BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

      Baffa ya je can Turkay ya dawo musu da labari mara daɗi a kan basu je can ba, wannan labarin ya sake ɗaga musu hankali matuƙa, bare da suka ga kwanaki nata tafiya babu labarin su, yau ga shi kusan kwana shida babu su babu wani bayani daga bakin ƴan sanda

Tuni Aunty Amarya da Kaka sun kasa jure wa sun zube an kai su asibiti, yanzu haka an kasa samun kansu, domin tunda suka sume basu farfaɗo ba, duk wani taimako an basu amma an kasa shawo kansu

Ita kuma Hajiya na gida sai faman kuka take yi, ko abinci ta dena ci saboda halin da take ciki

Bazan iya misalta muku halin da waɗannan bayin Allan suke ciki ba, haƙiƙa sun ga iftila’i a cikin ƙanƙanin lokaci, ɓacewar mutane biyu, ga kuma halin da su Kaka suke ciki, domin shi Kaka ma numfashi ba ya yi a halin yanzu sai da oxygen

Tuni ƴan uwa dangi na nesa dana kusa labari ya kai musu duk sun zo, har Fadila da take cikin halin lalura sai da aka zo da ita, duk da cikin ta yanzu har ya soma girma amma kullum ciwo kamar yanzu ta samu cikin, duk ta rame abun tausayi, yanzu tana lafiya, anjima sai aga jikin nata ya rikiɗe an tafi da ita asibiti, an rasa dai me ke damun ta, likitoci sun ce ita nata cikin haka yake, zuwan nasu ma sai da aka yi mata ƙarin ruwa saboda rigigim ta kwanta ciwo, duk da rashin ganin su Ɗahira ne ya yi matuƙar ɗaga mata hankali, sai kuka take yi, daga nan kuma sai jikin ya rikice.

      Halin da ahalin nan suka shiga sai innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, abin tausayi idan ka gansu.

       Ƴan sanda sun je har asibiti sun yi bincike, dayake akwai ccTV Camera a asibitin, sun duba kuma sun ga tabbas a ranan Ɗahira ta bar asibitin a cikin motan ta, Dr. Said ne mutum na ƙarshe da ta zanta dashi a haraban Hospital ɗin, daga nan ta hau motan ta ta fice

A lokacin shi kuma murmushi yayi yana bin motan nata da kallo har ta fice, kana ya zaro waya yayi waya, duk da ba sa jin abinda yake cewa amma duk rashin gaskiya ya nuna a tare da shi, sai kuma suka ga ya shiga tashi motan ya fice.

     Wannan dalilin ne yasa aka je neman Dr. Said amma ba’a ganshi ba, domin tun ranan da abin ya faru be sake zuwa asibitin ba, hakan ya ƙara ɗarsa zargi daga zukatan ƴan sandan. Sai suka je har Zaria suka cafke shege, da yasha matsa sai ga shi ya faɗi gaskiya

An sha wahala kafin aka kamo sauran mutanen da suka yi aikin tare da taimakon Dr. Sabo tunda shi ne ya sanar musu inda suke, sun yi bayanin komi da ya faru a ranan da suka ɗauki Ɗahira, har wanda ya zo ya taimake ta da kuma faɗa wa ruwa da suka yi

A nan ne aka gane Usman ne tunda sun yi bayanin motan nashi, kuma zahiri shi ne.

        Koda aka je wajen an yi duk wani bincike tsawon kwana da kwanaki, amma motan su kawai aka gani a cikin ruwan, inda suka tabbatar dole su Usman sun rigada sun mutu a ruwan, tunda babban makwararan ruwa ne dake tafiya wani ƙaton tafkin kogi, daga can ma akwai yanki-yankin ruwa dake da alaƙa da wajen, takamaime dai baza a gane inda suke ba a cikin ruwan nan, duk wanda ya faɗa kuwa sai dai mutuwa ne bazai iya fitowa ba

    Wannan bayanin da ƴan sanda suka yiwa su Big Dady sun sake ɗaga musu hankali, domin har kuka sai da suka yi sosai a wannan gaɓar, shikenan an rasa su sun mutu. Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! Mutuwar da ya girgiza ahalin gaba ɗaya, wanda sanadin haka ne Fadila tayi ɓarin cikin ta lokaci ɗaya, shi kuwa Baffa ranga-ranga aka wuce dashi asibiti yana aman jini, ga su Kaka su ma dake asibitin har yanzu ba’a sallame su ba, ita dai Aunty Amarya ta farka, amma da jin wannan bayanin sai ta sake zube wa a sume, dole aka koma basu taimakon gaggawa, su kansu su Abba sun kasa taɓuka musu komi, su ma suna ji da kansu.

         Su Dr. Said kuwa suna hannu za su girbi abinda suka aikata, domin har an miƙa su kotu babu ɓata lokaci.
????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

        EPISODE Fifty Four

         A Waɗannan kwanakin da su Usman suka yi a wannan ƙauyen, har yanzu suna a yanda suke basu farfaɗo ba, Baba Jaure na ci gaba da kula dasu sosai yana musu magani, inda tuni ya gano suna tare da sihiri gaba ɗayan su biyun, tunda shi mutum ne me saurin gane sihiri, kasancewar sa wanda yayi gwagwarmaya da aljanu, tun farko su suka buɗe mishi idanu har yake bayar da magunguna, sai ya tafi jeji yayi kwana da kwanaki yana haɗo magunguna, shiyasa duk ƙauyen nasu shi ke basu magani, tamkar shi ne likitan su, kuma shi ne kariyan su har suka kasance a cikin ta har yanzu

Wannan dalilin ne yasa yake haɗa musu wasu maganin na karya sihiri yana shafa musu a jiki, dayake akwai nasha sai ya riƙa zuba musu a baki, duk da yana zube wa amma ya san wasu suna shiga cikin nasu.

     Ana haka Usman ya farfaɗo ya tsinci kansa a wannan yanayin da ya kasa banbance a cikin duniya yake ko a maƙabarta? Wurwurga ido kawai yake yi yana zare su a cikin ɗan ƙaramin bukkan da suke kwance, nan idanun sa suka faɗa kan Ɗahira dake kwance tamkar matacciya, da kallo ya bi ta da shi ko ƙyafta wa ba ya yi, yana son tuna me ya faru har yake kwance a nan kusa da ita, be gama dawowa tunanin shi ba yaji motsi a waje, ƙofan yabi da kallo

A lokacin ne Baba Jaure ya shigo da wani kwanon sha a hannun shi, shima ganin Usman zaune sai hakan ya saka shi farin ciki, nan da nan ya yalwata fuskar shi da murmushi yana me ƙarisowa kusa dashi tare da mishi sannu

Amma yanda ka san gunki haka Usman yake bin shi da ido, ko motsi ya gaza yi illa idanun sa da suke juya wa

“Yaro ka kwantar da hankalin ka kaji? Ba cutar da kai zan yi ba, alhmadulillah tunda ka tashi. amshi wannan ka sha”. Ya miƙo masa kwanon shan hannun sa

Usman be motsa ba bare ya amsa, a lokacin tunanin sa ya dawo duk ya tuna abinda ya faru, sai kawai yayi saurin saka hannun sa a kanshi yana shafa wa, sai da ya taɓa ɗin yaji zafi ya ratsa shi, yayi saurin janye wa yana bin hannun shi da kallo, lokaci ɗaya ya ruɗe cikin tashin hankali ya kalli Baba Jaure yace, “ina ne nan don Allah? Me ya faru damu ne?”

Baba Jaure be ce komi ba sai da ya zauna yace, “kayi haƙuri ka kwantar da hankalin ka sai in Yi maka bayani”.

Shiru Usman yayi yana bin hannun sa da kallo, yanda duk aka barbaɗa mishi wani baƙin abu da babu kyan gani, dashi aka cike ramin da hannun sa yayi, sosai yake jin azaba na ratsa shi har ruwan hawaye ne ke cika mishi idanu, sai dai kuma dauriya irin nashi bazai iya kuka ba, amma sosai yake jin azaba. Da kallo kawai yabi Ɗahira dashi yana kallon ƙafafuwan ta da suke a ɗaure alamun sun karye, shiru kawai yayi ya gaza ɗauke idanunsa a kanta, lokaci ɗaya yaji hawayen dake idanun sa sun zubo, sai yayi saurin kawar da kansa yana saka ɗaya hannun sa ya share

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button