FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2
A wannan ranan mutanen gidan sun kwana cikin ƙunci ne matuƙa, sai dai ƙalilan su da suka kwana cike da murnan abinda ya faru, ko Hajiya sai da taji ɗanta be kyauta ba, domin abinda yayi sai dai mara imani, bata taɓa tunanin ƙiyayyar da yake mata zai iya aikata mummunan abu makamanciyar haka ba, duk a ganin ta suna zaune lafiya, kawai son zuciya ne ya saka ta take nuna kyara ga Ɗahiran, da kuma zigi da yayi tasiri a zuciyar ta, wanda ada ko kaɗan ba ta jin tsanar ta, amma lokaci ɗaya ta ɗaura mata karan tsana, ga shi abinda ɗanta yayi ya fi komi muni, haƙiƙa har kunyan kanta take ji, “shin da wani ido zata sake kallon iyayen Ɗahira?” Yau sosai take nadama ga bin son zuciyarta. Kuma tunda ta koma ɗakin ta take kiran Layin Usman amma a kashe ake sanar mata, tayi kiran har ta gaji don kanta ta bari.
Washe gari sanda Ɗahira ta farka, gaba ɗaya yaran gidan ta gani a ɗakin Kakan har shi, illa Fadila da ba ta wajen, itama taji labarin komi, domin tuni Umma ta kira ta ta shafa mata, kuka sosai tayi tsaban tausayin ƴar uwan nata, tana jin kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a kusa da ita, amma babu hali.
Baffa ne ke zaune gefen ta ya riƙe mata hannun da ba’a yi mata ƙarin ruwa ba, su ma su Aunty Zainab da Aunty Zulaiha suna kan gadon zaune, sai Shakira dake kan drowan gadon, Kaka kuma yana can ɗaya side ɗin zaune a saman Wheel chair ɗin sa, ya zuba tagumi yana ta faman kallon ta. Inda Yusra ke zaune a can kujera, ita kanta duk taurin ranta yau dole ta tausaya wa Ɗahira, har tana jin zuciyar ta na karye wa tsaban tausayin ta, kamar ba Ɗahiran su ba, Ɗahira ƴar gayu wacce idan ma ka ganta tsaban haɗuwar ta baza ka taɓa cewa zata taɓa ƙasa ba, ita ce ta zama haka, ta zama tamkar wata almajira tsaban lalacewar da tayi, duk farin ta tsaban wahala sai da tayi baƙi, har da ƙuraje suka feso mata a fuska, wanda ada bata dasu ko ɗaya, gaskiya ta sha wahala tunda har ta koma haka kamannin ta suka sauya.
Yusra daga ita har Shakira suna da ciki, Sa’adatu ce kaɗai nata ma ya fi ƙanƙanta, don ita ko watanni biyu be kai ba, itama Fadila tana can tana fama da nata, ciwo sosai ma take yi har yanzu
Ita Sa’adatun tunda taji labarin dawowar Ɗahira ƙin zuwa tayi, tana ganin sanda Baffa ya fice amma ko bi ta kansa bata yi ba, taci gaba da kallon ta.
Baffa shi ya soma ganin farkawan ta, don haka ya sake riƙe hannun ta sosai cike da jin daɗi yana kiran sunan ta
Hakan ya ankarar dasu, sai duk suka bi ta da sannu ko wacce tana murna
Ita kuma Ɗahira kallon su kawai take yi ta kasa furta komi, duk da a ƙasan ranta daɗi ne ya cika ta
Duk sannun da suke mata ta kasa amsa wa
A lokacin ne Fadil ya shigo ɗakin, ganin ta farka sai ya fita a guje don sanar wa da Aunty Amarya, tunda dama ita tace masa, “idan ta farka ya zo ya sanar mata domin ta kawo mata abinci”. Tare suka dawo ɗakin da Fadil ɗin, ya riƙe mata coolarn abincin
A lokacin har Ɗahiran ta tashi zaune da taimakon Baffa, har ta buɗe baki tana amsa musu gaisuwar nasu tana murmushi
Kaka sai tambayar ta inda ke mata ciwo yake yi, “idan da akwai ta sanar mishi sai a sake duba ta?”
Murmushi tayi masa tana kallon sa tace, “tsoho me ran ƙarfe, babu abinda ke damu na yanzu, tunda har na ganku kusa dani hakan ya fiye min komi Wlh”.
Sallaman Aunty Amarya suka amsa da suka shigo a yanzu ɗin
Taƙarisa ta zauna inda Baffa ya tashi ya bata wuri, a nan take mata “ya jikin?”
Ɗahira ta kalle ta kamar zata yi kuka tace, “da sauƙi Mama na, babu abinda ke damu na”.
“To shagwaɓa ya tashi ko? An ga Mama”. Cewar Aunty Zulaiha tana dariya
Su ma sauran duk taya ta suke yi, har Ɗahiran da idanun ta suka cika da ƙwalla
Aunty Zulaihan ta sake cewa, “amma fa kar kiyi kukan don Allah kin ji ƴar ƙanwa ta?”
Gyaɗa mata kai tayi, tana kai hannu ta share hawayen tace, “to bazan yi ba”.
Kaka yace, “ai idan akwai ki dole sai kin saka ta kuka, sai dai idan ba Zulaiha bace ke”.
Dariya duk kan su suka yi
Aunty Zainab ta amshi coolarn daga hannun Fadil ta zuba mata abincin
Sai da Shakira ta taimaka mata ta shiga Toilet ɗin Kaka ta wanke bakin ta, kana ta soma cin abinci ana zuba hira, ita dai bata sake magana ba sai dai ta riƙa bin su da murmushi
Kaka sai da ya kore su a kan “suna damun ta” amma sun ƙi tafiya
A lokacin ne Hajiya itama ta kawo nata abincin, tayi mata “sannu da jiki?”
Yanda Hajiya ta saki fuskar ta ne, sai duk Ɗahira taji daɗi, a ranta tana mamakin sauyawan ta, wani zuciyar nata kuma tace mata, “ƙila tausayin abinda ɗanta yayi miki ne”. Gyaɗa kanta tayi kamar da wani take yi
Abincin Hajiyan duk kowa ya ɗiba suna ci ana ci gaba da hira, ita dai Hajiya tuni ta juya ta fice
Babu daɗe wa su ma su Big Dady suka shigo, sai a lokacin ne wasu suka rage suka koma Parlour
Sannu da jiki suka yi mata cikin kula wa sosai
Ɗahira ta amsa su cike da fara’a
Big Dady yace, “Daughter babu wani abinda ke damun ki yanzu ko? Kina jin ƙarfin jikin?”
“Eh Dady, alhmadulillah babu komi”.
“Ok to ga Maganin ki sai ki sha yanzu, idan kin gama Baffa kayi mata wannan alluran barcin, don ya kamata ta samu hutu sosai, in yaso idan ta tashi sai tayi sallolin da ake bin ta, amma yanzu kam hutun ta ake buƙata, ku ma ya kamata ku bar ta haka ta huta”.
Abinda Big Dady yace hakan suka yi, duk suka fita suka bar ta. Inda Baffa ya anshi maganin da alluran ya riƙe domin idan ta gama ya bata.
Bayan ta gama cin abincin sai ya bata maganin, sannan yayi mata alluran, babu jima wa kuwa barcin ya sure ta.
Zuwa yamma kuma duk su Aunty Zulaiha suka wuce gidajen su.
????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
بسم الله الرحمن الرحيم
⚖
FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
JIKAR LAWALI CE✍️
Wattapad: UmmuDahirah????
\F.W.A????/
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY
EPISODE Fifty One
Washe gari Hajja Fatu ta tashi da tashin hankali ne, tun sassafe aka kira ta da wayan Shakira aka sanar mata bata da lafiya, a lokacin tana tsaka da shirin tafiya Office ne, domin har Abba ya wuce, nan ta zari mayafi jiki na rawa tayi gidan Shakira ba tare da ta sanar da kowa ba
Koda ta Isa ta cidda ƙanwar Sahabi ne ita kaɗai da Shakiran, dama ita ta kira ta tafaɗa mata rashin lafiyan da ta zo ta tarar da Shakiran a mawuyacin hali, ga shi Sahabin ba ya nan ya fita tun safe shima, a lokacin ne ciwo gadan-gadan ya taso mata, Allah ya jeho ƙanwar Sahabin ta biyo ta gidan domin ta amsa kuɗi wajen Yayan ta sai ta wuce school.
Sosai hankalin Hajja Fatu ya tashi da ganin Shakiran na ta zubar da jini, gaba ɗaya ta gama fita hayyacin ta. Nan ta saka ƙanwar Sahabin ta taimaka mata suka kai ta cikin motan ta, sannan taja suka nufi asibiti, yayinda ƙanwar Sahabin kuma ta koma gida don sanar da mahaifiyar su.