BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Big Dady yace, “subhanallah… Garin ya? Ya aka yi be kai ki asibiti ba? Ba shi wayan.. ba shi wayan”.

Bata ce komi ba ta cire wayan a kunnen ta ta miƙa masa, a lokacin sosai wani kukan ya taho mata, sai tayi saurin saka hannun ta ɗaya ta rufe bakin ta tana shashsheƙan kuka me fita da sauti kaɗan-kaɗan, kasancewar ɗaya hannun nata yana riƙe dashi ya ƙi saki sai sake matse mata yake yi, wanda shi tuni ma ya manta da hakan, daɗi da taushin skin ɗin ta ya shagaltar dashi, har ya mayar da abin kamar wasa yana ta faman matsa mata dantse, while ita kuma zafin hakan take ji

Big Dady ce masa yayi, “yayi maza-maza ya kai ta asibiti, idan har be kai ta ba wlh sai yayi mummunan saɓa masa”. Ce masa ma yayi “suna zuwa asibitin ya haɗa sa da doctor ɗin”.

Hakan da Usman yaji ne yasa yace mata “ta shirya su je” da ya gama wayan, sannan ya tashi ya fice

Ita kuma daƙyar ta iya miƙe wa jiri na ɗiban ta, bango ta dafe sannan ta soma bin bangon har ta kai bakin ƙofa, ko bi ta kan ta rufe jikin ta bata yi ba, sabida ba ta cikin hayyacin ta, daga ita sai doguwar rigan less me ruwan Powder, kanta kuma babu ɗankwali illa gashin ta dake ɗaure da ribom baƙi, amma duk ya tuttuge ya mitsitstsike kamar na mahaukata

Tana fita ta tsaya tana faman haki, sabida gani take yi kamar zata faɗi idan har ta rabu da bango, kuma ga shi dole sai ta rabu da bangon zuwa haraban gidan, hawaye kawai take saki tana gunjin kuka

Usman dake cikin mota yana faman jiran ta, nan ya danna mata horn da ƙarfi yana faman kallon ta daga cikin mota, kuma duk a yanayin halin da yake ganin ta hakan be sa ya ji tausayin ta ba, yana gani kamar wannan shi ne dai-dai da hukuncin da ya kamata ya ɗauka a kanta, babu tausayi a tsakanin su bare taimako, ko wani hali take ciki ita ta ja wa kanta

Daƙyar a duƙe- a duke ta soma taho wa wajen motan, sosai ta sake fashe wa da kuka sabida yanda take ji, kafin ta kai motan sai dai ta ƙarisa da rarrafe, sabida ƙafafun ta sun gaza ɗaukar ta, tana isa ta dafe motan sannan ta buɗe ƙofan baya ta shige

Be ce mata komi ba ya ja motan ya nufi kan titi, kasancewar gidan babu Gate sai compound da ƙaramin ƙofa me raga-raga, kuma motan nasa na fake ne a ta wajen ƙofan a ɗan ƙaramin haraban wajen

Ƙudundune wa tayi sosai tana rawan sanyi, coz yanda motan ta ɗau sanyi sabida a.c, sai karkarwa take yi da haƙoran ta tana faman sakin sauti me ƙara

Tsaki yaja a daƙile yace da ita, “ki yi min shiru a wajen nan”.

Tamƙe bakin ta tayi, amma duk da haka haƙoran ta karo suke yi, sai dai sautin na fita a hankali, kuma ya sauya ƙara, tamkar dai wacce aka toshe wa baki tana gunjin ceton rai

Be sake ce mata komi ba har suka kai wani kyakykyawar asibiti da babu nisa da su, fita yayi ba tare da ya tanka ba

Itama sai ta saka hannu ta buɗe ƙofan ta fita, a duƙe take tafiya kamar zata faɗi tana sake sabon hawaye sabida azaba

Shi tuni yayi gaba abin sa

Hakan yasa wata nurse da ta hango ta, ta taho da sauri ta taimaka mata, tana tambayar ta, “are you sick?”

Ɗahira bata amsa mata ba, illa kuka da ta saki me tsuma ran me sauraro, domin tamkar dai jira take yi dama ayi mata maganar; ta fashe da kuka

“Sorry! Sorry!”. Abinda take ta faman ce mata kenan har suka shige cikin Hospital ɗin

Usman dake tsaye bakin wani Office yana jiran shigowar ta, nan ya hange su da nurse ɗin, har ta zo nurse ɗin zata gibta shi domin bata san tare suke ba, sai yace mata “ta tsaya”.

“Doctor are you together?” Cewar nurse ɗin tana kallon sa

Fuska babu fara’a ya ɗaga mata kai yana shige wa cikin Office ɗin

Hakan yasa Nurse ɗin ta taimaka mata suka bi shi ciki tana me mamakin halin sa, duk da kuwa dama sun san haka yake, “they were sick together but he came and left her outside?” Take tambayar kanta a ranta

Suna shiga ciki, Doctorn dake gaisa wa da Usman ya kalle su, sai kuma da sauri yace, “Beha what’s wrong with her?”

“I don’t know Sir, but they seem to be together”.

Sai Doctor ɗin ya kalli Usman yace, “Doctor, are you together?”

Fuska a ɗaure Usman yace, “Yes. I brought her to check on her”.

“Ok. Beha help and calm her down”.

Kamar yanda yace ɗin, haka Nurse ɗin tayi, ta nufi kan gadon dake cikin Office ɗin ta kwantar da ita, sannan ta ɗauki excuse wajen doctor ɗin ta fice.

“Doctor Man amma ya aka yi haka ka bar ta har ciwo ya yi mata zafi haka? daga gani tana shan jiki, kai fa doctor ne”. Cewar Doctor ɗin cikin turanci dake tsaye yana kallon Usman

Gajeren tsaki Usman yaja yace, “Please ka duba ta, ba surutu nace kayi min ba”. Shima ya maida masa da turancin

Doctor ɗin be ce komi ba, illa kaɗa kai da yayi ya nufi gadon da Ɗahira ke kwance, ya san halin abokin sa sarai, shiyasa be yawaita binciken ba ya ƙyale sa. Fara duba ta yayi, duk wani taimako na gaggawa ya bata, domin ya ɗau tsawon mintuna arba’in yana duba ta, inda daga bisani ya ɗaura mata drip ya dawo kan kujeran sa ya zauna, kallon Usman dake ta latsa waya yayi kamar babu abinda ke damun sa a rayuwa, kana yaja numfashi yana ɗaura hannayen sa da ya haɗe su waje ɗaya a saman table ɗin sa, cikin harshen turanci yace, “Amma doctor ya aka yi ka bar pation a tare da kai ta shiga wannan mummunan yanayin baka kawo ta Hospital ba? Yarinyan tana cikin wani mawuyacin hali, zazzaɓin jikin ta yayi tsanani sosai, ga kuma damuwa dake damun ta matsananciya a zuciyar ta, wanda hakan zai saka ta samu matsala, domin idan taci gaba da zama a haka da yawan damuwa a ranta, tabbas komi zai iya faruwa, kuma duk baka ɗau mataki ba, why?”

Ɗago Kai Usman yayi yana kallon sa da fuskar sa kamar kullum, cikin miskilanci irin nasa yace, “wannan be shafe ka ba, tunda ka duba ta shikenan, zaka iya ba mu sallama mu wuce”.

“Sallama kuma? Kana jin fa abinda na faɗa, jikin ta yayi tsanani da yawa sosai Doctor, dole zata zauna a nan har ta warware, baza mu iya bata sallama ba”.

Miƙe wa Usman yayi yana saka wayan sa cikin aljihun wandon sa, kana yace, “fine. Sai ka riƙe ta har sanda ka so, Ni ka ga tafiya na bani da time ɗin ku”.

“But doctor Wai ba ƙanwar ka bace? na ga kun yi kama sosai, amma yanda kake nuna wa kamar da akwai matsala”. Cewar Doctorn cike da mamakin Usman ɗin

Shiru Usman yayi yana kallon sa, sai kuma ya juya zai fice don a ganin sa be da lokacin sa, har ya kai bakin ƙofa sai kuma ya dawo yana ciro wayan sa ya kalle sa, “Please Doctor Shamel I will call my Daddy, he will ask you about this girl, Please and please I don’t want you to tell him anything, just tell him her body is easy “.

Sosai mamaki ya sake cika Doctor ɗin, sakin baki kawai yayi yana bin Usman da kallo cike da al’ajabin halin sa

Miƙa masa wayan yayi bayan ya kira Big Dady

Inda Doctor ɗin ya amsa ya kara a kunne yana me gaishe da Big Dady cike da girmamawa irin nasu

Nan Big Dady yake tambayar sa halin da Ɗahira ke ciki

Inda Doctor ɗin ya sanar masa “da sauƙi jikin nata, zazzaɓi ne kawai ke damun ta”

Hankalin Big Dady ya ɗan kwanta, inda ya roƙi Doctor ɗin “da ya kula da ita sosai, kuma kar ya bata sallama da wuri har sai ta warware sosai”.

Murmushi Doctorn yayi yace, “ok Sir, dama ba yau zan sallame ta ba”.

Daga nan dai sun ɗan sake tattaunawa, inda suka yi sallama. Doctor ɗin ya miƙa wa Usman dake tsaye ya tsare shi da ido wayan sa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button