BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Ai kuwa sai suka koma yiwa Aunty Zulaiha dariya

Ita kuma tana cewa, “dalla can ina Ilham tayi kukan wannan yaron, ai wlh ita idan kin ga tayi kuka sai dai abinci take nema”.

Ajiye yaron tayi tsakiyan su tace, “to ga shi ku riƙe mata shi, tunda ku ne babu yara a hannun ku bari inje in dawo”.

Har ta juya zata tafi caraf Aunty Zulaiha ta riƙe mata hannu tace, “dawo. Dawo nan babu inda zaki tafi ki bar mana yaron nan wlh, ki bari uwar sa ta dawo”.

Su Yusra sai dariya suke musu da Shamsiyya da ta dawo sawo miya

Inda ita kuma Ɗahira ta nace sai ta tafi ta bar musu

“Ke wlh bar ganin yanzu kin soma kumari ba fi na ƙarfi kika yi ba, yanzu sai in zaune ki a nan, ki ɗauke shi kinji ko?”

Kama haɓa Ɗahiran tayi tace, “kai Aunty har da kuma sharri. Don Allah wlh yanzu zan dawo zan je wajen Kaka ne”. Tayi maganar cikin marairaice fuska

Hararan ta tayi kana ta kalli Aunty Zainab da itama dai dariya take musu tace, “gane min hanya Zainab, wannan yarinyan ba tayi ƙiba ba?”

“Tayi mana, wlh da gaske Ɗahira kin yi kumari kamar ba ke ce silindiyan gidan mu ba, duk ɗauka na ma yanda kike kamar a huren nan babu abinda zai saka ki ƙiba, amma tunda kika dawo ƙauyen can naga kin sauya sosai, da alamu furan ruga ya karɓe ki dole in ce aunty Amarya ta nema miki fura ya zama abincin ki idan har tana son ɗiyar ta ta zama irin mu tubarakalla”. Aunty Zainab ta ƙare maganar nata da dariya

Sai duk kan su suka fashe da dariya kowa na faɗin, “ai wlh da gaske ne yanzu duk ta sauya”.

Itama dai Ɗahiran murmushi kawai tayi don ta san zancen su ba ƙarya bane

Fadila da ta shigo ɗakin yanzu take cewa, “wai me ake tattaunawa ne babu mu?”

Nan Shamsiyya take sanar mata suna dariya

Sai itama tayi dariyan tana cewa, “kin ji sister ki riƙa addu’a kina tofa wa wlh, idan ba haka ba sai dai ki tashi ki ga kin tsiyaye tsaban idanu dake yawo a kanki, ba dama dai aga mutum yayi kumari yayi ɗan kumatu sai a saka shi gaba, dama waye yace baza kiyi ƙiba ba? ai ba haka zaki zauna ba kamar ana ɗiban ki ana miya. komi da lokacin sa”.

             Da haka dai suka yi ta hiran su inda suka canza zancen kuma da labarin Amaryan da za'a kawo musu, kowa na faɗin albarkacin bakin shi.

       Da yamma aka kawo Amaryan Abba me suna Jamila, tare da yaran ta guda biyu Suhail da Abdulra’uf, an sauke ta ɗakin Abba inda aka gyara mata shi aka cika mata maƙil da kaya sai son barka. Su kuma yaran ta za suna kwana a ɗakin Shakira na da, don Abba har ya saka an gyara musu

Babu abinda ya kai wannan baƙin ciki wajen Hajja, tamkar ta mutu sai dai babu yanda zata yi ne, tana ji tana gani wata banza ta zo zata mallake mata gida, ina bazai saɓu ba dole ne sai ta samar wa kanta mafita.

        Haka a ranan dai aka sha biki duk aka watse don ba wanda ya kwana sai ƴan nesa.

         *

           Washe gari Usman na Office ɗin shi wani staff ya shigo kamar yanda ya saka a nemo mishi shi

Gaishe shi yayi cikin girmamawa kafin yace mishi, “ga shi ya zo”.

Kallon shi Usman ɗin yayi sosai, kana kuma yace, “kai ne wanda aka taɓa aiko ka da envelope ka kawo min?”

“Eh Ni ne”. Ya amsa shi shima idanun shi a kanshi

“Ok zaka iya gane wanda ya aiko ka?”

Shiru yayi na ɗan daƙiƙu, kana yace, “eh insha Allahu idan har na ganshi zan iya gane shi”.

“Ok you can go”.

Fita yayi a Office ɗin

Shi kuma Usman ɗin sai ya jawo drowan table ɗin shi ya yago pepper a jikin wani memo, rubutu yayi kafin ya ɗago pepern yana kallo, tabbas idan be manta ba wannan address ɗin shi ne ya gani a jikin pictures ɗin, sake ƙura wa peppern idanu yayi yana sake nazartan rubutun, sai kuma ya lumshe idanun sa yana jan numfashi, ya buɗe su yana cije leɓen bakin sa, kana kuma ya ajiye takardan tare da ɗaura biron akai.
????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

        EPISODE Sixty Two

           AFTER TWO WEEKS

          Yana cikin ɗaura agogon sa daga hannun sa na hagu, sai yaji wayan sa ta soma ƙara, sai da ya ɗan leƙa ya tabbatar da wanda yake tsimaye ne kafin ya ɗauka yana karawa a kunne

Daga can mutumin yace, “ranka ya daɗe! gani tare da su na gama aikin”.

“Ok turo min address ɗin”. Daga haka ya kashe wayan yana ajiye wa

Ci gaba yayi da ɗaura wrest watch ɗin, bayan ya gama sai ya miƙe daga bakin gadon shi da yake zaune, takalman sa ya zira cover shoes baƙi sannan ya ɗauki wayan sa ya zira a aljihun gaban rigan shi ya fito ya rufe gidan ya fice, kai tsaye Part ɗin iyayen shi ya wuce, yana shiga da sallama ciki-ciki

Hajiya ta amsa mishi da ke zaune a kan dainning tana yin kari

Wajen ta ya nufa ya zauna a ɗaya daga cikin kujerun, sannan ya gaishe ta a miskilancen da ya saba

Amsa mishi tayi tana bin shi da kallo, sai kuma dai tace, “ina zaka je da safen nan?”

Hannu ya saka yana haɗa tea yana bata amsa, “zan je wani wuri ne”.

Bata sake mishi magana ba haka suka zauna Kamar kurame

Sai kuma can yace, “Dady ya tafi ne?”

“Eh ya fita tun ƙarfe 06:30am. Amma kai ya batun maganar ku da Ɗahira? Ka san cewa ya zura maka ido ne yaga iya gudun ruwan ka da ya neme ka kaƙi kazo, ya kamata tun wuri ka kawo mishi takardan yarinyan nan kafin haɗuwar ku, idan kuma ka ce baza ka sake ta ba kamar yanda kace ɗin ne, to, tun wuri ka neme shi ka ba shi haƙuri, don na san shi ne yafi ɗaukan zafi, idan kuma ba son zama da ita kake yi ba gwara ka sake ta ka dena cutan ƴar mutane da auren ka a kanta”.

Shiru yayi be ce komi ba, illa shan tea ɗin shi da yake yi, amma kuma abaɗini juya kalaman Hajiyan yake yi

Ganin be kula ta ba itama sai ta tashi ta wucewar ta ta bar shi nan

Be ƙara mintuna biyu cikakku ba shima ya tashi ya fice, kai tsaye gidan su ya koma ya ɗauki mota ya fice, a lokacin ne ya duba wayan sa yaga address ɗin hotel ɗin da aka turo mishi, sai ya wuce can.

              Har ciki ya shiga da motan shi yayi parking, kafin ya fito sai da ya saka baƙin glasses a fuskar sa sannan ya fita ya nufi room ɗin da aka turo mishi, yana zuwa dai-dai ɗakin yayi Nocking

Sai ga wani saurayi ya buɗe mishi ƙofan

Ya shiga yana bin ko ina da kallo ta cikin glasses ɗin sa yana yatsina

“Suna cikin wancan ɗakin”. Cewar saurayin kanshi a ƙasa

“Ka tabbatar su ne?” Yayi maganar yana kallon sa fuska a ɗaure

“Eh wlh su ne suka bani aikin, bazan manta su ba tunda na san ɗaya daga ciki”.

“Ok mu je”. Yafaɗa yana yin gaba cikin bedroom ɗin

Shi kuma mutumin yabi bayan shi jiki na rawa

Da shigan shi ya sauke idanun sa a kan Safra da Ayush dake zaune an ɗaure musu hannu da ƙafa kuma an rufe musu baki, zare idanu kawai suke yi ganin Usman sai zufa ya fara keto musu tsaban tsorata fiye da yanda suke a farko

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button