CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske writers association????

Haske Writers association????⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

90____91

Har bayan 2 dayz Junaid bai kuma kallon inda wives din nasa suke ba, yana dawowa daga aiki baya fitowa daga bedroom dinsa, su ma ko damuwa ba su nuna sun yi ba barin Zahrah, yanda suke abubuwan su sai ka rantse ba kishiyoyi bane duk da ba wai wani magana can suke ba amma ko da yaushe suna tare, nace to ko don basa nuna sun damu da mijin kamar yanda shima yake nuna bai damu da su bane oho, gwara Humainah idan sun hada ido tana gaishesa duk da baya bin ta kan gaisuwar nata, Zahrah kam ko kallo bai isheta ba, wani takaici yake ji har cikin ransa, kuma ya rasa abinda yasa yake jin haushin halin ko in kula da suke nuna masu, ranan asabar yana kwance daki kawai ya mike ya fita, downstairs ya sauka jin kamar girki ake don a tunaninsa Humainah ce, Zahrah ya gani kitchen din tana juye dafaffen shinkafa a warmer, kallo daya yyi mata ya fice ita ko duk da taji alamar shi ne bata ko dago kanta ba, sama ya koma ya bude kofar dakin Humainah ya sameta kwance, tana ganinsa ta mike xaune, xaunawa yyi gefen gadon yana kallonta yace “Irin kema kin tsiri wani hali da ba naki ba yanxu koh?” Bata ce komai ba ya hade rai yace “Magana nake maki malama” turo baki tayi tace “Toh me nayi?” Yace “Bbu ruwana da abinda kika yi, just that daga yau idan Zahrah ta shiga dakin ki just leave the room for her nd come to my room, nd daga yau kika sake min gaisuwar rainin wayo a parlor xaki sha mamaki, infact bedroom dina xaki dinga xuwa gaisheni daga yanxu, and… I don’t care altitude din da kika tsira ma ya tsaya iya idan bana gidan nn, duk girkin da xa ayi ki tabbatar kin kai min bedroom…..” Kallonsa take kawae, can tace “Ae bni kadai bace matar ka naga” mikewa yyi strictly yace “Ke kadai nasa hakan, if you want to dare me just ignore any of this instructions” daga haka ya fice daga dakin ta bi sa da kallo. Zahrah na gama girki Humainah ta sauka ta dibar masa nasa, ita dai Zahrah bata ce komai ba, bedroom dinsa ta kai masa tana ajiyewa xata fita yace “Come back here” hade rai tayi ta dawo ya nuna mata kan gado yace “Sit” karasawa tayi ta xauna, bai wani ci abincin ba ya sha ruwa ya tura ya ci gaba da kallonsa a system, gajiya Humainah tayi da xama ta mike yace “Ina xa ki” tace “Jirana fa take mu ci abinci” yace “ta ci ita kadai, ga wannan idan yunwa kike ji ki ci” tsaye tayi tana kallonsa ganin bai kuma kallon inda take ba ta koma ta xauna, can dai ta gaji da xaman ta kwanta lkci daya bacci ya dauketa. Har yamma bai bari ta fito daga dakin ba, wayarsa dake ring ya sa shi mikewa ganin bata da niyar dauko masa ya dau wayar, kallon screen din kawai yake ganin yayan Zahrah ne Abdul, can ya daga kiran ya koma ya xauna, gaisawa suka yi Abdul din yace “Captain ya Lil sis dita…. Her phone is not going through!” Mikewa junaid yayi yace “Ohk bari in kai mata” daga haka ya fita daga dakin ya shiga nata, xaune ya ganta kan gado hannunta rike da novel, karasawa yyi kusa da ita ya mika mata wayar, bata dago ba bare ta karba, wani kallo ya dinga yi mata, can dai ya dake yace “Take this” nn ma taki dagowa, katse kiran yayi yace “Ba magana nake maki ba?” Mikewa tayi ta sauka daga kan gadon xata fita daga dakin ya fixgota, wani tsawa tayi masa a fusace tace “Stay away from me Ahmad!” Runtse ido yyi jin tsawar har tsakiyar kansa, bai san lkcin da ya saketa ba ya fice daga dakin ya shiga nasa ya dau makullin motarsa ya fito ya koma dakin har lkcn tana tsaye, hijab dinta ya dauka ya kama hannunta ya nufi kofa ta shiga kokarin fixge hannun tace “Let me, just go away from my life….” ganin xata bata masa lokaci ya dauketa ya fice daga dakin bai dire ta ba sai cikin mota, ya kulle ya xaga ya shiga ya tada motar ya bar gidan, bai damu da haukan da ta dinga masa bayan motar ba ya dinga driving dinsa, tafiyar kusan minti talatin suka yi taga yayi parking, bude motar yayi ya fito ya xaga ya bude side din da take ya fito da ita, taku daya biyu ya cikata yana mata wani kallo, kalle kallen wajen ta dinga yi ganin duk bola ne, ya dawo gabanta ya tsaya yace “Kin ga nan?” Kallonsa kawai take bata ce komai ba, yace “Toh a nan na dauke ki bbu kyan gani da hannuna, kuma a lokacin da kowa ke kyamatar ki baki da wani sauran gata a duniya kina tsaka da hauka, wanda da a lkcn royal family dinki sun ganki a hakan ba lallai su taba ki ba sai dai su sa a dauko masu ke, kuma har duniya ta nade bbu wanda xae taba maki abinda na maki… Har ni xa ki ce ina shiga rayuwar ki, har na xaki wani dinga daga ma kai ke ga ki royal blood” Kallonsa kawae take hawaye cike idonta, can ta fashe da kuka sosai ta durkushe wajen, jikinsa yayi sanyi yana kallonta, bai san lkcn da ya durkusa gabanta ba shi ma ya dago kanta yace “Look I never mean to hurt you Zahrah just that….” Ganin yanda take kallonsa hawaye na sauko mata kawai ya mike ya daga ta suka koma mota, har suka isa gida bbu wanda yace komai cikinsu, yana parking ta bude mota ta fita tayi cikin gida ya fito ya bi bayanta, tuni ta shige daki ta sa key ta dinga rusa kuka, jin kofar a rufe yasa ya koma bedroom dinsa ya dau spare key ya fito ya bude dakin, ji yayi duk ya tsani kansa ganin yanda take kuka, ya karasa kusa da ita a sanyaye ya durkusa ya dago kanta yana kallonta, rungumeta yayi a hankali yace “Am sorry Jasmine…. I shouldn’t have done that, forgive me pls” ita dai bata ce komai ba sai kuka, bai sake cewa komai ba, amma sun kusa minti talatin a haka jin ta daina kukan ya dago kanta yaga idonta lumshe, janyeta yyi jikinsa ya kwantar da ita ya mike ya fita daga dakin don lkcn magrib yayi. Ko da ya dawo masallaci dakin Humainah ya shiga ya ganta xaune kan darduma juyawa yayi ya koma dakinsa ya dau wayarsa mis cals din Abdul ya gani ya dauka ya kirasa ya basa hakuri snn yace bari ya kai mata, xaune ya tarda ita kan darduma ya karasa gabanta ya durkusa ya mika mata wayar, karba tayi tana kallon screen din can ta kai kunne a hankali tace “Brotherna!” Murmushi tayi ta gaishesa sai kuma ta koma harshen fullanci, kallonta kawai Junaid yake har dai suka gama wayar ta mika masa, karba yayi yana murmushi yace “thought xa ki ce masa cikin ruwa na jefa maki wayar, sai kuma naji kin ce yana gu na!” Kallonsa tayi da sauri sai kuma ta sunkuyar da kai, ya wara ido yace “You thought bana ji koh?” Bata ce komai ba yace “Don’t worry I will get you a new phone princess” mikewa yyi ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, tun daga lkcn Zahrah ta d’an sauya in dai yyi mata magana ko yayane xata amsa masa, ta kuma fara gaishesa, sai dai miskilanci nan na nan, a haka har tayi sati uku gidan har lokacin kuma tare da Humainah suke kwanciya, shi dariya ma take basa, sau dayawa Humainah kan barta ita kadai dakin ta tafi dakinsa amma hakan bai sa ta daina shigowa da daddare ta kwanta ba, kwata kwata Zahrah bata nuna masu wai tana kishi, duk da irin abubuwan da yake ma Humainah a gabanta don ma Humainahn bata yarda wani lokacin don nauyinta take ji ganin shirunta yyi yawa kuma ko sau daya baxa ka ga alamar tayi fushi ba, amma fa ba haka abun yake gun Zahrah ba a can kasan ranta, so tari sai ta shiga daki xata fara kuka tayi mai isarta ta fito kuma kamar ba komai, mamakinta Junaid yake ganin yanda ko sau daya bata taba nuna ta damu da komai ba, ya rasa yanda xae yi kuma ta saki jiki da shi, bai son El-ameen yyi masa dariya shi yasa bai gaya masa komai ba, Yau da ya kasan ce Sunday duk suna parlor da daddare shi yana kwance yana kallo, lkci lkci ya ke kallon Zahrah dake xaune tare da Humainah suna cin abinci sai dai ita ba wani ci take ba jujjuyawa kawae take tana kallon ita ma, da ganinta kasan duk jikinta a sanyaye yake don actress din film din mahaukaciya ce, Humainah ma kallon take tana cin abinci, kawai gani suka yi ta sake spoon din ta mike ta wuce sama, Humainah ta kallesa, ya mike ya bi bayanta, xaune ya ganta daki tana ganinsa ta fashe da kuka, sosai ta basa dariya ya xauna gefenta ya kamo hannunta yace “What’s wrong princess?” Kanta ta daura kan shoulder dinsa tana ci gaba da kuka, bakinsa ya kai kunnenta murya can kasa yace “Film din nan ne ya sa ki kuka?” A hankali ta gyada masa kai, yayi murmushi ya dago kanta yana kallon kwayar idonta, sauke nata idon tayi don baxata iya ci gaba da kallonsa ba, can kasan breathe dinsa yace “My princess, My Jasmine!” Ta kallesa kamar baxata ce komai ba sai kuma a hankali tace “My prince, My Hero”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button