FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2
Ɗahira wanda tasha azaba tayi sharkaf da zufa, inda majinu da hawaye suka yi mata caɓe-caɓe a fuska, fuskar nan tayi jazur kamar tattasai tsaban wahala, yanzun ma gunjin kuka take yi sosai ta lafe kanta a jikin Usman sai faman sakin numfashi take yi
Shi kuwa Usman ƙam ya riƙe ta yana shafa mata kan alamun rarrashi, ya kasa cewa komi illa tsaban tausayin ta dake cin sa a rai, ji yake yi kamar ya mayar da ciwon jikin sa, sosai yake jin tausayin ta na tsarga masa ta ko ina a jikin sa, yana bin jiki da ɓargon sa, wanda har ji yake yi tsigan jikin sa na tashi.
Baba Jaure tashi yayi ya fita, sai ga shi ya dawo da fura cikin kwanon sha, ya miƙa wa Usman yace, “ga shi ka bata Idan zata iya sha, ki daure kinji ki sha”.
Amsar kwanon Usman yayi
Baba Jaure ya fice a ɗakin
Shiru yayi yana tunanin yanda zai iya lallaɓa ta tasha maganin, kamar mintuna biyar da fitan Baba Jaure sai ya saka hannu ya mirgino kanta yana kiran sunan ta a hankali kamar wanda ke raɗa
Bata amsa mishi ba domin idanun ta ma a rufe suke ruf, hawaye sai sake tsiyaya suke yi, sai ta mayar da kanta ƙasa ta kwantar tana ci gaba da shashsheƙan kuka
Sake kiran sunan ta yayi yana cewa “ta tashi tasha furan”.
Duk yanda yaso tayi magana ko ta buɗe idanun ta amma ta ƙi
Ko kaɗan ba ta ƙaunar ta sake tozali da fuskar sa, Da ya san abinda take ji a game dashi da be kusanto inda take ba, da ya san yanda muryan sa ke sauka cikin kunnen ta yana sake ƙara mata wutar tsanar sa da haushin sa da be ci gaba da mata magana ba, da ace zata iya yin magana a yanzu ɗin da ta faɗa masa “ta tsane sa fiye da kowa a duniyar nan! ba ta son ganin sa ba ta son taimakon sa, shi be da wani amfani a duniyar ta,” zata faɗa mishi “dashi da dabba a wajen ta ɗaya suke”. Sai dai kuma ina baza ta iya ba, baza ta iya buɗe ido ta kalle sa, duk azaban da take ji kaɗan ne da yanda take ji a zuciyar ta, sosai zuciyar ta take tafarfasa tsaban tsanar da take mishi.
Usman tashi yayi ganin taƙi kula shi, sai ya kai ma Baba Jaure yace mishi “taƙi sha”.
Baba Jaure ya dawo ɗakin da furan, sai ya bar Usman a can waje. Zama yayi yana cewa, “ɗiya ta”.
Sai a lokacin Ɗahira ta buɗe idanuwan ta da suka kaɗa suka yi jawur
“Kar ki sake gardama idan na baki abu kinji? Lafiyar ki ake nema miki, idan babu abinci baza ki samu sauƙi ba, yau kimanin wata ɗaya kenan kina a wani hali baki farfaɗo ba sai yanzu, mijin ki ya damu ƙwarai, ki daure ki samu lafiya ko shima hankalin sa zai kwanta, bari in Kira shi ya baki”.
Cikin muryan kuka tace, “a’a don Allah Baba Kar ka kira shi, wlh mutuwa zan yi, ba na ƙaunar taimakon shi idan har shi zai taimake Ni, shi ba miji na bane”. Sai ta fashe da kuka me tsuma rai, da ya san yanda kalman mijin ta ya bugi zuciyar ta; da ko da wasa bazai sake ambata mata ba
Baba Jaure cike da mamaki yace, “ba mijin ki bane? Amma ya ce min shi mijin ki ne?”
????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
بسم الله الرحمن الرحيم
⚖
FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
JIKAR LAWALI CE✍️
Wattapad: UmmuDahirah????
\F.W.A????/
SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY
EPISODE Fifty Six
“Shi ba miji na bane, bani da alaƙa dashi”. Tayi maganar cikin kuka
“To ya isa haka, bar kukan kinji kar ki saka wa kanki wani ciwon, bari in taimaka miki ki sha furan”.
Gyaɗa masa kai kawai tayi tana faman sauke ajiyan zuciya akai-akai
Kallon ta kawai yake yi cike da tausayin ta, sai ya gyara mata kanta ya ɗan ɗago ya saka mata matashi, sai da ya bata ruwa ta kuskure bakin ta kafin ya hau kafa mata furan tana sha
Duk azaban ciwo ya ishe ta shiyasa kaɗan tasha tace masa, “ya ishe ta”.
Dole ya ƙyale ta be matsa mata ba, sannan ya bata wani magani tasha ya mayar da ita ta kwanta sosai, yace mata, “ta kwanta tayi barci ko zata samu hutu”.
Bata ce mishi komi ba har ya fita, sai ta mayar da idanun ta ta rufe har yanzu sai faman ajiyan zuciya take saki, fuskar ta tayi jazur da ita sai hawaye dake kwance sun bushe mata.
**
Baba Jaure kuma da ya fita a can gefe ya ga Usman ya zauna ya haɗa kai da gwiwa, kallon sa kawai yayi sai ya kawar da kansa, be ce mishi komi ba duk da yana son mishi tambayoyi, amma ya bari zuwa lokacin da Ɗahira zata samu nutsuwa hakan zai fi mishi. Ɗaki ya shige abin shi
Shi kuwa Usman be ma san da fitowar sa ba, illa tunani da ya faɗa hankalin sa na ga Ɗahira, zuciyar shi na matsa mishi da tunanin ta amma shi yana son kauce wa, sosai yake ƙaunar taimaka mata saboda tausayin ta da yake yi, ya san ba don ciwon dake jikin ta ba ba ya jin zai ji abinda yake ji a kanta, shiyasa duk wani tunanin da yake nata ya barshi ne a kan TAUSAYI kawai, kuma da zaran komi ya wuce zai dena matsa wa kansa
Sai a lokacin ya ɗago kai yana kallon Baba Jaure da ya fito daga ɗakin sa, sai yayi saurin tashi idanun sa a kansa yace, “ta sha furan Baba?”
Murmushi yayi masa yace, “eh na bata ta sha, amma yanzu na san ƙila tayi barci”.
Yana ganin yanda Usman ɗin ya saki ajiyan zuciya har da lumshe idanu, sai yace mishi, “zai fita yaje ya dawo”.
Har Baba Jaure ya fice be ce mishi komi ba, koma wa yayi ya zauna yana ci gaba da tunanin sa, gaba ɗaya zuciyar sa ta matsa mishi yaje ya duba ta, ko da fuskar ta ne ya kalla but ya daure ya ƙi zuwa. A nan ya zauna har sanda Baba Jaure ya dawo
Sai yace mishi, “daga yau zaka fara kwana a wancan bukkan kaji?”
Da kallo ya bi shi be iya ce mishi komi ba, sai dai mamaki da ya cika sa
Shi kuma Baba Jaure ya gane sarai yana son ƙarin bayani, amma ya ƙi sake ce mishi wani abun, idan ba tambayar sa yayi da bakin sa ba shi kuma bazai tanka sa ba, sai ya wuce abin sa ya bar shi.
Har aka kira sallan magriba Usman na zaune a wurin be jirga ba, sai daga baya ya tashi ya ɗauki mazubin ruwa yayi alwala ya fita zuwa Masallaci
Baba Jaure tuni shi ya fice ma, tunda dama shi ne liman.
Bayan an idar da sallah ya koma gida, kai tsaye ɗakin da Ɗahira take ya wuce, da sallama a bakin sa wanda shi kaɗai yaji kayan sa ya shiga ciki
Idanun ta biyu amma suna lumshe, motsin da taji yasa ta buɗe su a kanshi, sai suka shige cikin nasa
Da sauri ya janye nashi idanun saboda yanda yaji gaban sa yayi muguwar faɗi tamkar zai fito waje, har yana runtse idanu
Sai da ta sakar mishi wani banzan kallo da be san ma tana yi ba kafin ta ɗauke nata idanun, ta mayar dasu ta rufe ruf
Dauriya ya aza wa kansa ya sake kallon ta, ganin idanun ta a rufe sai ya taka a hankali ya shiga ciki ya zauna a gefen ta, shiru ne ya biyo bayan zaman nashi be ce uffan ba illa kallon ta da yake faman yi
Har a cikin jikin ta tana jin irin kallon da yake mata, wanda har ta kasa jure wa ta buɗe idanuwan ta a kansa tana mishi wani kallon da ya kasa fassara wa