BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Sosai ranta ya ɓaci da zagin uban ta da yayi, sau biyu kenan hakan ke faruwa. Shiyasa cikin ɓacin rai da baƙin cikin sa tace, “ba dai uba na ba wlh, domin ya fi ƙarfin ka har da zaka zauna kana zagin sa..”

Bata ajiye numfashi ba ya ɗaga hannu ya falla mata marin da sai da taga taurari suna shawagi a idanun ta, ɗif tayi kawai ta dena gane abinda ke duniyar.
????????????????????????????????????????
              FAMILY DOCTOR’S
                         ????
????????????????????????????????????????

????????????????????????????
   NAFEESAT RETURN
????????????????????????????

MALLAKAR:
                 NAFISAT ISMA’IL LAWAL

بسم الله الرحمن الرحيم


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

         \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

SAƘON GAISUWA GARE KU MASOYA NA Usman Aliyu Ahmad, Adama Aliyu, Nana Aliyu, Prencess Teema, Maryam Muh’d, Hafsah, Amina Umar Abdullahi, Zainab Muh’d Hussain, Fatima Bintu Muh’d, Sadiya, Asma’u, Lawisa, Rahma, da ma waɗanda ban lissafo su ba, duk ina gaishe ku, kuma ina godiya da soyayyar ku gare Ni.

.

        EPISODE Forty Three

     
        Bata gama dawowa duniyar gigitan da ta shiga ba. ya duƙa a gaban ta ya shaƙo mata wuya, cikin ɓacin rai yace, “idan har na sake magana kika mayar min da martani makamancin haka, Wlh sai na binne ki da ranki a gidan nan, idan kin isa ke tatacciyar mara kunya fitsararriya ce ke, ki sallake umarni na, zaki ga yanda zan yi biji-biji dake a gidan nan..” sai ya datse harshe ba tare da ya gama faɗin abinda yake son faɗa ɗin ba, miƙe wa kawai yayi bayan da ya dungurar mata da kai. Har ya taka zai fice, sai kuma ya dawo yana kallon ta da ɗaurarriyar fuskar sa da ba mutunci, cikin tsawa yace da ita, “biyo NI da kayan nan”. Ya nuna kayan ta dake zube a ƙasa

Ɗahira da gaba ɗaya duniyar ta juya mata sabida tsaban gigicewan da tayi da marin da yayi mata, tuni hawaye sun gama wanke mata fuska, tana me riƙe da kumatun ta da ta kasa saki. A tsorace ta tashi tabi umarnin sa kamar yanda yace mata ɗin, domin gani take yi kamar zai sake mata marin nan da yayi mata, ko kuma fiye ma da hakan, domin ko kaɗan bata ga alamun ɓurɓushin imani a tare da shi ba.

     Kai tsaye cikin ɗakin sa suka wuce, inda ya nuna mata cikin wardrobe ɗin sa ta zuba kayan, sannan ya rufe da keey ya ɓoye keey ɗin

Ita tuni ta fice da gudu ta isa inda ya nuna mata makwancin ta, wani irin rushewa da kuka tayi tana me haɗa kai da gwiwa ta soma rera wa, zuciyar ta na wani irin tafarfasa da ƙara jin tsanar Usman a ranta.

     Shi kuwa tuni ya nufi ƙofa ya ficewar sa, ya kulle ta ta waje, domin ya san cewa zata iya guduwa, tunda ita ba yarinya bace, kuma ita ba jahila bace.

      Kuka sosai Ɗahira take yi kamar ranta zai fita, gaba ɗaya idanun ta sun juye sun yi jazur sun kumbura, haka ma fuskar ta da inda ya mare ta ya kumbura suntum, sai shatin yatsun sa da suka fito raɗo-raɗo, haka fuskar ya sauya kamanni, abun ku da farar mace ya sake yin ja

A zuciyar ta babu abinda take yi sai Allah wadai da shi, tare da ƙara rura wutar tsanar sa.

      Har dare Ɗahira na zaune a wurin tana ta kuka, babu abinda ke tashin ta sai Sallah, kuma duk idan tayi sallan sai ta roƙi Allah ya saka mata, ya kuma fitar da ita cikin hannun sa, sosai zazzaɓi ya rufe ta saboda kukan da ta sha, nan ta nannaɗe da zani tana ta rawan ɗari.

     Usman kuwa be dawo ba sai wajen sha biyu, kuma ko kallon inda take be yi ba ya wuce ɗakin sa.

    A haka Ɗahira ta kwana a mawuyacin hali.

         Washe gari haka Usman ya tsallake ya bar gidan ba tare da ya damu da ya bi ta kanta ba

Wannan abun ya tabbatar mata da cewa, tabbas Usman ba shi da ɓurɓushin imani, be da ɗigon imani ko kaɗan, kuma ba zai taɓa tausaya mata ba, duk da tana jin jiki, amma hakan be sa ta ƙi bin umarnin zuciyar ta na guduwa ba. Sai dai kash bata san cewa ya rufe ƙofan ba, tunda ta jijjiga yaƙi buɗuwa ta hau rusa kuka kamar ranta zai fita, nan wani sabon ciwon ya sake kama ta, da ƙyar ta isa ɗakin sa ta hau dube-duben inda zata samu keey, amma duk ta duba babu, dole ta zo ta kwanta a makwancin ta, taci gaba da kukan ta.

     A ranan ma sai dare Usman ya dawo

Sanda ya shigo, daƙyar ta iya buɗe idanun ta da suka yi mata nauyi tsaban ciwo tana bin shi da kallo, dayake akwai hasken NEPA, ko motsin kirki a lokacin ba ta iya yi, hawaye kawai ke tsiyaya a face ɗin ta. Ganin zai wuce ɗaki be kalli inda take ba, sai ta buɗe baki murya na rawa tace dashi, “Please.. Please.. help.. me”.

Kallon inda take yayi, sai ya kawar da kai ya shigewar sa ɗaki, ko kaɗan be ji tausayin ta ba, illa ma manta shafin ta da yayi yaci gaba da harkokin sa.

      Ita kuwa tuni ta sake sakin wani sabon hawayen me tsananin raɗaɗi da baƙin ciki, “Allah gani gare ka! Allah kai ne gata na, Allah ka fitar dani hannun wannan azzalumin”. Kuka kawai taci gaba da yi a wannan halin da take zaton mutuwa zata yi, domin azaban da take ji baki ma bazai iya faɗa ba. Daga ƙarshe ma da jikin nata ya sake rikice wa, sai ta hau kwarara amai daga kwancen da take, amai kawai take kwarara wa kamar zata zubar da hanjin cikin ta, domin kuwa babu komi a cikin nata, babu abinda taci tun marin da yayi mata jiya

      Yanda take kwarara aman har ɗakin sa sai an ji, amma dayake tuni yayi barci be ma san tana yi ba

Tuɓus jikin ta yayi, wanda tuni ta fita a hayyacin ta, tamkar dai ba ta numfashi haka ta koma. A haka har washe garin Allah yayi.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

             NIGERIA

     Kamar yanda Hajja suka tsara za su koma wajen Malam, sun koma, inda ya sake musu sabon aiki bayan ya caska kuɗin sa wajen Hajja, “aikin dai a ƙara rura wutar tsanar da Usman yake yi wa Ɗahira ne, a haddasa musu rashin zaman lafiya, kullum ya riƙa ganin ta kamar baƙar kumurci, babu abinda zai riƙa shiga tsakanin su illa cin mutunci da zagi, daga ƙarshe ya koro ta da sakin wulaƙanci”, inda ta sake bayar wa aka yi mata aiki akan Aunty Amarya, sai dai suna baro wa wajen, Hajiya Sa’ima ta koma ta sauya sabon aiki, kuɗin da za’a yi wa Aunty Amarya aikin, ta saka aka yi wa ɗiyar ta, sannan ta ƙara masa kuɗi me yawa, a haka suka rabu akan zai yi mata aikin da Usman da kansa zai zo wajen ɗiyar ta neman auren ta, ba shi da wata mata a duniya illa Zeena

Hajiya Sa’ima ta tafi tana farin ciki, ta koma gida ta ba wa ɗiyar ta labari. Nan itama ta hau murna da farin ciki, tana ganin burin ta nan ba da jima wa ba zai cika.

            ***

     A fannin su Kaka kuwa, sun soma shiga damuwa da jin har yanzu Usman be kira ya sanar musu saukar su ba, haka ma Aunty Amarya da Abbu sun fi kowa damuwa, saboda jin shiru daga ɗiyar su, babu wani waya, ga shi duk an kira layin su be shiga, Numban da Usman ɗin ke amfani dashi idan ya je can an kira shima ba ya shiga

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button