BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Su kansu duk sun sha jinin jikin su ganin yanda Kaka ya nuna tsantsan fushin sa, abun da rabon shi da shiga irin wannan halin su kansu baza su iya tuna wa ba, ko kaɗan be da nuna fushi sosai ko da kuwa ranshi a ɓace ne, bare kuma duk sun san yanda yake son Fatima sosai, shi ne silan auren ta da Abba, don shi ya zaɓa mishi ita domin su cika burin su na son haɗa yaran su aure shi da Abokin shi kuma aminin shi Haidar, wato mahaifin ita Hajjan

Shiyasa ita kanta ta gama ruɗe wa sai kuka take yi, bata taɓa jin cewa akwai ranan da asirin ta zai tonu ba nan kusa sai yau, kuma bata taɓa tunanin zata yi nadama da sauri haka ba, gaba ɗaya jikin ta rawa yake yi ta san yau ta ƙare mata, raguwar igiyar auren nata ma duk za su ƙare.

               A cikin mintoci har sun gama taruwa gaba ɗaya, har da su Shakira da aunty Zainab da kuma Yusra, Aunty Zulaiha CE kawai babu ita sabida ta fi su nesa shiyasa ba a kira ta ba, sai kuma Hajiya Hannatu mahaifiyar ita Hajjan da kuma Hajiya Baseera mahaifiyar Umma, tunda har ita an kira sun dawo ita da Fadil, Ɗahira kuma na can

Sai Usman shima da sai yanzu ya dawo daga aiken da Big Dady yayi masa.
        

                 Nan  Kaka ya sake sanar musu da duk abinda Hajja Fatu tayi, inda ya ɗaura da cewa, “ba don ƙasa ta rufe min Aboki na ba; wlh wlh baki isa ki sake zamar min a gida ba, duk da ke ɗiyar ƙanwa ta ce yau da sai na raba auren ki da Babana, sai dai ina tuna girman Amintar mu da Haidar, wanda ina ganin kamar na ci amanar shi ne idan yau na wulaƙanta ki, Fatima kin ci arziƙin ke ɗiyar aboki na ne ba ɗiyar ƙanwa ta ba, shiyasa a yau zan bar ki kici gaba da zama da ahali na, idan kin tuba don kanki, idan kuma kina ganin hassada dake cikin ranki zai kai ki kici galaba a kan A’isha da ɗiyar ta, to, mu zuba ga ki ga duniyar nan, Allah yana kallon ki, shi ne kuma yake nuna miki ishara a duk abinda kike yi, idan zaki hankalta tun yanzu ya kamata ki yi tunda ga shi Allah ya ɗauke miki ɗan ki ɗaya a kan wannan baƙin halin naki, kaɗan ma kika gani, bazan hana Babana ɗaukan mataki a kanki ba, sai dai ban yarda ya sake ki ba sabida albarkacin wanda kika ci, amma ki sani wannan shi ne damar ki ta ƙarshe Fatima”.

“Yaya wlh ban ji daɗin abinda kayi ba, ka bar ta ya sake ta shi ne kaɗai maslaha, zaman Fatima a gidan nan be da wani amfani, tunda ita abinda ta saran ma kanta kenan, wlh kin yi asara kin kuma bani kunya, bazan miki baki ba amma kaɗan kika gani, kuma in Allah ya yarda yanzu zaman Usman da Ɗahira aka fara, duk sharrin da kike bin A’isha da Ɗahira sai dai ya koma miki, da Allah suka dogara kuma baza su taɓa taɓe wa ba”.

Gaba ɗaya parlour’n tsit suka yi suna sauraron faɗan Hajiya Hannatu da take tayi ba sassauta wa, in  banda kukan Hajjan babu abinda ke tashi

Daga baya ma Hajiya Hannatun ita da Hajiya Baseera sukai ta mata faɗan tare, sai da suka wanke ta soso da Sabulu

Kaka ne ma ya tsayar da su ya ce, “ya isa haka”.

Sai a lokacin Abba yayi magana, inda ya ce, “daga yau ya soke aikin Hajja Fatun baza ta sake zuwa aiki ba ko da kuwa wani asibitin ne, kuma ya raba ta da Hajiya Sa’ima, idan har ta sake mu’amala da ita ya sani, to, daga ranan shi ya yanke alaƙar aure da ita”.

Babu wanda ya hana shi kuma a kan hukuncin nasa, gani ma suke yi kaɗan yayi mata, domin ba don da Kaka ya hana sakin ta ba; da tuni ta tsufa a gidan su

Haka kowa ya tafi yana tirr da halin Hajja Fatu, inda ita kuma ta sha kunyan duniya

Usman haka ya tafi duk ranshi a ɓace, ya so ya tanka amma ya san sai dai ran kowa ya ɓaci a wurin, shiyasa yayi shiru. Shi ya ɗauki su Hajiya Hannatu ya tafi da su, domin so yake yi idan zai kai Hajiya Baseera ya gano Ɗahira tunda ya ji suna faɗin, “tana can”.

      Ɗahira na zaune a Parlour tun fitan su Hajiya Baseera ta tashi ta ɗauko lemo Mountain Dew ta hau sha, sai da ta kusa shanye wa kafin taje ta ɗauko mata madara na gari ta sake sauran lemon a Cup, sai ta dinga zuba madaran tana juya wa har sai da yayi kauri sosai, kafin ta saka cokali ta hau shanye wa

Dama kafin su fita ita da Fadil sun girka faten dankali sun ci tare, suna gama wa ne aka aiko kiran Hajiya Baseera shi ne suka koma tare.

             Tana gama shanye wa sai da ta lanɗe kofin tass kafin ta kai kichen ta dawo ta kwanta a doguwar kujeran ta, kamar zata yi barci sai kuma ta sake jin kwaɗayin girka shinkafa, haka ta wuce kichen ta haɗa shinkafan ta me manja da ya ji daddawa da yaji zaƙwai, ta dawo Parlour ta ware ƙafafu tayi ta tusa wa a cikin ta, duk da ta ƙoshi amma tsananin kwaɗayin girkin ya hana ta sukuni, haka take ci tana jan majina saboda azaban zafi dana yaji, amma bata saurara mishi ba har sai da ta kusa cinye wa tass ya rage saura loma biyu

A lokacin ne su Usman suka shigo parlour’n da sallama, gaba ɗaya kallon ta suke yi ganin yanda take ta faman haɗa gumi ta warware ƙafafu Plate a gaban ta tana ta siɗe yatsu

Itama kallon su tayi, lokaci ɗaya ta haɗe rai ganin har da Usman, sai tayi saurin janye nata idanun tana saka hannu da sauri ta kwashe sauran ta cinye tana miƙe wa tsaye, da Plate ɗin ta wuce kichen ta je ta ajiye Sannan ta je Toilet, sai da ta wanke hannun ta da baki sannan ta ɗauraye fuskar ta kafin ta fito tana zama can kujeran dake kallon wanda suka zauna a tare, tace, “har kin dawo Kakalle?” Tayi maganar idanun ta a kan Hajiya Baseeran

Ita kuma sai da ta sauke numfashi kafin tace, “iy na dawo, na tsaya ina ganin ikon Allah ne Ɗahira, yanzu ba da zan fita ba kika gama cika cikin ki da abinci ba?”

Ɓata fuska tayi tace, “Kakalle wlh kamar ban ci komi bane, kuma na ga ai kun daɗe da fita”.

“Eh na ga alama ai, tunda ga shi nan daƙyar kike numfashi”. Hajiya Baseeran ta faɗa tana kallon Ɗahiran dake ta faman gyara zama ta gagara zama waje ɗaya don daƙyar take iya nishi, sai jan skert ɗin ƙasa take yi saboda ya tamke mata cikin

Shi Usman ma dariya ta ba shi, shiyasa ya kasa jure wa, domin tunda ya shigo da kallo kawai yake ta bin ta yana ganin ikon Allah

Ganin yana murmushi sosai sai ta tsargu ta kalle shi ta balla mishi harara tana tashi zata wuce ɗakin da ta sauka

“Ah ah Ina kuma zaki je? Ko sannu ma baki yiwa mijin naki ba kuma Kinga tare muka shigo?”

“Ina zuwa Hajjaju bari in cire wannan skert ɗin ya matse min ciki”. Tayi maganar tana shige wa ɗakin

Dariya Usman yayi yana kallon Hajiyan itama da take taya shi, yace, “wai lafiyan wannan yarinyan ƙalau, ko dama haka masu cikin suke da cin tsiya tun ba’a kai ko ina ba?”

“To ai ka san kowa da irin nashi, wani sai yana ƙarami ne ka ga ya fi cin abinci, wani kuma sai ya girma, to ƙila nata haka yake, ga ta nan fa har raman nata ya shige, har ta fi kyan kallo ma yanzu wlh, da kam kamar a hure ta, ko kai ai zaka fi jin daɗin ta a haka mata tubarakalla”.

Murmushi kawai yayi yana zaro wayan sa cikin aljihu jin an yi masa Text.

        Lokacin Ɗahira ta fito ta sauya shigan ta cikin doguwar riga fara me gajeren hannu, tana da taushi sosai don kamar na Barcin nan ne, sai hula da ta sanya a kanta shima fari me tuntu a tsakiyar kai. Zama tayi tana faɗin, “me ya faru da aka kira ki Kakalle? Allah yasa dai lafiya?” Tayi maganar hankalin ta duk a kanta tana jiran jin abinda zata faɗa, don dama har da jiran ta take yi domin taji abinda ke faruwa, tunda ta so ta bi ta tace mata, “a’a baza ta je ba”. Kuma ta san ba lafiya ne ba, ba don haka ba da tuni ta shige ɗaki domin baza ta dawo ta zauna ba tunda ta ga da Usman suka zo

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button