CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association????
⚓ Captain Ahmad Junaid⚓
_By Khaleesat Haiydar_✍????
8….
Bude kofar kitchen da El-Ameen yayi yasa Junaid ya mike da sauri ya koma baya, El-Ameen ya tsaya daga bakin kofar yana mata wani irin kallo yace “Wato ni ta raina xata kwale koh?” Junaid yayi murmushi yace “Kai fa ka tsokaneta gashi ka sa ta xubda hawaye, haba Dr!” El-Ameen ya karaso palon yana kallonta kanta a sunkuye yace “Xa tayi me dalili ne ma ae, ba dae ni xata kwala ma Karfe ba” mikewa tayi tana kallon kofa, Junaid ya karasa da sauri ya sa key, kallonsa ta tsaya yi, El-Ameen ya xaga ta baya ba tare da ya bari ta lura ba, ya cafke hannayenta ta baya, ta kwala wani ihu, ya kai mata rankwashi yace “Shut up!” Hade rae Junaid yayi sae dae bae ce komae ba, El-Ameen ya ja ta ya nufi stairs da ita, kokuwan kwace kanta kawai take, ya dauketa cak ya haura sama da ita, Junaid ya lumshe ido ya bude ya karasa cikin palon ya xauna, da kyar El-Ameen ya daure mata hannu, snn ya samu yayi mata allurori guda uku, ta gama fixge fixgenta da ihu ta sulale wajen sae bacci, mikewa yayi daga durkushen da yake yana kallonta, ya karasa inda take ya kunce mata daurin da yayi ma hannunta ya dauketa ya kwantar kan gado, tsayawa yayi yana kallonta ganin yanda dogon gashinta ya hargitse, ribbon din da ya gani kasan dakin ya dauka ya karasa gadon ya xauna gefenta ya dago kanta a hankali ya shiga packing din dogon gashin, da kyar ya daure mata sannan ya mike ya gyara mata kwanciya ya fita, palo ya sauko yana kallon Junaid yace “Ina tsohuwar nan?” Junaid bae tanka sa ba, El-Ameen ya tabe baki ya fita waje, xaune ya sameta can gurin wani flower tayi tagumi, ta basa dariya sosae ya karasa inda take yace “Mama nan kika dawo, ae bata komae mama kawae tsokanarta nayi shi yasa tayi hakan” Mama tace “Uhn” dariya yayi sosae yace “Allah kuwa mama, ta ma yi bacci yanxu” Mama tace “Allah sarki” El-Ameen yace “Amma bata cin abinci ko mama?” Tace “Toh gskya ni ban sani ba don xubarwa take” yace “A’a bata ci gaskiya, xan taho da maganin cin abinci gobe, mu shiga ciki to mama” ba musu ta mike ta bi bayansa suka koma palon, mikewa Junaid yayi bayan sun shigo yana kallon El-Ameen yace “Xan tafi ni” El-Ameen yace “Eh nima tafiya xan yi” kallon mama El-Ameen yayi ganin har lkcn dari dari take yace “Na rufe kofar dakin mama, kuma baxa ma ta tashi yanxu ba sae can dare” tace “Toh Allah dae ya bata lfya” yace “Ameen” a tare suka fita da Junaid, ko wannensu ya shiga motarsa ya wuce. Junaid na isa gida bayan yayi wanka ya canxa kaya ya nufi part din mumyn sa, xama yayi gefenta ya kwantar da kansa kan shoulder dinta yace “Gud evenin mum” tace “Evenin dear ya aiki? Yhu are kinda late yau” yace “Yea mum, yau Abba xae dawo koh?” Tace “He said tomorrow da muka yi waya daxu” tace “Kasan Hajja ta xo kuwa” mikewa xaune yayi da sauri yace “haba Mumy, When?” Mumy tace “Kana tafiya aiki daxu da safe” yayi murmushi yace “Amma bata san Abba baya nan ba koh?” Mumy tace “Ta sani mana yanxu dae ka ci abinci ka tafi ka gaida ta tun daxu take shigowa tana tambayar ko ka dawo har ca tayi a kai ta gun aikin naka” dariya sosae Junaid yayi yace “Ta hakura ta dawo nan din kenan” Mumy tayi murmushi tace “Nima haka nace, tace inaa kwana biyu kawae xata yi ta koma” Junaid yace “Lallai Hajja” mikewa yyi ya nufi dinning, cikin ‘yan mintuna ya sakko yace ya koshi, Mumy tace “A’a wannan baka ci komae ba junaid” Da sauri ya nufi kofa yana cewa “Allah Mumy na koshi” bin sa da kallo tayi kafin ta tabe baki, yana fita ya nufi part din grandmum dinsa, ya tura kofa da sallama ya shiga palon, tana xaune sanye da glass din ido tana dama fura, cire glass din tayi tana kallonsa, yayi dariya ganin irin kallon da take masa ya dauke furan gabanta ya rungume ta yayi pecking goshinta yace “Oyoyo granny” ta tsuke fuska tace “Ni dae daga ni Amadidi” saketa yayi ya daure fuska yana kallonta yace “Wai baxa ki bar kirana da wannan sunan ba Hajja” tace “Toh toh Junaidu, shikenan?” bude baki yayi yace “Xan fa sa asa min ke a guard room in jefa ki cikin ruwa ko don baki ganni da uniform din ba” washe hakora tayi tace “To yi hakuri soja” dariya yayi yace “Ya mutan Daura Hajja?” Tace “Wannan kuma sae ka shirya ku je kai da ubanka” Junaid ya tabe baki yace “Toh ni dae yi ki dama furar ki debar min nawa” hararansa tayi tace “A’a wannan na ni da jikata ne” yace “Wace haka” Hajjo ta juya tana kallon kofar daki tace “ke fito ki gaida yayanki ‘yar nan kina jin ya shigo kin yi mukus a daki” Junaid yace “Wacece?” Kwalo mata kira Hajjo tayi kusan sau uku sae ga ta ta fito ta karaso cikin palon ta xauna kasa jikin kujera ta hade rai tace “Na’am” kallonta kawae Junaid yake ganin ynda take rurrufe fuska da hijab yace “Wacece wannan kuma Hajjo” Hajjo ta washe baki tace “ehh baka santa ba gaskiya” sae kuma ta hade rae tace “barin ma kai da ba shiga yan uwa kake ba, ga ka kai daya namiji gun Muhammad kmr tsiya, maimakon ka dinga shiga yan uwanka ku saba, ko da yake tana karama ka santa, ‘yar uwar ka ce Humainah, ‘yar wajen kawun ka, kuma matar da na xaba maka” fashewa da kuka yarinyar tayi ta mike tana kallon Hajjo tace “Ni bana son haka fa Hajjo” daki ta nufa da sauri tana kuka, Hajjo tace “Au! Ji shirme” Junaid ya tabe baki yace “Ni dae ki dama fura ki sammin inyi tafiya ta” Hajjo tace “kai ba fa xancen wasa ba, ita na xaba maka matsayin mata tunda ka ki fito da matar aure godai godai da kai” yace “Toh bana so!” daga can cikin daki yarinyar tace “Ni ma bana so!” Hajjo ta fashe da dariya tace “Au, naga ko in ku kuka haife kan ku, xumunci ne dae sae na hada” tsaki Junaid yayi ya mike ya fice daga palon tana kiransa ko waiwayowa bae yi ba, Hajjo tace “Ahaf abinda ma a gidan xan bar ta ta kare secondary ayi auren kawae” yarinyar ta kuma rushewa da kuka tace “Wallahi baxan tsaya ba Hajjo ni ki maida ni gida kawae” Hajjo ta tabe baki tana ci gaba da dama furar ta tace “Kwa yi ku kare” Junaid na komawa part din Mumy ta bi sa da kallo ganin mood dinsa, tace “Ya aka yi Ahmad?” Cikin bacin rae yace “Wae kina jin Hajjo ta kawo wata yarinya wae xata ce a hadani da ita” dariya Mumy tayi tace “Kai kanwarka Humainah ce fa, ‘yar gidan kawu Bala” Junaid ya xaro ido yace “Au ita ce ta girma haka mumy?” Mumy tayi dariya tace “Ita ce mana” ya d’an tabe baki yace “Mumy wani colleague dinmu bae da lfya, xan je duba sa” Mumy tace “Ayya, toh Allah basa lfya, my regardz” mikewa yayi yace “Ameen Mumy sae na dawo” fita yayi rike da makullin motarsa, kallo daya yyi ma Suhaima dake xaune balcony mac book a gabanta, ya shiga motarsa ya tada ya fice daga gidan bayan mai gadi ya bude masa gate, kafin ya isa main road ya kira layin El-Ameen, bugu biyu El-Ameen dake xaune kasa gaban mahaifiyarsa ya d’aga bayan ya nemi ixinin yin haka, Junaid yace “Kana clinic koh gida?” El-Ameen yace “Ina gida” katse wayar Junaid yayi, El-Ameen ya kalli Mum dinsa da ta wani hade rae, sannan yayi kasa da kai, tace “Yauwa, in kuma ban isa da kai bane sae ka sanar da ni in ji” marairaice mata yayi yace “Wllh Ummi ranan mun je, tare da Junaid ma muka je, ae yanxu xae xo sae ki tambayesa ki ji” Ummi ta watsa masa harara tace “Ku ka je ina, ba duk jirgi daya ya kwaso ku kai da Junaid din ba, kuma ni bance ae baka je ba, Ca tayi dariya kuka dinga yi mata kai da Junaid din” xaro ido yayi ya bude baki yace “Dariya kuma Ummi, wllh fa mun mata magana” ta galla masa harara tace “Da’alla rufe min baki malam, da ban san ka da sakarci bane, sannan ka kuma tafiya da d’an uwanka sakarai kamar ka” Murmushi El-Ameen yayi yana shafa lallausan gashin kansa, Ummi tace “Kuma Dad dinku yace baka xuwa clinic da safe kwana biyun nan, sannan baka ma xaman clinic din during day time, nan kuma da sassafe kke barin mana gida, ina kake xuwa Ahmad” shiru yayi na wani lokaci kafin ya hade rae yace “Nurses din ne suka gaya masa haka koh?” Ummi tace “Dake shi makaho ne ba” shiru El-Ameen yayi bae ce komae ba, dae dae lokacin da Junaid ya shigo palon, ganin El-Ameen xaune kamar me neman gafara yasa yayi kasa da kai yyi hanyar stairs sanin sanin sai Ummi ta iya hadawa da shi kai kace shi yayi laifin, Ummi ta bi sa da harara tace “Dawo nan ina xa ka? ka wani yi kasa da kai kmr munafuki” dariya Junaid yayi yana shafa kai, ya dawo cikin palon yace “Laifi ya maki ko Ummi?” Ummi tace “Xauna nan!” Ba musu ya xauna gefen El-Ameen, Ummi tace “Ranan da ku ka je gidansu iman sa ta gaba kuka yi wae kuna ta dariya koh?” Junaid ya xaro ido yace “Dariya kuma Ummi, ae ko mun yi magana me ma’ana, nine ma nayi maganan don shiru El-Ameen yayi” Ummi bata san lkcn da tayi murmushi tana kallonsu ba, ta girgixa kai tace “Ahaf ai magana ta lalace tunda kai kayi! Wato ku baxa ku yi ma kanku fada ba ko, babu me ba wani shawara cikin ku kan ya kamata ku ajiye iyali yanxu,” Junaid yayi kasa da kai yace “Ina yi masa wallahi Ummi” harara ta xabga masa tace “Common keep quiet my frnd ai har kai” El-Ameen yayi murmushi shi ma yayi kasa da kai, Ummi tace “Toh gaskiya it’s high time ku san me ku ke, don ku ba yara bane, and yhu guys ain’t getting younger, ku yi ma kanku fada ku fito da mata kuyi aure abun ku, as a mother nake gaya maku haka, in ma baka son Iman din sae ka nemo wata very soon, kai ma Junaid kayi kokarin yin hakan kafin wata uku, I want to see my boys getting married soon, in kuma kun ban wuka da nama sae in nemo maku mata wallahi” a tare kamar sun hada baki suka ce “A’a Ummi” dariya tayi tana kallonsu, Junaid ya shafa kai yace “In’sha Allah Ummi xa muyi ynda kuke so” tace “Toh Allah yasa, ya bamu aron ran ganin bikin boys dinmu” dariya suka yi gaba daya, Ummi tace “Toh ku tashi ku tafi, Allah maku albarka” mikewa suka yi suka nufi dakin El-Ameen bayan sun amsa da Ameen, xama Junaid yayi gefen gado yana kallon El-Ameen dake kakrin kunna desktop dinsa yace “Baxa mu je can gidan ba?” Ba tare da El-Ameen ya kallesa ba yace “Kai ka tafi mana, kaga ni am busy” Junaid bae ce komai ba sae kallonsa da yake, shi kam sae danne dannensa yake ba tare da ya damu ba, Junaid ya mike yace “Ohk am off” El-Ameen yace “So early, to ka gaida Mumy” Junaid bae tanka sa ba ya fice, El-ameen ya bi sa da harara yace “You think kowa ma bai da aiki kamar ka sai na mahaukaciya yanxu” Ummi dake Palo har lkcn ta kalli junaid tace “Har ka fito?” Junaid ya dan yi murmushi yace “Dama sako na xo karba Ummi, sae gobe” tace “Toh Allah ya kiyaye, ka gayar min da Hajiyar ka” yace “Xata ji.” Sannan ya fita.