BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

       Suna isa asibiti a rikice Hajja taje ta kira nurse’s, aka ɗauke ta a Wheel chair, emergency Ward’s aka wuce da ita aka soma bata taimakon gaggawa

Hajja duk ta rasa tunanin da zata yi ma, sai faman goge gumin dake tsatstsafo mata a goshi take yi, duk da kuwa garin babu zafi luf-luf ne kamar za’a yi ruwa ma. Ruɗun da ta shiga be bari ta sanar wa kowa ba

Sai Baffa ne da yazo wuce wa ya hange ta a wannan yanayin, sai faman sintiri take yi tana kaɗa hannaye, nan ya iso wajen ta yana tambayan ta abinda ke faruwa ya ganta a nan? Tunda ya san ba nan ne Office ɗin ta ba

Kallon sa tayi kamar zata yi kuka tace, “Shakira CE babu lafiya, an kira Ni na je na ganta a mawuyacin hali tana ta zubar da jini, tamkar ma bata da rai”. Sai ta fashe da kuka tsaban shiga tashin hankali, fatan ta kawai Allah yasa ba wani abu bane zai sami ɗiyar ta, su kenan mata su biyu, idan ta rasa ta bata san ya zata yi ba

Jin abinda Hajjan ta faɗa sai shima hankalin nasa ya tashi, nan ya soma tambayar ta “to garin ya hakan ta faru? Ina Mijin nata?”

“To wa ya san inda mijin nata yake, ƙila yana wajen aiki ne, amma Ni da naje babu shi”.

“To bari in faɗa ma su Abba, ina zuwa”. Yafaɗa da sauri yana yin gaba.

      Sanda likitan dake duba Shakira ya fito, sai duk suka nufa wajen sa, kama daga kan su Abba har su Yusra duk suna wurin, sai kuma mahaifiyar Sahabin ita da ƙannin sa biyu maza, tambayar sa “jikin nata suka yi?”

Likitan yace, “yanzu babu wani matsalan dake damun ta su kwantar da hankalin su, ɓari tayi shi ne yaja mata zuban jinin, amma da zaran ma ta farka komi normal ne sai abinda ba’a rasa ba”.

Kowa alhmadulillah yake faɗa, ba kamar Hajja Fatu da duk ta fi su shiga tention

Nan Doctor ɗin yace, “za su iya shiga su ganta”. Kafin nan yace, “yana son ganin su Abba a keɓe”.

Su ukun duk ka suka bi shi, sai da suka shiga Office ɗin nasa suka sami wuri suka zauna

kafin likitan yace, “am.. DOCTOR’S gaskiya yarinyan nan ba haka kawai cikin jikin ta ya zube ba, naga kun yi yawa ne shiyasa ban faɗa muku matsalan a waje ba, akwai ƙwayoyin da tasha su wanda su suka zubar mata da cikin, ba don Allah ya tsare an kawo ta da wuri ba wlh da an sami matsala, domin ƙwayoyin suna da illa sosai, saboda suna aiki a jikin mace in two minutes, ƙarfin sa yana sa mace ta sami matsala a mahaifar ta, ko kuma wasu matsalan dai wanda ba ma fatan hakan”.

Duk shiru suka yi da jin bayanin likitan

Inda yaci gaba da faɗin, “amma ya kamata ta kiyaye gaba, domin idan ta sake amfani dashi abinda ake gudu zai faru ne”.

“Ok mun gode Dr. Bashir, babu matsala yanzu zamu iya tafiya?” Cewar Abbu kenan yana kallon sa

“Eh babu komi, duk wasu magunguna mun rigada mun bata tasha, da zaran ta tashi zata farka da kuzarin ta insha Allahu”.

Sallama suka yi masa suka fito, babu wanda ya sake tayar da maganan har suka je suka duba ta suka fito, Office suka wuce tunda a lokacin tana barci ne. Sai bayan ta tashi ne Big Dady da Abbu suka dawo a tare, a lokacin babu kowa wajen ta sai Hajja Fatu

Don haka Big Dady bayan sun yi mata sannu da jiki sai yace da ita, “ke Shakira tashi zaune zamu yi magana”.

Tashi tayi kamar yanda yace mata, kanta a ƙasa ganin yanda suke bin ta da kallo, har wani zillo gaban ta yake yi domin gani take yi tamkar tayi laifi ganin yanda suka ɗaure fuskar su

Hajja dai itama shiru tayi tana jiran jin abinda zai faru

Big Dady yace, “ya aka yi kika sha maganin zubar da ciki? Dama ashe baki da hankali bamu sani ba?”

“Zubar da ciki kuma?” Inji Hajja Fatu tana bin su da kallo, kana kuma ta mayar da idanun ta kan Shakiran don itama taji amsar nata

Ita kuwa zare idanu tayi tana ƙifƙifta su, sai kuma ta fashe da kuka sosai kamar an yanka ta

Hakan yasa Abbu yace, “bayani zaki yi mana ba kuka ba, ba ma son sakarci kinji ko? Yanzu da ba don an kawo ki asibiti da wuri ba; bamu san matsalan da zai same ki ba, sai dai Allah ya rufa asiri ya tsare babu abinda ya faru dake, amma kin rasa cikin tunda hakan kika fi so”.

Cikin kuka tace, “wlh wlh Abbu wlh ku yarda dani ba Ni ce na sha maganin zubar da ciki ba, wlh sai dai idan Sahabi ya saka min a wani abun nasha, amma wlh ban sha komi ba”.

Hajja Fatu da tsaban takaici ya cika ta na jin an zubar mata da cikin jikan ta, tace, “Dan uban ki taya Sahabi zai baki maganin zubar da ciki ki sha? Idan ba ke ce kika san irin magungunan ba shi Sahabi taya zai baki ki sha?”

“Wlh Hajja shi ya bani, dama can ba ya son cikin, yayi-yayi in zubar amma naƙi na ce masa ina son Abu na, Amma sai da ya san yanda yayi ya zubar min”.

Big Dady yace, “to ya isa haka, kiyi shiru, but yau kin sha wani abu ne da safe da kika tashi?”.

Gyaɗa masa kai tayi sai tace, “eh nasha fura dana tashi, lokacin ina sha babu jima wa naji ciki na yana murɗa wa, daga nan ne na fara jin ciwo”.

Jinjina kai suka yi kafin suka sake mata sannu tare da kwantar mata da hankali sosai, sannan suka fice.

     Suna fita Hajja ta soma mata faɗa a kan “meyasa tun farko da yace zai zubar da cikin bata zo ta sanar mata ba? Ai da tayi wa tufkar hanci, amma ga shi yanzu ya cuce su ya zubar da cikin”.

“Hajja wlh ban yi zaton abun zai kai haka ba, da fari da ya tayar da fitinan sai an zubar faɗa muka yi tayi dashi, daga ƙarshe yace min ya haƙura, tunda mun yi hakan dashi ne tun lokacin da cikin yake ɗan wata ɗaya da muka gane ina da ciki, ashe wayau yayi min akwai abin a zuciyar sa har yanzu”. Ta ƙare maganar tana me fashe wa da sabon kuka

Hajja rarrashin ta ta hau yi kawai tunda me afkuwa ya riga da ya afku, sai dai kuma a koke gaba.

         Mutanen gida duk sun zo tunda labari ya je musu Shakira na asibiti, Ɗahira ne da Kaka kawai basu samu damar zuwa ba, Ɗahira na fama da nata jikin, tunda yanzu sosai zazzaɓi ya rufe ta, ko kaɗan ba ta jin daɗin jikin ta, ƙarin ruwa ake ta mata, duk da yanzu alhmadulillah ba kamar jiya da ta kwana dashi ba.

       Har yamma yayi babu Sahabi babu labarin sa, kuma duk ƴan uwan sa suna ta zuwa gaishe ta, zuwa dare aka sallame ta tunda jikin da sauƙi babu wani abu, kai tsaye su Big Dady gida suka wuto da ita, sun yanke shawaran baza ta koma ba har sai Sahabi ya zo ya same su.

       Be zo ɗin ba sai washe gari da rana, lokacin duk suna Hospital, Hajja Fatu ce kawai bata je ba ta zauna kula da Shakiran, wajen Kaka ya soma zuwa ya gaishe sa

Kaka ya amsa shi kamar babu wani abu tunda shima be nuna komi ba, illa neman gafara da ya nema a kan rashin zuwan sa a jiya ya duba ta, wai “akwai babban abinda ya tsayar dashi ne.”

       Waya Kaka ya ɗauka ya kira su big Dady ya sanar musu da zuwan Sahabi wai “ya zo ɗaukar matar sa”.

Tare da Abbu da Big Dady suka taho, don shi Abba ƙin zuwa yayi, suna zuwa suka tarar dashi har yanzu yana tare da Kakan, har an ajiye masa abin motsa baki. Bayan sun gaisa dashi

Sai Big Dady yace, “Sahabi abinda yasa muka nemi ganin ka kaima mun san ka sani, jiya matar ka ta yi ɓari har ta kwanta a asibiti amma ka kasa zuwa ka duba ta, Dalili kuwa shi ne saboda baka ɗauke ta da wani muhimmanci ba, sannan kuma saboda kai ne ka jawo musabbabin ciwon nata, kar ka manta mu nan gidan likitoci ne da ko wane fanni mun san matsalar sa, a tunanin ka idan har ka zuba mata magani a abun sha tasha cikin ya zube baza mu gane bane? To, kayi wa kanka ƙarya, don me idan ba ka son ciki zaka bari ku ɗauka? Idan da wani matsalan ya sami ɗiyar mu wato ba ka da asara ko?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button