BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Sosai tambayar ya baƙanta mata rai, sai ta kalle sa kamar zata make shi tace, “ba na ji ko dole sai nayi?”

Tsaki yaja yace, “na san kina ji tunda kin kwana biyu baki yi ba, sai dai idan Ni ne ba kya son na taimaka miki sai Baba Jaure”.

“Allah ya kiyaye na nemi taimakon ka, abubuwan ma da kake min da zaka fasa da nafi kowa murna, ba na ƙaunar ganin ka wlh ko kaɗan a kusa dani, ji nake yi kamar zan haɗiye zuciya na mutu, mugu azzalumi kawai”.

A zuciye yace, “Nafeesa Ni kike faɗa wa haka? Wato kina ganin ina ƙyale ki shi ne yasa kike faɗa min duk abinda kike so ko?”

“An faɗa ɗin, ka kashe Ni ka huta shi ne zan san ka isa”. Ta ƙare maganar tana sakar masa kallon tsana

Hannun sa ya saka ya murɗe mata baki yana cewa, “bakin zan fasa ko zaki dawo hankalin ki kisan da wa kike magana, Ni ba sa’an wasan ki bane, ina ƙyale ki ne kawai domin ina tausaya miki”.

Kuka ta fashe dashi jin ya murɗe mata baki sosai

Ganin tana kuka sosai sai ya sassauta riƙon amma fuskar sa a ɗaure yace, “ke ki shiga hankalin ki kisan da wanda kike magana, Ni ne Usman kuma na san baki manta halina ba, wlh bar ganin kina halin lalura biji-biji dake zan yi”.

Bata iya cewa komi ba illa kuka da take faman yi

Ganin haka sai yaja tsaki yana tashi zai fice

Ƙasa-ƙasa tace, “mugu azzalumi Allah zai saka min wlh, kuma kashi ne bazan yi ba, kuma ma ina jin yi har da fitsarin ma”.

Dariya taso ba shi sai dai be juyo ba yayi ficewar sa

Ita kuma taci gaba da kukan ta tana yi tana tsine masa a ranta

A haka har Baba Jaure ya dawo, yana shigo wa ya ganta tana kuka ya tambaye ta ba’asi

Sai tace mishi, “Usman ne ya murɗe mata baki sannan ya falla mata mari”. Har da riƙe kumatun ta tana me fashe wa da wani kukan

Salati kawai Baba Jaure yake saki yana faɗin, “ashsha.. be kyauta ba, wannan ai mugunta ne, ba ya ganin halin da kike ciki ne?”. Sai kuma ya koma kwaɗa wa Usman ɗin kira

Usman dake waje duk yana jiyo ƙaryan da Ɗahira ta shirga mishi, ci je leɓe kawai yayi yana jinjina kansa, sai ya miƙe ya nufi ɗakin ba tare da ya amsa ba, yana shiga idanun su suka shige na juna

Sai ta balla mishi harara tana kawar da kanta

Shi kuma fuskar nan a ɗaure kamar ko yaushe yake sauraron faɗan Baba Jaure ba tare da ya ɗauke idon sa a kanta ba, duk da kuwa ba kallon sa take yi ba, “zan kama ki ne yarinyan nan zai fita ai, zan mare ki sai ki sami faɗa mishi da hujja tunda ke baki da mutunci”. Yayi maganar a ranshi

Sai da Baba Jaure ya gama mishi faɗan kafin yayi ficewar sa be ce komi ba

Ita kuma sai a lokacin ta dawo da kallon ta ga Baba Jaure tace mishi, “tana buƙatar zata yi fitsari”.

“To kuma sauri nake yi ina da rubutu a gaba na, meyasa baki ce Usman ɗin ya taimaka miki ba?”.

“Baba na Ce mishi amma yace bazai taimaka min ba, shi ne dalilin da yasa ya mare Ni”.

Baba Jaure yace, “be kyauta ba kuwa, bari in taimaka miki to, zan yi masa magana daga yau bazai sake ba”.

Taimaka mata yayi ya ɗan ɗaga ta ya saka mata wani Robber me faɗi, sai ya koma bakin ƙofa har sai da ta gama ta gyara kafin ya dawo shi kuma ya gyara mata kwanciya ta yanda baza ta motsa ƙafafuwan ba.

     Duk abinda ta sake faɗa a kunnen Usman ya faɗa, kaɗa kai kawai yayi ya yi ficewar sa a gidan, ransa babu daɗi duk haushi ya cika sa, haka kawai yake jin haushin Baba Jaure Wanda be San dalili ba, “don me shima zai yarda ya riƙa taimakon ta bayan ga shi shi ne mijin ta? Ai wannan ma cin zarafin sa ne da kuma keta mishi haddin aure”. Sosai zuciyar sa ke a ɓace shiyasa ya nufi jeji kansa tsaye don keɓe kansa, amma wani zuciyar nasa tana faɗa masa, “kai meye naka na jin haushi bayan sakin ta zaka yi? Ko ka manta ka tsane ta ne? Sannan ma Baba Jaure ai kamar Kaka yake a wurin ta, halin lalura ne ya kawo haka dole sai an taimaka mata”. Dogon tsaki kawai yaja a fili ya furta, “to Ni ina ruwa na.. yayi mata wanka ma idan zai iya be shafe Ni ba”.
????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????

????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

\F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

            EPISODE Fifty Eight

           Sannu a hankali Ɗahira ta soma jin sauƙi, domin babu laifi yanzu tana iya ƙoƙarin ta wajen jure wa da zaman nata, ba ta motsa ƙafafuwan kullum kaffa-kaffa take yi, a haka rayuwa taci gaba inda kusan watanni huɗu kenan da soma jinyan nata, yanzu har ta soma taka wa

Baba Jaure ya haɗa mata sandan nan guda biyu da zata riƙa dogara wa

Tun ba ta iyawa da taimakon Usman da Baba Jaure ya saka shi yana koya mata tafiyan, har yanzu tana iya fita zuwa waje wani lokacin ba tare da taimakon shi ba, zaman jinya ba wasa ba, gaba ɗaya ta sauya tamkar ba ita ba, tayi wani irin haske kamar mara jini a jiki, sai kuma ƙara ramewa da tayi a fuska, sai kuma ɗan kumbura da tayi a jiki, sai dai jikin nan nata luwai-luwai kamar ka taɓa jini ya tsiyaya, saboda zama wuri ɗaya da ta jima tana yi, duk ta sauya dai. Yanzu haka har wanka tana yi da kanta, inda Baba Jaure ya samo mata itama kayan su na Fulani tana sauya shiga.

              Ga shi yanzu har sun gabatar da azumi a wannan ƙauyen, sai dai ita Ɗahira bata samu tayi ba saboda halin da take ciki, an yi sallah an gama lafiya kuma sun yi farin ciki matuƙa kasancewar sun fita sun kalli wasan sallan mutanen ƙauyen.

                Duk da gefe ɗaya kuma gaban su da Usman kullum daɗuwa take yi, kusan kullum sai sun yi faɗa, ita bakin ta bazai yi shiru ba babu ranan da baza ta sanar mishi ta tsani ganin shi a rayuwar ta ba

Shi kuma hakan na mishi zafi sosai, sai ya biye mata suyi ta yi tana ƙara ƙona mishi rai, shi kuma a ganin shi yana ƙyale ta ne don halin lalura, ba don haka ba zane mata jiki zai yi, amma duk da haka tsaban mugunta be fasa mangare ta ba ko kuma ya kwaɓe mata baki idan tana gaya mishi maganar da yayi mishi ɗaci a zuciya.

          Yau ma tana zaune a waje tana shan iska

While Usman na zaune can gefe ya buga tagumi yana bin ta da kallo, sai dai a baɗini tunani ya faɗa be ma san idanuwan sa na kanta ba

Ita kuma ganin yaƙi dena kallon ta tun ɗazu sai taja tsaki tana yinƙura wa zata tashi

Tsakin nata ya dawo dashi hayyacin sa, sai ya bi ta da kallo kawai har ta miƙe, ganin ta nufi ƙofar gida zata fice sai yace, “ina zaki je?”

Bata juyo ba bare ta tanka shi, taci gaba da ɗingisa wa a hankali zata fice

Shima sai be sake ce mata komi ba ya kawar da kansa gare ta, ya ɗaura tunanin sa daga inda ya tsaya.

              Ɗahira na fita ta soma bin garin da kallo, tun ranan sallah da ta fita sai yau ta sake saka ƙafafuwan ta a wajen, shiyasa kawai take ta bin ko ina da kallo, yanda ko ina yayi kore sharr da bukkokin gidaje sai ya bata sha’awa, tamkar dai babu kowa a garin haka wajen ya ɗaɗe, takawa ta soma yi tana ci gaba da tafiya tana kallon ko ina, jefi-jefi kuma ta soma ganin Mutane, yara a waje suna wasa da kuma hayaniyar mutanen cikin gida

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button