FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Wannan dalilin ne yasa Hajja ta ɗan samu sukuni da matsalolin ta, tana ga kamar aikin Malam ya ci tunda ga shi komi ya zama normal Kan yaran ta, sai dai matsalan yana ga Abba, domin tun abin be sake kallon inda take ba, ya ƙi mata magana ya dena cin abincin ta, hakan yasa tayi tunanin why not ta Kai shi wajen Malam domin magance mata matsalan ta, wannan tunanin zuciyar nata tabi ta wuce kanta tsaye wajen Malam ko bi ta ƙawarta bata yi ba, shi ne kaɗai wanda zai iya mata maganin matsalan dake shirin afkuwa ita da mijin ta, wanda tana ganin ɓaraka ne babba da rashin yarda yake shirin Kunno Kai a tsakanin su, wanda kuma hakan ne babban tsaiko ga rayuwan ta, yardan Miji ya fi komi a rayuwar aure.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
TURKEY
A kwanakin nan da suka shuɗe, Ɗahira tayi rayuwar ƙunci ba ni da ƙunci ba, ko kaɗan ba ta da walwala, ta zama tamkar wata wacce bata da gata, ta rame tayi baƙi kamar ba ita ba, bata da aiki kullum sai kuka da saka damuwa a ranta, ta kasa saba wa da halin da take ciki, komi na gidan ita take yi, da ta tashi da safe zata gyara gidan tayi wa kanta abinci domin shi ko bi ta kanta be yi bare tasa ran idan tayi abinci zai ci, bare kuma bata taɓa kwatanta hakan ba, ta gummaci ta girka ta zubar da tayi masa girki, ita take masa wanki da gyara ɗakin sa ko ina, idan ma bata yi ba ranan ya dinga caɓa mata magana kenan, kuma yace “idan bata yi ba sai yaci uban ta”. Kalman cin uban ta shi yake matuƙar ɓata mata rai ainun, sai ta zauna tayi kukan ta son ranta ta share hawayen ta, haka zata yi masa wankin ta shanya masa a Toilet ta gyara masa ɗaki ko ina, domin ba ta son ko kaɗan ya sake taɓa lafiyan jikin ta, a haka take ta ƙare wa tana ciwo a tsatstsaye, kullum fama take yi da kanta sakamakon damuwan da ta kasa cire wa a ranta, kuma tun ranan da ya bata waya suka gaisa da ƴan gidan su be sake bata ba, sosai take buƙatar jin muryan ƴan gidan su amma ba hali, dole ta haƙura domin ko magana ba ta ƙaunar tayi masa bare ta tambaye sa wani abun
Duk idan taje gyara masa ɗaki, sai tayi binciken ko zata samu keey ɗin ƙofa, amma duk inda ta duba bata taɓa cin karo dashi ba, haka zata mayar masa da komi a muhallin sa ta gyara masa ta koma inda ya zame mata ɗaki, kusa da kichen. Idan damuwa yayi mata yawa sai dai tayi ta karatu, da dare kuma ko ishashshen barci ba ta samu illa sallah da take faman yi ko yaushe tana kaiwa Allah kukan ta
Rashin zaman Usman a gidan ya fi mata komi daɗi, tunda idan ya fita tun safe ba ya dawowa Sai dare, wani lokacin ta ɗan sami barci ya fizge ta, wani lokacin kuma idanun ta biyu zai shigo, ita yanzu har ta saba da duhun gidan, domin sabida tsaban mugunta irin nasa ya lalata komi na na’uran gidan, ko NEPA babu a gidan, bare dama ita ba gwanar kallo bane bare ya ɗebe mata kewa, haka take rayuwar ƙunci da duhu a gidan, koda da safe ne gidan babu wani haske sosai, sai idan ta yaye cootin, wani lokacin kuma sanyi ya addabe ta ta rasa yanda zata yi, dole ta mayar ta rufe.
Yau ma tana kwance kamar kullum, ko kaɗan ba ta jin ƙwarin jikin ta, daƙyar take iya taɓuka wani abun saboda rashin ƙarfin jiki, ga ta ba auki ba
Tunda ya fita take kwance ta kasa yin komi, ko karya wa ta kasa, tunani ne kawai ta afka tana ta faman yi. Can kuma sai ga hawaye ya silalo mata a kunci, sai ta yunƙura ta miƙe ta nufi kichen kamar zata faɗi, ruwa ta samu ta dafa ta haɗa tea me kauri, shi ne ta samu ta ɗan sha ko zata samu ƙwarin yin aiki
Tana gama wa ta dawo parlour’n tana bi da kallo, ganin ba wani datti ne ba sai ta wuce kanta tsaye ɗakin sa, nan ne yayi mutsu-mutsu da gadon sa, duk ya jefar da kayan sa, haka ta tattare sannan ta gyara gadon, ta wuce Toilet ta wanke masa, wankin sa dake shanya tun jiya da tayi masa ta kwashe ta ninke, sai ta ɗaura masa a kan gado, kana ta koma Parlour ta shiga wanka, tana fito wa ta zira riga da skert ko lotion bata shafa ba, rabon ta ma da shafa wani abu a gidan nan tun lokacin da tayi ciwo, komi yanzu ya fitan mata a rai
Tana zaune tana gyara kayan nata tana mayar wa cikin akwati, sai ta jiyo motsin buɗe ƙofa, tsayawa tayi kawai tana kallon ƙofan, ta san ba ya dawo wa da rana shiyasa tayi mamaki
Shi ne kuwa ya shigo ciki, wani saurayi na biye dashi a baya. Be bi ta kanta ba ya shige ɗaki, yayinda saurayin nan sai bin ta yake yi da kallo, sai kuma ya gaishe ta da harshen turanci
Amma ko ci kanka bata ce mishi ba, illa ɗauke kai da tayi fuskar ta babu fara’a taci gaba da abinda take yi.
Usman ne ya fito da Trolly babba ya miƙa wa saurayin, dayake shi yake ba wa gugan kayan sa, duk kwana uku zai haɗa masa kayan ya zo ya amsa da safe kafin ya fita, yau kuma be zo ba sai yanzu, shi ne ya kira sa ya sanar masa zuwan sa, wannan dalilin ne Usman ya dawo domin ba shi kayan.
Saurayin fita yayi da Trolly bayan sun Yi sallama, shi kuma ya koma ɗakin sa.
Sanda Ɗahira ta gama gyara kayan nata, sai ta rufe Trolly ta janye sa gefe, kana ta koma ta jingina da bango ta lumshe idanuwan ta, ta hau tunanin da ya zame mata jiki, ko ta so bari ba ta iya wa.
Can sai Usman ya fito da waya ya nufo inda take
Takun takalman sa dake tafiya da ƙarin bugun zuciyar ta, shi yasa ta buɗe idanu da sauri ta sauke su kansa
Fuskar sa ɗaure tamau ya miƙo mata wayan ba tare da ya ce uffan ba
Kamar kar ta amsa, sai kuma tayi tunanin ko gida ne, da sauri ta miƙa hannu ta amshi wayan, ilai kuwa gidan ne, mahaifin ta ne a kan layi.
Yana kanta be tashi ba har ta gama wayan da mutanen gida
Itama ko kallon sa bata sake yi ba, kuma bata yi wani abun da zai saka yayi mata magana ba, bare ya sauke mata tijara, iyakan gaisuwa ya haɗa ta dasu bata ce musu komi ba
Amsar wayan sa yayi ya wuce kan kujera, zama yayi yana ta faman latsa wa
Ita kuwa haɗe ƙafafun ta tayi ta rufe idanun ta, sai ga hawaye, “Allah gani gare ka, Allah ka fitar dani a hannun wannan azzalumin bawa naka, na tsane shi!”. Tafaɗa a hankali zuciyar ta na ƙuna kamar ta fashe. Motsin sa taji, sai ta ɗago kanta tabi bayan sa da kallo da har ya shige ɗakin sa, wani ƙunci ne ya sake tokare mata maƙoshi, sai ta lumshe idanu tayi shiru tana sauraron bugun zuciyar ta, bata ƙara motsa wa ba har sanda taji motsin fitan sa. A haka ta wuni har dare bata sake tashi ba, illa sallah da ke tayar da ita, ko abinci taƙi ci a haka har dare yayi ta kwanta, nan da nan yau barci ya ɗauke ta saboda ta tara shi da yawa bata yi ba.
Bata farka ba sai washe gari ƙarfe 07:00am. Sosai taji daɗin barcin da tayi, sai duk wani gajiya ya saukar mata, sosai ta ɗan ji sauƙin kan nata, miƙe wa tayi ta shiga Toilet ta ɗauro alwala, sai da ta gabatar da sallah tayi lazami sosai har wajen tara da rabi, sannan ta miƙe ta shiga kichen, Breakfast ta haɗa sannan ta ɗaura ruwan wanka, a nan kichen ɗin ta karya tunda a nan take cin abincin ta
Ruwan na zafi ta sake ta kai Toilet, sai da ta sirka shi yanda take so kafin ta fito ta hau tuɓe kayan ta, ta cire riga tana shirin ɗaura zani sai ji tayi ya buɗe ƙofa