FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Usman ne ya fito cikin shirin sa da ya saba ko yaushe na ƙananan kaya, babu ƙarya ya ƙure wanka yau, sosai yayi kyau sai tashin ƙamshi yake yi. Da kallo ya bi ta ganin yanda ta ƙudundune jiki lokaci ɗaya ta tsorata, har tana zame wa ƙasa saboda tsaban tsorata
Ita duk bata yi tunanin yana gidan ba, tunda da safe yake fita shiyasa ta cire kayan a Parlour.
Shi kuwa tsaki yaja me sauti, ya sake ɗaure fuska tamau ya fice da sauri abin sa.
Ajiyan zuciya ta sauke bayan ta raka bayan sa da harara, “ɗan iska. Allah ya isa tsakani na da kai”. Ta faɗa a fili tana shige wa Toilet. Wanka tayi ta sanya doguwar riga ja, tayi Rolling da gyalen sa, kai tsaye ɗakin sa ta nufa, sai da ta gama share masa tana shirin fita ta hangi wardrobe ɗin sa kamar be gama rufe wa ba, da sauri ta ƙarisa har tana cin tuntuɓe, tana jan shi ya buɗe, washe baki tayi kai tsaye bincike ta soma yi ko Allah zai sa taga keeys ɗin gidan, tunda be taɓa barin wardrobe ɗin sa a buɗe ba, ilai kuwa sai taci Sa’a ta samu keeys da yawa a ciki, har da passport ɗin su a ciki, nan jikin ta ya hau rawa tsaban farin ciki, da sauri ta kwashi keeys ɗin ta fita da gudu, ƙofan ta nufa ta hau gwada mukullan, nan ta samu na ƙofan, sai ta buɗe ta watsar da mukullan a nan, ko mayar masa bata bi ta kai ba, passport ɗin ta na hannu ta wuce wajen kayan ta taja Trolly ɗinta ta fice da gudun ta, domin ba ƙaramin rawa jikin ta yake yi ba, gani take yi kamar kafin ta fita zai iya dawowa gidan.
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
بسم الله الرحمن الرحيم
⚖
FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
JIKAR LAWALI CE✍️
Wattapad: UmmuDahirah????
\F.W.A????/
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY
.
EPISODE Forty Nine
Tafiya take yi tana waigen bayan ta, duk ta gama tsorata matuƙa, ta san haɗuwar su dashi bazai mata daɗi ba, ita kuma tarigada ta ɗau alwashin sai dai tayi yawo cikin ƙasar nan, amma baza ta taɓa koma wa gidan sa ba, ko bata sami taimako ta koma ƙasar su ba sai dai tabi duniya
Har ta fice a layin gidan, ta yanki hanya ɗoɗar, tafiya me nisa tayi Kafin ta samu wata mata me shago a bakin titi, nan ta tuna da Numban Zakeeya ƙawarta da tayi a cikin jirgi, wani zuciyar tace mata “ta gwada neman taimako ko Allah zai sa a dace”. Da sauri ta isa wajen ta tana maida numfashin gajiya, kafin ta ƙarisa wajen ta sai da ta ɗan samu ta daidaita kanta, sannan ta isa tana mata sannu da harshen turanci
Matar kallon ta tayi, duk da ba wani turanci ta iya ba, amma tana ji kaɗan-kaɗan, ta amsa mata cikin fara’a tana tambayan ta “me take so?” Cikin turancin
Nan Ɗahira tayi mata bayanin “don Allah ta taimaka mata da Aron waya, ita baƙuwa ce yau ta sauka, amma wayan ta ya faɗi, ta rasa ya zata yi ta isa gidan da tazo, tana buƙatar yin waya dasu ko za su san inda take”.
Matar bata wani tsawaita ba, duba da yanda taga Ɗahiran duk tayi laushi ta wani yamushe, da alamun tana matuƙar buƙatar taimako, nan tausayin ta ya kamata ta, ta ɗauki wayan ta miƙa mata tana bin ta da kallo kamar zata haɗiye ta
Ita kuwa bata damu da kallon da take mata ba, jiki na rawa ta buɗe jakar ta a ƙaramin Zip ta ciro takardan, kofewa tayi a wayan tayi kira, ba’a ɗau lokaci ba kamar ana jira aka ɗauka
Muryan mace taji tayi sallama
Sai Ɗahiran ta amsa mata tana cewa, “da Allah da Zakeeya nake magana?”
“Ita ce. wace ce?”.
Cikin Hausa take magana don kar matar taji me take cewa, ganin yanda idanun ta ke yawo a kanta, “suna na Ɗahira, Ni ce wacce muka haɗu dake a jirgi last three weeks, kin tuna Ni? Har muka zauna waje ɗaya muka yi exchanging number”.
Cike da ɗoki Zakeeya tace, “Laa Ɗahira ke ce? Wlh nayi tunanin baza mu haɗu ba, sabida yanda nake ta kiran wayan ki ba ya shiga, kuma ke baki kira Ni ba”.
“Haka ne. Amma ina buƙatar taimako, don Allah ki taimaka min”.
Yanda tayi maganar yasa Zakeeyan ta gane akwai matsala, nan da nan ta tashi hankalin ta tana tambayan ta “me ya faru?”
Ɗahira tace mata, “maganar ba ta waya bace, ki taimaka ki zo ki tafi dani in yaso sai muyi maganar”.
“Ok.. ok aina kike yanzu?”
Tambayar matar nan tayi, ita tayi mata kwatancen inda take
Zakeeyan tace, “gata nan zuwa yanzu, basu da nisa da wurin ma”.
Sosai zuciyar Ɗahira tayi mata sanyi a wannan lokacin, gani take yi zata iya tsira ba tare da Usman ya sake ganin ta ba. Matar ta miƙa wa wayan tana ta mata godiya sosai kamar zata yi kuka.
Babu jima wa kuwa sai ga Zakeeya a motar ta, da sauri ta fito ta nufo Ɗahiran
Itama Ɗahiran wajen ta ta nufa domin ta shaida ta
Sosai Zakeeya take ware idanun ta a kan Ɗahira gani take yi kamar ba ita ba, har sanda suka kusanci juna ta gane tabbas ita ce, amma kuma yanda ta sauya mata fiye da tunani, ga baƙi da tsananin rama da tayi, duk ta bushe kamar babu jini a jikin ta. Cikin sauri ta riga ta magana da tambayar ta, “Ɗahira ke ce? Ke ce haka meke faruwa ne?”
“Don Allah mu je sai in Yi Miki bayani, ke kaɗai na sani a ƙasar nan ina buƙatar taimakon ki Zakeeya”.
Jiki na rawa kuwa Zakeeyan taja hannun ta ganin har ta soma hawaye, motan ta buɗe mata ta shiga daga ita har kayan ta, itama ta zagaya ta shiga taja motan da sauri. Sun yi tafiya me nisa babu me magana cikin su
Kai tsaye Zakeeya gidan su ta wuce da ita, suna isa suka fito taja hannun ta suka yi ciki
Auntyn Zakeeyan na zaune a Parlour suka shigo Zakeeya na sallama
Amsa mata tayi tana bin su da kallo, ganin ta da baƙuwa sai ta bi su da ido har suka zauna, kana kuma ta soma tambayar Zakeeyan “aina ta samo ta kamar ƴar ƙasar su?”
Zakeeya tace mata, “eh Aunty, ƴar Nigeria ce, domin a jirgi muka haɗu da ita sanda na dawo nan, tana buƙatar taimako ne shi ne ta kira Ni”.
“Ok Allah Sarki, Allah yasa dai lafiya baiwar Allah? Sannu ko? Zakeeya kawo mata ruwa tasha naga kamar hankalin ta a tashe yake har kuka take yi”.
Zakeeyan bata amsa ta ba illa miƙewa da tayi da sauri ta kawo mata ruwan
Duk da Ɗahira tana buƙatar ruwan domin ta jiƙa maƙoshin ta, amma yanzu ba tashi take yi ba, burin ta kawai abinda ke cikin zuciyar ta ya cika, na ganin ta a ƙasar ta na haihuwa, daga nan ne hankalin ta zai kwanta
“Ki sha ruwa kinji?” Cewar Zakeeya tana dafa mata kafaɗa
Kallon ta Ɗahira tayi lokacin kuma wani sabon hawayen ya Kunno mata, cikin rawan murya tace, “wlh ba na jin zan iya saka wani abu a ciki na idan har ba a ƙasa ta na ganni ba, don Allah don Allah ku taimaka min na koma ƙasa ta, bani da kowa a nan, ku taimaka min da kuɗin jirgi, wlh idan na koma zan tura muku kuɗin ku, Ni dai fata na na bar ƙasar nan”.
Sosai kansu ya ɗaure da zantukan ta
Cikin al’ajabi Auntyn tace, “baiwar Allah bamu gane ba? Me ke faruwa ne kiyi mana bayani kinji don Allah yanda zamu fahimta”.