BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

.

        EPISODE Forty Seven

       Washe gari Hajja Fatu da ta gama shirin ta na zuwa Office, sai ta biya ta gidan su Baffa, sai dai kuma bata cid da Sa’adatun a ɗakin ta ba, kai tsaye ƙofan ɗakin Baffa ta hau buga wa, domin a zaton ta suna ciki tunda ta ga motan Baffan be fita ba, kuma ko kaɗan bata kula da babu na Sa’adatun ba; tunda ta san babu inda zata je

Kiran sunan sa take yi daga shi har Sa’adatun

Baffa dake kwance be gama wartsake wa daga giyan da ya sha jiya ba, shiyasa yayi lattin tashi, sai hayaniyar Hajja ce ya farkar da shi, dole ya miƙe yana saka riga a jikin sa, ƙofan ya nufa yana ɓame bottles ɗin rigan, guda uku kacal ya saka ya buɗe ƙofan yana faɗin, “wai Hajja lafiya? Me ke faruwa ne?”

“Biyo ka nayi in ci maka mutunci, ina ita Sa’adatun? Ta fito duk ta faɗa min abinda kake mata, Wlh idan ka sake naji mummunan abu wlh yau Ni da kai ne. ka kira min ita mana ka tsaya kana kallo na”.

Wuce ta yayi zai nufi ɗakin Sa’adatun

“Ina kuma zaka je? Ba tana ɗakin ka ba?”

Gajeren tsaki yaja kafin yace, “ba ta ciki tana ɗakin ta”.

“To ba ta ciki; na duba ban ganta ba, me ke faruwa ne? Ina zata je da safen nan ba tare da ka sani ba? Yanzu ma na kula kamar ba motan ta a waje”.

“To Ni Hajja ina Nasan inda zata je?”

Zata yi magana wayan ta ta soma ringing, ciro wa tayi cikin jaka tana cewa, “ka nemo ta wlh ko inci ƙaniyar ka Baffa, ban son shashanci”. Wayan ta amsa ganin sunan Dr. Zubairu

“Hello”.

“Dr. Na iso na ga Office ɗin ki a rufe”.

“Eh ban fito ba wlh, yau nayi late na tsaya yin wani abun, amma ka jira Ni yanzu zan taho ai kayan naka suna office ɗina”.

“Ok to ba damuwa, sai kin zo”.

Daga haka suka gama wayan, inda tabi bayan Baffa da ya shige ɗakin Sa’adatu don duba ta.

    Sai dai kuma gaba ɗaya sun duba Part ɗin babu ita, dole Hajja ta ɗauki waya ta kira Numban ta, sai dai ba’a amsa ba har sai da tayi Three missed calls, memakon taji muryan Sa’adatun, sai muryan Mahaifiyar ta taji

Hajja tace, “Amina ya aka yi wayan Sa’adatu ya zo hannun ki? Me ke faruwa ne wai nan mun neme ta ba mu same ta ba?”.

Cike da faɗa Hajiya Amina tace, “ina kuwa zaki sani Yaya tunda yaron ki be faɗa miki ba, to Sa’adatu ta dawo gida domin ta gaji da abinda yake mata, kuma na gode da abinda kika min Yaya na gode, babu damuwa”. Tana gama faɗar haka ta katse kiran ba tare da taji me Hajjan zata ce ba

Juyowa Hajja tayi ta kalli Baffa tace, “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! Baffa yanzu me kayi mata da har ta tafi gida? Me ya haɗa ku?”

“Hajja babu abinda ya haɗa mu, nima ban san sanda ta tafi ba”.

“Dalla rufe min baki, ashe ban isa da kai ba? Yanzu har sai da kayi sanadin da Sa’adatu ta tafi gida? Ka nuna min ban isa ba ko? To wlh yau na baka ka je ka ɗauko ta tun wuri tun kafin mutanen gida su ji zancen nan, idan ba haka ba zan mummunan saɓa maka”. Daga haka ta fice fuuuu ranta a ɓace tayi gida, tana zuwa motan ta kawai ta ɗauka ta fita.

     A hanyan layin gidan ta haɗu da Shakira a cikin motan ta, nan Hajja ta danna mata horn tana faka wa

Itama Shakiran dayake ta gane motan Hajjan, sai ta tsaya tana me fito wa ta nufi motan

Lokacin har Hajjan ta fito tana bin ta da kallo tare da tambayar ta “me tazo yi da safen nan bata wuce asibiti ba?”

“Hajja wlh yaji na yo”.

“Innalillahi… Yau na shiga uku na, yaji kika yo kamar ya Shakira? Kina nufin kin baro gidan mijin naki? To uban me yayi miki?”.

Baki a zumɓure tace, “wlh Hajja na gaji da abinda Sahabi yake min, kullum be da lokaci na, yanzu ya kai har wulaƙanci yake min, ko yaushe yana waya da mace, kuma idan nayi magana ya dinga min faɗa kenan, yau har mari na yayi don kawai na tanka masa saboda na ga an turo masa text, kuma mace ta turo masa da daren jiya, wai ya fito su haɗu, shi ne ya mare Ni, wlh Hajja bazan koma ba dole sai na ɗanɗana masa azaban da ya ɗanɗana min”.

“Uban azaba zaki ɗanɗana masa, angaya miki ana wa namiji haka ne? To wlh idan wani ne zai ce sai dai ki shekara a gida baki dawo ba, kuma da kike tunanin zai biyo ki sai dai ki ji ya sake wani auren ya bar ki banza kawai, dalla ki kama hanya ki tafi, wlh kar ki soma ki shiga gidan nan idan ba so kike mutanen gida yau su yi min dariya ba, ina fama dana Baffa ke kuma kin dawo, ki kama hanya ki tafi ko”. Ta ƙare maganar da daka mata tsawa

“Wlh Hajja babu inda zan je, sun daɗe ba su yi miki dariyan ba, ina faɗa miki mari na yayi kina ce min za’a miki dariya, babu inda zan je wlh”. Wuce wa tayi wajen motan ta zata shiga

Sai Hajjan tayi saurin ƙarisawa wajen ta tace, “yi haƙuri to, yanzu mu wuce Hospital in yaso sai in sama mana mafita, amma ba na son ki shiga gidan nan a san abinda ya faru, ki kwantar da hankalin ki Sahabi kamar ya dawo tafin hannun ki ne, dani yake zancen”.

Da wannan kalaman Hajja ta shawo kan Shakira, sanna suka shiga mota suka wuce Hospital, Kai tsaye Hajja Fatu Office ɗin ta ta wuce, tana shiga ta ciro wayan ta ta danna wa Hajiya Sa’ima kira, nan ta sanar mata “anjima kaɗan tana nan zuwa ta raka ta wajen Malam”.

“To babu matsala, sai kin zo”. Cewar Hajiya Sa’ima

Suna gama wayan Dr. Zubairu ya shigo Office ɗin

Hajja Fatu tace dashi, “to ga kayan naka nan, amma dai ka san yanda zaka yi ka fita dashi Hospital ɗin nan ba tare da an ganka ba, ka san mutane yanzu sai ace magungunan asibiti ka sata”.

Dariya Dr. Zubairu yayi yace, “ai bani da matsala dacta, ba ma yanzu zan fita da shi ba sai zuwa magriba idan an shiga Masallaci, sannan zan dawo in ɗauka, yanzu Office ɗina zan kai”.

“Yauwa hakan ma yayi, sai na ji ka zuwa anjima, yanzu ina son na gama duba patiens ɗina ne domin akwai wurin da zan je”.

Yace, “to shikenan, dama akwai maganar da zamu tattauna, idan kin samu lokaci sai ki kira Ni kawai”.

“Ok”.

Da haka ya fice

Ita kuma ta ɗauki wasu files ta fice, kai tsaye patiens ɗinta taje ta duba, bayan ta gama ta dawo Office, waya ta ɗauka ta kira Safna, tana zuwa tace mata “taje ta ba wa Maman yaron nan takardan sallama”.

Amsa tayi Safnan tana shirin fita

Sai kuma Hajja ta kira wo ta tace, “zuwa anjima ina ga shima ɗayan yaron na kusa dashi za’a sallame sa, so bazan daɗe ba idan kinga jikin nasa da sauƙi sosai sai ki ba shi sallama”.

“To”. Safna tace da ita tana fice wa.

      Awanni biyu Hajja Fatu ta ƙara a asibitin kafin ta wuce gidan ƙawarta, kai tsaye bata zauna ba suka wuce wajen Malam, inda Hajja ta zube masa kuɗi don ayi ma yaran ta biyu aiki, ko kaɗan ba ta son a sake samun ɓaraka a tsakanin su, ita Shakiran a kama mata Sahabi sai yanda tayi da shi, shi kuma Baffa a saka mishi ƙaunar Sa’adatu a rai su zauna lafiya kar wani abu ya sake faruwa.

    Daga nan gida kawai ta wuce bata koma aiki ba.

   Ta dawo babu daɗe wa Abba ya shigo a rikice, cikin tashin hankali yace da ita, “ke ɗauko gyalen ki mu wuce Hospital”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button