BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Baba Jaure dai duk yana kallon sa be sake ce mishi komi ba, amma tausayin sa ne sosai a ransa, a lokacin sai yace, “yau kwanan ku goma a waje na sai yanzu da ka samu kai ka farfaɗo, na tsince ku a gefen kogi ne cikin mawuyacin hali, wanda ita ƴar uwan taka ta samu karaya a duka ƙafafuwan ta sai raunuka. kai kuma ka samu ciwo a kanka da hannun ka”. Shiru yayi

Usman dake bin shi da kallo tun soma maganar nasa yace, “amma ina ne nan don Allah?”.

Murmushi Baba Jaure yayi yace, “kar ka damu zaka sani, nan wani yanki ne dake cikin jeji, kuma zagaye muke a ruwa”.

Duk da Usman yana son sake mishi magana amma ya kasa buɗe baki yayi, illa hannun sa da yake tabi da kallo yana cike da raɗaɗin azaba

Ganin yayi shiru be ce komi ba sai yace, “ga magani ka sha”.

Still shiru Usman yayi kuma be ɗago ya kalle sa ba

Sai shima be sake cewa komi ba illa tashi da yayi ya koma gefen Ɗahira, a nan ya ɗibi maganin a cikin tafin hannun sa yana zuba mata a baki

Da kallo kawai Usman yake bin shi dashi yana yamutsa fuska, har ya gama yaga ya soma shafa mata magani a raunukan ta

Sai da ya gama yace mishi, “ka sha maganin nan, shi zai taimaka maka wajen rage raɗaɗin da kake ji, kaji ko?”

Gyaɗa kansa Usman yayi, ya amshi maganin ya kafa kai ya sha

Baba Jaure fita yayi, sai ga shi ya sake dawowa da wani kwanon, ya miƙa mishi ya sake ba shi umarnin yasha

Hakan kuwa yayi ya amsa yasha, wannan duk ɗaci amma be ce komi ba har ya gama sha

Sai ya sake fita, zuwa can ya dawo mishi da fura ya bashi

Usman amsa yayi ya kafa kai ya shanye domin yana buƙata

Sai da ya gama Baba Jaure yace mishi “zai fita zuwa jeji, bazai daɗe ba zai dawo”.

Shi dai Usman be ce mishi komi ba har ya fice, kana ya mayar da idanun sa kan Ɗahira, kallon ta kawai yake yi kamar ya sami t.v, abinda tunda yake be taɓa mata ko kallon second uku bane, a ƙasan zuciyar shi yana jin wani abu na taso mishi me kama da tausayi, ita yake tausayi ko kuma kanshi yake tausayi ya kasa sani, sai ya ɗauke kai kawai yana mayarwa kan hannun shi, duk idan ya kalli yanda hannun nasa yayi rami sai kawai yaji hawaye suna son cika mishi idanu, “kenan nashi azaban nafila ne a kan yanda ita take ji? Ko ya ya take ji?” Ya yiwa kansa tambayar yana me sake mayar da idanun sa kanta

Kamar zata yi magana haka fuskar ta tayi, sai dai kuma babu inda nata yake motsi, har ta numfashin ma ba ya ganin tana yi

Sai yayi saurin kai hannun sa mara ciwon ya tsinci kansa da aza shi saman ƙirjin ta, memakon yaji bugun zuciyar ta, sai nashi ne tayi wani irin buga wa sabida saukar hannun sa a saman ƙirjin ta. Saurin janye hannun nasa yayi yana ɗaura wa a kan nasa ƙirjin, lokaci ɗaya ya lumshe idanun sa yana me ci je leɓen ƙasan bakin sa, sosai yake jin bugun zuciya wanda yaja tsawon lokaci a haka ya kasa taɓuka komi, so yake yi ya sake ɗaura hannun sa don yaji bugun numfashin ta, domin be ji komi ba sanda ya saka, amma kuma tsoro ya hana shi mayar wa, haka kawai yanayin da yake ji a jikin sa yasa ya kasa buɗe ido bare ya mayar da hannun sa a ƙirjin ta

Tsawon mintuna biyar kafin ya buɗe ido yana bin ta da kallo, shiru kawai yayi shi be dena kallon ta ba; shi kuma be yi abinda yake ninyan yi ba. A haka har Baba Jaure ya dawo ɗakin, a nan ne ya samu kanshi da tambayar Baba Jaure, “ita yaushe zata tashi?”

Baba Jaure da ya sami wuri ya zauna yace, “gaskiya tana cikin wani hali sosai, ta fi ka shan wahala shiyasa zai yi wuya ta farfaɗo yanzu, sabida tasha ruwa da yawa, amma idan an dace tunda ina bata maganin da ya kamata tasha, insha Allahu zata tashi ba da jima wa ba, sai dai mun yi haƙuri”.

Usman kallon sa yayi yace, “ina son mu koma gida saboda a bata taimakon gaggawa”.

Baba Jaure yace, “yaro ba na tunanin za ku samu barin nan wajen a nan kusa”.

“Meyasa?” Yayi masa tambayar har yanzu yana bin sa da kallo

Gyara zama sosai Baba Jaure yayi kana yace, “kamar yanda nace maka ne nan wani yanki ne dake cikin jeji, muna cikin tsakiyar ruwa ne gaba ɗaya ƙauyen namu, kuma gaskiya mutanen cikin ta ba sa fita idan har wannan lokacin ya yi, ma’ana lokacin damina ba ma iya fita zuwa cikin gari, sakamakon yanda ruwa ya tabaibaye mu, sai idan damina ya wuce shi ne hanya zata kafe har mu sami hanyar wuce wa, amma idan muka sake muka bi ta cikin ruwan a cikin kwale-kwale, to, mutuwa ake yi, Ni kaina nasha mamakin ganin ku kun fito daga cikin ruwan ba tare da kun rasa ranku ba, saboda gaskiya ruwan nan duk wanda ya faɗa ko ya sake ya shiga ciki, yana ji yana gani za’a janye shi a nemi gawan sa a rasa, wanda na tabbatar da cewa mutanen ruwa ne suke hana mu fita duk sanda aka ce damina yayi, dole duk wani zirga-zirga muna yin ta ne ba lokacin damina ba, zamu shiga cikin gari mu nemi duk abinda zamu iya buƙata, sabida ana fara ruwa mu da fita har sai damina ta ƙare, to ka ga kuwa fitan ku cikin garin nan sai bayan damina idan muna da rai Zaku yi ta zama har lokaci yayi”.

Usman kasa ce mishi komi yayi sabida tashin hankalin dake tattare dashi

Baba Jaure yace, “amma ina son ka faɗa min abinda ya faru da ku har kuka tsinci kanku cikin wannan ruwan? Da kuma alaƙar dake tsakanin ku”.

Usman samun kansa yayi da faɗa mishi gaskiya, ma’ana “ita matar shi ce wasu suka sace ta, shi ne ya biyo bayan su wannan tsautsayin ya faɗa musu,” duk abinda ya faru dai sai da ya faɗa mishi

Jinjina kansa Baba Jaure yayi cike da zallan tausayin su yace, “haƙiƙa na tausaya muku, kuma Allah yasa da rabon zaku sake tsawon rai a gaba shiyasa har kuka samu kuɓuta. Allah ya kyauta gaba, sai kayi ta addu’a har sanda matar taka zata farka, amma mene ne sunan ka?”

“Usman”. Ya sanar mishi a taƙaice

“Ita kuma fa?”

Sai da Usman ya ɗago kai ya kalle shi kafin tunanin shi ya kai ga Ɗahira, a hankali ya buɗe bakin shi yace, “NAFEESA”. Sai ya samu kanshi kuma da maimaita sunan a ranshi

Baba Jaure dai fita yayi ya barshi a ɗakin

While shi kuma ya haɗa kanshi da ƙafafuwan shi sai ya hau faman tunani, tunanin kawai yanda zai iya rayuwa a nan yake yi, sai tunanin dangin shi suka faɗo mishi, lumshe idanun sa kawai yayi yana ta tunani cikin ranshi.

                   Tun ranan da ya farka ko ƙofar ɗaki ya ƙi fita bare ya ga yanayin garin, kullum be da aikin yi sai tunani da kallon Ɗahira, a kullum gani yake yi kamar zata yi magana ko kuma motsi, amma dai yanda take har yanzu haka take

Baba Jaure shi ke zuwa ya shafa musu magani, idan yazo yana jan Usman da hira amma shi komi ba ya iya ce mishi, sai dai ya riƙa sauraren shi

Yau ga shi kimanin kwana biyar kenan da farfaɗowar shi, ganin har yanzu Baba Jaure be ce mishi idan zai yi wanka ya fito ba, sai shi yayi masa maganar “yana son yayi wanka”.

Baba Jaure yace masa, “idan zai iya to bari ya ɗumama mishi ruwan, dama yana jiye mishi ciwukan shi ne kar ya taɓa ruwa”.

Bayan ya ɗumama mishi ruwan ya sanar mishi

Sai Usman ya tashi ya fito, da kallo kawai yake bin gidan, fili ne fetete da aka zagaye shi da kara, sai bukkoki kusan guda shida a jere har wanda suke ciki, sai kuma ɗaya dake can gefe ƙato, da alamu shi ne ban-ɗaki

Baba Jaure ya Yi masa nuni da wajen

Sai ya taka ya wuce ya shiga, tsaban ƙyamƙyami irin na Usman ya kasa yin wankan, duk da babu komi a bayin domin a tsaftace yake. Haka ya wanke fuskar shi da bakin shi, sai kuma ƙafafuwan shi ya watsar da ruwan ya fito, fuskar shi duk babu alamar fara’a, yana jin taya ya ma zai iya rayuwa a nan babu kulawa babu wanka

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button