BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Gumm Sahabi yayi kansa a ƙasa, har gumi ya haɗa domin be yi tunanin sun gano shi ba, ga shi kai tsaye suke tuhumar sa da shi ne ya saka mata, be da kuma da yanda zai yi

Abbu ya amshe maganar da cewan, “ai Yaya babu maganar yana so ko ba ya so, tunda har yayi aure to dole ne ya haihu kamar yanda Annabi yace mu hayayyafa domin yayi alfahari damu, idan be son haihuwar babu dole sai ya sakar mana ƴar mu, idan ba haka ba wata rana zai je ya naƙasa mana ita kuma shi be da halin biyan mu, kayi magana ka tsaya ka sunkuyar da kai? Amma wlh ka bamu kunya bamu zaci haka a gare ka ba, ka watsa mana ƙasa a ido”.

Kaka dai duk yana sauraron su be ce komi ba

Haƙuri ya soma basu Sahabin yana cewa, “insha Allahu bazai sake ba, wannan ma kuskure ne amma wlh yana son matar sa”. Duk ya gama haɗa gumi ya nuna musu nadamar sa a fili

A nan ne Kaka ya saka baki, inda yayi mishi nasiha me ratsa zuciya, kafin yace, “ya tafi zuwa gobe sai ya zo ya tafi da matar sa, amma yau dai ya bar ta a nan tunda zata fi samun kulawa”.

Godiya sosai yayi musu kana ya miƙe ya bar gidan, be ma nemi ganin Shakiran ba ya wuce.

        To al’amarin haka dai ta faru, zuwa gobe Shakira ta koma gidan ta.

      Inda rayuwa taci gaba da tafiya sannu a hankali, kwana na wuce wa haka satikai, har ga shi yau wata ɗaya da dawowar Ɗahira daga Turkey, kuma har yanzu babu labarin Usman gaba ɗaya, wayan sa ma ba ta shiga. Zuwa yanzu Ɗahira ta samu lafiya sosai, ta koma kamar ba ita ce ta dawo ƙoɗai-ƙoɗai ba, ta murje tamkar bata yi wani ciwo ba, tunda tana samun kulawa sosai, yanzu haka ma har ta koma bakin aikin ta duk sabida ya ɗebe mata kewa, tunda ko yaushe neman hanyar da zai ɗebe mata kewa suke yi, su Abbu sosai suke iya ƙoƙarin su wajen sun saka ta cikin nishaɗi, alhmadulillah kuma komi na tafiyan mata normal, don ita har ta manta ma ta taɓa yin aure, ko Usman ɗin ba ta tuna wa bare auren dake kanta, jira kawai take yi yanzu ya dawo mata da takardan sakin ta, aure kuma ta cire sa a ranta tuni, ko idan zata sake aure ba yanzu ba.

       Yanzu sosai suka sake jone wa da Baffa, don shaƙuwar su ta yanzu har tafi na da.

         Hajja Fatu sai dai ta zuba musu idanu babu yanda zata yi dasu, domin dai duk faɗan da take masa ba ya sauraron ta, shi a ganin sa kusantar Ɗahira na rage masa raɗaɗin da yake fama dashi, tunda har giyan nasa ya dena sha sosai, duk yanda ya lalace ya bar ƙasumba a fuskar sa yanzu duk ya gyara, ya koma ɗan gayen nan nashi da duniya ta san shi, burin sa yanzu kawai Usman ya dawo ya bata takardan sakin ta, a lokacin shi kuma zai fito ya nuna wa kowa shi zai aure ta, ya shirya tsaf ko wani irin Fitina ne ma a yi.

      Ana haka sai ga Usman ya dira a ƙasan, ba da sanin kowa ba ya hayo taxi ta kawo sa gida, ana sauke sa ya nufi gidan su, ta Gate ɗin gidan ya shiga, har ya isa Part ɗin sa babu wanda ya ganshi ba ya ga me gadin da ya buɗe masa Gate.

    Gaba ɗaya Part ɗin yayi ƙura sosai, kusan wata biyu babu wanda ya sake shiga tun tafiyar su, be bi ta kai ba ya wuce kansa tsaye ɗakin sa, wanka ya soma yi ya fito ya sanya jallabiya ya soma ramukon sallolin sa, yana idar wa yabi lafiyan gado sai Barci, da zummar idan ya farka sai ya je gidan su ayi duk abinda za’a yi, ya shirya wa ko ma meye ne, bare ma ya san cewa yanzu sun sauka daga fushin da suke yi dashi, cikin kwanciyar hankali yake barcin sa babu abinda ke damun ruhin sa.

Yanzu aka soma wasan fa, ku gyara zama kawai.
????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????

????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

          \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

              EPISODE Fifty Two

         Bayan ya tashi daga barcin alwala yayi ya gabatar da sallan la’asar da ake kira a lokacin, bayan ya idar sai ya shirya cikin ƙananan kaya kamar yanda ya saba ko yaushe, riga baƙa da blue ɗin wando jeans, kayan sun haska shi sosai domin sosai suka yi masa kyau, komin sa yana yi ne a natse a kuma sanyin yanayin sa, turare ya feshe jikin sa dashi kana ya ɗauki wayan sa ya saka a aljihun bayan wandon sa ya fito daga gidan, hannayen sa zube cikin aljihu yana bin yanayin garin da kallo, da alamu hadari ne ke son haɗuwa domin har an fara yayyafi kaɗan-kaɗan duk da akwai rana be gama shige wa ba, murmushi kawai yake saki wanda samun ka ga yayi sa aiki ne, yana bala’in son wannan yanayin na damina, a ransa yana jin daɗin dawowar sa a dai-dai, ya san yanzu can kafin daminan su tayi nisa nan sun sha ruwa sosai

Tafiyan sa a natse yake yi har ya isa cikin babban gidan su, kai tsaye Part ɗin su ya wuce, yana tura ƙofan da sallama a bakin sa

Hajiya dake ƙoƙarin zama a kan kujera domin fitowar ta kenan daga ɗaki ta idar da sallah, da zummar idan ta huta ta tashi ta ɗaura girkin dare, sai jin sallaman ɗan nata tayi kamar a mafarki, hakan yasa tabi sa da kallo don ta kasa amsa mishi sallaman ma

Shi kuwa murmushi ya sake saki, sabida haka kawai yake jin sa cikin farin ciki, duk da a wani ɓangare na zuciyar sa yana jin wani irin buga wa da take yi tamkar wani abu na shirin samun sa, amma hakan ya ɗaura dalilin ne kan dawowar sa da gamuwar sa da iyayen nasa, amma kuma duk abinda za su yi shi dai a shirye yake

Muryan Hajiyan ne ya dawo dashi hayyacin sa

“Usman idon ka kenan?”

Takowa yayi ya zauna a kan kujeran dake kallon inda take tsaye

Hakan yasa itama ta zauna tana shirin magana

Sai ya riga ta ya gaishe ta

Amsa wa tayi fuskar ta babu wani walwala tace, “yanzu ka kyauta kenan? Abun da ka aikata ka kyauta mana kenan Usman ina tambayar ka?”.

Shiru yayi kawai be ce mata komi ba, illa shafa ƙeyan sa da yake yi, sai dai ya rage walwalan dake fuskar sa

Cike da takaicin halin sa tace, “wlh kai da Dadyn ka tunda irin tarbiyyan da muka baka kenan, ka jira shi ya dawo zaka ka hukuncin da za su yanke a kanka”. Tana faɗa ta tashi tayi hanyar kichen

Shi kuwa da kallo ya bi ta har ta shige, kana ya miƙe ya nufi kan dainning ganin cololi da yayi a jere, sai da ya buɗe yaga akwai abinci kafin ya zauna bayan ya zaro wayan sa daga aljihu, zuba abincin yayi a Plate ya soma ci, latsa wayan yake yi yana faman zira abincin kaɗan-kaɗan a bakin sa, duk da yunwa sosai yake gallabar sa amma hakan be sa ya ƙi wa abincin cin yanga ba.

            Be gama cin abincin ba Big Dady ya shigo parlour’n da sallama, babu inda idanun sa ya sauka sai kan Usman dake shirin kai abinci bakin sa a wannan lokacin, ido kawai Big Dady ya zuba masa

While shi kuma tuni ya tashi tsaye yana gaishe shi daga inda yake

Be amsa mishi ba illa tahowa da yayi cikin parlour’n, fuskar sa murtik yake kallon sa har ya shigo ciki sosai, kana kuma ya ɗauke kai yana kwaɗa wa Hajiya kira

Hajiya ce ta fito daga kichen da sauri tana amsa mishi, kana kuma ta ɗaura da mishi sannu

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button