BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Ba ta jin zata iya ɓoye musu komi, sabida tana ganin kamar idan suka ji labarin ta za su taimaka mata, don haka ta basu labarin komi game da rayuwan ta wajen Yayan ta da ya kasance miji a gare ta

Sosai suka tausaya mata, Zakeeya har da hawaye sai da ta zubar mata

Nan Auntyn tace, “za su taimaka mata, zuwa gobe da yardan Allah zata koma gida”.

Amma Ɗahira sai ta roƙe su “su taimaka a yau ta bar ƙasar, baza ta iya ko ƙwaƙƙwaran mintuna bane, tunda ta samu ta gudo gwara ta koma ga iyayen ta hakan zai fi mata, su taimaka mata idan za’a samu jirgi ta bar gidan”.

Auntyn bata yi musu ba, sai ta kira mijin ta ta shaida masa komi

Nan yace mata, “ga shinan zuwa”. Babu jima wa kuwa sai ga shi ya zo, shi ne ma yaje ya nema mata jirgin, sai dai ba’a sami wanda zai je Direct to Nigeria ba dole za’a yi biye-biye wasu ƙasashe, kuma da yamma zai tashi. Direct to Nigeria kuma sai zuwa dare za’a samu

Ɗahira tace, “tana so, gwara ta tafi wani ƙasan, baza ta iya jira har dare ba,” wataƙil ma ya biyo bayan ta,” abinda take tsoro kenan.

     Haka suka taimaka mata har ta bar ƙasan, sosai Ɗahira take kuka sabida wannan karamci nasu, idan ba Allah na son ta ba, kuma sun kasance mutanen kirki, da bata san ya zata yi ba, sosai tayi musu godiya tana kuka

Amma su sun ce “sun yi mata don Allah ne ba sai ta biya ba tunda suna da halin yi, kuma kasancewar ta ƴar ƙasar su me buƙatar taimako”.

Itama Zakeeya sai da tayi kuka da za su rabu, jin ta take yi tamkar ƴar uwan ta, ga tausayin ta da take ji, Allah ne ya haɗa jinin su.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

           Usman kuwa be koma gida ba sai dare kamar yanda ya saba, yana taɓa ƙofan zai buɗe yaji ta a buɗe, mamaki ne ya kama sa ya shiga yaci karo da mukullai a bakin ƙofa, da kallo yabi wajen, sai kuma yabi parlour’n da kallo zuciyar sa na hasaso masa faruwar wani abu, da sauri ya isa cikin parlour’n yana faman kiran sunan Ɗahira, shi kansa be san cewa ya san sunan ta har haka ba, domin tunda yake be taɓa kiran sunan ta ba, tun tana ƙarama bare yanzu, sai ji yayi bakin sa na furta wa

Ko ina ya duba a gidan be ganta ba, wanda har wardrobe ɗin sa ya duba, nan yaga babu password ɗin ta, zargin sa ya tabbata guduwa tayi, duk da hankalin sa be tashi ba amma ya kasa haƙura sai da yabi bayan ta ko zai ganta, sosai ya ƙudurta a ransa “muddin ya ganta sai ya ci uwar ta yau ba uban ta kaɗai ba”.

Duk inda yabi da mota be ganta ba, ko me kama da ita be gani ba, dole ya isa wajen wani Abokin sa suka nufa airport tare, dayake shi yana da hanya, ya san nan da nan za’a bincika masa idan ta hau jirgi, duk da ba ya tunanin zata iya barin ƙasar da sauri haka, ba kuɗi ne da ita ba bare ƴan uwa

A lokacin ne ma jirgin da zata ɗaga zuwa Nigeria Direct zata tashi, nan abokin ya saka a duba musu list ɗin masu tafiya, amma babu sunan ta, sai ya tambaya “ko akwai wanda ya tashi kafin wanann?”.

Nan ne aka faɗa musu “akwai wanda ya tashi ƙarfe 04:00pm. Amma kuma ba Nigeria kaɗai zai wuce ba.” Koda aka bincika sai aka samu sunan ta

Usman be iya cewa komi ba illa jan abokin nasa da yayi suka shiga mota suka yi gaba

Abokin na tambayar sa “amma lafiya?” Tunda be san makaman zancen ba

Sai Usman yace masa ,”ƙanwar sa ce yarinyan ya neme ta ya rasa, shi ne yake bincike ko ta koma gida ne”.

      Koda ya koma gida kwanciyar sa yayi domin ko kaɗan be saka damuwa a ransa ba, hakan ma shi yafi masa, gwara da ta gudu da ƙafar ta, fargaban sa ɗaya kawai yanda iyayen sa za su ɗau fushi dashi, amma ya shirya musu dama tun farko, kuma yanzu bazai koma gida ba har sai sanda suka huce, in yaso sai ya koma musu tare da takardan sakin ta. zuwa da safe ma zai sauya Simcard don kar ma su neme sa su samu. A haka yayi barcin sa cikin kwanciyar hankali har da munshari, babu abinda ke damun rayuwar sa.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

                NIGERIA
 
      Kwana biyu su Ɗahira suka yi a jirgin kafin suka isa Nigeria, sun sauka ƙarfe 03:30pm. Amma kasancewar akwai hadari garin; sai ka zata yamma ne sakaliya, kowa sai haraman wuce wa gida yake yi tunda hadari gadan-gadan ne ya taso, dayake farko-farkon damina ne.

     Itama kanta tsaye wajen masu Taxi ta nufa, amma duk wanda ta taya ba sa ɗaukan ta tunda kowa ta kansa yake yi ganin har an fara yayyafi. Sai ta fito bakin titi tana ci gaba da tare wa, zuciyar ta gaba ɗaya ta tsinke burin ta kawai ta ganta a gida

A lokacin da ruwan ya sauko sosai, a time ɗin ne ta samu wani me kirki ya faka ya ɗauke ta, lokacin gaba ɗaya ta gama jiƙe wa sai rawan ɗari take yi

Shi kansa me taxi ɗin har ya wuce ganin ta cikin ruwan ne ya tsaya, koda ya ɗauke ta be jirga a wajen ba tunda ana tsula ruwan ne. Wajen mintina goma sha biyar kuma sai ruwan ya tsaya cak, sai ɗan yayyafi da ake yi jefi-jefi, hakan yasa ya tada motan ya nufi inda ta sanar masa.

    Suna isa bakin ƙofar gidan su kamar an yi mata bishara da gidan aljana, fita tayi tace masa, “zata kawo masa kuɗin yanzu”.

Yace, “babu damuwa yana jira”.

Ƙwanƙwasa Gate ɗin tayi, gateman ya buɗe mata

Shima be wani gane ta sosai ba, har yace, “baiwar Allah daga ina..?”

Ta katse sa da cewa, “Hamisu Ni ce Ɗahira, don Allah ka sallami me motan can”.

“To.. to Hajiya, to sannu da zuwa, sannu an dawo lafiya?”. Yafaɗa jikin sa na rawa tsaban murna

“Lafiya lau”. Tace dashi tana shige wa da sauri ta doshi cikin gidan

Tun daga nesa ta hangi Mahaifin ta da Big Dady suna tsaye a bakin ƙofan shiga gidan suna magana

Su ma sai suka tsaya kawai suna kallon ta ganin ta jaye da akwati, duk tunanin su sai ya tafi ga Ɗahira ce wannan? Duk da sun hangi wannan ɗin tamkar bata da haske kamar Ɗahira, kuma sun san cewa Ɗahira ba ta ƙasar nan, ba yanzu zata dawo ba bare su ganta a nan, amma kuma sak tafiyan ta da yanayin ta ya basu ita ce.

            Ilai kuwa itan ce don basu gama hasashen nasu ba ta gurfana a gaban su, mamaki zalla ne ya cika su ganin tabbas ita ce, sai suka buɗe baki suna bin ta da kallo ko wanne ya kasa furta komi ganin yanda tayi mugun sauya musu

Ita ko nan da nan hawaye ya wanke mata fuska, cikin rawan murya tace, “Abbu.. Dady..” sai tayi shiru tana me fashe wa da wani irin kuka me shiga zuciya

Sosai hankalin su yayi mugun tashi, lokaci ɗaya kamar an tsikare su suka yo kanta ko wanne yana me riƙo mata hannu da tambayar “me ke faruwa? Ina Usman ɗin? Ya aka yi ta dawo?” Haka suke jero mata tambayoyin ba tare da sun jira ta amsa musu ba.

.

Mu haɗu jibi don jin ya za’a kaya, idan kuma bani da aiki za ku iya samun update gobe, amma fa sai naga ruwan comments, shi ne kawai zai ɗan saka min ƙwarin gwiwan muku.
????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button