FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2
⚖
FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
JIKAR LAWALI CE✍️
Wattapad: UmmuDahirah????
\F.W.A????/
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY
.
EPISODE Fifty
Ganin ta kasa magana sai rusa musu kuka take yi kamar ranta zai fita, sai hankalin su ya sake tashi matuƙa, inda Big Dady ya riƙo hannun ta suka nufi cikin gidan
Shi kuma Abbu ya janyo mata akwatin ta yabi bayan su, zuciyar sa tamkar zata tsinke, gaba ɗaya ya rasa ma takamaiman tunanin da zai kama wanda zuciyar sa ke bijiro masa da afkuwan sa ga ɗiyar sa.
Kai tsaye General parlour suka nufa, inda Kaka da Fadil ke zaune suna hira, Kaka na shan dariyan shirmen Fadil ɗin da yake ba shi, shigowar su yasa duk suka bi su da kallo, inda Kaka yake tambayar su “lafiya?” Yana kallon Ɗahira don be gane wace ce ba, saboda fuskar ta na ɓoye jikin Big Dady
Sai da suka zauna, Big Dady ya zaunar da ita gefen sa, kana yace ma Kaka, “Baba Ɗahira CE muka ganta ta dawo, kuma mun tambaye ta amma sai kuka take yi, Allah yasa ba wani abun Usman yayi mata ba?” Ya ƙare maganar da ɗacin rai, domin tuni hasashen sa ya ba shi duk yanda aka yi Usman ya muzguna mata, amanar da suka ba shi be riƙe da gaskiya ba, duba da yanda suka ga Ɗahiran ta koma
Shi kuwa Kaka jin furucin Big Dady, sai nan da nan jikin sa ya soma rawa, hankalin sa yayi mugun tashi, ya soma kiran sunan ta yana faɗin, “Mata ta, Mata ta ke ce? Ya aka yi kika dawo? Sanar damu don Allah, wani abun ne ya faru? Zo kusa dani”.
Da sauri ta miƙe ta isa wajen sa tana durƙushe wa ta sake fashe wa da kuka, domin yau ji take yi duk wani baƙin cikin da ta ƙunsa na zaman ta dashi suna dawo mata, yau take iya amayar da duk abinda ta ƙunsa, kukan kawai shi ne zai kawo mata sauƙi a gare ta
Duk yanda suka so tayi magana, Ɗahira ta kasa yi, riris take kuka kamar ana yanka ta, har wani shashsheƙa take yi tana faman ajiyan zuciya
Wanda hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankali yayi ba, musamman Kaka da jikin sa sai rawa yake yi, sai ma a lokacin yake iya ganin yanda ta koma, ta fita hayyacin ta gaba ɗaya kamar ba Ɗahiran da suka sani ba, kowa ya ganta ya san cewa wahala ne ya mayar da ita hakan
Shi kuwa Fadil tuni ya sheƙa a guje ya garzaya ya sanar wa Aunty Amarya, domin yanda yaga Ɗahiran na yi har kuka sai da ya fashe dashi
Nan da nan itama sai Aunty Amarya ta saki tuƙin tuwon da take yi, gaban ta na matsanta faɗi tayi General parlourn da sauri
Umma na take mata baya ita da Fadil, domin lokacin da Fadil ɗin yake sanar wa Aunty Amarya tana zaune a Parlour tana ji, kai tsaye sai da ta wuce ta shafa wa su Hajja Fatu da Hajiya labarin dawowar Ɗahira, kana suka wuce can parlour’n.
Suna shiga suka ga yanda su Big Dady suka tasa ta gaba suna rarrashi, a lokacin har da Abba da shigowar sa kenan ya jiyo kuka daga parlour’n, shi ne ya garzayo da sauri don ganin waye ne
Aunty Amarya kuwa ta kasa zama saboda ganin tilon ƴar ta yanda ta koma, nan da nan hawaye suka cika mata idanu zuciyar ta na sake tsintsinke wa, dama tun farkon tafiyan su hankalin ta be taɓa kwanciya ba, kullum da ita take kwana kuma take tashi, sosai taji a jikin ta ɗiyar ta ba ta cikin kwanciyar hankali, a kullum ranan duniya sai tayi mata addu’ar kariya da zaman lafiya ita da mijin ta.
Su Umma kuwa murna na ciki an kasa fito dashi fili, ko wanne sai zuba idanu yayi yana kallon ta, musamman Hajja da tafi kowa murna, tuni zuciyar ta ta bata aikin Malam ne yaci, kuma tabbas ta san cewa da takardan saki ta taho, dama abinda take burin ya faru kenan, kuma ga shi ya faru, yau tsaban murna ai sai ta zuba ruwa a ƙasa tasha.
Daƙyar Abba ya rarrashe ta tayi shiru, sai sakin ajiyan zuciya take yi tana shashsheƙa
Shi kuwa Big Dady tuni ya yi kiran wayan Usman amma a kashe ake ce masa, hakan yasa zargin sa ya sake tabbata, shi ne ya sake tambayar Ɗahiran abun da ke faruwa
Sai a lokacin ta samu bakin fallasa musu duk zaman da suka yi, kama daga farkon kai ta tun suna gidan nan, har rayuwar uƙuban da tayi a can Turkey, tana Yi tana wani sabon kukan da ya taho mata ta kasa tsayar dashi
Sosai Aunty Amarya a wannan karon take zubar da hawaye tsaban tausayin ɗiyar ta da kuma raɗaɗin da take ji a zuciya
Haka zalika shima Fadil sosai yake taya Yayar tashi kukan tausayin ta
Su Big Dady kuwa sun kasa cewa komi, ko wanne zuciyar sa tafarfasa kawai take yi da jin abinda Usman ya aikata, haƙiƙa da yana wajen nan ne, yau da sai sun taru sun yi masa ɗan iskan duka, komin girman sa kuwa tunda be wuce duka ba, ƙanwar sa jinin sa ita ce yayi wa wannan riƙon, wanda kashi me ɗoyi ya fita daraja a wurin shi, yanzu da ace bata gudo ba sai ta mutu zai kawo musu gawan ta? Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un
Kaka ne kaɗai ya iya yin magana a wannan lokacin, duk da shima ɗin sosai ransa yake a matuƙar ɓace, duk son da yake yiwa jikokin sa, ba ya haɗa su da son da yake yiwa Ɗahira, zai iya ɗaukar mummunan mataki a kan abinda Usman yayi mata da ace yau yana gaban sa. Cewa yayi, “aje a duba ta domin be yarda da lafiyan ta ba, maybe wannan uƙuban da ya bata yayi sanadin sanya mata ciwo, saboda yanda ta koma, idan kuma hakan ya faru, Wlh sai yayi mummunan saɓa wa Usman, domin sai ya ga fushin sa da be taɓa gani ba”.
Daga Abba har big Dady su ma faɗan suka hau yi, domin sai yanzu bakin su ya iya buɗe wa tsaban ɓacin rai, Abbu ne kaɗai be iya cewa komi ba, amma baƙin cikin abinda Usman yayi wa ɗiyar sa, har hawaye yake share wa tsaban ɓacin rai, haƙiƙa yau da ba don akwai na gaba da shi ba, da be san me zai yanke a kan Usman ba, sai dai kawai ya bar komi wajen ƴan uwan sa, domin ya san duk matakin da zai iya ɗauka, za su ɗauka a kan shi, kuma idan ma ya ɗau mataki ya nuna ba ya da kara kenan, ƴan uwan sa basu isa da ɗiyar sa ba sai shi.
A ɗakin kaka aka duba Ɗahira, sannan aka sanya mata drip, bisa umarnin Kaka, domin yace, “babu inda za’a matsa mishi da ita, a barta ya riƙa ganin ta ko zai samu kwanciyar hankali da raɗaɗin da yake ji a zuciya”. Dole a ɗakin zata zauna, domin har alluran barci an yi mata domin samun hutu, tunda sun ga matsananciyar damuwar dake zuciyar ta na barazanar kawo matsala ga zuciyar ta, ga kuma ulcer da suka gano tana fama dashi, wanda ada bata dashi ko kaɗan
Hakan ya ƙara ɗaga wa su Big Dady hankali, haƙiƙa Usman ya cutar da ita, kuma tabbas maganar sa ya tabbata, tunda har ya ce “sai sun yi nadamar aura mishi ita da suka yi” to, tabbas yau sun yi matuƙar nadama, haɗin zumunci be amfana musu komi ba sai tsantsan nadama da dana-sani a rayuwa, haƙiƙa sun cutar da Ɗahira wanda ba sa jin za su iya yafe wa kan su har sai ita ce ta yafe musu, me ake yi da irin wannan auren na ƙaddara, sun ɗau duk wani laifi sun ɗaura wa kan su, duk wani abu su ne sila.
Aunty Amarya ta kasa fita a ɗakin Kaka, ko kaɗan ta kasa jirga wa wajen ɗiyar ta, duk dauriyan ta, da kuma kawaicin ta yau ta gaza ɓoye abinda ke ranta, domin daga baya ma kuka sosai ta dinga yi, dole Abbu ya koma rarrashin ta, ƙarshe dai Umma ta koma ta ƙarisa musu girkin daren, domin Aunty Amarya bata da juriyan ƙarisa wa, ta ɗiyar ta take yi a yanzu ɗin.