FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2
*
Ciki kuwa Ɗahira sanda ta shiga ta sake tabbatar wa da tabbas zaman makokin Baffa ake yi, inda ta zo shiga Part ɗin su taji Aunty Zulaiha na kuka tana buga waya tana sanar wa wasu daga cikin dangin mijin ta, tana ce musu “har an yi jana’izar sa yanzu aka dawo ma”.
Cak ta tsaya a inda take tana jin wani abu ya tsarga mata, so take yi ta ƙarisa inda Aunty Zulaiha ke tsaye ta juya baya amma ina ƙafafuwan ta sun gaza ɗaukar ta, saboda ruɗu da tashin hankalin da ya riske ta, sai kawai ta zube a wajen ta faɗi a sume.
Wanda yayi dai-dai da juyowar Aunty Zulaiha tana shirin koma wa ciki, ganin mace zube bata tabbatar da ko waye ba sai ta nufe ta da sauri, ta mirgino da fuskar ta sai fuskar Ɗahira ya bayyana gare ta. Wani irin ja da baya tayi muryan ta tana rawa tace, “Ɗa..hiraa”. Sai kuma ta tashi da gudu ta shige part ɗin tana ihun kiran mutanen gidan da son sanar musu “Ɗahira ta gani”.
Gidan mutuwa fa ya rincaɓe da ganin dawowar su Ɗahira, don tuni su Abbu su ma sun shigo tare da Usman, lokacin an wuce da Ɗahira ɗakin Aunty Amarya, sai dai duk wani taimako da aka bata bata farfaɗo ba. Hankula sun ƙara tashi, dole aka bar zancen bin ba’asi zuwa dare lokacin an nitsa da shigowar jama’a.
Sanda Ɗahira ta farka kuka tay ta yi; domin ba kaɗan ba mutuwar Baffa yayi mugun taɓa ta, ko magana ta kasa ma kowa sai kuka, abinci ma taƙi ci duk ta fita hayyacin ta, sai dai rarrashin ta da ake ta faman yi.
Sai dare jama’ar gidan suka taru gaba ɗayan su har da su Hajiya Laila Hajiya Ikram da yaran su, da duk wani me ruwa da tsaki sai da suka cika General parlour fam, kowa so yake yi yaji labarin abinda ya faru dasu
Usman ne ya basu labarin komi, don ita Ɗahira har yanzu ba ta iya magana, tana jikin Aunty Zainab sai zubar da hawaye take yi wanda suka kasa tsaya mata tun farkawan ta, har yanzu gani take yi ƙarya ne Baffa be mutu ba, ji take yi kamar zata ganshi cikin jama’ar parlour’n, shiyasa sai ware ido take yi tana kallon mutanen ciki.
Sosai aka tausaya musu da wannan iftila’in da ya same su, barin ma Ɗahira ita da ta shiga mugun yanayi, karaya har biyu a ƙafafu wanda tasha jinya ba kaɗan ba, sai sannu suke mata suna “ta auna arziƙi Allah ya kyauta gaba”. Sai dai su Aunty Zulaiha su amsa amma ita ko uffan ta kasa cewa.
Da haka aka tashi a taron, duk yanda Kaka yaso ya gana da Ɗahira sai dai ya haƙura kasancewar ba ta cikin mood ɗin ta, ranan mutane da yawa basu runtsa ba a gidan nan, kar ma ace Hajja Fatu, domin mutuwar Baffa ya taɓa ta ainun, tasha kuka har ta gode wa Allah, duk tayi yaushi itama maganar ma ba ta iya yi
Yayinda Sa’adatu tana can asibiti ana jinyan ta, tunda tun sanda aka sanar musu rasuwar Baffa ta zube, ga tsohon cikin ta haihuwa ko yau ko gobe, duk da watan sa takwas ne amma yayi mugun girma, wasu ma cewa suke kamar ƴan biyu zata haifa saboda girman cikin, sai dai dayake likitoci ne gidan tuni an bincika an ga ɗa ɗaya ne a ganin su.
Washe gari kuma sai aka tashi Yusra babu lafiya, naƙuda gadan-gadan yazo mata, ba’a ma kai ga kaita asibiti ba ta silliɓo ɗan ta namiji. Kowa ya yi murna duk da ana cikin baƙin ciki.
Ranan bakwai ɗin Baffa da ya kasance kwana shida da haihuwar Yusra aka yi sunan ɗan nata, kasancewar duk wasu za su tafi a ranan ne, Sulaiman yayi musu kara inda ya saka wa yaron sunan Baffa. Al’ameen. Za su na kiran shi da Little Baffa.
Fannin Ɗahira kuwa gaba ɗaya ta sauya har ciwo sai da ta kwanta sabida damuwa, sai da Aunty Amarya tayi da gaske kafin ta soma shawo hankalin ta, sannan ta koma tana cin abinci har tana iya magana
Yau ma ce mata tayi “taje ta yiwa Hajja Fatu ta’aziyya tunda bata je ba,” ga shi dama Hajjan ba lafiya ne da ita ba
Shi ne ta tashi ta fita, sai da taje wajen Kaka kafin ta wuce Part ɗin Hajja, lokacin da ta shiga babu kowa kasancewar kowa ya watse, har Shakira ta koma gida, dayake yau kwana takwas kenan
Bayan tayi sallama taji babu kowa sai ta wuce ɗakin Hajja Fatu, sai da ta sake sallama kafin ta shiga ciki
Hajja dake kwance saman gadon ta duk ta wani rame sai kace ba ita ba, mutuwar babban ɗa kamar Baffa ba wasa ba. Tana ɗago kai taga Ɗahira ce sai tayi kicin-kicin da fuska zuciyar ta na ƙuna
Ita kuma sai ta taho ta zauna a kan drowan gadon tana gaishe ta tare da mata “ya jikin?”
Ai kuwa tuni Hajja ta yunƙura ta cafke wuyan Ɗahiran ta maƙure ta, cikin hayagaga take cewa, “kutumar uban ki dake da jikin matsiyaciya annamimiya, burin ki ya cika kin raba Ni da ɗana shi ne ke kika dawo ko? To wlh kamar yanda ya mutu kema wlh sai kin bi shi bazai taɓa yiwuwa ki kashe min ɗa ke kuma ki dawo ki ci gaba da rayuwa ba, wlh baki isa ba”.
Idanun Hajja fa sun rufe sai zagin Ɗahira take yi kamar zata kashe ta
Gaba ɗaya idanun ta sun fito waje taji shaƙa tana neman taimako
Amma Hajja taƙi sakin ta sai ƙunduma mata zagi take yi ta uwa ta uba tana faɗin “itama sai ta kashe ta”.
Hayaniyar su ne ya shigo da Abba ɗakin, domin shigowar sa kenan Part ɗin ya jiyo zagin da Hajja take ƙunduma wa, yana shigowa yaga abinda ke faruwa sai ya nufe su da mugun sauri ya ɓanɓare Hajja Fatu yana falla mata mari. “Baki da hankali ne Fatima kashe ta zaki yi? Me tayi miki?” Sai kuma ya koma kan Ɗahira da ta faɗi ƙasa tana ƙaƙarin amai kamar zata mutu, gaba ɗaya fuskar ta ya jiƙe sharkaf da hawaye domin ta ma kasa kukan. Ɗago ta yayi yana mata sannu
Amma Hajja ta soma faɗin, “wlh tallahi sai naga bayan ta babu wanda ya isa ya dakatar dani tunda tayi min sanadin mutuwar ɗana, sai na kashe ta nima”.
Tsiya fa sai ya kaure daga ita har Abba sabida jin kalaman ta da take faɗa wa Ɗahira
Lokacin ne Hajiya ta shigo taga me ke faruwa, domin hayaniyar har Part ɗin ta dayake sun fi kusa. sai taje ta sanar wa Big Dady, kankace me gida ya ɗauka da abinda ya faru, har an kai maganar wajen Kaka
Shi kuma Abba dole sai da ya matsa Hajja ta faɗi abinda yasa take son ganin bayan Ɗahira, tunda ya gane ta san komi, kuma dama ya ƙyale ta ne tun ba yau ba domin a fice taron jama’a, yana son tambayar ta ta sanar mishi alaƙar dake tsakanin Ɗahira da Baffa da har basu sani ba
Dole da ta ga bala’in sa ta faɗi gaskiya ita ta hana Baffa ya auri Ɗahira wanda sanadin haka ya faɗa shaye-shaye sannan ya kamu da ciwon zuciya
Da jin haka sai Abba ya miƙe ya kife ta da maruka har uku, duk yanda su Big Dady suka so su dakatar dashi amma ina ya gagara, be jira wata-wata ba yace, “ya sake ta”.
Tashin hankali kenan da ba’a saka mishi rana, yau ga Hajja Fatu a tsaka me wuya, domin lokaci ɗaya ta kurumce gidan da ihun ta saboda abinda bata taɓa zaton zai faru bane.
So ku yi manage please.
????????????????????????????????????????
FAMILY DOCTOR’S
????
????????????????????????????????????????
????????????????????????????
NAFEESAT RETURN
????????????????????????????
MALLAKAR:
NAFISAT ISMA’IL LAWAL
بسم الله الرحمن الرحيم