BABU SO HAUSA NOVEL

FAMILY DOCTORS HAUSA NOVEL PART 2


FEENAH WRITER’S ASSO????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

JIKAR LAWALI CE✍️

Wattapad: UmmuDahirah????

          \F.W.A????/

SADAUKARWA
Na sadaukar ga Family na gaba ɗaya. GOMA’S FAMILY

.

             EPISODE Sixty

            Take a nan Kaka ya saka shi ya mayar da ita ɗakin ta, kuma yayi mishi faɗan saurin ɗaukar fushi abin duk be kai haka ba duk da tana da laifi, amma Allah ne ya ƙaddara wannan hanyar ne silan mutuwar Baffa

Ba da son ran Abba ba ya mayar da Hajja Fatu, amma a ranshi ya ƙudura aniyar sai ya ƙaro aure, don bazai yiwu ya ci gaba da zama da ita a matsayin mata ba tana ƙunsa mishi baƙin cikin ta, ita kenan kullum haɗa mishi jaraba sai kace ita kaɗai ce matar aure a gidan, babu me nemo magana sai ita.

         Ataƙaice dai aka sasanta komi, inda Kaka yayi mata faɗa sosai ya kuma ce “kar ta sake zargin Ɗahira da ita ce silan kashe Baffa, idan kuma zata yi hakan sai dai ta zargi kanta tunda ita ce taja komi”.

           Bayan an ƙarƙare maganar sai Big Dady yace ma Usman “ya miƙo mishi takardan sakin Ɗahira”.

Duƙar da kanshi yayi yace, “Dady kuyi haƙuri a kan abinda nayi muku baya wlh nayi nadama, insha Allahu yanzu zan yi muku biyayya gwargwadon iyawa ta, na yarda zan zauna da ita kamar yanda kuka zaɓa min ita”.

Ɗahira da kanta ke cinyoyin ta tana ƙananun kukan ta saboda har yanzu raɗaɗin zafin shaƙan da Hajja Fatu tayi mata be barta ba, bata san sanda ta ɗago a firgice tana kallon Usman ɗin cike da haushin jin kalaman sa ba

Bata kai ga magana ba Big Dady ya riga ta da cewa, “wannan zancen banza zancen hofi kake mana a nan, tunda har ada ka nuna mana bamu isa da kai ba kaƙi zaɓin mu, to yanzu baka isa kace zaka wulaƙanta mu ba, saki ne babu fashi dole ne sai ka sake ta dan uban ka”. Ya ƙare maganar nasa a zafafe kamar zai kai mishi duka

Kaka da ya kafe Usman ɗin da ido sai yace, “abinda za’a yi yanzu a bar maganar nan ba yanzu ne ya kamata mu yi shi ba, muna ji da raɗaɗin mutuwa a yanzu mu bari zuwa nan gaba, yanzu kowa zai iya tafiya”.

Duk tashi suka yi suna fice wa, inda Ɗahira da duk ta cika tayi fam da jin rainin hankalin Usman, sai bin shi da kallo take yi tana son su haɗa ido, sai dai shi tuni ya yi ƙofa yayi ficewar sa. Da sauri tabi bayan sa tana zuwa ta bangaje shi ta wuce

Sai ya tsaya kawai yana kallon ta cike da mamakin abinda tayi masa

Ita kuma sai da tayi taku kamar uku kafin ta jiyo tana kallon sa ta balla mishi harara cike da haushin sa da tsanar sa tayi gaba abinta ba tare da ta tanka shi ba

Sai abin ma ya bashi dariya ya kasa tafiya har sai da ta ƙule, sannan ya taka ya wuce Part ɗin iyayen sa yana jin zuciyar sa na sake cika da nishaɗi, fuskar shi kuma yalwace da kyakykyawar murmushin da sai ya jima kafin yayi shi, be san meyasa ba duk wani yanayi da yake ji a kanta yanzu yake burin jin sa a ko yaushe, musamman bugun zuciyar sa da sauyin yanayin da yake ji a jikin sa, yana son ya kalli idanun ta yaji tsoron nan dake riskan shi wanda ada yaƙi jini, har dariya yake yanzu yana mamakin wai me ke kawo hakan. Shi fa be taɓa jin yanayin da yake ji a kan yarinyan nan wajen wani ba, shiyasa ada yayi wa abun mummunan fassara, wanda yana ganin idan ba ita mayya bace taya zata riƙa bashi tsoro da faɗar masa da gaba? Har kuma ya riƙa mafarkin ta haka kawai. sai duk ya tsangwami kansa a kan lallai-lallai sai ya raba kanshi da wannan yanayin, wanda kuma yanzu kusantan da suka yi da juna na ɗan zaman nan da suka yi a ƙauyen nan, yasa ya soma saba wa da yanayin har yana jin ya riƙa kansacewa a haka idan har zai ganta kusa dashi.

      Mu je zuwa. ????

             ⚫⚫⚫

      Ɗahira na zuwa Part ɗin su ɗakin ta ta shige ta zauna a kan gadon ta

Sai ga Aunty Amarya itama ta shigo da sallaman ta

Amsa mata tayi tana kallon ta kamar yanda itama take bin ta da kallon, kana kuma tazo ta zauna kusa da ita

Tace, “meyasa baki sanar min soyayyar dake tsakanin ki da Baffa ba?”

“Mama Ni kaina ban san shi ne wanda muke soyayya dashi ba, sai daga baya na san hakan bayan mun rabu. Kuma naga hakan be da amfani tunda Hajja ta rigada ta raba mu, idan kuka sani baza ku ji daɗi ba”.

Ajiyan zuciya Aunty Amarya ta saki kana tace, “haka ne. Amma ba na son ki saka damuwa a ranki ko kaɗan tunda kin san halin kanki, duk wani abu yanzu ki bar shi ya wuce, kuma ki mayar da hankalin ki wajen ibadan Allah kina neman kariya wajen sa, domin Ni yanzu abubuwan tsoro suke sake bani, baki tare wa kowa komi ba ke kuma ba fin su kika yi ba amma maƙiyan ki sun yi yawa Ɗahira”.

Murmushi Ɗahiran tayi tace, “insha Allahu Mama zan kasance me neman kariya wajen Allah na, na san shi zai kare Ni”.

“Batun kuma Usman kar shima ki saka shi a ranki, babu me miki tilas a wannan lokacin domin su kansu su Kakan ba mara su hankali bane da za su sake saka ki ki koma gidan sa, babu wanda zai tilasta ki sai da yardan ki kinji?”

“Mama idan har da yarda na ne kuwa bazan taɓa koma wa gidan shi ba, ki dena ma zancen nan domin Ni na cire sa a raina tuni wlh, dole ne sai ya sake Ni don bazan taɓa zama dashi ba”. Tayi maganar kamar zata yi kuka

Murmushi Aunty Amarya tayi tana shafa kanta, kana kuma ta tashi tsaye tana cewa, “ki tashi ki je ki sake cin abinci don ɗazu ina ganin ki baki ci da yawa ba”.

Itama Ɗahiran tashi tayi tana cewa, “to. zan yi wanka ne yanzu zan fito, don Allah Mama ki turo min Fadil yazo min da wayan shi”.

Amsa mata tayi Aunty Amaryan tana fice wa

Inda ita kuma Ɗahira ta ɗauko tawul ɗin wankan ta tana shige wa Toilet.

⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫⚫

         An sallami Sa’adatu daga asibiti, sai dai ko da iyayen ta suka so su tafi da ita Legos, Kaka yace, “A’a a nan zata zauna har sai ta haifu sannan zata koma”. Dole ba don sun so ba suka haƙura, inda ta dawo Part ɗin Hajja ana kula da ita

While Yusra itama tana gidan sai tayi arba’in zata koma, abun mamaki kuma tunda Ɗahira ta dawo sai kuma duk idan suka haɗu sai tayi mata magana

Da fari hakan ya saka Ɗahira tunani da tsantsan mamaki, amma kuma duk idan taje duba little Baffa sai tayi ta janta da hira, ba ita kaɗai ba har Hajiya, sai duk abin yayi mata banbaraƙwai wai na miji da suna Inna ta Hajara. Duk da a zuci hakan yayi mata daɗi amma kuma da ta tuna ko suna yi ne don ta koma gidan Usman sai ta soma jin haushin su, daga baya sai ta ɗauke ƙafa da zuwa, amma kuma haka Yusra take biyo ta har ɗakin ta wai “ta ji ta shiru bata zo taga Little ba”. Tun ba ta kula ta har dai ta saki jikin ta tunda a ganin ta hakan ma sauƙi ne ga rayuwar ta, ace yau maƙiyin ka ya koma masoyin ka

Fannin Usman kuma basu sake haɗuwa da shi ba, kuma ko kaɗan ba ta ƙaunar haɗuwar nasu ma.

             ***

            Rayuwa taci gaba da tafiya inda har an yi sadakan arba’in ɗin Baffa

Inda ita kuma Yusra ta gama jegon ta ta koma gida itama.

             Sai a lokacin ne Ɗahira ta samu damar koma wa bakin aikin ta, inda taci gaba da aikin ta cikin salama da kwanciyar hankali, sai dai har yanzu kewan Baffa na maƙale a ranta, ta kan tuna sa wani lokacin tayi ta zubar da hawaye tana mishi addu’a, kuma har lokacin bata sake jin ɗuriyan Usman ba, ga shi ba’a sake yin zancen sakin ta ba, itama shiyasa bata sake kula maganar ba, tunda dole ne dai sai ya sake ta, ko kotu ne sai an je babu wanda ya isa ya saka ta ta koma gidan Usman.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button