FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Jikin Fadila da sauki shiyasa ana sallaman ta Big Dady yace “su koma da ita gida”.
K.B ya wuce da ita, duk da tana ta kuka a kan “baza ta je ba”.
An yi zaman makoki duk da babu gawan su, an yi musu zaman makoki har kwana bakwai aka yi addu’a, sannan kowa ya watse, su kuma su Kaka suna asibiti ana ci gaba da kula da su.
Alhmadulillah ana samun sauƙi daga Kaka, tunda yanzu har yana iya magana, jikin sa da sauki sosai, sai dai Baffa ne jiya iyau, har yanzu tunda aka kai shi be farfaɗo ba.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Da sannu da sannu Usman ya saba da rayuwar ƙauyen nan da ya tsinci kansa a ciki, tun ba ya sakin jiki da Baba Jaure har dai yanzu sun saba sosai, ya kan gaji da zama a cikin ɗaki har ya fita wajen gidan ya sha iska, ya riƙa kallon mutanen garin da zirga-zirgan su, duk da ya ƙi sakin jiki sosai da su illa Baba Jaure, don wani lokacin har jeji yana raka shi, amma be cika zuwa sosai ba, babu abinda ke faɗo masa a rai illa Ɗahira, ya kan ji hankalin sa be kwanta ba duk idan zai yi nesa da gidan, sai yaji kamar wani abun zai same ta, shiyasa sai idan ya gaji sosai ne yake iya bin Baba Jaure cikin jejin
Ya zama abun kallo ga mutanen ƙauyen, duk da ba wasu mutane ne da yawa ba, ba samarin ba ba ƴan matan ba kowa so yake yi ace ga shi yana mu’amala da Usman, sai dai ya ƙi sakin musu fuska, wasu samarin idan har suka ganshi a waje har zuwa suke yi su zauna wai “sun zo taya shi hira,” ga su da shegen surutu dole sai sun yi mu’amala dashi kamar wasu mayu, duk da wulaƙanta su da yake yi, don idan suka soma mishi zuba ko ci kansu ba ya ce musu, ko abin dariya suka yi sai dai ya kawar da kansa idan yana jin dariyan, daƙyar yake iya murmushi wanda basu san ma yana yi ba, iya kanshi dasu gaisuwa da amsa sallama, su da farko ma abin mamaki yake ba su, ayi mutum ba ya magana ba ya dariya, amma kuma dayake iyayen naci ne dasu sun ga ɗan birni zubin ƙetare, su hakan ma daɗi yake musu tunda sun zauna dashi
Su kuwa ƴan matan ma ko kallo basu ishe shi ba, idan za su wuce sau dubu su gaishe shi ba ya kallon inda suke, amma gobe idan sun ganshi a wurin baza su fasa gaishe shi ba, shiyasa yanzu ma ya rage fita, sai dai yayi zaman shi a cikin gidan wajen Baba Jaure yana kafa mishi idanu yana aiki.
Abin mamaki tunda Baba Jaure yace mishi ya riƙa shafa wa Ɗahira magani yana bata na shan, be yi masa musu ba, shi yake bata kullum yana kula da ita, wani lokacin ma har yana ɗan wanke mata jiki da tsumma, shi kansa abinda yake yi wlh mamaki yake ba shi tsantsa, be san meyasa ba yanzu kwata-kwata ba ya jin tsanar ta kamar da, hasali ma zallan tausayin ta yake ji
Be san cewa tuni asirin dake tasiri a jikin su an karya musu ba, tsanar da aka saka mishi na Ɗahira tuni Baba Jaure ya karya sihirin, kuma har yanzu be fasa basu na tsari ba, sai dai shi Usman ɗin duk a tunanin shi magungunan raunukan da suka ji ne.
* *
Yau ma kamar kullum shi da kanshi yaje ya ɗauko maganin ya soma shafa mata, dayake Baba Jaure ya fice zuwa jeji tun ɗazu, yana yi yana kallon fuskar ta da be gajiya da kallo, har ya rame fuskar nata sosai ko da gani ka san tayi jinya
Motsi yaga kamar tana yi sai ya tsaya yana bin ta da kallo, sai kuma cikin sauri ya soma kiran sunan ta a hankali yana faɗin, “Nafeesa.. Nafeesa”.
Kamar daga sama take jin muryan, wanda daƙyar ta iya motsa hannayen ta jin ƙafafuwan ta sun riƙe sosai ta gaza motsa su, sai kuma ta soma juya kanta a hankali
Ganin haka yayi saurin saka hannun sa yana riƙe nata, ya ci gaba da kiran sunan ta a zaƙe da son ganin ta buɗe idanu, sosai yaji wani irin farin ciki ya tabaibaye shi dashi kanshi be san na mene ne ba, yau har so yake yi yaga waɗannan idanuwan nata masu ba shi tsoro da fargaba, sunan ta ya sake kira yana matsa mata hannun ta da ya riƙe gam a cikin nasa
Idanun ta ta soma buɗe wa a hankali tana sake rufe su, a haka har ta ɗan buɗe su kaɗan tana ganin dishi-dishi, tayi kamar mintuna biyu ba ta iya ganin komi, kafin kuma ganin nata ya soma dawowa, ta soma gane abinda ke cikin ɗakin, kana kuma ta sauke idanun ta a kansa, wanda sai da ta sake rufe idanun ko gizau yake mata, kafin kuma ta sake wartsake su a kanshi, kallon kallo kawai suke ma juna yayinda ta tsayar da idanun ta a kanshi ƙyam
Shi kuwa fuskar shi yalwace da murmushin da ya daɗe be yi ba yake kallon ta, don ya ma kasa yin magana
Wani irin zabura tayi lokaci ɗaya tamkar mahaukaciya tana yanka ihu, ihu sosai take yi tuni ta ɗage ƙafafuwan ta tana son tashi da gudu
Hakan da ya gani ne tuni hankalin sa ya tashi, nan ya saka hannu yana riƙe ta yana faɗa mata “ta tsaya”.
Amma ina ihu kawai take yi sosai hawaye tuni sun yi mata caɓe-caɓe saboda azaban da ya ziyarce ta, sai a lokacin ma tabi ƙafafun nata da kallo, ai nan ta sake haukace wa a kuka, ga shi jikin ta babu ƙarfi amma yanda ka san mahaukaciya haka take son fizge jikin ta a jikin sa
Shi duk a tunanin sa haukan ne ya same ta, shiyasa lokaci ɗaya ya ruɗe ya riƙe ta gam yana faman kiran sunan ta da faɗin “ta natsu don Allah”. Shi ba komi yake jin mata ba illa ɗaurin dake ƙafafun ta kar ta goce.
A lokacin ne Baba Jaure ya shigo da saurin sa, domin ihun nata ne ya jiyo tun daga wajen ya taho da saurin, shima ya ruɗe sosai ganin yanda take yi, saurin saka hannu yayi ya riƙe ta yana faɗin, “dakata mana ƴar nan, me kike yi haka? Ki zauna don Allah kin ga akwai karaya a ƙafafuwan ki”.
Amma ina azaba ya hana ta jin kalaman Baba Jaure, duk da ta dena motsi da ƙafafun, amma kukan ta sai ƙaruwa yake yi har da su majinu
Baba Jaure duba ƙafan yayi yaga dole sai an sake sabon ɗauri, cike da tausayin ta yace, “amma me ya faru ne da ta tashi a firgice haka? Ka ga dole sai an sake sabon ɗauri”.
Usman be iya cewa komi ba, shi dai yana riƙe da ita da tayi lagwab kanta a jikin sa sai kuka take yi sosai
“Yanzu je ɗauko min wani magani a ɗaki na yana nan a kwalba ka kawo min”. Baba Jauren yace dashi yana kallon sa
Tashi Usman yayi yana aza kanta a saman shimfiɗan da take kai, yayi saurin fice wa
Shi kuma Baba Jaure sai bata baki yake yi duk da ba ta fahimtar sa, azaba da zugin ciwo ya hana ta saƙat, riƙe mata ƙafafun yayi don kar ta motsa duk da tana son ƙwace wa
Bayan Usman ya dawo da maganin ya miƙa wa Baba Jaure
Shi kuma ya amsa yana taɓa ƙafan ɗaya wanda ya san shi ne ya goce
Sai ta yanka ihu tana janye ƙafan, tana faman girgiza kai da son magana amma ina ta kasa
“Kai Usman sai dai ka riƙe min ita a sake sabon ɗauri, idan ba haka ba ƙafan nata zai yi tsami da yawa”.
Gyaɗa kai Usman yayi kamar ƙadangare, ya duƙa ya riƙo mata hannaye gam ya ɗaura kan ta a jikin sa
Duk yanda taso ta ƙwace amma ina ta kasa, azaban da ya sake ziyartan ta tuni ta buɗe baki tana roƙon Baba Jaure yayi mata rai, kuka sosai take har da majinu yayinda ta koma kiran sunan Usman tana roƙon sa “ya taimake ta”.
Usman har sai da yayi mata ƙwalla tsaban tausayin ta, shi kansa be san ma yayi ba
Shi kuwa Baba Jaure ya ƙufe sai da ya gama gyaran tas kafin ya ƙyale ta, sannan ya kalle ta yace, “sannu baiwar Allah, kiyi haƙuri kinji? Kuma kar ki sake motsa ƙafafuwan nan tunda kin ga wahalan da kika sha, muddin kika sake gotar wa dole a sake sabon ɗauri idan ba so kike yi ki dauwama a karye ba. Allah ya ƙara lafiya kiyi haƙuri”.