BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

“Amma kin sha magani?”

“A’a”.

“To maza tashi ki je kici abinci sai ki sha, me ke miki ciwo ne?”. Aunty Amaryan tafaɗa tana kallon ta

Shiru tayi don baza ta iya cewa ga inda ke mata ciwo ba, kawai ba ta jin daɗin yanayin ne sam, sai kuma zazzaɓi dake son kama ta kaɗan-kaɗan

Jin tayi shiru sai tace mata, “kin yi shiru ina magana?”

“Mama zazzaɓi ne kawai”.

“Ai ba kawai ba ne, gwara a tare shi tun kafin ya kwantar dake, je ki ci abincin”.

“To”. Ta amsa ta tana tashi ta fice

A lokacin Umma na zaune a parlour’n

Sai tace, “Umma sannu da huta wa”.

“Ɗahira kin dawo? Lafiya ko?”

“Lafiya lau Umma, yau dai ba na jin daɗe wa ne shi ne na dawo in huta”.

“Ai kuwa dai gwara ki riƙa huta wa da aikin nan, ayi mutum kullum babu hutu dole ki gaji”.

Murmushi kawai Ɗahiran tayi tana zama saman kujeran dainning, ta soma ɗiban abincin ta zuba a Plate

Ita kuma Umma tuni ta mayar da hankalin ta ga kallon ta, tana kallon maimaicin LABARI NA da ake yi

Ɗahira da har ta soma cin abincin sai duk tunanin ta ya koma ga abinda Usman yayi mata yau, sai ta soma jin zuciyar ta na tashi, duk yanda taso ta daure amma ta kasa, da sauri ta tashi ta wuce ɗakin ta, ta shiga Toilet ta dinga kwarara aman kamar zata amayar da hanjin cikin ta, ga shi babu komi a cikin nata shiyasa duk ta gama galabaita, sai da ta gama kafin ta wanke bakin ta ta tashi ta fito, kan gadon ta ta dawo ta zauna sabida gaba ɗaya jikin ta babu ƙarfi

Kamar mintuna biyu da zaman ta kafin ta tashi ta fito Parlour

Umma da kallo take bin ta cike da tuhuma tace, “lafiyan ki ƙalau kuwa Ɗahira? Kamar naji kina ƙaƙarin amai ko?”

Hannun ta ta cire daga bakin ta tana bata amsa da faɗin, “lafiya lau Umma, abincin nan ne be min daɗi ba shi ne ya saka Ni amai”.

“To fa?” Umma tayi maganar tana waro ido waje, sai kuma ta koma taɓe baki tana sake bin ta da kallo

Ita dai Ɗahira tuni ta wuce ta zauna, memakon taci gaba da cin abincin sai ta tsaya juya cokalin, sai kuma daga baya ta tashi ta wuce ɗakin Maman ta

Da ta tambaye ta “taci abincin?”

Sai tace mata “Eh”.

Sai ta ɗauko mata first eid box ɗin maganin su, ta ciran mata na zazzaɓin ta miƙa mata

A nan tasha sannan ta kwanta a doguwar kujeran ɗakin.

       Abu kamar wasa sai Ɗahira ta wuni a ranan tana amai

Tun Aunty Amarya bata sani ba har ta gane, dole ta buga wa Abbu waya ta sanar mishi halin da Ɗahiran take ciki, tunda duk ta sha magani har da na tsayar da aman amma yaƙi tsaya wa. Sai daga baya kuma zazzaɓi ya rufe ta ciwo sosai.

       Da sauri ya nufo gidan, yanda ya ganta sai yace, “kawai a wuce da ita asibiti”.

Lokacin duk mutan gida sun ji labari, Kaka ne kaɗai ba’a faɗa mishi ba.

      Da isar su asibiti aka fara bata taimakon gaggawa, wata likita ce me duba ta

Kamar mintuna talatin sai ta fito ta buƙaci ganin su Abbu

Sai da suka shiga suka ga jikin nata da sauƙi sosai, don lokacin idon ta biyu ana mata ƙarin ruwa, sannan sai suka wuce wajen likitan.

        Sanda ta faɗa musu result ɗin Ɗahiran ya matuƙar girgiza su, a tare suka furta, “ciki?”

Murmushi tayi likitan tace, “eh mana DOCTOR’S ko kuna mamaki ne?”

“Amma kin tabbatar Dr. Maryam?” Cewar Abba

“Eh ƙwarai ciki ne da ita har na tsawon three months, I congratulate you all”. Ta ƙare maganar still tana murmushi

“Ok mun gode Doctor, babu dai wani abu dake damun ta ko?” Big Dady yayi maganar

“Babu gaskiya, sai dai fatan Allah ya raba lafiya”.

        Fitowa suka yi suka wuce ɗakin da Ɗahiran ke ciki

A lokacin Yusra ta cire ma Ɗahiran drip ta shiga Toilet

Sai ita da Aunty Amarya suke ɗakin zaune

Bayan sun shigo ne Abbu ke tambayar “Ɗahiran fa?”

Yusra ce ta ba shi amsa da “tana Toilet”.

“Ok”.

Aunty Amarya ta tambayi Abbun abinda ke damun Ɗahiran?

Shi ne yake sanar mata

A lokacin Hajiya da Umma da kuma Aunty Jamila Amaryan Abba suka shigo ɗakin, sai maganar ya faɗa kunnen su

Kowa mamakin cikin yake yi duba da yanda suka san ba zaman lafiya ne a tsakanin su ba. Sai dai kowa yayi gum ya bar mamakin sa a ciki tunda dai sun san mace da mijin ta bare su yi zargi, hakan na nufin daga can ƙauyen da suke abun ya faru…

                Ɗahira dake shirin fitowa, tana jin abinda Abbu ya faɗa ai sai tayi taga-taga zata faɗi, tayi saurin jingina da bango jikin ta na rawa sosai, wani irin gumi ne ya soma keto mata nan da nan hawaye suka soma zirya a fuskar ta, bakin ta na rawa daƙyar ta furta, “ciiiik..cikiiii”.

????????
Flash Back…
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

\F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

      *EPISODE Sixty Three*

              Ta san cewa wannan watan ne kawai bata ga period ɗin ta ba, amma bata ɗau abun da wani tunani ba tunda wani time ɗin tana tsallaken wata. amma taya har tana da cikin wata uku ba tare da ta sani ba?

“Ya ilahi… Allah kasa mafarki nake yi ba gaske ba”. Tayi maganar tana zubar da hawaye sosai daga fuskar sa

Sai kuma ta lumshe idanun ta lokaci ɗaya abinda ya faru a wancan ranan ya dawo mata, tabbas ranan na ɗaya daga cikin ranakun da baza su taɓa gushe wa a duniyar rayuwar ta ba…

       A ranan Baba Jaure ya tafi jeji da yammacin ranan wanda yace musu “sai zuwa gobe zai dawo”

Zuwa dare sai ga hadari ya haɗu. Tana zaune tana ɗan matsa ƙafafun ta tana bin su da magani

Sai ga Usman ya shigo ɗakin. Zama yayi yana bin ta da kallo wanda ita tuni ta kawar da nata idanun tunda tayi mishi kallo ɗaya tana sake haɗe rai

Kamar ta tambaye shi abinda ya shigo dashi ɗakin, sai kuma taga wahalar da kanta zata yi kawai

Kamar shuɗewar mintuna biyu duk idanun sa na kanta, sai kuma ya buɗi baki yace, “kawo in taya ki”.

Shiru tayi masa bata kalle shi ba bare ya sa ran zata tanka shi

Sai ya taɓe baki yace, “don ma kin samu ina kula ki shiyasa kike min abinda kika ga dama ko? Yayi kyau”. Yafaɗa yana ɗauke kai

Duk bata kula shi ba, domin yi ma tayi kamar babu shi a ɗakin.

      Ruwan ne ya sake kece wa kamar da bakin ƙwarya, sai ta ɗaga kai ta kalli ƙofan, sannan ta mayar da idanun ta kanshi tace, “Malam ka fita zan kulle ƙofa”.

“To na hana ki ne?” Yayi maganar ba tare da ya kalle ta ba

A fusace tace, “ka san dai bazan iya kwana da kai a ɗakin nan ba ko? Ko ka fita ko in fice in bar maka”.

Ɗan kallon ta yayi yaga alamun fa a sama take, sai be ce komi ba ya tashi ya fice

Taja tsaki tana raka shi da harara wanda be san ma tana yi ba, lallaɓa wa tayi ta tashi a hankali ta isa ƙofan ta tura shi, kana ta koma ta kwanta a shimfiɗar ta, ta ɗan jima tana tunanin da ya zame mata jiki, wanda ba komi bane sai tunanin mutanen gidan su, sai kuma daga baya tayi addu’a ta shafa ta juya kwanciya tare da rufe idanun ta, babu jima wa kuwa barcin ya fizge ta.

      Fannin Usman kuwa tunda ya fita sai yayi tsayuwar sa a tsakar gidan ruwa na ta dakan shi, sai da yayi sharkaf wanda ya ɗau kusan mintuna goma a cikin ruwan, kafin ya samu ya wuce ɗakin kwanan shi, kayan jikin shi ya cire ya sauya da wani riga da wando farare na Fulani, sai kuma ya kwanta yana ta faman tunani, gaba ɗaya zuciyar sa ta hana shi sukuni babu abinda yake tuna wa sai Ɗahira, da sanda lokacin bata farfaɗo ba yana wanke mata jiki, har tunanin sanda ya ganta babu riga a can Turkay sai da ya faɗo mishi, shi kansa be san yana murmushi ba tsaban nishaɗin da yake ji a ranshi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button