FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Sai dai ba kaɗan ba kallon ya shige sa ainun, sai ya janye nashi idanun ba tare da ya ɗauke su a kan fuskar ta ba, cikin cool voice da be taɓa sanin yana dashi ba yace, “zaki yi sallah ne sai in taimaka miki”.
Shiru babu amsa
Sai ya kalle ta yaga har yanzu idanun ta na kanshi tana mishi wannan banzan kallon da ya kasa gane kallon mene ne, sai dai kuma yanda ya daure ya kasa cire nashi idanun a kanta, tuni ya gane kallon tsantsan tsana ne, sake maimaita abinda ya faɗa mata yayi ba tare da ya ɗauke idon sa a kanta ba
Rufe idanun ta kawai tayi kafin tace, “ba na buƙatar taimakon ka har abada, Please ka taimaka ka tashi min a nan wurin saboda kana cutar dani da yawa”.
Yanda ka san gunki haka Usman ya koma a wurin, ya gaza ina zai saka kalaman ta bare yayi musu filla-filla ya gane me take nufi, sai dai juya su da yake yi amma kuma ya gaza tunani ƙwaƙƙwara, sai dai zuciyar sa na cike da mamaki tsantsa
Tsawon lokaci yana wurin be iya jirga wa ba, kuma be tashi ya fita ba, amma idanun sa har yanzu suna kafe a kan fuskar ta
Sai ta ware nata idanun a kanshi cike da baƙin cikin kallon da yake mata tace, “dalla ka tashi ka bani wuri a nan, na ce maka ba na buƙatar taimakon ka, wlh gwara na ruɓe a nan da ka taimaka min”.
Da yatsa ya nuna kanshi yace, “Ni kike faɗa wa haka Nafeesa?”
Wani irin juya idanu tayi cike da harzuƙa kuka na son kufce mata tace, “who you are?” Na faɗa idan ka so kar ka bar Ni da rai kaji ko?”.
Shi sosai kalaman ta suka bashi mamaki shiyasa yaji sa wani iri wanda ya kasa taɓuka komi, jin sa yake yi komi nasa yayi sanyi, memakon kalaman ta su sanya shi baƙin ciki sosai kamar yanda a baya suke saka shi, sai dai kuma wannan karon ko kaɗan ba haka ba, duk da yaji zafin kalaman ta, amma yana ganin ya ƙi mata wani abun ne domin ganin ta cikin lalura, amma da ba don haka ba…
Muryan Baba Jaure ne ya dawo dashi tunanin sa, “Fito mana Usman mu je Masallaci”.
Be ce komi ba ya tashi ya fice, har yayi Sallah be da wani kuzari
Ko da ya dawo zama yayi a waje ya haɗe kai da gwiwa
Baba Jaure da ya shigo ya soma tambayar sa “me ke damun sa?”
Amma sai yace mishi “babu komi”.
Yace, “ka wuce wancan bukkan ka kwanta kaji? Ka tashi a waje ka ga garin yana kaɗa wa”.
Be yi musu ba ya miƙe ya nufi ɗakin da ya nuna masa, ya shige yayi kwanciyar sa, sai dai ya gaza hana kansa tunani, be san meyasa ba kalaman ta kawai suke dawo masa, duk inda ya juya muryan ta yake ji ya rasa ya zai yi, duk da ya san cewa komi zata iya masa sakamakon abubuwan da yayi mata a baya
Ƙarshe tashi zaune yayi ya sake haɗa kansa da ƙafafu yaci gaba da tunanin sa, yana jin sanda ruwa ya ɓarke kamar da bakin ƙwarya amma be motsa ba, ga sanyi dake shigan sa saboda rashin rufa da be yi ba.
A haka har garin Allah ya waye Usman yana zaune digirgir, wanda shi kansa ya sha mamakin wannan al’amarin, domin duk yanda ya so ya hana kansa tunani ya samu barci ya gaza, haka ya tashi jiki babu ƙwari ya fita yayi alwala suka wuce masallaci shi da Baba Jaure, sai da ya dawo ne ma ya samu barcin ya ɗan sure shi cike da mafarkai kala-kala.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Sanda labarin mutuwar Usman ya riski Ayush hauka ne kawai bata yi ba, tayi kuka sosai kamar baza ta dena ba, wanda har sai da ta kwanta ciwo ranga-ranga domin ba ƙaramin shigan ta mutuwar yayi ba, dole iyayen ta suka ɗauke ta suka wuce da ita asibiti, kwanan ta biyar sannan ta soma samun sauƙi, sai dai sauƙin a jikin ta ne amma ba a zuciya ba, zuciyar ta ta rigada tayi tabon da baza ta taɓa warke wa ba, bata shirya rasa Usman a rayuwar ta ba, ko kaɗan bata taɓa kawo wa kanta zai mutu ba tare da ta cika burin ta a kanshi ba, ita kanta bata san soyayyar da take mishi ya kai haka ba sai da ya mutu, ƙarshe dai ko da aka sallame ta suka koma gida ta dena walwala gaba ɗaya ta rame, mahaifyar ta tayi-tayi ta faɗa mata abinda ke damun ta amma ina taƙi, sai dai kullum tana cikin tunani da kuka, ko abinci ta dena ci, kuma ta dena zuwa aikin ta.
Safra har gida tazo ta duba ta, itama ta bata baki sosai amma Ayush taƙi jin ta, har tace mata, “idan har wani saurayin ne wanda ya fi Usman zata samo mata, amma yanzu ta cire damuwa a ranta tana cutar da kanta”.
Ayush kallon ta tayi tana zubar da hawaye tace, “baza ki gane bane Safra, na rigada na saka shi can cikin zuciya ta da fitar shi zai yi wuya a gare ni, har yanzu ji nake yi a jiki na be mutu ba, na kasa yarda wlh, taya Usman ɗina zai mutu ba tare da na aure sa ba? Taya? Gaba ɗaya rayuwa ta na tsara ta ne dashi, abubuwan da nake gani a mafarki na yanzu duk sun rushe baza su gasgata ba”.
“Hmm Ayush dole ki yarda ya mutu tunda iyayen sa ma sun yarda, batun kuma ki cire sa a ranki wannan kuma me sauƙi ne, sai dai idan ke ce kika ƙi hakan, duk da na san na ɗan lokaci ne dole ki manta shi, akwai waɗanda suka fi Usman komi a duniya zaki same su, kar ki hana wa kanki jin daɗin rayuwa a kan ɗan ƙanƙanin abu Ayush, ki manta shi please, ke Kinga yanda kika koma ne?” Ta ƙare maganar tana sake bin Ayush ɗin da kallo
Numfashi kawai Ayush taja ba tare da ta sake cewa uffan ba, domin ta san duk abinda zata faɗa Safra baza ta taɓa gane wa ba, gwara tayi shiru ta ƙyale ta zai fi
“Zan tafi muje ki raka Ni, amma wlh ki sauya tunani tun kafin ki naƙasa kanki, aikin da kike matuƙar so ga shi har kin dena zuwa saboda wannan damuwar taki, idan baki yi wasa ba zaki rasa komi naki wlh”. Cewar Safran tana tashi tsaye
Itama Ayush tashi tayi ta bi ta suka fita
Mahaifiyar Ayush dake zaune tana tankaɗe Safra tayi mata sallama sannan suka fice
Har ƙofar gida ta raka ta sannan suka rabu, Ayush ta dawo ciki, ita kuma Safra ta shiga motan ta taja ta tafi.
⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫
Kaka ya samu sauƙi har an sallame sa, sai dai abinda ba a rasa ba, inda za’a ci gaba da kula dashi a gida ana ba shi magunguna, duk ya koma wani iri kullum maganar sa ɗaya Ɗahira, mutuwar ta ta shige sa ba kaɗan ba, duk da ba ita kaɗai ba har Usman ɗin, amma ya fi jin mutuwar Ɗahiran.
Shi kuma Baffa har yanzu ba ya sanin su waye a kanshi, jiya iyau ake har yanzu
Babu wanda ya kai Hajja Fatu shiga damuwa, ta koka ta koka har ta gaji, duk da ta san mutuwar Ɗahiran ne ya saka ɗanta shiga wannan matsanancin halin, amma bata yi nadama Ba, ji take yi da Ɗahira zata dawo duniya a yanzu haka; wlh da babu me ƙwatan ta a wurin ta, domin tasha alwashin sai ta salwantar da rayuwar ta me munin gaske, har yanzu kuma bata fasa tsine mata a zuciya ba, kullum da ita take kwana take tashi, gaba ɗaya ta sauya wa Aunty Amarya fuska, ko gaisuwar ta ba ta amsa wa, har habaici take mata, ta kasa ɓoye ƙiyayyar ta yanzu a fili, ƙiri-ƙiri take faɗa mata “ɗiyar ta ne tayi silan shigan Baffa a wannan halin, kuma wlh idan be tashi ba ta rasa shi sai taga abinda zata yi mata, daga yanzu babu mutunci a tsakanin su”.
Aunty Amarya takan bi ta da kallo ne kawai, tun abun yana bata mamaki tana ganin kamar wasa ne, sai kuma taga eh lallai Hajja Fatu da gaske take yi, sai kuma abun ya soma damun ta, “meye haɗin Ɗahira da Baffa da zata yi silan shigan sa cikin wannan halin har ya sha giya? Ta san dai babu soyayya a tsakanin su, shaƙuwa ce kawai wanda kuma Allah ne ya haɗa jinin su, tunda tana ganin ga shi jinin su ya haɗu, amma kuma Allah da ikon sa ba sa shiri da Usman, to taya ya zata ɗaura wa ɗiyar ta wannan zargin?” Ta kasa jure wa sai da ta sanar wa Abbu