CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????

Haske Writers Association????
Captain Ahmad Junaid

  _By Khaleesat Haiydar_✍????

7…..

Fara ce sosai ba kadan ba don kamar ka latsa ta jini ya fito, dama ashe wahala ce ya maida kalanta baki, ko kadan bata da jiki sai tsayi, bakin gashin kanta ya rufe kusan rabin fuskarta sbda yanda tayi kwanciyar, d’an karamin bakinta me kalan baki da ja Junaid ya kalla yyi murmushi yace “Uhnn! Kamar me hankali koh? Da xata tashi ynxu duk sae mun yi bayani ryt?” murmushi El-ameen yyi ya mike yace “Yea! Exactly!” Juyawa yyi ya fice daga dakin Junaid ya bi sa da kallo sae gashi ya dawo da wasu alluran har uku, ya dawo gabanta ya durkusa, Junaid na ganin haka ya mike ya fita daga dakin, ya sakko palo ya dauki ledan abinci daya ya ba Mama, tayi masa godiya yyi murmushi kawae ya xauna, bayan kusan minti goma El-Ameen ya sakko falon ya xauna gefen junaid yace “Kana ji na, akwae drugs din da xa’a siya har biyar, kuma duk pack daya kusan dubu 40 ne kafin ayi diagnosing dinta….” Junaid yace “Ohk xan maka transfer ltr” El-Ameen ya mike ya dauki ledan abincin da ya rage da ruwa ya nufi sama, ajiye mata yyi bayan ya bude snn ya fito ya sa ma kofar key, ya dawo palo yana kallon Junaid yace “Let leave!” Mikewa Junaid yyi, El-Ameen ya kalli dattijuwar da ke xaune yace “Mama za mu tafi sae gobe, duk buge bugen da xata yi kar ki bude mata kofar” tace “Toh Allah ya tashe mu lfya, yayi maku albarka,” duk suka amsa da Ameen suka fita palon. A bakin gate El-Ameen ya tsaya yana kallon Junaid yace “ka ba mai gadi kudi ya siyo ma tsohuwar abinci da safe ya kai mata ciki don am not coming here da safe” Junaid ya ciro dubu uku aljihunsa ya mika ma mai gadin snn suka fita, Suna isa gun motocin su El-Ameen yace “Gobe kuma foodstuffs xaka siya idan xaka xo” Junaid bae ce komae ba ya shige motarsa ya tada ya bar wajen, El-Ameen ya bi sa da kallo yana murmushi, snn shima ya shiga tasa motar. Karfe takwas da wani abu Junaid ya isa gida, bangarensa ya nufa yyi wanka snn ya dauro alwala ya fito yyi isha yana xaune kan darduma ya ji an bude kofar palonsa, bae motsa daga inda yake ba har aka bude kofar bedroom, ya daga kai don ganin waye, Mumy ce ta shigo dakin, yayi murmushi ganinta yace “Yanxu fa xan shigo d’a Mumy” ta xauna gefen gadonsa tace “Sae ynxu kake isha Junaid?” Yace “Mun hadu da traffic ne sosae a hanya Mumy” ta tabe baki ta mike tace “Toh taso mu je ka ci abinci” ba musu ya mike ya linke pray mat din ya ajiye ya bi bayanta, Mai aikinta ce ta dauko abincin nasa daga dinning ta ajiye nan tsakiyar lallausan rug din falon da ya ke xaune, Mumy ta sakko gefensa ta bude warmern dake dauke da Shinkafa fara ta dauki plate ta dibar masa iya yanda tasan xae cinye snn ta bude miya ta xuba masa k’adan a gefe don bae fiye son miya da yawa ba, sae cow meat da ta cika masa a abincin, spoon ya dauka yace “Thanks sweet mum” snn ya fara cin abincin ita kuma ta dauki wayarta da ke ring, ganin Abba ne yasa ta nufi daki. K’asa cin abincin Junaid yyi ya kuma rasa dalilin hakan, ya lumshe ido ya jinginar da kansa jikin kujera, ya kusa minti goma a hka sanin Mumy na fitowa sae ta sa shi ya cinye abincin yasa ya kira mai aikinta, yarinyar ta taho daga dakinta da sauri, ya dauki abincin ya mika mata yace “ina fatima?” Tace “Ta kwanta” yace “Ohk tafi daki ki ci na koshi” ba musu ta koma dakinta da abincin, juice ya diba ya shiga sha a hankali, a hka Mumy ta fito ta samesa tace “Har ka cinye?” Yace “Eh Mumy” ya ajiye cup din hannunsa yana lullumshe ido yace “Nafara jin bacci mumy” tace “Toh Allah ya tashe mu lfya, kayi alwala kafin ka kwanta, don’t forget to pray also” ya mike yace “In’sha Allah mum” wayarsa ya dauka ya fita ya nufi side dinsa, sae da ya dauro alwala yyi shafa’i da wutr snn ya kwanta ya ja bargo. Washegari yana office yayi ma El-Ameen transfer din dubu dari da hamsin, yana barin office dama kasuwa ya shiga ya siyo food stuffs sannan ya wuce gidan El-Ameen, mai gadi ne ya shiga da kayan abincin palo, Junaid ya xauna bayan sun gaisa da mama yace “El-Ameen din ya xo ne mama” tace “Eh ya xo da safe, ya kuma xuwa daxu, bae dde da tafiya ba amma yace xae dawo” Junaid yace “Ohk, bacci take ne?” Mama tace “A’a gskya, sae dae yace kar a bude kofar makullin na jiki ma” Junaid yace “Tana cin abinci kuwa?” Girgixa kai tayi tace “Gskya ban sani ba don kifarwa take duka, bana gane ko ta ci ko bata ci ba” Shiru yyi bae kuma cewa komae ba, yana son ganinta amma shi gskya tsoro yake, dama El-Ameen na nan ne, can ya kalli agogo ya ga har biyar yayi, mikewa yyi yace “toh ni xan tafi mama, bbu matsala dae koh?” Tana murmushi tace “Babu komae wallahi” xae yi magana aka bude kofa El-Ameen ya shigo, ya d’an kyabe baki ganinsa, shi dae Junaid bin sa da kallo yayi har ya karaso cikin palon, ledan hannunsa na magunguna ya ajiye yace “Ba dae har xaka tafi ba, kuma kama duba mahaukaciyar taka kuwa?” Junaid ya dauke kai bae ce komae ba, El-Ameen yace “Ehh Lallai ma, wato ni xaka yi ta bari da wahala koh, daxu da safe ma sae da na xo nan kafin in tafi clinic nasan kai ko tashi kila baka yi ba lokacin” yana kai wa nan ya nufi sama, Junaid ya sauke ajiyar xuciya ya bi bayansa, El-Ameen ya bude kofar dakin da key ya tura kofar a hankali, tana xaune ta rakube waje daya bayan ta kuma cire labulayen dakin gaba daya kamar yanda ta saba, doguwar rigar kanti ne jikinta ja da ya haska farin fatar ta, duk ta birkita dogon gashinta kmr ba da safe Mama ta kuma daure mata ba tana bacci, kayan ma da gani ta kasa cire shi ne don duk ta yamutse shi jikinta, El-Ameen ya balla mata harara yace “Wai ke wace irin mutum ce, wllh kika sake cire min labule sae na gaura maki mari, baki da aiki sai barna” Junaid dae na d’aga bakin kofa yana leko dakin, El-Ameen ya kallesa yace “Da’alla matsoraci shigo baxa ta ma komai ba” kin shigowa junaid yayi yace “Nan ma ya isa” El-Ameen ya hade rae yace “Ohh wato ni ne ban san ciwon kai na ba da nake shigowa koh, sae in daina shigowa nima in dinga tsayawa daga bakin kofa in ga ta ynda xa ayi maganin” a hankali Junaid ya d’aga kafa ya shigo dakin yana kallonta sae shishshigewa jikin bango take a tsorace, El-Ameen ya kalli Junaid dake tsaye shi ma duk a tsoracen, Junaid bae ankara ba sae gani yyi El-Ameen ya fixgosa ya tura sa har sae da ya fada kanta, a tare suka kwala ihu daga shi har ita, El-Ameen ya dinga kyakyata dariya har da rike ciki, da kyar Junaid ya mike, ita ma ta yunkura ta mike, tsorata junaid yyi ya nufi bayi da sauri, ita kuma ta wawuri d’aya daga karafunan labulen dakin tayi kan El-Ameen dake dariya har lokcin, xaro ido yyi ya hadiye dariyarsa ganin haka, ya juya da sauri xae fita ae da hanxarinta ta bi bayansa, me Junaid xae ban da dariya, ya dinga kyalkyala dariya ya bi bayansu, har downstairs ta bi El-Ameen, mama na ganin hka ita ma tayi waje da gudu, El-Ameen ya dinga cewa “Junaid wllh ka xo ka riketa, junaiddd” Junaid ya durkusa nan stairs ya dinga dariya ganin yanda El-Ameen ya rude yana xaga palon, ita ko sae binsa take xata buga masa karfen, Hadiye dariyar Junaid yyi ganin El-Ameen ya shige kitchen ya sa key ya barsu su biyun a palon, ta dade tsaye bakin kofar kitchen din, kafin ta juyo tana bin ko ina na palon da kallo, k’asa motsi Junaid yyi daga inda yake xuciyarsa na bugawa, ta jefar da karfen hannunta ganin kofa a bude ta nufi kofar da sauri, Junaid bae san lkcn da ya nemi tsoron ya rasa ba ya bi bayanta cikin hanzari ya riga ta isowa kofar ya rufe gam, juyawa tayi tana kallonsa tana maida numfashi, sae kuma ta fasa wani ihu tayi kansa ta fixgosa, rungumeta yyi ya riketa gam, ta dinga fixge fixge ya ki saketa, Sosae suka jigata daga ita har shi, don kin saketa yyi, ita kuma bata fasa kokuwa da shi ba, daga karshe tayi lamo jikinsa bata sake yunkurin kwatar kanta ba, a hankali ya saketa ta sulale nan kasan palon, hawaye yaga kwance fuskarta, jikinsa yyi sanyi ya durkusa gabanta yana kallonta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button