BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Shi kuma Abbu sai yace mata, ” ta ƙyale ta tayi ta kanta, kuma duk abinda zata ce kar ta soma ta kula ta”.

Da wannan maganar na Abbu Aunty Amarya tayi amfani, duk wani haushin karen da Hajja Fatu take yi ba ta kula ta, iya kan nata ido ne.

ku yi haƙuri babu yawa, so kuyi manage.
????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

        EPISODE Fifty Seven

       AFTER THREE WEEKS

        A wannan kwanakin da suka shuɗe Ɗahira ta sha wahala sosai, bazan iya misalta muku azaban da ta fuskanta ba, tabbas karaya babu daɗi, barin ma ita da take mace me rauni, kuma har ƙafafu biyu, duk juriyan ta ta kasa jure wa, sai da ta sake goce ƙafa ɗaya Baba Jaure ya sake gyara mata, azaban duniya ta sha shi har suma tayi, tasha kuka kamar zata tsiyayar da hawayen ta, domin a ranan ma kwana tayi tana kuka taƙi cin komi

Daga Baba Jaure har Usman sun kasa rarrashin ta, shi Usman ma har sai da yayi mata hawaye, sosai yake jin tausayin ta na tsarga mishi ta ko ina a jikin sa, yana jin dama zai iya da ya dawo da ciwon jikin sa.

     A haka Baba Jaure yake ta rarrashin ta yana bata bakin “ta jure idan ba haka nan ba sai dai a yanke mata ƙafafun muddin basu warke ba”.

A haka kwanaki suke ta shuɗe wa Ɗahira na a wannan halin, amma duk da zafin ciwon nan ba ta bari Usman ya taimake ta, idan har ba Baba Jaure ne zai taimaka mata da wani abun ba, to, ta gwammace kar tayi, gaba ɗaya ta tsani ma ganin sa kusa da ita, baza ta taɓa manta abinda yayi mata ba, shiyasa duk idan ta ganshi sake jin tsanar sa take yi a zuciya, ya riga ya dasa mata tsanar shi me girma a rai, wanda duk duniya ba ta jin akwai mahalukin da tafi tsana idan ba shi ba, da ace za’a bata bindiga da tuni ta harbe shi

Shi kansa Usman yana mamakin wannan halin da take nuna mishi, duk da azaban da take ciki amma haka take iya nuna masa tsana tsantsa, ya kula ko kaɗan ba ta son ta buɗe ido ta ganshi, duk maganar dake bakin ta haka take yaɓa mishi ba tare da taji shakkun shi ba.

          Baba Jaure dai da yaga abun yayi yawa sai ya kira Usman zuwa ɗakin da Ɗahira take kwance, yace mishi “ya zauna”.

Bayan ya zauna ya dube sa yace, “wai ya alaƙar ku da Nafeesatu ne? Ina son in San tsakanin ku?”

Shiru Usman ɗin yayi, sai ya kalli Ɗahira wacce ta rufe idanun ta tayi kamar bata san dasu ba a ɗakin

“Faɗa min mana ina magana? Ko ba kai kace min matar ka bace?”

“Eh Mata ta ce”. Yayi maganar bayan ya mayar da idanun sa kan Baba

“Amma ya aka yi ke Nafeesatu kika ce min ba mijin ki bane? Kuma na kula kwata-kwata ba kya son ya taimaka miki, idan be taimaka miki ba a wannan halin da kike ciki wane ne zai taimaka miki? Kina buƙatar taimako sosai domin ke abar tausayi ce, Shin ko wani abun yayi miki?”

Buɗe idanun ta tayi da suka soma tara ruwan hawaye, ga zuciyar ta dake mata ƙunci da jin kalmar da Usman ya faɗa, shiyasa sai da ta kalli Usman ɗin ido cikin ido kafin tace, “Baba shi ba miji na bane, ban san shi ba, bani da wani alaƙa da shi a rayuwa ta”.

Usman tsimi yayi ya kasa ɗauke idanu a kanta, ko kaɗan be ji daɗin abinda ta faɗa ba, sai ya lumshe idanun sa kawai yana haɗiyar yawu

Shi kuwa Baba Jaure jinjina kansa yayi yana sake kallon ta da kyau, sai kuma ya kalli Usman ɗin yace, “yanzu maganar wa zan yarda? Kai kace min Mijin ta ne, ita kuma tace min bata sanka ba. Amma ya aka yi kuke kama da juna, daga ganin ku kuna da alaƙa da juna?”.

Usman da ya buɗe ido yace, “Baba wlh ita Mata ta ce kuma ƙanwata, jini na ce ita..”

Cikin kuka Ɗahira ta katse shi da faɗin, “wlh Ni ba miji na bane shi, sam Ni ba na ƙaunar sa ko kaɗan, na tsane sa fiye da komi a duniyar nan! kuma takardar saki na zai bani”.

Kamar zuciyar sa zata ƙone a wannan karon sabida jin kalmar tsana a bakin ta, sosai yaji ciwon kalmar, shiyasa a harzuƙe yace, “to Ni nace miki ina ƙaunar ki ne? Ko cewa nayi bazan sake ki ba? Idan ba don laluran ki ba baki isa ki zauna kina gaya min wannan maganar ba ban yi ƙasa-ƙasa dake ba”.

“An faɗa maka kai waye? Ka sake Ni yanzu ba sai anjima ba, banza kawai..”

Hannu ya kawo zai wanka mata mari jin zagin da tayi masa, saura ƙiris hannun sa ya kai fuskar ta sai ya dunƙule, cike da wani irin fushi yake kallon ta yace, “Ni kike zagi.. Ni?” Ya nuna kansa da hannu idanun sa jawur har jijiyoyin kansa suna tashi

Sosai Ɗahira ta tsorata har tana janye jikin ta, domin ta manta ma da wani karaya a ƙafan ta, lokaci ɗaya ta saki azababben ihu

Salati kawai Baba Jaure yake yi domin ya kasa komi illa kallon su da yake faman yi, sai da yaga Ɗahira ta saki kukan ne nan ya matso yana cewa, “subhanallah mene ne me ya same ki? Kin taɓa ƙafan ko?”

Yanda take kuka kamar ana yanka naman jikin ta sai duk jikin Usman ya soma rawa, shima ya matso kusa da ita sosai amma ya kasa cewa komi illa kallon ta da yake yi

“Kun gani ko ba kya jin magana, ban ga ranan da zaki bar ƙafan nan su warke ba sai kin ja ma kanki, kai kuma Usman da girman ka kake biye mata?” Sosai Baba Jaure yake bala’i kamar zai ari baki, sai da ya haɗa su tass yayi musu masifan kafin ya kalle ta yace, “ba na son shashanci daga yau kar in sake ganin kin goce ƙafafun nan, kuma duk wani taimako da ya kamata zai riƙa taimaka miki tunda Ni ba zama nake yi ba, kinji ko kar in sake ganin kinyi wani abun da kanki?”

Gyaɗa kanta tayi tana shashsheƙan kuka

“Mu je waje Usman”. Yace dashi yana fice wa

Shima bayan sa yabi ya fita

Ita kuma Ɗahira kamar an kunna ta sai ta ɓare baki taci gaba da kuka sosai

Daga waje suna jin ta amma babu wanda ya tanka, sai dai sosai kukan ta ke shigan Usman, ji yake yi kamar ya shiga ya rarrashe ta amma ya san hakan bazai taɓa yiwuwa ba, baza ta taɓa mishi kallon arziƙi ba, shi kansa har tsoro take ba shi saboda bala’in ta, “ko dama haka take?” Yake tambayar zuciyar sa. “ko kuma zafin ciwo ne ya mayar da ita hakan ba”. Wata zuciyar tace mishi haka.

     Daga ranan dole Ɗahira take bari Usman yana taimaka mata da wani abun idan babu Baba Jaure, sai dai ko magana ba ta mishi, shima haka, sun zama tamkar kurame, ko shekara za su yi a wuri ɗaya baza ta tanka shi ba, ko ya tambaye ta tana buƙatar wani abun ba ta kula sa, ta gummaci ta zauna har Baba Jaure ya dawo

Abun da ke ba wa Usman haushi tun sanda ta soma ba-haya (kashi) dayake ba’a bata komi sai Nono gudun kar ta riƙa ba-haya, sai ta bari Baba Jaure na nan sannan zata nuna tana buƙatar yi, shi ke taimaka mata, ta gummaci shi ya taimaka mata da Usman ya taimake ta, shiyasa abun ya soma ba wa Usman haushi, yana a matsayin mijin ta ai shi ne ya kamata yaga jikin ta ba wani ba, shiyasa da abun ya dame sa wajen kwana huɗu da bata yi ba, sai kawai ranan na biyar ɗin dai ya cire baki ya tambaye ta “ko tana jin Kashi ko fitsari ne ya taimaka mata?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button