FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Sai be amsa ba ya jeho mata tambayar “me wannan yaron yake min a nan? Ban faɗa miki saƙo na duk ranan da ya dawo kar in sake ganin ƙafafun sa a nan ba?” Be bari kuma Hajiyar tayi magana ba ya mayar da idanun sa kan Usman dake tsaye har yanzu kansa a ƙasa, “fitar min a gida dan uban ka, kai wato baka da mutunci ko Ban isa da kai ba? Wuyan ka yayi kaurin da har zamu zaɓa maka abu, amma ka ce mun yi kaɗan, dole sai ka nuna mana iyakan mu, to, saƙon da ka aiko ta tafaɗa mana ta sanar mana, cewa “sai mun yi dana-sani ko?” Eh tabbas mun yi dana-sani wlh ba sau ɗaya ba, yanzu zaman uban me kake min a wajen nan?”
Sumui-sumui Usman yazo zai wuce ya fice
Big Dady ya dakatar dashi, “dan uban ka ina takardan nata?”
Shiru yayi
Nan kuwa Big Dady ya zuciya ya daka masa tsawa, “da kai nake magana kayi min shiru?”
Cikin sanyin murya yace, “ban rubuta ba”.
Ƙwafa yayi kafin ya zauna yana cewa, “kar ka sake in sake maka magana a karo na biyu”.
Juya wa Usman ɗin yayi ya fice.
Hajiya dake tsaye duk ranta babu daɗi, ta san dama za’a rina duk da tabbas kamar yanda Usman ke hasashe ne fushin da suka ɗauka sun huce, amma da a lokacin ne ta san faɗan da zai sha sai ya fi haka, tana matuƙar son Usman duk cikin yaran ta, shiyasa ko kaɗan ba ta ƙaunar wani abu ya shiga tsakanin su da mahaifin sa, duk da shi ya jawa kansa. Ajiyan zuciya ta sauke kana ta sami wuri ta zauna tana kallon Dadyn, tace, “Dadyn Zainab don Allah ka sassauta wa wannan yaron, abinda ya faru ya rigada ya faru, yanzu sai dai mu ce Allah ya kyauta na gaba..”
Katse ta yayi da faɗin, “dalla rufe min baki, duk ba ke kike ɗaure wa yaron nan gindi ba, kar ki manta fa duk wani rashin ƙaunar auren nan da kike yi a baya yana raina kuma ban manta ba, ta yiwu da haɗin bakin ki yayi ma Daughter wannan abun da yayi”. Ya ƙare maganar yana miƙe wa cikin zafi ya wuce ɗakin sa
Sosai Hajiya ta shiga damuwa da jin zancen sa, “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un yanzu Ni yake zargi na saka Usman abinda yayi?” Shiru tayi kawai duk jikin ta yayi sanyi domin ta kasa tashi ma tayi abinda ke gaban ta, zuciyar ta na nadamar abinda ta aikata tun farko na nuna ƙiyayyar auren, yanzu ga shi hakan na son jawo mata matsala da mijin ta, yana zargin ta da ita ce ta ziga Usman, kuma babu yanda za’a yi ta kare kanta tunda tun farko ta nuna ba ta ƙaunar auren.
⚫⚫⚫
Usman kuwa yana fita gida ya koma ya ɗauki motan sa ya fice, be damu da dauɗan motan ba so yake yi kawai ya samu relif a zuciyar sa, gaba ɗaya yanzu jin sa yake yi wani iri, abinda yake ji a ƙasar zuciyar sa dake buga wa tana sake taso masa tana mamaye zuciyar, tsaki yaja a ransa yace, “kai fa kace zaka iya ɗaukar duk wani abinda zai faru? Ba ga shi yanzu faɗan Dadyn naka ya wuce ba, saura kuma nasu Kaka suyi nasu su gama”. Da wannan tunanin nasa ya ɗan samu ƙwarin gwiwa, sai dai yanayin da yake ji a zuciyar sa kwata-kwata ba ya jin daɗi, ya fi jin hakan duk sanda ya haɗu da wancan yarinyan (yana nufin Ɗahira. Fargaba da tsoro a zuciyar sa) amma abun mamaki yau kuma ba ta kusa dashi amma yake ji. Kamar an ce ya wulƙa idanun sa gefen daman sa, ai kuwa sai ga ta tazo ta wuce sa a motan ta, be yarda ita bace sai da yabi motan da kallo ta mirror, kuma tabbatas ya gane ita ce tunda ya ga fuskar ta, sosai ya haɗe rai ganin motan nata ta faka a bakin titi, sai ya ɗauke kai yana jin kamar ya koma ya sanar mata tun yanzu ya sake ta, sai dai kuma ba ya ƙaunar ganin fuskar ta, gwara idan ya koma gida ya rubuta sakin ya miƙa wa Dady, haka ya ƙara wa motan wuta yana jin kamar ya ciro zuciyar sa ya jefar tsaban abinda yake ji.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Ɗahira kuwa da ta faka motan ta a bakin titi fito wa tayi, duba tayan ta soma yi abinda take zargi ne tayi faci, sai taja dogon tsaki cike da takaici, “oh Allah ka taimake Ni, wlh motan nan kin yi min wulaƙanci tunda kika tsaya min a hanya, yanzu ya zan yi?” Sai ta sake jan tsaki tana koma wa cikin motan, wayanta ta ɗauka tana neman Numban bakaniken su, amma a kashe ake ce mata, maida akalan kiran tayi kan Numban Baffa, shi kuma ba service, gaba ɗaya duk ta damu domin ta san ruwa zai iya riskan ta a nan, dole ta yanke shawaran hawa keke napep ya ƙarisa da ita gida, inyaso ta bar motan a nan me gyara yazo ya gyara. Jakan ta ta ɗauka ta fito ta rufe motan da keey, kana ta ƙarisa bakin titin sosai don ta samu abun hawa, kasancewar hanyar babban titi ne ba kasafai suke tsaya wa ba, duk yawanci ma akwai mutane shiyasa tasha wahalan samu. Tana nan tsaye sai mota ta faka a ɗan nesa da ita kaɗan, kallon motan tayi da kyau, ta gane ko na wane ne, na Dr. Said ne tunda yanzu ma kafin ta fito sai da suka yi sallama dashi a wajen motan nasa, kafin ma ta gama tunanin nata
Sai gani tayi Abokin sa Dr. Sabo ya leƙo yana mata alama da hannu ta taho
Nufan wajen tayi kanta tsaye, tana isa sai ta leƙa gaban domin tayi masa magana, sai dai ba shi ne a motan ba, wani mutum ne sai Dr. Sabo a gaban, murmushi tayi tace, “sannu Doctor ai nayi zaton Dr. Said na ciki ne?”
Shima yana murmushi yace, “a’a ba ya ciki, amma ki shiga sai mu sauke ki ko? Ina ce motan taki ce ta samu matsala?”
Gyaɗa kai tayi tace, “eh tayi faci ne”.
“Ok ki shiga kawai mu sauke ki”.
Godiya tayi masa ta buɗe baya ta shige, suna jan motan suka tafi.
Usman da yaje ya kewayo zai koma gida duk a kan idanun sa Ɗahiran ta shiga cikin motan, taɓe baki yayi yana bin bayan su, a ransa yana mamakin “ita wannan yarinyan har yanzu bata dena abun tsiyan nata ba?” Tsaki yaja a fili ya furta “karya kawai, idan da kun san abinda na sani a game da halin ta wlh da baku yi fushi dani ba”. (iyayen sa) Yayi maganar yana sake haɗe ransa tamkar da wani yake yi a gaban sa.
Sanda suka isa layin anguwar su memakon yaga motan ta shiga cikin anguwan nasu, sai yaga taci gaba da tafiya, be yi mamakin hakan ba illa shige wa layin gidan su da yayi, amma a ransa sai yayi tunanin "why not yau ya samu hujjar da zai gabatar wa iyayen sa a matsayin abinda ya saka yaƙi yarda da zaɓin su? Idan ya bi su ya gano abinda suke yi sai ya ɗauka a waya ya nuna musu". Wannan shawaran ta zuciyar sa ita yayi na'am dashi a lokaci guda, sai ya juya motan nasa nan da nan yabi hanyar da suka bi, ko kaɗan ba ya hango motan tasu, hakan yasa ya ƙara Speed sosai, ai kuwa sai ga su har ya kamo su yana bin su a baya ba tare da sun sani ba.
*
A cikin motan kuwa tunda Ɗahira ta shiga ciki bata yi tunanin akwai kuma wani a baya ba, sai da ta zauna kafin ta kula dashi, har taji tsoro tana shirin magana ya rufe mata hanci da baki da handkerchief, Lokaci ɗaya numfashin ta ya ɗauke tayi luuu ta zube jikin sa
Dariya suka kwashe dashi duk kan su, shi kuma yana gyara mata zaman ta da kyau
Wanda ke tuƙin yana ci gaba da dariyan yace, “ai wlh aikin nan da muka yiwa Dacta dole sai ya ƙaro farashi, don bazai yiwu ba muna ganin wannan zuƙeƙiyar budurwan kyakykyawa da ita muna gani mu barta ba tare da mun dangwali fa’ida ba”.
Dr. Sabo yace, “kai ina ruwan ka? Kana ji fa ya ce auren ta zai yi idan sun tafi can, ka dena haka don Allah”.
“Ai don na san yace hakan ne shiyasa baza mu siɗe masa kwanon ba, dole ne fa ya ƙaro mana kuɗi idan dai muka kai ta, domin duk wanda muka yi masa wannan aikin yana barin mana siɗi, amma shi babu abinda zai bar mana”.
Na bayan yace, “haka ne wlh, domin wlh oga wannan yarinyan tana da farashi kamar yanda kace, ka ganta kuwa?”. Ya ƙare maganar yana shafa fuskar Ɗahira da bata san ma yana yi ba