BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

“Mamy har yanzu Abba be dawo bane?” Maganar sa ta katse mata guntun tunanin ta

“Be dawo ba, lafiya dai ko? In ce dai ba wani abun ka samo zaka bashi Ni ka hana Ni ba?”. Tayi maganar cike da barkwanci

Hakan ya saka shi sakin yalwataccen murmushin da yafito da jerin haƙoran sa

Sanyi taji aranta ganin ya ɗan saki ransa fiye da ɗazu ɗin, hakan yasa taci gaba da jan sa da hiran tsokana don dai tadawo mishi da walwalan sa

Shiyasa sau tari yafi ƙaunar kasancewar ta kusa dashi fiye da kowa a duniyar nan, tabbas uwa daban ce, a duk sanda yake cikin matsala, ita ke fara gane damuwar sa fiye da kowa dake gidan, that’s why yake tsananin ƙaunar mahaifiyar shi fiye da komi da kowa dake cikin duniya.

         ▪️▪️▪️

      Koda Maimuna tadawo kiran Aƙilu drever, zaman ta tayi a Parlour batare da tayi yunƙurin komawa cikin ɗakin Mamyn ba.

       Tana zaman itama Batool tafito tazauna gefen ta tana tambayan ta, “shin ta kira Aƙilun?”

Kafin ma taba ta amsa Aƙilu ya shigo yana baza idanuwa cikin parlour’n, hannun sa ɗaya riƙe da aswakin da yacire daga bakin sa ya ƙariso cikin parlour’n, ya zube ƙasa yana faman washe baki tare da yiwa Batool kirarin da ya saba

Ita kuwa nan ta biye masa suna kwasan dariyan Aƙilun daga ita har Maimuna, kasancewar sun fi saba wa da Batool ɗin, kullum suna cikin surutu da junan su, ita kuma Maimuna koda yaushe dama nata ido ne idan suna yi, sai kuma ta dara idan abun ya bata dariya, idan kuma sun sako ta sai ta tsulmiya baki, dayake ita ɗin ba me yawan surutu bane, bata da hayaniya ko kaɗan.

         Lokacin ne Mamy da ABUL KHAIRI suka fito daga ɗaki

Kai tsaye ABUL KHAIRI hanyan ɗakin sa ya wuce ko kallon inda suke be yi ba

Mamy ne taƙariso cikin parlour’n ta zauna tana amsa gaisuwar Aƙilun, sannan ta kalli Maimuna tace, “Maimuna tashi ki haɗa wa yayan ku abincin sa ki kai masa”.

Amsa mata tayi da “Toh”. tana miƙe wa tsaye, ta kalli Batool tana mata alama da ido tabiyo ta

Maƙe kafaɗa Batool tayi tana mata dariya ƙasa-ƙasa

Sai Maimunan ta marairaice fuska tasoma tafiya, har da haɗe hannayen ta biyu alamun roƙo

Amma ƙiri-ƙiri Batool taƙi motsa wa, sai ma gwalo da tabi ta dashi

Babu yanda ta iya haka tanufi kichen jiki a sanyaye, tasan halin Yayan nasu yanzu abu kaɗan zaka yi masa kuskure yaci uban ka, bare ma shi da ya tsane ta fiye da kowa dake gidan, ko kaɗan bata san meyasa ba ya ƙaunar ganin ta ba, shiyasa ba ta son ma a aike ta wajen sa bare tayi kuskuren abun da zai haɗa su.

       Ita Mamy tuni ta maida hankalin ta kan Aƙilu tana bashi saƙo, sai kuma tajiyo tana kallon Batool ɗin tace, “ke baza ki je ki shirya bane kin zauna? Ai kuwa idan Abban ku ya dawo ya hana ku fita babu ruwana, ki zauna kasa kunne kina ji na kar ki tashi ki wuce”.

Ai kuwa dasauri Batool ɗin ta tashi tayi hanyan ɗakin su tana faɗin “wlh Mamy Ni ban ma ji me kuke cewa ba”.

Itama Mamy bata tanka ta ba tamayar da hankalin ta ga Aƙilu tana sallaman sa.

      Lokacin ne Maimuna ta fito daga kichen riƙe da Faranti a hannun ta, kanta tsaye tanufi ɗakin ABUL KHAIRI ta soma Nocking a bakin ƙofan, sai dai har ta gaji babu amsa, dole ta haƙura ta tura ƙofan ta shiga da sallama.

     Yana zaune a bakin gadon sa idanun sa kafe a kan ƙofan, ashe duk yana jin Nocking ɗin but yaƙi amsa wa

Shiyasa tana shigowa idanun su suka haɗe cikin na juna, saurin sad da kanta ƙasa tayi gaban ta na matsanancin faɗuwa, ko kaɗan ba ta ƙaunar ta haɗa idanu dashi sabida kwarjinin da yake mata, shi kaɗai ne mutumin da idan suka haɗa idanu dashi take jin daban a cikin rayuwan ta, tana shiga wani yanayi da har yanzu ta kasa fassara shi

Jiki a sanyaye ta ƙariso cikin ɗakin, tanufi gefen sa inda Centre table ke ajiye gaban gadon da yake zaune, akai ta ajiye farantin muryan ta na ɗan rawa ta soma gaishe shi, tare da son isar da saƙon abincin daga Mamy

Amma kuma ko ci kanki be ce mata ba

Don haka ta juya da ninyan fice wa batare da ta kalle sa ba, sai jin saukar dakakkiyar muryan sa tayi yana faɗin, “Kee Ina zaki je da wani dogon goshin ki anan wajen? Wa kika bari ya zuba miki?”

Saurin juyowa tayi kanta a ƙasa ta duƙa ta soma zuba masa abincin a cikin Plate, sai da ta gama sannan ta zuba masa Coke cikin Cup; tunda tasan yana so sosai, kuma ko ta tafi zai iya dawo da ita, shiyasa tayi gwanintan zuba masa kar tayi laifi

Mi ƙe wa tayi da zumman tafiya, sai ji tayi an riƙe ta.

      wannan salon labarin na daban ne, ku kasance dani don jin cikakken labarin.

Zaku iya samu na a WATTPAD ɗina UMMUDAHIRAH. Please kuyi following ɗina na gode. ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button