CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske writers association????⚓ Captain Ahmad Junaid⚓
By Khaleesat Haiydar✍????
92____95
Kallonta kawai junaid yake kamar bai yrda da abinda tace ba, can yyi murmushi ya daura forehead dinsa kan nata a hankali murya can kasa yace “Sure?” Rufe idonta tayi bata ce komai ba, ya lumshe idonsa yace “I love you princess!” Boye fuskarta tayi jikinsa tana murmushi, ya kai bakinsa kunnenta yace “Ohk, am only ur hero but not ur love koh?” Murya can kasa tace “uhmm Whatever!” Misalin sha daya yana kwance yana danna waya yaji ta bude kofar dakinta, mikewa yayi ya karasa gun kofa da sauri ya bude, tana kokarin bude dakin Humainah ta juya tana kallonsa, hannu ya mata alama da ta xo, ta tsaya tana kallonsa, can ta make kafada ta girgixa masa kai, bata fuska yayi, tayi murmushi ta karasa gun kofar ta tsaya ta rungume hannayenta bata ce komai ba tana jiran jin me xai ce, fixgota yayi cikin dakin ya rufe kofar ta xaro ido tace “What’s this?” Yace “Nan xa ki kwana yau!” Ta hade rai tace “And Why?” Yace “Just” hannunta ya kama suka karasa kan gadon ya xaunar da ita, a hankali tace “Ita fa?” Ya d’an bude ido yace “Ko in je in daukota?” Gyada masa kai tayi yayi murmushi ya ja dogon hancinta hade da daura finger dinsa daya a kan lips dinta yace “Gobe ita xata kwana nan ba ke ba!” Bata kuma ce masa komai ba, sai dai mamaki take a ranta to da can yana magana haka ashe, kan gadon ya hau ya jinginar da pillow ya kwanta ya nuna mata gefensa, kin tasowa tayi a hankali yace “Jasmine” sunkuyar da kanta tayi ta hau kan gadon ya nuna mata pillow din dake gefensa ba musu ta kwanta a hankali ya daura kanta, ya juya yana facing dinta yace “Bani labari har bacci ya dauke ni” kallon handsome face dinsa kawae take ko kiftawa bbu, hade kansa yyi da nata yace “Jasmine” ta koma baya da sauri tace “What?” Yace “Ban labari nace” tace “Bn iya ba” yace “Ohk in baki ni?” Gyada masa kai tayi, ya kashe wutan dakin ta mike xaune da sauri tace “Why is that?” Jawota yayi jikinsa yace “Shhhh! Da Hausa kike son labarin ko da fillanci, ko da larabci ko kuma turanci” murmushi tayi tana kallonsa tace “Fillanci….” Xaro ido yayi don ji kawai yake bai iya speak ba, kallon fuskarsa kawai take cikin duhun tana murmushi, kawai ji yayi tayi dariya tace “Ohk Hausa, tunda baka iya fillancin ba” dariyar yayi shi ma yace “No na iya mana, amma bari muyi da Hausan, kina ji na?” Kai ta gyada masa, ya hade hannunsa da nata murya can kasa yace “Watarana ne dai watarana ne dai, wani bawan Allah ya je course Egypt daga nan Nigeria, cikin ikon Allah ya kare course din ya dawo gida Nigeria, washegarin ranan da ya dira yayi deciding ya je gun amininsa abokinsa kuma d’an uwansa….” Kallonsa kawai Zahrah take, ya shafa fuskarta yace “are you there?” Ta gyada kasa kai, ya lumshe ido yace “Yana driving a hanya ya ga wani taro me yawa, a tunaninsa hatsari aka yi, kawai yayi deciding ya tsaya ya bada nasa taimakon… Yana fitowa ya shiga taron kin san abinda ya gani?” Boye fuskarta tayi a kirjinsa, ya dago kan yace “Are you there princess?” Ji yayi ta fashe da kuka, ya mike xaune da sauri ya dagota yace “Jasmine!” Ta kuma fashewa da wani kukan, jikinsa yyi sanyi lokaci daya, rungumeta yyi yace “Ohh I am sorry plss tunda ba ki so, sorry plss Princess na daina” lamo tayi jikinsa, a hankali yace “I didn’t mean to hurt you” suna nn a haka har yaji alamun tayi bacci ya lumshe ido ya daura fuskarsa kam gashinta da ya cikasa da kamshi. Washegari da asuba kafin ya dawo daga Masallaci ta fita ta koma dakinta, yana dawowa dakin Humainah ya shiga ya tarda kwance ya karasa ya xauna kan gadon yace “Sallah fah?” Tace “Nayi” yace “Ohk Gud morning” mikewa xaune tayi tace “Ina kwana!” Yayi murmushi yace “Kin tashi lafiya” komawa tayi ta kwanta tace “Yeah” yace “to babyn fah” bata ce masa komai ba hakan yasa ya mike ya fita. Bakwai da minti goma ya sauka downstairs bayan yayi shirin fita aiki, kallo daya Zahrah da ta gama ajiye kayan breakfast kan dining tayi masa ta dauke kai, ya isa kusa da ita ya tsaya, ta gefen ido ta kallesa tace “Good morning” ya rungume hannayensa yana kallonta jin bai amsa ba ta juyo tana kallonsa ita ma, karasawa tayi gabansa ta langwabar da kai cikin sanyin murya tace “Gud morning” bai amsa ba still sai kallonta da yake, can ya kamo hannunta ta fixge tayi masa buttoning masa button din karshe na farin uniform din jikinsa ta kara gaba. Da yamma yana parlor xaune bayan ya dawo daga aiki su kuma suna kitchen aka danna bell, mikewa yayi ya isa gun kofar ya bude, El-ameen ne tsaye daga gefensa kuma Dr Sumayya, El-ameen ya wara ido yace “ko mu koma” Junaid yayi murmushi yana kallon Dr sumayya ya bata hanya yace “Sannu da xuwa Dr, bismillah” murmushin ta mayar masa ta shiga parlon tace “Yauwa Captain ina daughter nah” yace “Uhm tana ciki bari in kirata” daga haka ya nufi kitchen, xama tayi parlor El-ameen ma ya xauna tace “Allah sarki rayuwa, kamar ba ayi ba yanxu koh?” Murmushi kawai El-ameen yayi, tace “Allah ya baku lada gaba daya…. Amma na so ace kai ka sameta ba wnn Capt mara son son jama’a ba” Junaid na shiga kitchen ya kamo hannun Zahrah dake tsaye Humainah kuma na ta aikin, yace “You know what princess, xaku gaisa da bakuwa yanxu, ta taimake ki ita ma sosai lkcn da baki da lafiya, you stayed with her for 3 month ta kuma kula dake sosai, she’s Dr sumayya by name, tare suka xo da El-ameen” kallonsa kawai Zahrah take yayi murmushi yace “Yeah princess,” juyawa yayi ya kalli Humainah dake ta harkan gabanta yace “Wife ki kawo masu drink pls” daga haka ya kama hannu Zahrah suka fita, kallonta kawai Zahrah take kamar yanda ita ma Dr Sumayyar ke kallonta har suka karaso parlon, Dr Sumayya ta mike tana murmushi ta bude mata hannunta, karasa Zahrah tayi ta shige jikinta, Dr Sumayya tace “Am happy you are back my baby…. Alhmdulillah, am happy for you baby” Zahrah ta rufe idonta da ya cika da hawaye Dr Sumayya ta janyeta jikinta tana kallonta cike da tausayinta. Su El-ameen na barin gidan bayan magrib Junaid ya shiga dakin Zahrah bai yi mamakin ganinta a sanyaye ba ya xauna kusa da ita ya kamo hannunta yace “Yeah you owe a lot to her, after you loosed ur memory ita ta rike ta kuma dinga nuna maki abubuwa, komawarsu abroad yasa kika dawo gidana,then baki ma son rabuwa da ita you were crying xa ki bita” kallonsa kawae Zahrah take, yayi murmushi ya lakaci hancinta yace “Yess princess…” Danna bell da aka yi downstairs ya sa ya kalli bakin kofa can yayi peck din cheek dinta ya mike yace “Am coming princess” daga haka ya fita ya sauka kasa, yana bude kofar yayi still yana kallon wa enda ke tsaye bakin kofar, Hajiya ce ta kirkiri murmushi tace “Ahmad, ina yini” bai amsa ba sai kallonta da yake, Umma dai sai wurga ido take, Hajiya tayi karfin halin bin ta gefensa ta shiga parlon sai a snn ya juya ya bar bakin kofar ya koma parlor, Umma ma ta shigo duk suka karasa parlon kamar masu tsoron taka tiles din parlon, xaman sa yyi parlor suma suka shigo suka xaxxauna, Umma tace “Sannu Ahmad ina yini ya aiki” sai a snn ya kallesu, can yyi kasa da kai yace “Sannun ku da xuwa” washe baki Hajiya tayi tace “Sannu Ahmad, ya iyali” yace “Alhmdllh” daga haka ya mike ya wuce sama, bin sa da kallo suka duk jiki yayi sanyi, dakin Humainah ya shiga ya ga tana bayi, ya fita ya koma dakin Zahrah tana nn yanda ya barta ya xauna kusa da ita ta kallesa tace “Waye?” Hannunta ya kama yace “My step mothers” d’an bude ido tayi tace “You have them?” Murmushi yayi ya daura goshinsa kan nata yana rike da hannunta yace “Yeah, and they don’t like me” tace “Why?” Ya girgixa Kai yace “tafi ki kai masu ruwa” ba musu ta mike ta fita, tunanin abinda xai kawo su gidansa ya shiga yi, can ya mike ya koma dakin Humainah tana xaune gaban mirror yace “Ki tafi ki gaida su Hajiya” tana kallonsa ta madubi tace “Wace Hajiya” yace “warce kika sa ni mana” daga haka ya fita, ta kusa minti biyar tana naxari kafin ta mike ta sa hijab ta fita. Kasa karasawa parlon tayi yanda suke kallonta haka ita ma take kallonsu, Zahrah dai na xaune kasa bayan ta kawo masu ruwa har da abinci, can Humainah ta karasa ta xauna ita ma kasa tana kirkiran murmushi tace “sannun ku da xuwa” amsa ta suka yi ko Wanne na murmushin dole, bata kuma cewa komai ba can dai ta mike ta koma sama, har aka yi isha Junaid bai shigo parlon ba iyaka ya tafi masallaci ya dawo ya koma sama, can dai Umma na kallon Zahrah tace “D’an yi mana magana da shi xa mu koma ne” mikewa tayi ta tafi sama ta shiga dakinsa, yana danna laptop ta samesa ta karasa tace “Xa su wuce wai” kudi ya ciro har dubu hamsin ya mika mata yace “Ki basu” xaunawa tayi kusa da shi ta karbi kudin ta ajiye tace “Nooo, ka fito kuyi sallama” yace “Why?” A hankali tace “From there expression sun yi regretting everything” yayi murmushi ya dago fuskarta yace “And that’s because basa gidanmu yanxu” tace “Kamar ya?” Mikewa yayi yace “Am coming” daga haka ya dau kudin ya fita, xaunawa yayi parlon ba tare da ya kallesu ba Umma tayi karfin halin cewa “Ahmad dama mun xo ne mu roki alfarmar ka taimake mu kayi ma Alhaji magana mu koma dakin mu, sai kuma a yafe juna abubuwan da suka faru a baya…. Sharrin shaidan ne” shi dai kansa na kasa can yace “Toh…” Ya mika masu kudin yace “Allah kiyaye hanya” Hajiya ta karba tace “A’a har da wahala haka Ahmad, to Allah yayi albarka” Ameen kawai yace ya mike ya nufi stairs yace “Bari in kirata” daga haka ya haura sama. Yau Zahrah kin fitowa tayi xuwa dakin Humainah don ma kar ya kuma kiranta dakinsa, duk ya kagu ya ji fitowarta amma shiru har Karfe sha biyu, to ko dai har ta xo ta wuce bai sani bane, mikewa yayi ya fita ya nufi dakinta, a hankali ya tura kofar ya ganta kwance, tana ganinsa tayi saurin rufe ido ya karasa ya xauna gefenta yace “Yau baki tsoron kwana ke daya kenan?” Ba tare da ta bude ido ba tace “Eh” wara ido yayi yace “Da gaske?” Xata juya masa baya ya rikota yace “Jasmine” bude ido tayi ta mike xaune ta buda masa hannu alamar what, murmushi yayi ya kamo hannunta yace “Nothing, m just missing you” tace “Ohk thank you, Gud nyt” yace “Uhm korata kike?” Gyada masa kai tayi yayi dariya yace “Ohk xan tafi, but you know what?” Kallonsa kawai take, ya lumshe ido ya bude murya can kasa yace “Ba mu taba sallah tare mun roki Allah ya albarkaci auren mu ba” tace “Ni na taba yi” ya buda ido yace “I mean togeda princess, c’mon tashi kiyi alwala muyi sallah” tace “Ina da alwala na” ya d’ago kanta yace “Gud” daga haka ya mike ya dau darduma ya shimfida masu, juyawa yyi yana kallonta yace “Taso mana” ta nuna masa hijab dinta tace “Bani” yace “Meyasa baxa ki dauka da kanki ba” tace “Nothing” murmushi yayi ya dauko ya mika mata ta sa sannan ta mike. Nafila ya ja su raka’a biyu, ya jima xaune yana addu’a bayan sun sallame snn ya juya yana kallonta, murmushi ya sakar mata ya dafa kanta, a hankali yace “Let me pray for you princess” rufe ido tayi bata ce komai ba har ya gama sannan ta bude ido tana kallonsa, langwabar da kai tayi tace “Is that all” ya gyada mata kai, ta mike ya bi ta da kallo, kofa ta bude ta juyo tana kallonsa tace “Gud nyt, I want to go to bed!” Wara ido yayi yana kallonta can yayi murmushi yace “Oh korata ma kike ko?” Girgixa masa kai tayi tace “A’a bacci xan yi ne” yace “toh ni a nan nake son in kwana” shiru ta d’an yi tana kallonsa can tace “Ohk,” ta rufe kofar ta dawo tayi kwanciyarta ta ja bargo tace “Gud nyt” kai kawai ya gyada mata, kusa minti goma xaune snn ya mike ya kashe wutan dakin ya dawo ya kwanta ya birgina kusa da ita, Juyowa tayi da sauri murya can kasa yace “Baki yi bacci ba” “Uhm” kawae tace xata kuma juyawa ya jawota jikinsa. Washegari da asuba ko da ya fito daga bayi bai tarda Zahrah a dakin ba, tsaye yyi dakin don yasan baxata je dakin Humainah ba, bude kofar yyi ya fita ya bude dakin dake kusa da nata, nan ya ganta kwance ya karasa ya durkusa kusa da ita a hankali yace “Zahrah!” Idonta rufe yake, ya mike ya xauna kusa da ita ya dago ta yace “Nasan kina jina, open ur eyes pls” ganin baxata bude idon ba ya rungumeta cikin sanyin murya yace “Am sorry Jasmine” dumin hawayen ta ya ji a bayansa, ya dago kanta ta rufe idon da sauri.
3 month later.
Zahrah na daki kwance bayan junaid ya fita aiki, tana chatting da ‘yar uwarta ummi taji kamar Humainah na kiranta, mikewa tayi ta ajiye wayar ta fita ta shiga dakinta, durkushe ta ganta dakin ta karasa da sauri ta durkusa kusa da ita tace “Me ya faru?” Humainah ta dago da kyar tace “Am not okay” mikewa Zahrah tayi da sauri ta fita xuwa parlor, Mama jummai dake goge goge ta kalleta ganin yanda ta sauko a rikice tace “Me ya faru Zahra’u?” Zahrah da ke shirin kuka tace “Wai tace min bata da lafiya ban san me ya sameta,” mikewa mama jummai tayi ta haura sama da sauri ta bude kofar Humainah ta shiga, dagota tayi tana mata sannu ta kalli Zahrah tace “Maza je ki yi ma driver magana mu tafi asibiti” da sauri Zahrah ta kuma fita don yi ma driver magana, ita kuma mama jummai ta fito da Humainah da banda daurewa bbu abinda take, kafin su isa asibiti sai ka rantse Zahrah ke nakuda, duk ta cika masu kunne da koke koke ganin yanda Humainah ke wahala, ana shiga da Humainah dama ta kira junaid, yana dagawa ta fashe masa da kuka tana cewa “captain kaga kila haihuwa xata yi ka xo pls, she’s in pain” Mama jummai ta karbe wayar tace “Rabu da ita soja kar ta daga maka hankali, ka taho muna asibiti” daga haka ta katse wayar don ko ba a gaya mata ba tasan Zahrah ta gama ruda shi, karban wayar Zahrah ta kuma yi tace “xan kira Mumy” Mama jummai ta karbe tace “A’a ki bari sai ya xo kin ji, in shaa Allahu xata sauka lafiya ki daina kukan nan” ba a dau lkci ba sai gashi ya taho asibitin, da sauri ta je ta rungumesa ta kuma fashe wa da kuka tace “My prince ni daga yau kar ka sake ce min xan haifan maka yara bana so” kallonsu kawai ake a reception din wasu na dariya kasa kasa, ya kamo hannunta yace “Ohk princess na daina” ko minti uku bai yi hospital din ba Humainah ta haifo santalelliyar ‘yar ta, sai dai kuma bata san ma wa enda ke kanta ba, nan hankalin Junaid ya tashi, mama jummai ce tayi karfin halin karban yarinyar bayan an fito da ita, Zahrah kam tun da abinda likitan ya gaya ma junaid ya samu shiga kunnenta ita ma ta dinga rusa kuka ita fa sai ta shiga wajenta, har sai da nurses suka fita da ita daga reception din ma gaba daya, wata nurse da gulma ke ci ta isa gun mama jummai da tayi jigum tace “Allah sarki yar uwarta ce wancan da aka fitar ko?” Mama jummai ta girgixa kai a sanyaye tace “Kishiyarta ce” nurse din ta kwalalo ido sai kuma ta juya ta koma gun sauran nurses din ta fesa masu abinda ta ji su ma. Ba karamin karfin hali Junaid yayi ba ya kira Abba ya sanar da shi haihuwar ya kara da cewa bata da lafiya bayan ta haihu, kafin minti ashirin sai ga Mumy da su Umma da Hajiya sun iso asibitin, duk hankalin Mumy ya tashi suna asibitin har dare bbu wani improvement, Abba ma har ya xo ya koma shi ma rai ba dadi, karfe tara Mumy ta koma gida da Zahrah, sai a snn Junaid ya tuno da El-ameen don duk Zahrah ta gama rikita masa lissafi ya ma rasa da wanda xai ji, cikin few minutes El-ameen ya karaso clinic din, da yake yawancin doctors din ya san su yana neman alfarmar a bar sa ya shiga gun Humainah aka barsa ya shiga tare da wasu doctors biyu, ba a dau lokaci ba ya fito nan ya shiga kwantar ma Junaid hankali yace “Don’t worry frnd she will be Alryt, tayi loosing blood ne da yawa amma xuwa gobe xa ka ga she will be okay, haihuwar ne yayi gardama” kallonsa kawae Junaid yake, El-ameen yayi masa murmushi assuringly yayi Pat din shoulder dinsa sannan ya isa gun mama jummai ya karbi babyn ba tare da ya kalli su Umma dake gun ba. Washegari kamar yanda El-ameen ya fadi cikin ikon Allah jikin nata da sauki sosai kamar ba ita ba, murna gun Zahrah kamar xata yi yaya, haka duk ta bi ta takura babyn da riko ta ki kwantar da ita, ba ita ba hajja dake ta mata gorin ita ma tayi tayi ta haifo nata dai, Da taji ance mata haka mood dinta ke canxawa, junaid sai dai yayi dariya can ciki, kwanan su biyu asibiti aka sallamesu, a ranan kuma Umman Zahrah da Ummi sai Kanwar mai martaba suka iso katsina don yin barka, kaya ba na wasa ba suka yi ma Humainah da jaririyarta, hajja ta rasa inda ta sa su don murna, kwanansu biyu suka koma bauchi, ranan suna baby ta ci sunan late mum din Humainah fatima, washegari Hajja ta tattara Humainah da yar ta suka yi gida tare da mama jummai wai sai ta gama mata wanka xata dawo, Zahrah bata ji dadi ba amma bata ce komai ba don tasan balbaleta Hajja xata yi, da daddare tana dakin Junaid tace “My prince ya xa mu dinga kiran babyn?” Junaid na danna laptop din gabansa yace “Amm baby xa mu ce koh?” Tace “Noo let call her Jasmine” kallonta yayi yace “No, I have a wife Jasmine….” Tace “yess, a wife Jasmine, a daughter Jasmine” murmushi yayi yace “Ohk, to ke yaushe xa ki haifo min naki babyn, nd I want two boys” bata rai tayi sosai ta mike xata fita ya fixgota ya rungumeta, ta fashe da kuka tace “My prince ni ka daina cewa xan haihu Allah bana so” ya buda ido Yace “Toh sbda me?” A hankali tace “Kana son in mutu koh” danne dariyarsa yayi yace “Nooo, bana son ki mutu wife toh naji kiyi ta rike babies din nawa a ciki koh?” Kai ta gyada masa ya kankameta yana dariya, tace “My prince I want to continue with my education” shiru ya d’an kafin yace “Ohk” amma da jin ohkn kasan fadi kawai yayi, har aka yi bikinsu fatima da khadija Hajja bata bari Humainah ta dawo dakinta ba, ae ko tana tafiya kai amare ya dauko matarsa suka yi gida, Zahrah dai na rungume da Jasmine da tayi wayo sosai, yarinya me kyau da ita komai na babanta ne jikinta. Satin Humainah daya da dawowa Zahrah ta dinga yi ma junaid magiyar ya kai su bauchi, ko kadan bai son bacin ran princess din tasa washegari ya daukesu gaba daya ya kai su bauchi shi ya koma gida, iyayen Zahrah basu nuna banbanci tsakanin yar su da kishiyarta ba, komai aka ma Zahrah sai an mata hatta gwalagwalen da aka ba Zahrah sai da aka ba Humainah sak irinsa, kwanansu biyar Junaid ya koma ya dauko su, da daddare yana kwance Humainah dake shirya Jasmine tace “Ya Ajay?” Kallonta yayi yace “Wife!” A hankali tace “Plss ina son kayi min wani alfarma” mikewa xaune yayi ya jawota jikinsa yace “Ina jin ki dear” sauke idonta kasa tayi tace “Ina son ka raba mana gida da Zahrah” shiru yayi na kusan minti uku kafin yace “Sbda me?” Hawaye ne ya cika idonta tace “Bana son ranan da xai xo mu fara xama irin na kishiyoyi da ita, bana son komi ya hada ni da ita, idan bama tare za mu ta xumuncin mu bbu abinda zai hada mu plss dear” shafa kanta yayi yace “Hakan baxae tafa faruwa ba wife, Zahrah me saukin kai ne kema kin sani, snn the both of you kuna da ilimin addini baxa kuyi kishi mara amfani a kai na ba, bana son raba kan family dina I want to see you both together” shiru tayi bata ce komai ba, yayi peck din cheek dinta yace “Yeah wife” a hankali tace “Toh school fa ya Ajay” murmushi yayi yace “Duk sai kun gama haifa min kidz dina xa ku koma sch” kallonsa tayi ya wara ido yace “Yess wife” Washegari da ya kasance sunday Humainah na gama hada breakfast don ita ce da girki snn ta koma sama, tayi mamakin rashin saukowar Zahrah which is very unusual, dakinta ta shiga tana cewa “Antyn Jasmine,” don haka take kiranta, Kwance ta ganta tana bacci ta karasa ta tada ta Zahrah ta bude ido ta mike xaune tace “Momyn Jasmine” Humainah tace “Ki sakko muyi breakfast” toh kawai Zahrah tace mata ta juya ta fita, Mikewa Zahrah tayi ta shiga bayi ta wanke baki sannan ta fito, Junaid na xaune dining yana danna waya Ita kuma Humainah na serving din breakfast din, xaunawa Zahrah tayi Junaid dake kallonta ta gefen ido ya harde kafarsa da nata ta karkashin dining table din, turo baki tayi bata ce komai ba, ya matso da kujerarsa a hankali ya daura hannunsa kan cinyarta, buge masa hannu tayi ta mike ta koma wani kujerar dake nesa da nasa, murmushi Humainah dake lura da su tayi ta gama zuxxuba masu tayi xamanta ta fara cin nata, Junaid ma ya dau nasa ya fara ci, Plantain kawai Zahrah ta dauka ta Kai bakinta ta fara ci bata gama hadiyewa ba ta mike da sauri duk suka daga Kai suna kallonta, juyawa tayi ta bar dining din da gudu ta haura sama, bin ta da kallo duk suka yi, Humainah ta tallabi kuncinta tana murmushi tace “Hmmm” don kusan sati biyu kenan da ta gaya mata ita fa bata ga period dinta ba kamar xata mata kuka take gaya mata, kwantar mata da hankali kawai tayi tace ai yana yin haka wani lokacin, sai a snn ta kwantar da hankalinta ta ci gaba da harkokin gabanta, kallonta kawai junaid ke yi ganin irin kallon da take masa, can yayi murmushin shi ma ya mike ya bi bayan Zahrah, xaune ya ganta bakin kofar bathroom dinta har ta gama aman, ya durkusa da damuwa yace “Ohh sorry princess, plantain din ne baki so” bata iya tace komai ba ta mike da kyar ya riketa tace “Am feeling dizzy my prince” daukarta yayi ya kwantar da ita yayi kan gado yace “Toh bari mu je asibiti koh babyna” girgixa masa kai tayi tace “No I will be Alryt, bacci xan yi” ya jima yana kallonta har ya ga kamar ta fara bacci ya mike ya fita, yana sauka kasa Humainah ta wara masa ido tace “Congrat My Capt” xaunawa yayi kusa da ita ya jawota ya rufe bakinta da yatsa yace “Shiii don’t tell her that plss” dariya tayi sosai tace “Ohk ohk”