BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2

Yanda suke wasan ne sai ya ɗauke mata hankali ta shagala tana kallon su

Suna ta wasan ƴar gala-gala ne maZan su da matan su, sai dai sun raba ne idan mata suka yi sai maza su yi, kowa yana son ace su ne gwani. Duk basu lura da ita ba duk tsayuwar ta

Har ta soma gajiya tana shirin juya wa sai sandan nata ya gurɗe zata faɗi, sai ji tayi an tare ta ta faɗa jikin mutum. Da sauri ta ɗago kai tana kallon sa zuciyar ta na wani irin bugawa a lokaci ɗaya da nashi, waro ido tayi kawai tana kallon shi tana ɗauke numfashi tsamm sabida yanda taji wani abu ya tsarga mata a cikin jikin ta wanda baza ta iya fasalta shi ba

Shima haka zalika abinda taji shi ya ziyarce shi, shi nashi ma har wani nauyi zuciyar tashi tayi mishi tare da tsantsan tsoron da ya saba ziyartan shi a duk sa’ilin da ya haɗa ido da ita, sai dai kuma yanda yake jin wani iri kamar an manne masa idon cikin nata ya kasa ɗauke su a kanta

Illa ita ce da tayi ƙoƙarin fizgar kanta sa’ilin da ta gama tantance a jikin wanda take, wani irin fisga tayi wa kanta saboda haushin ganin ta a jikin sa da saura ƙiris ta gurɗe ta zube ƙasa

Sai ya ƙara azamar riƙo ta da sauri yace, “ke kina da hankali kuwa?”

Wani kallo ta sakar masa cike da baƙin ciki ta kasa ce mishi uffan, ta sake yinƙurin janye jikin nata da ƙarfi duk dan ta raba kanta dashi

Yana shirin sakin ta ganin abinda take so kenan, sai sandan ta ɗaya ya faɗi, dole ta ɗage ƙafa ɗaya don baza ta iya ba da ƙarfin ta a ƙafafuwan gaba ɗaya ba, tuni hawaye sun cika mata ido saboda azaban da take ji tayi saurin ƙanƙame mishi hannu, shi kuma sai ya duƙa ya ɗauko mata sandan

Yaran wajen tuni hankalin su ya dawo gare su sun tsaya suna ta kallon su kamar wasu t.v

Su kuwa basu san ma suna yi ba, domin tuni Ɗahira ta bizge sandan nata ta daidaita su ta soma ɗingisa wa a hankali

Yanda take yi ne kamar zata sake faɗi sai yayi saurin kawo hannu zai sake tare ta yana cewa, “Please kiyi a hankali manaaaa”. Ya ƙare maganar cikin jan kalman ƙarshen in a cool voice

“Kar ka sake taɓa Ni?” Tayi maganar hawayen idanun ta na sauko mata a kunci. Sai ta sake janye jikin ta sosai kafin tace, “ko kaɗan ba na buƙatar taimakon ka. Ko ka manta a baya ma baka taimaka min ba sai yanzu? So please zan iya da kaina ba tare da taimakon ka ba, kar ka sake yinƙurin taimaka min na roƙe ka”.

Kalaman ta sun ba shi haushi sai yace, “kina tunanin zaki iya wani abun ne ba tare da taimako na ba? Idan da ban taimaka miki ba babu yanda za’a yi ki kawo yanzu a raye. Waɗannan mutanen da suka ɗauke ki da tuni yanzu sun aikata nufin su a kanki da ban amso ki a wajen su ba, so ki iya bakin ki Please ba na son cika baki, kar kuma ki ga ina kula ki ki ce komi ne zaki riƙa faɗa min”. Yaja dogon tsaki yayi gaba abin shi fuuuu kamar ana tunƙuɗa shi

Ita kuwa da kallon banza ta bi shi hawaye na sake kwaranya a fuskar ta kamar an kunna famfo, tana jin zuciyar ta na mata ƙuna da maganganun sa. Shiyasa ko jirgau ta kasa yi duk da kuwa yanda yaran nan suka mamaye ta suna bin ta da kallo sai surutu suke yi, amma ba ta jin su illa bin hanyar da yabi da kallo da take yi ta kasa ɗauke idanun ta..

“Nafeesatu lafiyan ki kuwa? Me ya fito dake waje?”

Maganar Baba Jaure da yayi ya dawo da ita tunanin ta. Saurin kallon sa tayi

Sai ya sake cewa. “Subhanallah.. kuka kike yi lafiyan ki me ya faru? Ina Usman ɗin?”

Duk bata iya amsa mishi tambayoyin ba illa hannu da ta sanya tana share hawayen ta

Yaran ya kalla yace, “kai ku tafi kuyi wasan ku kunji ko?”

Hakan yasa suka dare a wajen sai dai basu tafi ba sun tsaya suna kallon Ɗahira

Shi kuma hannu yasa ya gyara mata sandan da kyau yana cewa, “zaki iya tafiyan dai ko?”

Gyaɗa mishi kai tayi sannan ta soma tafiyan a hankali yana biye da ita a baya.

      Suna shiga gidan ya nufi ɗakin da Usman yake kwana ganin be ganshi a waje ba

Yana ciki kuwa ya kwanta idanun sa a rufe, sai dai tunani ne fal cikin ransa da kuma haushin Ɗahira da yake ji, sosai ransa yake a ɓace

Nan Baba Jaure ya ɗaura masa da faɗan “barin ta da yayi ta fita ita kaɗai”.

Kanzil be ce mishi ba har ya gama ɓaɓatun shi shi kaɗai yabar wurin.

     Itama Ɗahira tuni ta shige ɗaki ta zauna tana ci gaba da zubar da hawaye, baƙin ciki ne sosai ke nuƙurƙusan ta na rashin mayar mishi da martani har ya tafi, ga tsantsan tsanar shi dake ƙara rufe ta, ta tsani ta buɗe idanun ta ta ganshi kusa da ita, babu abinda ke tuna mata illa rayuwar ƙuncin da tayi sanadiyar shi, da kuma azabtarwan da yayi mata. Ita a yanzu burin ta su koma gida su Kaka su amsar mata takardan sakin ta. Nan kuwa kewan ƴan gidan su ya cika ta, ta kwanta nan tana ta murƙususu tana faman tunani.

      A kwana a tashi kamar yau ne suka zo cikin wannan ƙauyen, sai ga shi sun shafe kimanin watanni shida a karkaran, wanda ciwon Ɗahira ne ya tsayar da su har wannan lokacin domin tuni an samu hanya, shiyasa tana warke wa suka yi haraman tafiya

Inda sosai Baba Jaure ya nuna rashin jin daɗin sa, domin ba kaɗan ba ya shaƙu da su a wannan watannin da suka yi tare da shi, bare shi ba me kowa ba, shiyasa rabuwar nasu zai yi masa ciwo, sosai yayi musu nasiha a kan riƙe addu’a domin shi ne takobin mumuni, duk wani halin da suke ciki su dage su riƙa kare kan su da addu’a don suna da maƙiya masu bin su da sharri, sannan yayi musu nasiha kan zamantakewar aure da ya taɓa musu zuciya ainun, kuma yace “idan da hali su zauna su sasanta su riƙe auren su hannu bibbiyu, duk wani saɓani dake tsakanin su su yi ƙoƙarin ganin sun daidaita kan su, domin ba ƙaramin dace wa suka yi da juna ba”.

A sanda yake faɗan wannan kalaman nasa har ɗago kai Usman yayi yana kafe Ɗahira da ido, inda yake son ganin abinda yasa Baba Jaure ya faɗi hakan, a kuma ƙasan ranshi yana jin wani nishaɗi da be san na mene ne ba, ko kaɗan memakon maganar tashi ta ba shi haushi sai be ji hakan ba, har yana ji a ransa a yanzu zai iya yin ma iyayen sa biyayya ya riƙe ta a matsayin matar sa ba tare da ya sake ta ba, wanda kuma a ganin sa Nasihan Baba Jaure ne ta taɓa masa zuciya ainun har yayi wannan tunanin

While ita kuma Ɗahira ko kaɗan bata yi tunanin wai zata iya ci gaba da rayuwa da shi ba, ta rigada ta saka wa ranta zaman su ya ƙare har abada, shiyasa ko ɗar bata ji ba a zancen Baba Jaure, kamar yanda yake shiga ta wannan kunnen haka yake fita ta wancan kunnen, har ya kuma gama ɗin. Sai dai zuciyar ta fal da kewar sa da za su yi, har a ranta ta ƙudura wata rana zata kawo mishi ziyara ko da ita kaɗai ce.

     Sun fito inda Baba Jaure yayi musu jagora suka yi sallama da mutanen ƙauyen, daga nan aka ɗauke su a motan ɗiban kaya aka fita dasu har titin da zai kai su cikin gari, inda aka sauke su suka sami abin hawa suka miƙa gida, zuciyar ko wannen su cike da wani irin farin ciki da murna na ganin yau za su koma su haɗu da ahalin su. Ɗahira tsaban zumuɗi bakin ta ya ƙi rufuwa sai wani zillo take yi ta kasa zama waje ɗaya

Inda Usman kawai kallon ta yake yi yana sake jin wani irin nishaɗi a ranshi

Dayake waje ɗaya suke zaune kuma motan a cike take fal, ita tana ƙarshen baya; shi kuma yana kusa da ita, sosai suka matsu da juna

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button