BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Dr. Sabo dai be ce musu komi ba illa ƙoƙarin kiran Dr. Said da yake yi, sai dai layin ba ya shiga saboda yanzu hadari sosai ya haɗu, garin yayi duhu sai iska da aka fara, ɗagowa yayi yana kallon me tuƙin yace, “layin sa fa ya ƙi shiga, ina yace zamu same sa a hanyan?”

“A’a ai be faɗa mana ba, sai dai idan zamu juya da ita mu kai ta gidan da muka haɗu dashi”.

Shiru dai Dr. Sabo yayi yana ci gaba da gwada layin, sai kuma yace, “wlh ka san Allah ba don ta ganni cikin motan nan ba baza ta hau ba, komawan mu akwai matsala, kawai ka faka a can mu nemi service mu rabu da alaƙaƙai tun kafin ƴan sanda su cafke mu, Ni wlh ban ma san ya aka yi na biye wa Dr. Said a wannan shirin nasa ba, da ya zo yayi kayan sa da kansa”.

Faka motan suka yi a gefen titi, domin har sun kusa fita cikin gari sun tasar wa hanyar Zaria, dama a hanya suka yi da Dr. Said ɗin zai amshi Ɗahiran ya wuce da ita Zaria, a can iyalan sa suke, daga can yake zuwa nan aiki, shirin da suka yi ya saka a sato masa Ɗahira ne domin yaje ya ajiye ta a wani gidan sa da yake dashi a Zarian ba inda matar sa take zaune ba, dawowar Ɗahiran a bakin aikin ta ya sake shige mata sai da suka ƙulla alaƙa, domin tun sanda ya sake ganin ta burin da ke ransa ya sake taso wa, dama yana kwaɗayin ta sosai, sai kuma zuciyar sa ta raya masa why not ya sace ta ta zama nasa kawai? Da taimakon wani abokin sa ya ba shi ƙwarin gwiwan ya sace Ɗahira ya ajiye ta a ɓoye ta zama tamkar matar sa, kuma zai riƙa zuwa wajen ta ne ba tare da ta san shi ne ba. Hakan yasa ya faɗa wa Dr. Sabo ƙudurin sa, shi kuma ya samo masa waɗannan mutanen domin su yi masa aikin, tunda dama kidnapping shi ne sana’ar su, da kuma yiwa yaran mutane Fyaɗe idan sun sace su.

           ******

              Usman dake bayan su yana ganin duk abinda ke faruwa, da tsayar da motan nasu da kuma fitowar da suka yi har su uku, suka ɗan yi gaba suna ɗaga wayoyin su, hakan ya gane suna neman service ne, sosai wannan abun ya ba shi mamaki, har a ransa ya ɗarsa zargin su lokaci ɗaya, “kar dai ace kidnappers ne su? To me zai saka taje wajen su da kanta?” Wani zuciyar nasa tace masa, “ta yiwu neman taimako take a wajen su tunda motan ta tayi faci”. Sai yayi shiru kawai yana tunanin abun yi, duk yana kallon su, kuma be damu su juyo su hange sa ba, tunda tazaran su babu nisa da inda yayi parking

Lokaci ɗaya yabi shawaran zuciyar sa, sai ya fito ya nufe su, ba tare da fargaba ko wani tsoro ba, shima wayan sa na hannun sa yana shirin neman layin wani daga cikin ƴan gidan su ya sanar musu da abinda ke faruwa, amma kuma wayan babu service, gaba ɗaya kiran da yake yi taƙi zuwa. Yana isa wajen motan duk basu san da zuwan sa ba tunda suna ta gaban motan ne sun juya wa motan baya. Leƙa motan yayi, ilai kuwa zargin da yake yi haka ne, kwance ya ganta tamkar matacciya ba ta numfashi, lokaci ɗaya ya saka hannu ya janyo ta tare da saɓata a kafaɗa yana juya wa da sauri ya nufi motan sa

A lokacin ne aka saki ruwa me ƙarfi wanda yaja mutanen suka juyo don shiga motan su su samu mafaka, kawai sai suka hangi Usman har ya kusa isa motan sa ɗauke da Ɗahira a hannun sa, basu tabbatar ba sai da suka duba cikin motan suka tabbatar da ita ce, ai kuwa nan suka bi bayan sa da gudu, ɗaya daga cikin su ya ciro bindiga ya soma harba masa

Take a nan Usman ya ƙara da gudu, yana isa motan ya buɗe ya ajiye ta a wajen me zaman banza, shi kuma ya zagaya ɗaya side ɗin da gudu yana duƙa wa don kar su same sa ya shige yaja motan, saboda ruɗewa ma kasa yin reverse yayi sai ya Yi kansu

Ganin haka sai suka dare don neman ceton ransu

Shi kuma tuni ya yanki jeji da gudu

Ɗaya daga ciki yace, “Mu bi shi mana me muke jira? Kaji min ɗan isa har yana da ƙarfin halin biyo mu ya ɗauke ta?”.

Tuni sun isa motan su sun shige, amma Dr. Sabo ya kasa bin su, gaba ɗaya ya ruɗe domin gani yake yi asirin su ya tonu, duk da be gane Usman bane amma ya san cewa duk wanda ya biyo bayan su ya san su, shiyasa duk ya ruɗe

Su kuwa tuni sun tafi sun bar shi a wurin sun bi bayan Usman

Usman dake tuƙi a cikin sunkuru, neman hanyar da zai yi ya fita titi yake yi, sai buga uban tsaki yake yi cike da dana-sanin abinda yayi, sai yanzu ma hankalin sa ya dawo jikin sa ya tuna wacce yazo ceto, maƙiyiyar sa wacce ya tsana a duk faɗin duniyar nan, ji yake yi kamar ya tsaya ya buɗe motan ya jefar da ita don haushi, sai dai yana tsoron kar su kama sa su harbe sa tunda yana hangen sun kusa kamo shi ma, sosai yake gudu a sunkurun ga ruwa da ake zuƙa wa a yanzu ɗin, titi ya nufa da gudun sa ko kaɗan be damu da ruwan ba, fatan sa kawai ya fita titi don yaji daɗin guje musu, sai dai be kula ba ashe ta wajen gada ya biyo, babban magudanan ruwa ne a wurin. santsin ruwa dana ciyayi suka ja shi ya karkace hanya lokaci ɗaya motar tasa ta gangara ƙasan gadan dake cike da ruwa, duk ƙoƙarin da yayi don ganin ya samu ya fita kafin motan ta shige sosai amma ya kasa, lokaci ɗaya suka afka ciki ji kake yi cindimm..

       Ba don Allah yasa su ma sun ja wawan burki ba, da tuni tasu motan su ma ta afka, domin uban gudun da suka shanyo, dole suka ja birki lokaci ɗaya, ganin motan Usman har ta nitse ai tuni sun juyar da nasu sun bar wurin, inda Dr. Sabo yake suka je suka ɗauke shi suka gudu.

????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

        EPISODE Fifty Three

         Aunty Amarya shiru-shiru taji yau Ɗahira bata dawo kamar yanda ta saba ba, domin tunda ta koma bakin aiki, to, ba ta wuce 05:30pm. Take dawowa gida, ko shida ba ta kaiwa yanzu, bare yau ana ruwa tayi tunanin zata dawo da wuri. hankalin ta duk ya tashi hakan yasa bayan ta idar da sallan magriba sai ta fito Parlour ko cire hijabin jikin ta bata yi ba, zama tayi tana jiran Abbu ya dawo masallaci sai ta sanar masa, dayake wayan ta ta lalace kwana biyu, to, bata samu an gyara mata ba

Zaman ta babu daɗe wa Fadil ya shigo da sallaman sa

Tana amsa mishi sai tace, “yauwa Auta zo ka kira min Numban Yayar ka, har yanzu bata dawo ba ban san me ya tsayar da ita ba”.

“To Aunty bari in ɗauko wayan a ɗakin Umma na bar ta da zan je Masallaci”. Wuce ta yayi da sauri ya shiga ɗakin Umma dake sallah ya dauko ya dawo

Koda ya kira wayan a kashe ne, yayi try har sau biyu a kashe ake ce masa, sai ya kalli Aunty Amarya dake kallon sa ko ƙyafta idanu ba ta yi, duk da tana jin an ce wayan a kashe, amma ta kasa magana, yace da ita, “Aunty a kashe ne fa”.

“Sake kira min, me ya sami wayan nata da zata kashe? Ai yaci ace ta dawo yanzu ko?”

“Haka ne Aunty, yanzun ma ga shi a kashe”.

A lokacin Abbu yayi sallama ya shigo parlour’n

Duk suka amsa mishi suna bin shi da kallo

Shima ganin su cirko-cirko sai yace, “lafiya me ke faruwa?”

“Wlh ba lafiya ba Abbun Zulaiha, Ɗahira CE har yanzu bata shigo ba, kuma na san idan wani wuri taje dole zata faɗa mana, sannan wayan ta ba ya shiga ma”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button