayi ba na ganin ta bata amsa tace “Yauwa!” Daga haka ta fice daga dakin, Zahrah taji duk jikinta yayi sanyi, a ranta kuwa tunani take ashe akwai warce xata fi ta kyau, kallon junaid tayi taga har lokacin idonsa na kanta, ta sunkuyar da kai da sauri, Hajja da baki ya ki rufuwa tace “Toh ki karasa ki masa sannu man, amanata ya ci Allah ya kamasa kin san gudu suka yi basu je da ni ba, daxu da asuba ina idar da sllh na daga hannu biyu nace Allah na yafe masa, kila shi yasa kika gansa a haka yanxu” murmushi Zahrah ta kirkira tana jan kafa ta karasa gaban gadon da kyar tace “Ya jikin?” Bai ce komai ba bai kuma fasa kallonta ba irin kallon da na kasa fassarawa, ji tayi kafafuwanta sun gaza daukarta, ta kasa ci gaba da kallonsa, ta durkushe wajen.