BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Amma hakan be sa Ɗahira ta damu ba, ta ma manta shaf illa tunanin gida da take yi da ƙosawan su kai

Sai shi ne da zuciyar sa ta hana sa sukuni, da kuma yanayin da yake ji sanadiyyar haɗuwar cinyoyin su wuri ɗaya, lumshe idanu kawai daga ƙarshe yayi yana amsar baƙon yanayin da ya zo mishi, wanda ya kasa fassara ko mene ne, tare da tunanin abinda ya kasa ɓace mishi a rai.

     Fans ku sanar dashi idan kun sani.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

      Kwana biyu kenan da farfaɗowar Baffa, wanda ya sanya ahalin farin ciki matuƙa, duk da jikin sa babu daɗi sosai amma kuma sun ji daɗi matuƙa. Haka aka ci gaba da kulawa dashi sosai kuma alhmadulillah yana samun sauƙi, tunda har ya soma magana kaɗan, sai dai abin mamaki babu abinda yake faɗi sai sunan Ɗahira, maganar tashi kenan Ɗahira.  Ɗahira, wanda hakan ya ɗaure wa su Big Dady kai, “ko dai ya san ta mutu ne?” Tambayar da suke wa kansu kenan

Ganin abin nashi gaba yake yi kullum maganar nasa kenan,  sosai hakan ke ƙona ran Hajja Fatu, cike da haushi kuwa tace dashi, “gwara ma ya cire ta a ranshi, idan ba haka ba sai dai shima ya mutu yabi ta”.

Maganar nata ta taɓa shi, duk da yana jin jiki haka ya ɗago yana tambayar ta fuskar shi sharɓe da hawaye, “don Allah Hajja meyasa kike wannan maganar? Yanzu kenan kina nufin baza ki bani damar auren ta ba ko da Usman ya sake ta?”

“To wa ya faɗa maka an gansu? Ai ina ce ɓacewar nata ne ya sanya ka wannan halin? To yanzu haka kimanin watanni shida kenan ba’a samu inda suke ba, mu har mun yi jana’izar su tuni…”

Tarin da ya sarƙe shi ne ya tsayar da ita daga maganar ta. Yanda yake yi tuni hankalin ta ya tashi ta ruɗe lokaci ɗaya tana kiran sunan shi

A lokacin ne su Big Dady suka shiga dai-dai da lokacin da ya fara aman jini

“Subhanallah.. innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. what’s going on?” Inji Abbu da duk ya ruɗe shi ke riƙe da Baffan

Hajja Fatu da duk ta ruɗe ta karaɗe ɗakin da kuka, hakan ya jawo hankalin Abba dake waje yana amsa call be shigo ba, shima nan ya faɗo ɗakin yaga halin da Baffa ke ciki, sai sambatu yake yi yana kiran Ɗahira. Dole suka soma ba shi taimakon gaggawa cike da ruɗewa ganin yanda yake yi. Daƙyar suka samu suka tsayar da jinin suka saka mishi oxygen don ba ya iya numfashi da kyau

Al’amarin da ya ƙara ɗaga hankalin su kenan, duk sun shiga damuwa suna murna ya samu sauƙi ashe zai koma gidan jiya

Inda gefe ɗaya Hajja sai faman kuka take yi, tana dana-sanin sanar mishi da abinda ke faruwa, ga shi itama zata rasa ɗanta.

          Kwanan sa ɗaya ya samu ya farka, sai dai jikin babu sauƙi ko kaɗan, lokacin su Big Dady duk suna kanshi suna sake duba shi

Sai ya soma musu kuka yana tambayar su “da gaske ne Ɗahira ta mutu?”

Sosai suka yi mamakin ya aka yi ya sani

Nan Abba tunanin sa ya ba shi Hajja ce ta sanar mishi, ranshi ya ɓaci sosai amma babu yanda zai iya yace, “kayi haƙuri ka san duk me rai mamaci ne, ƙaddaran su kenan kuma babu me tsallake wa..”

Big Dady katse shi yayi yana cewa, “haba Abubakar ka dena maganar mana, ka ga ashe shi ne silan tashin ciwon shi me zai sa ka riƙa mishi bayan kana ganin halin da yake ciki?”

Baffa dake riƙe da gefen ƙirjin sa yana kuka kashirɓan yace, “wlh nima bazan iya rayuwa babu ita ba a duniyar nan, ina son ta Abba don Allah ku nemo min ita, bazai yiwu ace Ɗahira ta ta mutu ba. Tana raye don Allah ku nemo min ita Kar in mutu”. Sai ya fashe da wani sabon kukan yana cewa, “Hajja ta cuce Ni ta raba Ni da ita, amma yanzu bazan iya haƙura ba sai na aure…” Sai ya fara tari be ƙarisa ba, nan da nan jini ya soma zubar masa ta baki

Tashin hankali ba a saka mishi rana.

    Duk taimakon da su Abba suka so ba shi amma abin ya citura, tuni zuciyar sa ta gama bugawa lokaci ɗaya numfashin sa ta ɗauke daga jikin sa, wanda hakan ya tabbatar musu da Baffa ya rasu, ya tafi ya bar duniyar.

           Sai suka daskare kawai ba tare da sun san meye next abinda za su yi ba, amma tuni hawaye ya wanke musu fuska

Barin ma Abba da shi ya kasa tsayuwa waje ɗaya, sai kai komo yake yi cikin tsantsan tashin hankali, ƙwaƙwalwan sa ta kasa yarda Baffa ya rasu, sai ya taho kawai ya sake taɓa shi yana son tabbatar wa, cikin raunin murya yake cewa, “Baba na.. Baba na Ka tashi mana don Allah ka tashi.. Ɗahira tana raye bata mutu ba, ka tashi kaji Ni zan baka ita babu me raba ka da ita, da ka sanar min tun farko ai da tuni na aura maka ita, ka tashi kaji don Allah ka tashi”.

Da su Abbu suka fahimci sambatu ne kawai yake yi sai suka kama shi suka zaunar suna tausan shi, inda gaba ɗaya hawaye suke yi kashirɓan, sun kasa fita su sanar wa mutanen gidan dake bakin ƙofa suna jiran su.

     Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. kullu nafsin za'ikatul mauti ????????

Bazan iya fasalta muku halin da ahalin nan suka shiga ba sanda labarin mutuwar Baffa ya riski kowa. But think for yourself.
????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

        EPISODE Fifty Nine

       Motar na sauke su suka hau keke napep ta nufi dasu gida, har suka kai babu me magana a cikin su, kowa tunanin da yake yi daban dana ɗan uwan sa.

         Tun sanda suka doso layin gidan su suka ga mutane cike fam, wasu a zaune a cikin rumfa wasu kuma a tsaye, wasu kuma cikin motocin su inda gaba ɗaya wajen cike yake da ababen hawa

Al’amarin da ya soma tayarwa su Usman hankali kenan, duk suna tunanin abinda ke faruwa a ƙofar gidan su mutane suka taru haka. Daga gate ɗin su har babban Gate ɗin gidan duk an buɗe mutane nata ɓulɓulowa, wasu na shiga wasu na fita.

         Shima me napep ɗin da yaga ya kasa kutsa motar tashi sai ya sauke su a wurin, inda tuni Ɗahira tayi gaba tabar Usman da biyan kuɗi, shima sai ya biyo bayan ta yana bin mutanen wurin da kallo, duk yaga waɗanda ya sani cikin dangi, amma dayake wurin maƙil ne ba kowa yake kula dasu ba, bare kuma yanda duk suka sauya duk kan su.

          Ƙwaƙwalwan su fa ta kasa ɗaukar abinda kunnuwan su suke jiye musu wajen mutanen dake gaisuwa, don tuni maganganun wasu mutanen ya faɗa kunnen su inda suke gaisuwa suna faɗin sunan Baffa

Tuni Ɗahira ta ƙara sauri tana ƙoƙarin shigewa gidan

A lokacin ne kuma su Big Dady dake zaune a rumfar ƙofar gidan suka hange su, gaba ɗayan su tashi suka yi suna bin su da kallo, tabbas su Ɗahira suke gani, su ne suka dawo basu mutu ba

Usman dake shirin shiga gidan shima ya hange su nan yayo wajen su yana ɓashe baki

Sai suka tsaya kamar gunki suna bin shi da kallo sun kasa kataɓus, mafarki ne ko gaske shi ne abinda suke son sani, Waɗanda suka cire rai da tsammanin dawowar su; su ne yanzu suke gani a gaban su.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button