BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Kuma zaman gidan ma yayi mata daɗi tunda Usman ba ya zama, sai hakan ya saka ta farin ciki ainun, gwara kar ya dawo tayi ta zama ita kaɗai da ta ganshi a cikin gidan.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

              NIGERIA
   

       Fitowa tayi daga ɗakin majinyata na yara, kai tsaye ta nufi Office ɗin Hajja Fatu

Ita kuma a lokacin tana shirin fita daga Office ɗin nata

Safna tayi saurin dakata wa tana me ce mata, “Dr yaron nan fa ya farka, yanzu time ɗin ba shi maganin sa ya yi, kuma na duba lockern gadon sa babu komi”.

Tsaki Hajja Fatu taja, tana bin Safnan da harara tace, “ke dai wlh baza ki taɓa sauya wa ba, ban san wani irin yarinya ce ba, common dalla shige ki ɗauka ga yi can, Ni Bani da time ɗin ki”. Da gama faɗar hakan; sai ta wuce ta tafi

Murguɗa baki Safna tayi tace, “kai wannan Matar kullum jaraba, bazan sauya ba ko baza ki sauya ba? Ni ban san me na tare miki ba wlh”.

A Haka Safna take ta mita a ranta har ta ciro maganin cikin wani kwali da ke ajiye tsakar Office ɗin, domin ta duba ma’ajiyar maganin bata ga komi ba, tana buɗe kwalin sai ta ga kamar shi ne, bata tsaya bincika wa ba tayi waje da sauri. Kai tsaye ɗakin yara ta wuce, inda ta je kan wani yaro dake kwance magashiyan Mahaifiyar sa na riƙe da shi, haɗa maganin tayi ta ba shi, sannan tayi masa alluran da ta haɗo dashi, kana tayi wa matar sallama ta wuce gadon gaba, duk sai da ta tabbatar babu wani matsala kafin ta fito ta nufi Office ɗin ta, haɗa kayan ta tayi tunda lokacin tashi yayi, tana fito wa ta wuce Lifter tayi downstairs. A reception suka kusa cin karo da Baffa, tayi saurin matsa wa tana ba shi haƙuri

Be bi ta kanta ba ya yi waje abin sa, motan sa ya hau ya bar Office ɗin, gaba ɗaya idan ka kalle sa duk ya gama sauya wa, tamkar ba shi ba, yanzu kwata-kwata ba ya da fara’a, be son yawan yin magana bare dariya, wuni yana kaɗaita kansa yana faman tunanin Ɗahira, har yanzu yayi iya yin sa ya kasa cire ta a rai.

     Yana zuwa gida kai tsaye ɗakin sa ya wuce ya buɗe ya shige

Ƙaran buɗe ƙofan nasa ne ya janyo hankalin Sa’adatu dake zaune a ɗakin ta, sai ta fito ta nufi ɗakin nasa kanta tsaye, domin yau so take yi ayita ta ƙare; ta gama gajiya

Shiga ɗakin tayi ko sallama

Baffa dake duƙe a bakin Fridge yana shirin buɗe wa domin ɗaukan win ɗin sa, sai ganin ta yayi a cikin ɗakin sa, hakan yasa ya dakata da abinda yake yi yana bin ta da mugun kallo

Ƙarisowa inda yake tayi tana cewa, “Baffa Ni fa na gaji da abubuwan da kake min a gidan nan, na gaji wlh, yau sai dai ka faɗa min matsayi na a wurin ka, don bazai yiwu ina zaune a matsayin matar ka ba amma ka maishe Ni tamkar ba kowa ba, babu wani zaman soyayya, kullum ba na sanin halin da kake ciki, idan ka saka ƙafa ka fita ba ka dawo wa sai sanda ka ga dama, kuma idan ka dawo sai ka ƙule ɗakin ka ka rufe kanka baza ka bar Ni na shigo ba, kai kuma ba ka zuwa ɗaki na, ba ka cin abinci na, wannan wani irin rayuwa ce? In CE dai aure na kake yi ba wani abun ba?”

Da mugun kallo kawai yake bin ta be da ninyan cewa komi, haka ya miƙe ba tare da ya buɗe Fridge ɗin ba yayi bakin gado ya zauna

Hakan da yayi mata sai ta zuciya ta isa gaban sa tana girgiza tace, “wai don Allah me nayi maka ne da zafi da ka dena min magana? Wlh idan har baka sauya ba zan bar gidan nan, tunda kai ba ka ƙauna ta ai iyaye na suna so na”.

“To dama na riƙe ki ne? Ki fi ruwa gudu mana, ki fice min a ɗaki da Allah ina da abin yi”.

Kuka ta fashe dashi tace, “wlh bazan fita ba, sai ka faɗa min abinda nayi maka ka sauya min, idan ba haka ba ƙaran ka zan kai wajen Abba tunda ka dena jin maganar Hajja”.

Miƙe wa yayi ya kama hannun ta ya ja ta zuwa waje, ya tura ta yace, “ki je ki sanar wa Baban Abba ba Abba ba, dama Ni na gaji dake”. Ƙofan ya maida ya rufe, har da saka keey

Nan Sa’adatu ta dinga dukan Ƙofan tana kuka tana faɗa masa magana, “wai don ya ga ya gama da ita dole yace zai yar da ita, to wlh sai ta zubar da cikin jikin ta don baza ta haife sa ba”.

Yana jin ta amma be tanka ba, illa ma ɗauko win ɗin sa da yayi ya hau kurɓa wa

Har ta ƙarishe fitinar ta ta shige ɗakin ta, harhaɗa kayan ta ta hau yi tana kuka, bayan ta gama ta ja Trolly ɗin zuwa wajen motan ta, “wlh yau sai na bar gidan nan, na gaji da wulaƙancin da Baffa yake min kuma Hajja ta kasa ɗaukar mataki, babu dole auren”. Ta faɗa tana ci gaba da kukan ta, tana saka kayan ta ta shige taja motan ta ɗauki hanyar Lagos, duk da ta san dole dare zai yi mata a hanya amma hakan be shafe ta ba, Fatan ta kawai ta isa gidan su ta sanar wa da Momyn ta komi.

          Shi kuwa Baffa be ma san wainar da take toya wa ba, ƙarshe ma da giyan ta bugar da shi; barci ya hau yi, be tashi ba kuwa sai dare, alwala kawai yayi ya nufi masallaci ya gabatar da sallolin da ya wuce sa, inda daga nan ya wuce Part ɗin iyayen sa

A nan Hajja take tambayar sa “ina Sa’adatu?” Domin yau kwata-kwata bata shigo sun gaisa ba

Sai ma lokacin shi ya tuna da ita, sai yace mata, “tana ɗaki”.

“To amma dai kana kula da ita ko? Ka san me ƙaramin ciki dole sai ana bata kula wa, kuma har yanzu ƙorafin ta ɗaya ne ka ƙi ka koma yanda kake, kaji tsoron Allah Baffa, wlh akwai ranan da Allah zai tambaye ka”.

“Hajja ki dena min irin haka don Allah, ai kullum jin tsoron sa nake yi, da ba na jin tsoron sa da bata kawo iyanzu a ɗaki na ba”.

“Au iyeeeee? Me kake nufi to?”.

Kumbura baki yayi yana shafa ƙeya yace, “to ke ne ai Hajja da wani magana, ke ma kin san ba na son ta, ban taɓa son ta ba, ga wacce zuciya ta take so can amma kika liƙa min ita”.

Hajja tace, “lallai kam wuyar ka ta isa yanka Al’ameen, yau kuma rashin kunya zaka yi min? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Allahumma ajirni fi musibatin..”

Miƙe wa kawai yayi ya fice ba tare da ya sake tanka mata ba

Sai kawai Hajja ta fashe da kuka tana cewa, “eh lallai A’ishah, kin rantse sai kin ga bayan ɗana, yanzu ji be yanda kika mayar min dashi, gaba ɗaya ya dena min biyayya kamar baya, ko kaɗan yanzu ba ya jin kunyan faɗa min duk abinda yake so; duk a dalilin ɗiyar ki, Allah ya isa tsakani na dake A’ishah, insha Allahu sai kema kin ɗanɗana abun da naji, kuma wlh Al’ameen ya fi ƙarfin ki har abada, bazai taɓa auren ɗiyar ki ba, da yardan Allah zan tashi masa tsaye sai dai duk wani sharri ya koma miki. Kai kuma mu zuba dani da kai zan gyara maka zama, Allah ya kai mu goben har gidan naku zan zo in ci uban ka hankali kwance”.

             **** ***** *****

       Baffa kuwa yana koma wa gidan su, kai tsaye ɗakin sa ya wuce, be duba ko Sa’adatun tana nan ba, ko ta aikata abinda tace zata yin na tafiya gida ba, shi dai be bi ta kanta ba tunda dama tuni ya daɗe da fita shirgin ta, ɗakin sa ya shige, sai da ya kora kamar yanda ya saba sannan ya haye gadon sa, haka yake ta sambatu yana kiran sunan Ɗahira har barci ya sure sa.

28/6/2021.
????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button