BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Baba Jaure da kallo ya bi shi dashi har ya shige bukkar, sai ya saki murmushi kawai yaci gaba da rubutun shi cikin allo, sosai ya gama kula da halin Usman, shiyasa be damu da wannan ɗaurewar fuskar nashi ba, domin tunda ya tashi be taɓa ganin haƙoran shi a waje ba, ko da kuwa magana zai yi ba ya buɗe baki sosai a ciki-ciki yake yi.

        Usman kuwa yana shiga mayar da kayan sa yayi zuciyar sa duk babu daɗi, sai yayi kwanciyan sa a gefen Ɗahira, yayi rigingine yana bin ta da kallo, yanda yake jin zuciyar sa da ya kalle ta sai ya ɗan samu sauƙi, sai kuma tunanin ta suka fara mishi yawo a zuciya, babu abinda yake tuna wa sai rayuwan da suka yi a can Turkay, da kuma abubuwan da yayi mata, sai kawai ya tsinci kansa da tambayar kansa “shin meyasa yayi mata wannan muguwar tsanar da har ya saka shi ya ƙuntata mata da yawa har haka? Anya shi ne kuwa?” Sai kuma wata zuciyar nasa tace, “to wa kake tunanin zai yi mata bayan kai? Ko ka manta tun sanda aka haife ta ka ɗaura mata karan tsana har zuwa kuwa wannan lokacin?” Sai ya lumshe idanun sa yana sake buɗe wa a kanta, a ransa ya furta “amma meyasa yanzu ba na jin tsanar nata sosai kamar yanda nake ji a zaman da muka yi a turkey?” Hasali ma yana jin wani irin tausayin ta ne a ƙasan ransa tare da nadamar abinda yayi mata

Saurin tashi yayi yana tankwashe ƙafafuwan sa, sai ya buga tagumi idanun sa a kanta, the more Yana tuna abubuwan da yayi mata the more Yana jin zuciyar sa na zafi, meyasa ya zama mugu mara tunani a wajen ta? Shi ya ma kasa tuna wani abu ne mummuna da tayi masa da har yayi mata mugun tsanar nan? Ya san dai tun sanda aka haife ta ya kalli cikin idanun ta, faɗuwar gaban da ya same shi tare da wani irin tsoro duk shi ne ya haddasa mishi tsanar ta, ko kaɗan ba ya ƙaunar ya ganta kusa dashi wannan dalilin ne yasa yake muzguna mata ko don ya rage haushin ta a zuciya, sosai ta hana ma rayuwar sa sukuni tun soma girman ta, shiyasa a lokacin da ya gama karatun shi na secondary School shi ya matsa wa Kaka dole ya tura su Turkay karatu shi da Baffa, ba don komi ba sai don nesanta kanshi da ita, sabida har a mafarkin sa zuwan mishi take yi, ba ta da aiki sai tsorata shi da waɗannan idanuwan nata, wanda yake ganin kamar da gayya take yi tunda ta san be son Kallon ta, shi har ya fara mata kallon aljana, sai dai kasancewar shi shima mugu ne shiyasa duk sanda ya same ta yake kiman ta, a cewar sa “ai ko ita aljana ce wlh sai ya rama abun da take mishi a mafarki,” duk inda ya same ta duka ke haɗa su, har ya zamo idan ta ganshi ba ta iya zuwa wajen sai idan babu shi, idan kuma suka haɗu a hanya gudu take yi, sabida muddin ya kama ta dukan mutuwa yake mata. Iyayen su tun ba sa damuwa har dai kowa ya gane tsana ce kawai Usman yake mata, sun yi faɗan sun yi faɗan don ya dena dukan ta amma ya ƙi, shiyasa a lokacin da suka gama karatun su suka dawo, sai Usman ya nemi “a barshi ya koma can yayi aikin sa tunda an yi masa tayi”.

To shi kuma Kaka be ja da zancen ba ya bar shi, ba don komi ba sai don ba ya son ya takura wa Ɗahira, saboda a lokacin har ya soma kiman ta duk da da girman ta a time ɗin, su ma sun dawo hutu daga Zaria  lokacin suna karatu a ABU, daga sun haɗa ido da ita a ganin shi na farko da yayi mata, ita kuma tuni ta tsere sabida ganin sa don bata yi tunanin yana ɗakin Kaka ba, shi ne fa ya tashi a lokacin tsam yabi bayan ta, su Kaka duk basu san me ya tayar dashi ba, tunda a ganin su ta girma ta wuce duka a wurin sa

Ashe shi Usman har Part ɗin su ya bi ta ya zaƙulo ta a ɗakin su yayi mata shegen duka, ba komai ya saka shi haka ba sai yanda ta faɗar masa da gaba har yana datse haƙora, ga kuma mugun tsoron da ya riske shi a lokacin, don a time ɗin ta zama ƴan mata idanun nan sun ƙara girma da kyawu

Aunty Amarya ita tazo ta ce ce ta tana tambayar sa abinda tayi masa, kasancewar ta ba me son faɗa da hayaniya ba shiyasa bata nuna ɓacin ranta a kan abinda yayi wa Ɗahira ba

Shi kuwa be ce komi ba ya juya ya fice a zuciye

Fadil ya shafa da gudu ya sanar wa su Kaka. Mafarin kenan Kaka ya amince da komawar sa can Turkay yayi aikin sa, duk da suna da buƙatar sa a nan sabida suna da asibitin su, amma kuma hakan shi ne zai kawo sauƙi wajen Ɗahira, su baza su iya hana Usman ba tunda duk faɗan da zaka yi masa wlh bazai dena ba, abinda yayi ninya kawai shi yake aikata wa, da ace faɗa zai saka Usman ya dena dukan Ɗahira da tuni ya dena, amma ga shi ashe abun gaba yayi ba baya ba.

        Tunda ya tafi kuma sai Ɗahira bata sake saka shi a idon ta ba, a lokacin sosai ya koya mata tsanar shi, bata da maƙiyi a duniya sama dashi, ko da ya dawo hutu to zata bar gidan Idan har lokacin su ma suna gida, ko ta tafi gidan ƙanwar Kaka Hajiya Hannatu (Ihsan) ko kuma ta koma Zaria can Soba dangin Maman ta tayi zaman ta har sai sun koma school, ita da ta dawo gidan sai kuma wani hutun idan Usman ba ya gida, bata ƙara yarda sun sake haɗuwa ba sai dawowar sa gaba ɗaya da yayi wanda kuma sun gama school, lokacin tana ganin baza ta iya juran waɗannan abubuwan da yake mata ba…

           Numfashi Usman yaja sanda yaji muryan Baba Jaure Yana mishi Magana.
????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

.

        EPISODE Fifty Five

         Bayanin Farko da aka sanar musu a kan Baffa ya yi matuƙar ɗaga musu hankali, ya kamu da ciwon zuciya, ga kuma shaye-shayen da yake yi wanda yayi mishi illa sakamakon ya sha wanda ya fi ƙarfin shi

Ai hauka ne kawai Hajja Fatu bata yi ba jin wannan bayanin

Su kuwa su Abba basu yarda da result ɗin ba daga farko, domin a cewar su “ɗan su ba ya shan giya, sannan babu abinda ke damun sa da har ciwon zuciya zai kama shi,” duk da sun san cewa shi ciwon zuciyan Allah na saka maka haka kawai, jarirai ma da ake haifa suna iya kamuwa da ciwon zuciya, amma da suka yi gwajin da kansu sai suka fi yarda tunda ga result zahiri, ga shi kuma ciwon yayi masa mummunan kamun da ya shiga coma lokaci ɗaya, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, tashin hankali ba’a saka mishi rana, ban san ya zan kwatanta muku halin da suka shiga ciki ba, sai dai kamar yanda suka yarda da Allah sun kuma yarda da ƙaddara, shi ne yasa komi yazo musu da sauki. A yanzu dai Aunty Amarya ita jikin nata da sauki duk da ba dena kuka tayi ba, sai dai tana kukan zuci wanda ba ta jin nan kusa zata dena, ɗiyar ta ɗaya tilo Allah ya amshi abin sa

Kaka kuwa da Baffa ba’a magana a kan jikin su, gwara-gwara Kaka yana iya farka wa amma dai da oxygen yake numfashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button