BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Yaƙe Ɗahira tayi tace, “Na gane ki mana. Ai na san ki a Hospital ɗin nan”.

“Haka ne. Wannan ƙawata ce sunan ta Safra, mun zo miki ta’aziyya ne, sai kuma taya ku murna a kan dawowar ku”.

“Allah Sarki Nagode sosai”.

“Allah ya jiƙansa Allah ya gafarta masa”. Suka haɗa baki ita da Safran suka faɗa

Ɗahira ta amsa da “Amin Amin”. Tana jin idanun ta suna ciko wa da hawaye.

“To zamu tafi, sai kuma mun sake kewayo wa”.

Daga nan sallama suka sake yi sannan suka fice.

        Suna fita Ayush ta kalli Office ɗin Dr. Usman, ji take yi kamar ta ganshi ya fito

Safra ta dafa mata kafaɗa tace, “zo mu wuce don Allah, ai komi ya kusa zuwa ƙarshe tunda ga shi Allah ya bayyana su basu mutu ba, so yanzu burin mu zai cika, kar ki soma ko da da wasa ki je Office ɗin sa sai sanda muka cika aikin mu. Yanzu abun da ya kamata mu shiga jikin ita matar tashi, ta hakan ne zamu samu muna shiga gidan su har mu samu gashin kanshi, wannan hanyar shi ne me sauƙi da zamu bi, dole sai mun zama ƙawayen ta”.

Murmushi Ayush tayi tace, “gaskiya ne ƙawalli, ziyaran gaba kuma gida za mu kai mata”.

“Ashe kin gane. Mu je mu ƙarisa maganar a mota akwai wani Alhaji da na samo miki, na san zaki fi jin daɗin harka dashi yana da kuɗi sosai. Kin san ya kamata mu soma shirye-shiryen biki ma tun yanzu”.

Dariya suka yi har da kashe wa suka yi gaba cike da nishaɗi, barin ma Ayush da bakin ta yaƙi rufuwa, tun ranan da bayyanar su Usman ɗin yazo kunnen ta, kullum ba ta iya barci tsaban murna.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

          Fannin Abba kamar yanda yayi ƙudirin sake aure ashe be fasa ba abun na ranshi, har ya sanar wa su Big Dady da Kaka, inda Kaka yaso ƙin amince wa tare da tausan sa “ya haƙura yaci gaba da zama da ita a haka”. Amma shi yace, “dama shi yana da burin sake auren, kuma ya rigada ya yi niyya”. Dole Kakan ya ƙyale shi tare da saka mishi albarka a kan maganar

To abu kamar wasa sai ga shi Abba ya samo wata bazawara dake cikin anguwan nasu, yaran ta biyu duk ka yara ne, na farkon ma sa’an Fadil ne, mijin ta ya rasu ne wajen shekara biyu, Abokin shi yayi mishi hanyar ta, don haka tuni Abba ya amince da batun nata

Har aka saka rana Hajja Fatu bata sani ba, domin yaƙi sanar mata, sati Uku aka saka, sai da ya rage saura sati ɗaya sannan ne ya sanar mata, shima don taga yana kwashe kayan ɗakin shi yana mayar wa ɗakin Baffa ne, don a ɗakin nasa zai ajiye ta

Nan fa Hajja ta tashi hankalin ta a kan “sai ya faɗa mata dalilin sa na cire kayan shi ya mayar can”.

Shi ne yake faɗa mata, “aure zai yi”.

Bazan iya fasalta muku haukan da Hajja Fatu tayi ba, tayi borin tayi kukan domin ya fasa auren

Amma sam yace, “bata isa ba tunda yayi ninya”.

Wannan dalilin ne ya kawo saɓani a tsakanin su me girma har Hajja tayi yaji ta koma gida. Ko kwana bata yi ba Hajiya Hannatu (Ihsan) ta dawo da ita, tace, “sam wannan shirmen ba dai a gidan ta ba, kuma wlh muddin ta tafi wani wuri yaji; zata haɗu da fushin ta”. Dole ba don taso ba Hajja ta zauna a gidan, amma fa fitina yaƙi ƙare wa a dole sai Abba ya janye auren nan

Sai dai kuma babu abinda ya fasu sai ci gaba da bikin ake yi, domin har Kaka ya zaunar da ita ya kwantar mata da hankali amma ta ƙi ji, dole suka zira mata ido tayi ta gaji ta bari.

      Ana saura kwana huɗu bikin ne Sa’adatu ta haifi ɗiyar ta mace ƙatuwa, abun mamaki duk girman cikin nan kuwa, domin har ya zarta wata tara kowa yayi tunanin ƴan biyu ne, sai dai Allah ya nuna ikon sa ashe mace ce. Dole aka ɗaga bikin zuwa ranan suna sai a haɗa ayi tare.

                SUNDAY
      Ranan biki da ya kasance ranan suna, an raɗa wa yarinya sunan Hajja Fatu, Fatima za su na kiran ta da Zahra

Gida ya cika maƙil tubarakalla, mutane sai dai suka tare a sauran Part ɗin, amma Hajja ta hana kowa shigo mata sashi, Shakira ma bata zo ba saboda tana taya uwar ta kishi

Su kuwa duk yaran gidan suna sashin su Ɗahira, dayake yafi girma nan, a nan suka shantake suna ta hira. har da su Fadila da su Salma ita ma da babyn ta ita da Shamsiyya duk sun zo

Ɗahira na cikin su ana ta washe baki, duk kansu sun yi ankon kamfala doguwar riga me ruwan zuma da ratsin fatsi-fatsi na milk

Yanzu haka ma abinci suke ci shi ne suke ta shewa

Uwar surutu Firdausi ta kalli Ɗahira tace, “wai ke yaushe ne mu kuma zamu dawo musha sunan ɗan mu? Kin wani ƙaƙabe tunda kika shige gidan Yaya Usman kin ƙi sulluɓo mana ɗa”.

Dayake su ba su da labarin zaman da suka yi, iyakan iyayen su suka ji labari

Ɗahira hararan ta tayi tace, “sai ranan da kika yi naki auren kika fara sulluɓo ɗanki kafin Ni in diro nawa”.

Dariya suka yi

Inda Salma ta amshe zancen da faɗin, “ai wannan rasa kunyan ba yanzu ba, zaki sha wahala kuwa idan kika ce zaki jira ta”.

Gyara zaman ta Firdausin tayi tace, “faɗa mata dai, sai kun yi yara bibbiyu ko uku-uku kafin Ni nawa ke tafe”.

Su Aunty Zulaiha dake zaune saman gadon Fadila na da, sun yi ɗai-ɗai suna ci a saman, a tare suka haɗa baki ita da Aunty Zainab wajen faɗin, “keee Firdausi kiji tsoron Allah, da gaske kike yi?”

Sai duk ɗakin suka kwashe da dariya

Yusra da ta bigi bayan Firdausin tana cewa, “ai kuwa da kin shiga uku kuwa, kiyi ta zama a gida babu Aure, ko da kuwa da gaske kike yi zan sami Gwaggon namu in kitsa mata ayi-ayi kema kin ƙosa tunda shigowa cikin manya kike yi kina kwasan gulma”.

“Oh su Yusra manya, wlh kin daɗe baki ce mata ba, ga ƙuda can zai riga ki”. Cewar Firdausin tana fuske wa

Ɗahira tace, “wai ba batun wasa ba da gaske kike yi don Allah?”

“Da gaske ne mana”. Tafaɗa tana kai loman tuwon ta

Sai duk suka tsaya suna kallon ta

Shamsiyya da ta miƙe da kwanon tuwon ta, dayake ita kaɗai take ci tace, “kin ga banu kuwa, ki zauna har sai kin tsofe”. Ta ƙare maganar da fice wa

Salma tace, “ku kun dauka da gaske ne? Ku dena biye ma wannan wlh an kusa saka mata rana, domin Ni da Daddy muka yi zancen nan kwanaki da naje gida”.

Sai Firdausin ta ɗaka mata duka a cinya tace, “wato dama ke kika ziga shi ko? Ashe shiyasa yazo min da zancen in turo Wanda nake so, ga babban muna-fuka a gefe ina tare da ita”.

“Kambu… Ni kika duka Firdausi? Dan Allah Ɗahira riƙe min yaron nan wlh sai na rama, zan ga dani dake waye muna-fuka kina so kina kaiwa kasuwa”.

“To kaji kun fara ko? Dama babu daman ku haɗu waje ɗaya”. Inji Aunty Zulaiha

Ita kuma Firdausi tunda taga ta yunƙuro ta tsame hannun ta cikin tuwon ta ruga aguje tabar ɗakin

Salma na mara mata baya tana cewa, “wlh ko cikin Momy kika koma sai na ƙwaƙulo ki na rama, gwara ma ki tsaya”.

Me za su yi ƴan ɗakin ba dariya ba, sosai suke dariya. Inda Aunty Zulaiha take ta kwaɗa wa Salma Kira a kan “kar ta bi ta ta dawo”. Amma ina tuni ta fice

Ɗahira dake ta faman dariya tashi tayi tana girgiza yaron Salman tace, “ai gwara ta bi ta ta zane mata jiki tunda Firdausi ta raina ta, kamar ba yayar ta ba”.

Aunty Zulaiha tace, “to ai ga shi nan ta bar miki wannan yaron me shegen kukan jaraba, kema ki bi ta wlh duk ya kure mana kunne”.

“Haba Aunty. Kema fa kin kusa haihuwar ba’a san ke kuma wanda zaki haifa ba, kin manta goyon Ilham da idan kika zo da ita gidan nan har Abbu sai yayi Magana tsaban jaraban kukan ta?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button