CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske writers association????

Mata-Maza ce Khaleesat Haiydar ba namiji ba????⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

89…..

Zahrah ta kalli cikin idonsa tace “Who’s Jasmine?” A hankali yace “You!” Dauke kai tayi ya mike ya dawo gefenta ya xauna yace “Baki bani amsar tambayata ba” shiru tayi bata ce komai ba, matse mata hannu yyi ta wurga masa wani kallo tace “Stop that” yyi d’an murmushi yace “Nasan abinda zan maki ki sauke girman kan nn naki….” Fixge hannunta tayi ta mike ta nufi toilet tace “You can’t change who I am, beside you are more arrogant” daga haka ta shige toilet ta rufe, mikewa yyi ya fita daga dakin yana murmushi har lkcn, sai bayan ya fita ya dinga mamakin kansa, then what just came over him, karfe goma saura Zahrah ta shirya cikin kayan bacci ta fita daga dakinta, dakin Humainah ta tura ta shiga, suna xaune kasa ta gansu, Humainah ta daura kanta kan kafar Hajja, magana suke amma suna ganinta suka yi shiru, ko a jikinta ta karasa ta xauna gefen gado ta kalli hajja tace “Sannu da hutawa!” A dakile Hajja tace “Yauwa!” Daga nn Zahrah ta maida dubanta kan tv, Hajja ta kalli Humainah kmr xata yi magana sai kuma tayi shiru ta kyabe baki, Humainah ta d’an kalli Zahrah tace “Abincin ki downstairs” ba tare da Zahrah ta kalleta ba tace “Am not hungry” Hajja ta galla ma Humainah harara ta hade rai, har kusan sha daya Zahrah na dakin ita dai bata ce masu ba suma haka, tun da ta shigo kuma sun ki yin hirar da suke, can dai ta kalli Hajja tace “Sai da safe” da sauri Hajja tace “Ehh Allah ba mu alkhairi” ba sai Hajja ta ga tana kkrin kwanciya kan gado ba, ta yo waje da ido tace “Mai xan gani haka?” Humainah da ta danne dariyar da ya kusa taho mata tace “Nan xata kwanta mana” Zahrah ta kalli Hajja tace “Bacci xan yi a nn” Hajja ta wage baki tana mata kallon mamaki can dai tace “Su wa kika bar ma dakin naki ne” Zahrah tace “A nn nake kwana” Hajja ta kalli Humainah tace “Wai?” Humainah ts gyada mata kai, Zahrah ko tayi kwanciyarta, can dai Hajja ta rufe baki tace “Wai tun da aka kawo ta nn take kwanan maki?” Humainah tace “Uhm” Hajja tace “Tabdi, toh me salubabben yace?” Humainah tayi yar dariya tace “Ba ruwansa” Hajja tace “Toh Allah ya sauwake maku gaba daya” tuni Zahrah ta ja bargo, Hajja da ta kasa daina mamaki tace “Wai meye haka nake gani, to ni ina xan kwanta?” Humainah tace “Ki tafi dakinsa ku kwanta” dai dai nn Junaid ya shigo dakin, yayi mamakin ganin Zahrah kwance dakin, Hajja tace “Yanda yake wawa haka ya samo mata duk wawaye, banda haka ni ko a tarihi ban taba jin kalan abinda nake gani a dakin nn ba, toh shigowa Kayi Kai ma ka kwanta a tsakiyarsu ko ko?” Mikewa Humainah tayi ta dinga dariya, Junaid dai sai kallonta yake don har ya mance rabon da ya ga tana dariya haka, dauke kai yyi yana murmushi can dai ya kalli Hajja yace “Toh yau kinga hakan a gidan Ahmad Junaid” wani kallo ta wurga masa tace “Yi man shiru, gantalalle har kullum wautan yan fari ba cika ka xai yi ba, dama Kai kace ta dinga xuwa kwana nn?” Junaid ya kalli Humainah yace “You leave the room for them nd come to my room” daga haka ya juya ya fita, a fusace Hajja tace “Ka xagi Muhammadu wllh, ke kuma uwar me yace?” Humainah tayi murmushi tace “Yace kije dakinsa ki kwanta” duka take shirin kai mata ta mike da sauri ta fita daga dakin, daga nn bata sake ganin Humainah ba tayi jiran tayi jiran har ta gaji, kwafa Hajja tayi tace “Lallai yaran nn, dakin mijinta ta tafi ashe” kallon Zahrah da tayi bacci tuni kan gado tayi, sai kuma ta fara mamaki, taga dai ko kwana hudu ba ayi da tarewarta tabe baki tayi ganin ta kasa gano komai ta mike ta dau bargo ta shimfida a kasa da pillow, can misalin biyu Zahrah ta farka mikewa xaune tayi ita kadai ce kan gadon, can ta kalli Hajja dake ta sharar bacci a kasa, sauke kafafuwanta kasa tayi ta mike ta xaga inda take ta durkusa ta shiga tada ta, bude ido Hajja tayi tana salati, Zahrah tace “Akwai sanyi kasa meyasa baki hau gado ba” Hajja tace “Kai ai sai jikina yyi ciwo, nn ya ishe ni” Zahrah tace “Toh” mikewa xaune Hajja tayi tace “Toh ae gwara da kika tada ni, xan yi tsayuwar dare dama” Zahrah tace “Ina take ita?” Hajja ta tabe baki tace “Ae kya bar ni budurwa” daga haka ta mike tana salati ta shiga bayi, mikewa Zahrah tayi ta koma tayi kwanciyarta, da asuba hajja ce ta tada ta tayi sllh, tana idarwa tana daga kan darduman ta gaida Hajja dake ta jan carbi, Hajja ta amsa tace “Kin tashi lafiya?” Zahrah ta gyada mata kai, Hajja tace “Amma kina da ciwon baki koh? Naga kmr magana na maki wahala?” Murmushi Zahrah tayi, Hajja tace “Toh ae ba abun dariya bane sai in sa a sama maki Magani….” Zahrah tace “A’a lafiyata lau!” Hajja tace “Tohhh! Kuna waya da mutan gidan ku?” Girgixa kai Zahrah tayi, Hajja tace “Sbda me” Zahrah tace “Ba waya” Hajja tace “Baki xo da waya bane dama?” Girgixa kai kawai Zahrah tayi, Hajja tace “Toh Allah ya kyauta” daga haka bata sake cewa komai ba, can Hajja tace “Dawo nn in maki tambaya” mikewa Zahrah tayi ta koma kusa da ita ta xauna, murya can kasa Hajja tace “Halan gudun mijin ki kike?” Girgixa kai Zahrah tayi ba tare da ta kalleta ba, Hajja tace “Anya? Toh wace gulmar ta kawo ki nn jiya Idan ba gudunsa kike ba?” Zahrah tayi murmushi ta girgixa mata kai, Hajja tace “Ke ki fa bude baki ki min magana” a hankali tace “Ni dama a nn nake kwana” Hajja tace “Toh har ya maki kwanakin ki bakwai ne?” Kai Zahrah ta gyada mata, Hajja tace “Karya kike” murmushi Zahrah tayi ta mike tace “Zan je kitchen” daga haka ta fita Hajja ta bi ta da kallo tace “Ikon Allah yau naga halitta” Breakfast Zahrah ta shiga kitchen tana hadawa, cikin minti arba’ain ta gama soye soyen, ta kuma dafa hadadden lipton mai kamshi ta kuma dau nama a deep freezer ta gyara tayi pepper soup da shi, bakwai da kusan rabi ta kai ma Hajja nata, Hajja dake kan darduma har lkcn tace “Ahhh, Dama kuna girki ‘ya yan gidan sarauta, to wa ya koya maki girkin?” Murmushi Zahrah tayi ta ajiye mata ta hada mata tea snn ta mike tace “Zan yi wanka” daga haka ta fita ta koma dakinta, ta fito daga wanka tana gyara gashinta aka bude kofar dakin, juyawa tayi, tayi masa kallo daya ta dauke kanta, sanye yake da uniform, hannunsa rike da hularsa ya karaso cikin dakin har ya iso bayanta yace “Ashe an koya maki girki gidan ku” bata ko kallesa ba bare yasa ran samun amsa, kwace comb din hannunta yayi, ta jawo mai xata shafa ya karbe man, wani man ta kuma dauka ya kwace duk ya jefar da su kan gado, tana son tashi amma ta kasa sbda tawul kadai ta daura, gashi yana bayanta, ta madubi yake kallonta shi ma ya hade rai yanda tayi, “Pls ka daina shiga rayuwata Ahmad” bai san lkcn da murmushi yayi escaping lips dinsa ba yace “Ohh really kinsan sunana ashe” mikewa tayi kafin ta bar gun ya rikota, turasa take son yi amma ta kasa, kawai ta saki kuka, buda ido yayi yace “Kuka?” Ganin yanda take kukan sai ya tuno masa da lokacin da take da disorder, ya ji duk jikinsa yyi sanyi, ya kamo hannunta suka koma gefen gado ya xaunar da ita cikin sanyin murya yace “Ohk ohk… Am… am sorry princess, am sorry Jasmine” ganin taki daina kukan bai san lkcn da ya rungumeta ba ya lumshe ido a hankali yace “I said am sorry xan bar shiga rayuwar ki….” A hankali ta tsaida kukan nata, dogon gashinta ya kama ta fixge gashin a hannunsa, murmushi yayi murya can kasa yace “Jasmine dita ta da ba haka take ba, she alwayz wants to be with her Captain, always happy when ever she see’s her captain, she alwayz want to do everything with her captain, she’s timid, she’s alwayz afraid, she’s innocent, the sweetest of all, she’s alwayz happy and free, she was never arrogant, she don’t have I don’t care altitude, she never say who she is, she’s full of respect, and the amazing of all, she changed me to what I am today, she…..” Shiru yayi ta dalilin dago kai da tayi tana kallonsa da manyan idonta, lallausan murmushi ya sakar mata yace “Yeah, I want you to go back to ur former self…” Agogo da yayi stuck din karfe takwas ya sa shi bude ido yana kallon wristwatch dinsa yace “You made me late for work….” Bai karasa ba sai ji tayi ya fara kiss dinta, don kansa ya mike ya fice daga dakin daga karshe, haka ta bisa da kallo har lkcn ta kasa motsi inda take. Da kyar ta mike bayan ta ji fitar motarsa ta shirya cikin atamfa riga da skirt tana xaune gaban mirror tana sa xobunayen zinari guda biyu da ta fito da daga kayan lefenta Hajja ta shigo dakin, tace “Har yanxu wanka yar nn” kallonta tayi tace “Na gama kaya nake sa wa” Hajja tace “Ashe komai iri daya ne na dakunan naku” Zahrah ta gyada mata kai, Hajja tace “Toh taho ki hada min ruwan wanka wancan so mijin na can dakinsa tana sharbar bacci” mikewa Zahrah tayi tace “Toh bari in hada maki a nan” Hajja tace “Toh hada, ko kefa da kike bude baki kike magana yanxu” murmushi Zahrah tayi ta shiga bathroom dinta, ba a dau lokaci ba ta fito tace “Ga ruwan can na hada” Hajja tace “To tafi ki bude jakata xaki ga wani sabon atamfa duk yafi sauran sabonta ki dauko min, nima kwalliya zan yi yanda kika yi kar ina ji ina gani ki raba ni da Amadi in shiga uku” Dariya Zahrah tayi tace “Kai!” Daga haka ta fice daga dakin, Hajja tace “Ashe dai kina dariya ‘yar ayi” ko da Humainah ta fito misalin Karfe goma Hajja na dakin Zahrah har lokacin ta cikata da labaran duniya, ita dai Zahrah ta tallabi kuncinta ne tana kallonta, wani lbrin yasa ta fashe da dariya, wani kuma ta xaro ido wani kuma ta bata fuska, sha daya ta shigo dakin ita ma ta xauna tana kallon Hajja tace “Ina kwana Hajja” Hajja tace “Ahh lafiya lau so miji, sai yanxu kika tashi?” Zahrah ta sunkuyar da Kai kar tayi dariyar da ya taho mata, Humainah ta turo baki tace “Ehh” Hajja tace “Toh Allah ya kiyaye, kun gaisa da takwarar tawa” Humainah ta d’an kalli Zahrah tace “Kin tashi lafiya” Zahrah tace “Alhmdllh” nan dai Hajja ta ci gaba da labaranta masu kai da marasu Kai, gyangyadin da ta dinga yi tana labarin yasa Zahrah ta sauko mata da pillow tace “Toh ki kwanta sai ki ci gaba da labarin” ai ko tana kwanciya ta bingire da bacci, Humainah tayi murmushi ta mike ta fita don daura lunch, bayan kusan minti talatin da fitan ta Zahrah ta mike ta fita don taya ta. Da yamma tun kan Junaid ya dawo Hajja ta hada kayanta wai yana dawowa xai maida ta gida, Humainah tace “Dama ba sati daya kika xo mana ba hajja?” Hajja tace “Ba gantalalliya nake ba ai” Zahrah tace “Toh ki Bari gobe alhamis mana” Hajja tace “Toh ai ba yar iska nake ba” dariya suka yi gaba daya banda ita dake ta faman xuge jaka, tana gamawa tace “Toh dai ayi xama na Allah da annabi banda munafurci da munafukin kishi mara ma’ana, ku dau kan ku kamr yan uwan juna, ke Zahrah ki bar gudun mijin ki, ke kuma Humainah in ma ta shigo dakin ki ki korata idan ba son amshe kwananta kike son yi ba, ni har kishiyata ta rasu sau biyar muka taba dambe da ita, cacan baki kuwa mun yi yafi sau hamsin, Amma lafiya muka xauna bbu tashin hankali shi yasa ku ka gan ni da kyau yanxu, shi kuma salubabben mijin naku xai dawo ya sameni” dai dai nan aka bude gate Hajja tace “Toh Alhmdllh gashi can ma,” Junaid na shigowa Hajja tace “Taho ka xauna nn, nasan sokanci baxai bari Ka hada su kayi masu magana kamar yanda nayi yanxu ba”⚓ Captain Ahmad Junaid

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button