FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

“To fa subhanallah.. amma kin san halin ta akwai son aiki, yanzu haka ta samu wata patient ne hakan ya tsayar da ita wajen duba ta, kin san ta ai”.
“To yanzu shikenan Abbun su baza a bincika a gani ba? ka san fa bata taɓa kaiwa haka ba, yanzu ana shirin kiran sallan isha’i fa”. Cewar Aunty Amarya cike da damuwa
Abbu yace, “ki kwantar da hankalin ki don Allah, bari in saka takwara ya bi ta ya gano mana ko lafiya, kai Fadil kira min Baffa”.
“To Abbu”. Fadil ya amsa mishi yana fice wa
Itama Umma a lokacin ta fito tana tambayar abinda ke faruwa
Aunty Amarya ta sanar mata
Sai cewa tayi, “to Allah ya kyauta, Allah yasa dai lafiya”.
“Amin”. Inji aunty Amarya tana zama, tunda tun sanda aka soma zancen ta tashi tsaye
Shima Abbu zaman yayi yana ɗaukan wayan sa don ya gwada kiran ta
Yayinda Umma ta wuce kichen don kwaso abinci ta shirya a dainning.
Sanda Baffa yazo, Abbu ya sanar masa “yabi bayan Ɗahira asibiti ya dubo ta”.
Da Fadil suka tafi a lokacin ruwan ya ɗan tsakaita. sun je har asibitin an tabbatar musu da tafiyan ta, hankalin su sosai ya tashi da jin ta daɗe da tafiya ma tun biyar da ashirin yau ta fice.
Sanda za su dawo gida ne Baffa ya hangi motan ta a kan hanya, tunda da za su je be kula ba saboda ba ta side ɗin suka biyo ba, nan suka fito da sauri suka nufi motan, duk sun duba babu ita ga shi motan ma a rufe ne, a nan ne hankalin nasu ya sake tashi ainun
Cikin sauri Baffa yace wa Fadil, “su yi maza su wuce gida”.
Da sauri suka shige motan ya figa suka yi gida, suna isa suka tarar da Abbu ma a haraban gidan yana waya
Saurin katse wayan yayi ya nufe su yana tambayar Baffa “kun ganta? Ina take?”
Nan Baffa ya sanar masa da komi
Ai nan Abbu shima ya ruɗe yana faɗin, “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un.. me ke faruwa ne?”
Su Big Dady da suka fito za su tafi masjid, suka tambayi ba’asi, da jin abinda ke faruwa su ma hankalin su ya tashi ainun, Abba dake da Numban wani abokin sa ɗan sanda, tuni ya kira shi ya sanar mishi abinda ke faruwa.
Kan kace me kowa yaji labarin rashin dawowar Ɗahira, nan da nan Hankula suka sake tashi, ba kamar Kaka duk ya gama ruɗe wa, basu so ma faɗa mishi ba, amma kuma ganin har ƙarfe goma tayi babu labarin ta duk inda aka je, dole suka faɗa mishi. Gida dai ya rikice ana neman Ɗahira babu ita babu labarin ta, duk an kira dangi “ko sun ganta?” amma babu wanda yace, “ta zo”, hanya an bi ya kai sau goma amma babu ita, ƴan sanda kurɗa-kurɗa an baza su amma ba’a dace ba
Sai da wajen sha daya tayi kafin Hajiya ta lura shima Usman be dawo ba, dayake mutanen gidan har yanzu basu ji labarin dawowar sa ba, Big Dady be sanar musu ba, sai nan itama Hajiya ta ruɗe ta soma kiran layin sa, amma shiru shima a kashe, ta kira Big Dady ta sanar mishi
Shima tun yana ɗaukan abun da wasa, domin ko kallon inda take be yi ba sanda ta sanar masa, sai kuma abun ya soma damun sa ganin lokaci na ja, a nan ne yake sanar ma su Abba “ai shima Usman be dawo ba”.
Duk sun yi mamakin maganar nasa, basu kai ga magana ba Hajiya ta ƙariso wajen tana kuka tana sanar wa Big Dady “har yanzu ta kasa samun layin Usman, kuma ta je gidan shi babu motan shi babu shi a ciki”.
Abba yace, “dama ya dawo ne ashe?”
Sai a nan Big Dady ya tuna basu sani ba su, shi ne yake sanar musu da dawowar sa ɗazu.
Abu kamar almara an nemi su Usman ba’a samu ba, a wannan daren babu wanda ya runtsa a gidan nan sabida tashin hankali, kowa tunanin yanda mutane biyu aka rasa su a lokaci ɗaya, sai kuma duk tunanin su Big Dady suka koma kan “ko dai Usman ne ya ɗauke ta suka koma can Turkay ɗin?” Wannan tunanin yasa Big Dady safiyar Allah na yi yace, “zai je domin yaci uban sa a can, wlh idan har da gaske ne tunanin nan nasu Usman ya kaɗe a wurin shi,” sosai ransa ya ɓaci sai faɗa yake yi
Ganin haka yasa Kaka yace, “kar yaje, Baffa yaje shi ya gano musu”.
Wannan dalilin ne yasa Baffa ya shirya aka nema masa jirgi na ƙarfe 10:00am a ranan ya wuce TURKEY.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Duk yanda ya so ya buɗe ƙofan motan ya fice ya kasa, har sai da motan ta gama nitsewa zuwa ƙasa, kokuwa yayi ta yi amma ya gaza, ba don Allah yasa ya iya ruwa ba da tuni babu numfashin sa, amma duk da haka yanayin awannin da suka ɗauka a haka cikin motan babu jan numfashi bare iska sai duk ya galabaita, ya rasa ya zai yi har numfashin sa ɗauke wa yake yi kamar zai shiɗe
daƙyar da siɗin goshi ya samu ya buɗe ƙofan motan, har zai fice ya tuna da ita, nan ya dawo ya janyo ta suka fito daga cikin motan, sai dai yanda ake tsula ruwa ya kasa yanda zai yi ma yayi iyo, take a Nan ruwan yayi gaba dasu saboda yanda ruwan yake gudu sosai, ta cikin gadan wajen yabi dasu yay gaba dasu, dayake wajen makwararan ruwa ne na sassa-sassa dake tafiya ya isa babban kogin dake can wani yankin jeji dake cikin Kadunan.
Tun Usman na sanin halin da yake ciki, har shima numfashin sa ya ɗauke gaba ɗaya
Ita kuwa Ɗahira har yanzu bata farka ba ma bare tasan inda take.
A haka har garin Allah ya waye, inda wajen hantsi wani Tsohon Mutum yazo gaɓar ruwa zai ɗiba ruwan a tulu, a nan ya tsince su tamkar matattu ruwa ya fito da su bakin gaɓar ruwan, sosai hankalin tsohon nan ya tashi, nan ya nufe su cike da mamakin ganin su, sai da ya gama taɓa su ya tabbatar da tabbas suna da rai, sannan ne ya koma cikin ɗan ƙaramin ƙauyen nasu, ya kira wasu samari suka zo suka taimaka masa ya kai su gidan shi, aka zube su cikin ɗaya daga cikin bukkan gidan
Duk mutanen ƙauyen sun fito sun nufi gidan Tsohon nan me Suna Baba Jaure suna ganin ikon Allah wajen su Usman, sun zame musu kamar t.v, duk da ba wai bambanci ne dasu ba, sai dai su sun kasance ƙauyawa ne futuk makiyaya, kuma garin ɗan ƙarami ne a tsakiyar ruwa take, sannan kuma da jeji a kewaye dasu, Baba Jaure shi ne babba a cikin ƙauyen, kuma shi ne me faɗa aji, tsoho ne sosai kuma be da iyali.
Sai da Baba Jaure ya kore su saboda sun cika mishi gida sun hana shi ya duba su, sannan ne suka fita suka bar shi, shi kuma nan ya soma bincika su dayake shi masanin magunguna ne, duk sai da ya gama duba su ya gano raunukan da suka ji, kuma da alamu sun sha ruwa sosai domin daƙyar ma ake iya gane suna numfashi
Ita Ɗahira ta sami karaya a duka ƙafafuwan ta, tare da rauni a ƙafan ta na dama
Shi kuma Usman ciwuka kawai yaji, da alama shi be sha wahala kamar ta ba, sai dai tafin hannun sa na dama ta kwaye kamar dai cizon wani dabba haka, tunda har rami tayi, sai kuma a goshin sa nan ma yaji rauni.
Sai da ya gama duba su kafin ya shiga rumbin ajiye magungunan sa, ya haɗo wanda zai yi musu amfani da shi, nan ya jiƙa na jiƙa wa wasu kuma ya niƙa su da turmi, sannan ya saka musu a ciwon, yayi wa Ɗahira ɗaurin karayan ta, shi kansa sai da ya tausaya mata, domin ba ƙaramin karaya bane taji, da ace idanun ta biyu azaban da zata sha Allah kaɗai zai sani, sai dai har ya gama ko alamun motsi bata yi ba, hakan ya ƙara tabbatar mishi tana cikin wani yanayi wanda farfaɗoWar ta sai Allah ya yi, domin ita ko numfashin ma ba ta yi sai da ya taɓa hannun ta yake ganin jijiya na harba wa.