BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

DEDICATION to the family of GOMA’S Family, and to every family, joy and happiness be with them. Happy family❤️????‍????‍????‍????????‍❤️‍????

Mu haɗu a sabon book ɗina me suna ABUL KHAIRI (LABARIN DEEBIZAH RETURN) kar ku bari a baku labari.

                  ƊANƊANO

            ABUL KHAIRI

                 Lumsassun idanuwan sa da suke cike taf da barci ya ware su a kan ta

Tana kwance gefen sa, hannun ta ɗaya saman ƙirjin sa da babu riga, barci itama take shararawa wanda yayi wa cuty face ɗin ta kyau matuƙa.

     Idanu kawai ya zuba mata cike da takaicin ganin ta kusa dashi, sake ware idanuwan sa da suka sauya kala zuwa ja yayi, ya mayar dasu kan hannun ta dake ƙirjin sa, dogon tsaki yaja kafin ya saka hannayen sa biyu ya riƙo hannun nata ya sauke kan jikin sa ya yarfar dashi

Wanda hakan sai da yasa taji zafi sosai cikin barcin ta, babu shiri ta farka tana zare idanu ba tare da ta motsa ba

Shi kuwa tuni ya ma sauka akan gadon, yana gyara rigan zuwa jikin sa, tare da ɓame bottles ɗin gaban rigan da suke a buɗe gaba ɗaya

Kallon sa kawai take yi tana karantan yanayin sa, sai da ta gama ƙare masa kallo har ya gama abinda yake yi, ya zari makulle zai fice ba tare da ya sake kallon ko inda take ba, ai kamar ƙiftawar ido ta dira daga kan gadon tasha gaban sa da sauri, har da saka hannu tana kare sa alamun bazai wuce ba

Sauke idanun sa yayi akan ta cikin ɓacin rai da ya nuna a face ɗin sa, sai dai be iya ce mata komi ba illa kallon ta da yake yi yana sake haɗe rai

Ita kuma yatsina kyakykyawar fuskar ta tayi, kafin ta kafa masa manyan idanuwan ta tace, “Wai ina zaka je ne ka bar Ni bayan kasan me ya kawo Ni wajen ka? Bie babu inda zaka je wlh sai mun tsayar da maganar mu, tunda ka ƙi ɗaukar waya ta to na biyo ka”. Sai kuma taja numfashi tana ci gaba da faɗin, “Wlh idan har baka yarda da buƙata ta ba Bie, na rantse da Allah zan nemi mafita kamar yanda na faɗa maka, kasan kuma Ni ɗin ina da waɗanda suke jira na in Kai musu kain…”

“ZIYA..” Yafaɗa da ƙarfi cikin tsananin ɓacin rai da ya ninka wanda yake ciki, lokaci ɗaya farar fuskar sa ta sauya kala tayi jazur, haka ma jijiyoyin kansa sosai suka fito raɗau

Ƴar siririyan dariya ta saki tana kallon yanda gaba ɗaya ya sauya lokaci ɗaya, hakan kuma sosai ya faranta mata don tafi son yayi zuciya yabi ra’ayin ta, cikin yatsina tace, “kar ka yimin tsawa Bie, kasan bazan ɗauka ba, kuma kabar tunanin bazan iya rabuwa da kai bane, wlh akan haka sai mu raba hanya..”

Damtsen hannun ta da ya damƙe ƙam, shi ya hana ta ƙarisa maganar ta, domin sosai zafin ya shige ta

Matso da fuskar sa kusa da nata yayi yana huci, idanun sa sun sake yin jazur fiye dana da, cikin amon muryan sa me haɗe da fushi yace, “Wlh kinji na rantse miki idan har kika ba ma wani daman riƙe hannun ki; ba shiga jikin ki ba ma, wlh wlh sai kinyi dana-sanin sani na a rayuwan ki! bazan hana ki rabuwa dani ba, sannan bazan hana ki aikata duk abinda kike so ba, fine ki aikata kinji ko?” Yaƙarike maganar da girgiza ta yana ware mata jajayen idanun sa, sai kuma ya janye ta daga gaban sa ya nufi ƙofa dasauri ya fice

Duk da ba wani jan ta yayi ba sai da ta faɗi ƙasa, sabida rashin ƙwarin jiki, ƙofan tabi da kallo cike da tsoro a ranta, babu shakka tasan Kishin da yake mata zai iya aikata komi, idan tace komi tana nufin komi zai iya yi a kan ta, sai dai kuma ba ta tunanin zata nuna tsoro ko gajiyawa da buƙatan ta, domin baza ta zauna dashi ba ya biya mata buƙatan ta ba, sannan kuma ya hana ta zuwa inda za’a biya mata, tabbas zata ci gaba da tunzura sa don ganin ta cin ma burin ta

Itama miƙe wa tayi ta zura Takalman ta, sannan ta ɗau gyalen ta; ta rataya a kafaɗa tafice dasauri.

             ▪️▪️▪️

      Motan sa ya gangarar da ita gefen titi, babu abinda zuciyar sa ke yi sai suya, iska kawai yake faman fesar wa daga bakin sa yana riƙe da sitiyarin motan, ya rasa meke masa daɗi a lokacin, sabida kalaman ta daga jiya zuwa yau sai kai komo suke masa a rai

Hannu ya saka ya soma hargitsa gashin kansa cike da tsagwaron KISHI dake cin sa, sai kuma ya kwantar da kansa jikin kujeran yana lumshe kyawawan idanun sa, ya jima ahaka be ɗago ba illa numfashi da yake sauke wa yana faman ci je leɓe, daga ƙarshe kuma yayi wa motan keey ya fige ta da gudu yayi gida.

      Gate man na buɗe masa Gate ɗin gidan ya kutsa motan ciki, a parcking space yaja birki yana kashe motan, sai dai be yi yunƙurin fitowa ba illa ma gyara zaman sa da yayi yana dafe kansa.

▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️▪️

        Eyeglasess ɗin fuskarta ta sake gyara masa zama akan cikakkiyar kamilalliyar farar fuskar ta, murmushi yalwace a fuskar ta take kallon su tana magana, “Ba na son ku je ku zauna acan har in kira waya, idan kuwa kuka bari na aikata hakan, to Ni da ku ne, don kun san bazan sake barin ku zuwa ba”.

Da sauri Batool ta dafa gwiwowin ta, har da ranƙwafo da kanta tana faɗin, “Wlh Mamy baza mu daɗe ba, idan muka je ma muna gaishe ta da jiki zamu dawo”.

Jinjina kanta Mamy tayi kafin ta maida idanun ta kan Maimuna tace, “je ki kira min Aƙilun zan ba sa saƙo ne”.

Da sauri Maimuna ta tashi tafice daga ɗakin Mamyn, da gudu ta nufi hanyan parlour, ta buɗe ƙofan fita tana shirin saka kai waje taji tayi karo da mutum, kafin ta tabbatar da wanda suka ci karon, sai ji tayi an janye ta da ƙarfi an yi wurgi da ita gefe, ai babu shiri ta saki siririn ƙara jin ta faɗa a saman hannun ta, da sauri ta ɗago kanta tana bin sa da kallo idanuwan ta cike fal da hawaye

Shi kuwa be ma bi ta kanta ba, ya taka yashige fuskar sa a ɗaure tamau kamar be taɓa dariya ba

Bata dena kallon sa ba har ya shige ɗakin Mamy, sai taja majina tana matse idanunta hawayen ciki suka samu daman zubo wa, jiki babu ƙwari ta tashi tafice don kiran Aƙilu drever’n su.

        Tura ƙofan yayi da sallama ciki-ciki

Mamy da Batool suka amsa mishi duk kan su suna juya wa ga ƙofan, dasauri Batool ta miƙe tanufi ƙofan tana mishi sannu da zuwa

Be amsa ta ba, ita kuma tafice abun ta

Tako wa yayi ya zauna a kan kujeran dake cikin ɗakin, hakan yasa yake fuskantan Mamy dake zaune gefen gadon ta tana kallon sa

“Baba na lafiya kuwa?” Ta tambaye shi cike da kulawa sabida sauyawan da tagani a tattare dashi

Sakin faukar sa yayi sosai yana ƙoƙarin dai-dai ta kansa, cikin ƙwaƙulo murmushi yace da ita, “Mamy lafiya ƙalau me kika gani?”

Hakan yasa tasaki murmushi wanda ya zame mata ɗabi’a, koda yaushe fuskar ta a sake yake cike da annurin fara’a, sake tsare sa da idanu tayi tace, “Baba na kana son ɓoye min halin da kake ciki ko? Jiya haka ka wuni da ɓacin rai, yanzu ma ga shi ka dawo a yanayin, but kana son ɓoye min, Why?”

Sosa Kansa yayi cike da basarwa yace, “Mamy babu komi fa, ki yarda dani, idan da akwai ke ce ta farko da zan sanar ma wa”.

Mamy ta murmusa cike da ƙaunar ɗan nata, shi dai daban yake cikin ƴaƴan ta, koda yaushe a zurfin ciki yake, idan har abu ba yayi tsamari bane, ba ya iya fitowa fili ya sanar musu su da suke iyayen sa, ya dinga ƙumbiya-ƙumbiya dashi kenan a ransa, sai dai wuni yana cikin ƙunci da ɓacin rai, wanda hakan ya jawo ba kasafai zaka ga yana shiga cikin jama’a yana walwala ba..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button