FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2
Tana nan zaune kamar mintuna 20, sai ta jiyo buɗe ƙofa, sai dai bata motsa ba tunda ta san shi ne
Kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai, ba tare da ya ce komi ba ya sanya ƙafan sa ya fice, a ransa yana murmushin mugun ta, “tabbas zai koya wa yarinyan nan hankali, bata san waye shi ba har yanzu. Nan gaba ko yace kar tayi wani abun; to baza ta tsallake umarnin sa ba”.
Tana ganin ya fita, sai kuma ta tashi ta nufi kichen ɗin, dube-dube ta hau yi, wasu abubuwan duk bata taɓa ganin su ba, amma dayake tana karanta wa sai ta gane amfanin su, nan tazaƙulo indomie ta dafa, daga mai sai gishiri ta saka, saboda duk sauran kayan girkin su ba iri ɗaya bane, ta san ko da ta saka ba daɗi za su yi mata ba, sai dai a hankali zata soma gwadawa ta ga ko zata iya ci, amma yanzu yunwa take ji baza ta zauna tayi abinda baza ta iya ci ba.
Tana gama wa ta fito Parlor tayi zaman ta tana ci, sai da ta gama sannan ta koma ta wanke komi ta mayar muhallin sa, still ta sake koma wa Parlour tayi zaman ta, tunanin rayuwa kawai take yi tare da kewar gida, ga shi babu waya a hannun ta bare ta sa ran zata kira su, shiyasa ta yanke shawaran yana dawowa zata ce “ya bata wayan ta”, tunda dai ba nashi bane.
Ganin duhu ya soma yi ta duba agogon hannun ta taga magriba tayi, sai taje tayi alwala ta dawo, ta tayar da sallan ta, tana idar wa ta duƙufa addu’a, ta jima a wajen har lokacin isha’i yayi, ta gabatar. Ga duhu ko ina dole ta soma jin tsoro, tunda ba inda ta saba da shi ne ba, nan ta ƙudundune a kujera ta rufe idanun ta ta hau karatun Alqur’ani a hankali da muryan ta me tsananin daɗi, a haka har ta soma jiyo motsin buɗe ƙofa, tayi shiru tana buɗe ido tare da kallon wajen
Usman ne ya shigo riƙe da wayan sa yana haska wa, tunda ya shigo ya ƙyalla hasken kanta idanun sa suka sauka cikin nata idanun, yanda ya ga idanun suna wani ƙyalli sun sauya kala sai yayi saurin ɗauke kansa gaban sa na matsanancin faɗi, rufe ƙofan kawai yayi ya nufi ɗakin sa, domin so yayi tun yau ya soma mata tijara, amma ganin ƙwayan idanuwan ta bazai iya zuwa ba
Yana shige wa ta rufe idanun ta, “wai da gaske dai mutumin nan be da imani anan zai bar ta ta kwana?” Tafaɗa a ranta. Numfashi taja ta gyara kwanciyar ta tana sake ƙudundune wa, bata sake motsi ba illa tunani da take ta faman yi, sai daga baya ta samu barci daƙyar ya sumfice ta.
Washe gari ta farka a makare, ƙarfe 07:00am. A lokacin, shaf-shaf tayi alwala ta gabatar da sallan ta, ta zauna nan tana ta lazimin safe, sai da gari yayi haske sosai kafin ta miƙe ta nufi kichen, a tunanin ta ko ya fita ne tunda bata ji motsin sa ba, ga shi har sha biyu tayi, amma haka nan ta soma haɗa musu Breakfast har da shi, ruwan tea ta haɗa sai arish da ta soya, ta kwashe ta kai saman dainning, ta zo ta sake duba kichen ɗin ta ɗauko kayan haɗa tea ɗin, duk ta kai kan dainning ɗin. Sai da taje tayi bruch kafin ta zo ta haɗa tea ɗin ta sha da arish ɗin, tunda babu ko bread bata gani ba
Bayan ta gama ta tashi ta je ta ɗaura ruwan zafi, yana ɗumi ta sake tayi wanka ta shirya a Toilet ɗin, yau ma riga da skert ta saka na kanti, rigan t.shirt ne me gajeren hannu ja, ta zauna mata ɗas ta yi mata matuƙar kyau, sai ta saka skert Robber light green, irin me tsagin nan ta baya, sai da ta ɗan yi kwalliya kaɗan tunda sabon ta ne, gaskiya tayi mugun kyau matuƙa, musamman yanda take kyakykyawar nan. murmushi kawai tayi tana zaro siririn gyale ta yafa a kanta zuwa wuyan ta, sai ta zauna a kan kujera, a ranta tana tunanin ko ta tashi ta gyara parlor’n ne?
Buɗe ƙofan da Usman yayi na ɗakin sa, shi ne yasa ta ɗago manyan idanuwan ta ta sauke a kanshi, tare da dakata wa daga miƙewan da tayi ninya
haka zalika shima kallon ta yake yi, lokaci ɗaya ya ɗauke kai yana cin magani, da alamu dai fita zai yi saboda a cikin shirin sa yake
Takowa yayi ya isa wajen kujerun
Duƙar da kanta tayi kawai tana jin gaban ta na faɗuwa
“Keee”. Yayi maganar a maƙoshi yana ja
Ɗago kai tayi tana kallon sa, yanda ya tsare ta da ido da fuskar sa tamkar hadarin kaji, daga gani ba mutunci a tare dashi, hakan yasa ta ɗauke kai itama tana shan kunu, domin bata san da me ya zo ba
Zama yayi be sake cewa uffan ba, don be san ma ta ina zai fara ba tsaban miskilanci, ga shi matsanancin haushin ta yake ji, tare da sake jin tsanar ta me ƙarfi a ran sa, “ko uban wa zata yi wa kwalliya?” Ya faɗa a ransa yana sake kallon ta
“Ki tashi ki je ki ɗauko min Trolly ɗin ki”. Yayi maganar tamkar ba shi ba
Sai da ta kalle sa kafin kuma ta ɗauke kai tana me mamaki. Amma bata ce komi ba ta miƙe ta nufi wajen kayan ta, janyo wa tayi ta kawo masa har gaban sa
“Buɗe shi”. Ya sake bata umarni
Ita dai bata ce uffan ba sai mamaki da ke son kashe ta akan “me zai yi mata da kaya?”
Tana buɗe wa ya sake ce mata “ta fito da duk komi dake ciki”.
Hakan kuwa ta sake yi
Ɗaya bayan ɗaya ya saka ta tana ɗaga kayan, don shi bazai iya saka hannun sa ya taɓa kayan ta ba
Idan ta ɗaga sai ya ce “ta ajiye gefe,” wani kuma yace “ta mayar cikin akwatin”. Karkatakaf sai da ya gama zaɓe ƙananun kayan dake ciki, sai atamfa da Abaya kaɗai da yace ta zuba cikin akwatin
Ita dai duk yanda yace tayi hakan take yi, arziƙin ta ɗaya bata biye wa miskilancin sa ta fito da under-Wears ɗin ta ba, da yanda ya saka take ɗai-ɗai da kayan ta; da ta sha kunya
“Waɗannan kaɗai kike da damar saka wa a gida na, nan ba gidan karuwan ki bane da zaki zo kina saka min ƙananan kaya, and daga yau aikin gidan nan gaba ɗaya ya dawo kanki, ko ina na cikin gidan nan kullum Ina son ki share shi tsab, ko alamun datti ba na son gani, zan bar miki keeys ɗin ɗakunan, kuma daga yau inda nace ki koma nan zaki koma, kar in sake ganin ƙazantaccen jikin ki ya zauna min a cikin parlor. sauran aiki ya rage naki, ki bi ko kar ki bi, idan ba haka ba zan baki mamaki Wlh”.
Tun sanda ya soma magana ta ɗago kai tana kallon sa, sakin baki kawai tayi tana bin sa da ido domin mamakin sa ma ya kusa kashe ta. Ganin yana shirin tashi tace, “ban gane me kake cewa ba fa? Ni fa matar ka ce ba baiwar ka ba. fine naji aikin gidan zan yi tunda dama aiki na ne, amma meye haɗin ka da kaya na da sai ka zaɓa min waɗanda zan saka? Kuma da kake cewa ba gidan karuwai na bane, amma ai naga Gidan Mijina ne, kuma idan ma nayi karuwancin iyawa ne, kasan da haka ka aure Ni, so ba abun damuwa bane”.
Sosai yayi mamakin furucin nata
Ita kuwa ƙarfin hali ne ta azawa kanta har ta iya faɗan waɗannan kalaman, domin ba ƙaramin tsoro ne cike a zuciyar ta ba, amma kuma tana gani idan har taci gaba da shiru ba ta mayar masa da amsa, tabbas ya samu damar kullum yana sakar mata magana yana cusa mata baƙin cikin sa.
Kallon ta yayi da idanun sa da suka soma sauya kala, domin maganar nan ma da yayi me yawa ba ƙaramin dauriya yayi ba, amma kuma tsaban rashin mutunci irin nata take maida masa martani, “ke nan baza ta bi umarnin sa ba?” Ci je leɓen sa yayi yana bin ta da kallo, sai kuma ya ɗan saki guntun murmushi yace, “me yi ba ya faɗa, don Allah idan kin cika ke ƴar uban ki ne, ki tsallake umarni na”.